“Ɗauko hijabinki ki bar mani gida,” cike da taurin rai Asma’u ta miƙe tare da tambayar shi “Kamar ya in bar maka gida?”, hannu ya ɗaga da zimmar nuna mata ƙofa, aikuwa a tsorace ta yi baya har ta faɗa kan kujera, dan yadda yake ta huci ta yi tsammanin duka zai kawo mata.
Da a ce Nas ba cikin fushi yake ba, babu abin da zai hana shi yi mata dariya, musamman yadda ta yi wiƙi-wiƙi da idanu tana dubansa, cike da tsana ya riƙa dubanta har ta tashi tsaye, a ransa ya furta “Banza mai kyawun ɗan maciji”, a zahiri kuma amsa ya bata da “Eh ki tafi gidanku nake nufi, na gaji da iskancin banza iskancin wofi, idan kin koyo tarbiyya da yadda ake zaman aure kya dawo.”
Kamar yadda ya gaji da rashin tarbiyyarta, haka itama ta gaji da mugun halinsa, kuma bata jin zata iya dawowa idan har ta fice mashi a gida, tunda ta yanke tsammanin ba zata taɓa samun rayuwa mai cike da farinciki a tare da shi ba.
“Zan tafi gidanmu, amma ka sani ko na koyo tarbiyyar ba a gidanka zata yi amfani ba, dan na gama zama da kai nima muddin ba ka koyi yadda ake kulawa da mace cikin tausayi da tausayawa ba, dan haka ka ba ni shaidar da zan nuna a gida idan na je.”
Sosai Nas ya fahimci shaidar da take nufi, amma sai ya basar da maganar, saboda sakin Aisha ya koya mashi darasin rayuwa, dan haka ko da zai rabu da Asma’u ba yanzu ba. Tabarmar kunya ya shiga naɗewa da hauka, inda ya ce “Toh sai me idan baki dawo ba, kuma ki tafi, shaidar na nan zata biyo baya, dan ban ga amfanin zama da ke ba”, rufe bakinsa ke da wuya ya juya ya koma ɗakinsa.
Mutuwar tsaye Asma’u ta yi, dan ba ƙaramin abin kunya bane danginta da ƴan unguwa su ji Nas ya koro ta, musamman yadda ta riƙa yi masu ɗagawa lokacin da yake neman aurenta, tunani ta riƙa yi ko ta bashi haƙuri, wani sashe mai girman kan tsiya na zuciyarta ya ce “Shi ɗin banza”, dan haka bata yi wata-wata ba ta canzo kaya ta fito.
Nas na jin tafiyarta ya fito daga ɗaki tare da shiga kitchen zai ɗauki cup. Wani irin wari mai kama da na mushe ne ya daki hancinsa har ya fasa ɗaukar cup ɗin, hannunsa toshe da hanci ya shiga buɗe lakoki, a tunaninsa wani abu ne ya mutu a ciki, aikuwa tulin yana da kyankyasai gami da tsaka suka yi mashi maraba, dan kuwa alamu sun nuna tunda Asma’u ta zo gidan bata bata share cikinsu ba ko sau ɗaya.
Ƙuri ya yi ma cikin locker, wanda a zahiri zaka yi tsammanin kallon wasu kyankyasai da ke neman maɓuwa ya ke, sai dai inaa! Zuciyar ta lula tunanin yadda kullum Aisha ke kakkaɓewa tare da goge duk wani saƙo na kitchen ɗinta, ba ita ba ma, hatta yaranta basa iya ganin wani datti ba tare da sun kawar da shi ba a cikin gidansu.
Jikinsa a mace ya tashi ba tare da ya rufe lakokin ba. Kallon kitchen ɗin ya shiga yi, nan ya ƙara tabbatar da Kuɗɗar mace yake aure, dan babu abin da ke aje a mazauninsa.
Wata irin tsanar Asma’u ce ta tuƙaƙo mashi, saboda Allah kaɗai ne ya san irin ƙazantar da take girkawa a gidan suna ci, sauƙinshi ma ba kullum ya ke cin abincinta ba. Haƙiƙa Nas ya fara tabbatar da alkhakin Aisha ne ke bibiyar shi, dan bai taɓa gode mata a kan ƙoƙarin kular masa gida da take ba, sai ma son ganin laifin da zai kama ta da shi, toh ga irinta nan, dama duk wanda bai gode ma ni’imar Allah ba, toh zai gode ma azabar shi.
Yana cikin raba idanu a kitchen ɗin ne ya ga wasu ƙananun ƙwari na bin saman dustbin, ko da bai buɗe ba, ya tabbatar da nan ciki wannan azababben warin ke fitowa. Kamar zai yi kuka ya nufi dustbin ɗin, “Anya wannan yarinyar ta san ciwon kanta kuwa?”, abin da ya faɗa a ransa, lokaci ɗaya kuma ya saɓe shi, cike da ƙyama ya ja dogon tsaki, a dalilin ruwa da kuma baƙaƙen tsutsotsin da ke kwance a ƙasan dustbin ɗin, tunda Nas ya zo duniya bai taɓa ganin bala’i irin wannan ba. Fuskarsa a yamutsen gaske ya yi waje da shi, yana jin yadda ruwan ƙazanta ke ɗiga har a ƙafarsa, bai tsaya da shi ko ina ba sai wata bola da ke kusa da gidan, wurgi ya yi da shi ya juyo ba tare da ya tsaya duba abin da ke ciki ba, bare ya kakkaɓe shi ya ɗauko, saboda ya gama gane dattin cikin kifi ne ta loda a cikin sharar da zai iya rantsewa ta fi wata ba a zubar da ita ba.
Almajirai ya shiga nema waɗanda zai biya su gyara mashi kitchen ɗin, sai dai ya fi rabin awa bai ga ko ɗaya ba, dole ya koma ya yi aikin goge wannan ruwan tsutsa da kansa, aikuwa ya zubar da yawu ya fi a ƙirga, yana gamawa ya buɗe Fridge da nufin ɗaukar ruwa, turus ya yi saboda har wani gamsa kuka ke kwanciya a cikinsa. “Yanzu wannan masifar yarinyar nan ta ke bani ina sha?”, dan kuwa bai zaton Fridge ɗinnan ya taɓa ganin guga ko wankewa.
Sanin “Eh” ce amsar tambayar shi wani irin amai ya tuƙaƙo shi, a guje ya bi ƙofar sit out ya ta kwarara aman a can.
Ba dan taurin rai irin na maza ba, da ba abin da zai hana Nas kuka, domin fitinar dake cikin kitchen ɗin Asma’u kaɗai ta ishe shi bala’in duniya. Yana gama aman ya maka mashi ruwa ya bi ta wani ƙaramin maguji ya fita.
Ɗakinsa ya koma, tare da shiga banɗaki ya yi wanka, yana fitowa ya chanja kaya, sannan ya faɗa kan gado yana ta nishi, yanzu kuma ta lafiyarsa yake, ba ta hukuncin da zai yi ma Asma’u ba.
Idanunsa a lumshe ya tuno Aisha da irin tsantseninta, haƙiƙa ko a wurin kula da gida kaɗai Aisha ta ciri tuta, dan ko yawu bai taɓa zubarwa saboda ƙazanta ba, amma gashi har da amai a sanadin Asma’u. Shi yanzu ya rasa tsautayin da ya sa shi rabuwa da ita ma.
Asma’u kuwa tricycle ɗin ta aje ta na juyawa wata sabuwar 206 ash ta wuce ta gabanta. Wata irin faɗuwar gaba haɗe da karkarwa ce suke haɗe mata, da ta san su waye a ciki, da ta jinkirta zuwa unguwarsu na wani lokaci, domin kuwa Abbas ta gani a mazaunin driver, Khadija kuma na gefe sai dariya suke, ba ta ga alamun sun kalle ta ba, bare su san da tsayuwarta a wurin, domin yanayin farincikin dake ransu ya shagaltar da su, gabansu kawai suke kallo. Itama ɗin kallo ɗaya ta yi masu ta tabbatar da cikin kwanciyar hankali suke, baki sake ta bi bayan motar da idanu har suka shiga kwanar gidansu Khadija, a ranta ta tambayi kanta “Yaushe Abbas ya yi kuɗin siyen mota.?”
Wani azababben kishi da hassada ne suka taka muhimmiyar rawa wurin disashe mata baƙincikin da Nas ya ƙumsa mata.
Kamar wadda aka zare ma lakka ta shiga gidansu. Ba kowa a tsakar gidan, sai Aunty da take jiyo motsinta a banɗaki, kujera ta jawo ta zauna sai mazurai take, Aunty na fitowa ta ce “Toh ke ce Ashe?”, kai Asma’u ta ɗaga alamun “Eh”, Aunty ta lura da yanayinta, amma sai ta basar ta ce “Ya maigidan?”, leɓen Asma’u na kyarmar kuka ta ce “Yana can, cewa ya yi in dawo gida”, Gaban Aunty na faɗuwa ta ce “Kamar ya ki dawo gida?”, kasa cigaba da magana Asma’u ta yi, sai dai ta fashe da kukan da ya bayyana ma Aunty abin da ke faruwa.
“Toh Allah ya kyauta” kaɗai Aunty ta iya cewa itama, saboda tsoronta kada a ce Nas ya saki Asma’u. Ɗaki ta wuce, a can ta riƙa faɗa tana cewa “Ni dama jikina na bani ba za a zauna lafiya da mutumin nan ba, ko da yake ke ki ka ja ma kanki ai, kina zaune lafiya da mijinki kika kashe auren, yanzu ga sakamako nan tun ba a je ko ina ba, dan babu mai faɗin halin kirki ɗaya na Nas”, Asma’u kuwa tana jin haka kukan nadama ya ƙwace mata, dan kuwa a yanzu da Abbas ya yi ƙiba, asalin kyawunsa ya fito sosai babu macen da zata ce bata son shi.
Sannan yadda ta ga Khadija itama ta ƙara kyau ya tabbatar mata da ciki gare ta, haka kawai sai ta ji kishi ya ƙara mamaye ta, saboda ita tunda ta je gidan Nas ko ɓatan wata bata taɓa yi ba.
“Me ma zan yi da cikin wancan matsiyacin”, cikin kukan ta yi wannan maganar a ranta, dan yadda ta tsani Nas a yanzu ko Abbas bata tsana haka ba, illah ma da yanzu take jin son Abbas ɗin fiye da yadda take son komai a rayuwarta, wanda kuma za a iya cewa ta makaro.
Tana cikin kukan Aunty ta fito, cikin takaici ta tambaye ta “Toh wai meye silar cewa ki dawo gidan?”, dan ta san Asma’u ba ƙaramar marar kunya ce ba.
Kaf Asma’u ta kwashe duka yanayin zaman ƙuncita da Nas ta faɗa ma Aunty, duk da su Nafeesa suna ba ta labari, ran Aunty a ɓace ta ce “Ina amfanin zaman ƙunci, ko ni da nake da girma ba zan iya wannan mugun zaman da Nas ba”, Asma’u na jin haka ta ce “Na rantse ni ma na gama zama da shi Aunty”, mugun kallo Aunty ta jefe ta da shi “Baki isa ba wlh, ke kika ce kin ji kin gani, dan haka dole ki koma ki yi haƙuri, dan ba wanda za a yi ma lissafin aure a gidannan.”
Sabon Kuka Asma’u ta kama yi, dan ta lura ba alamun wasa a maganar Aunty, kamar Aunty bata san tana yi ba, sai ma faɗa ta cigaba da yi mata, inda ta nuna mata ta yi asarar miji, dan duk unguwa yanzu sai zancen Khadija da Abbas ake, kusan za a iya cewa a unguwarsu ma ba yarinyar da ke damawa a gidan miji kamar Khadija, domin rayuwarta take cikin jin daɗi, saboda babanta ya riƙe ma mijinta kan macijin, wasa kawai yake da wutsiyar. Duk wata kwangila da kamfanin su Abbas ke samu daga babansu take zo musu, har sun daina siyar da blocks ɗaiɗai, sai dai na kwangilar kawai, shi ya sa kuɗi ke shigo masu a koda wane lokaci.
Ba cizo ba, hatta cire yatsa Asma’u ta yi bisa ga azabtar da Abbas tare da tilasta mashi rabuwa da ita, sannan ta gane ashe ba ko wane gida ne ake samun kwanciyar hankali ba.
Ta ɓangaren Nas ma ƙunci kamar ya kashe shi. Tsawon kwana bakwai ko baccin kirki bai iya yi, abinci ma sam baya shiga cikinsa, sai dai Snacks da Yoghurt kaɗai, su ma gudun yunwa ta kashe shi ne, da ba zai neme su ba.
Ba kuma korar Asma’u ne sanadin shigarshi wannan hali ba, dan da ita da babu duk ɗaya, Aishar da yake ma kallon banza ce kewar ta ke azalzalar shi, kuma bai yi ma kansa musun son nata ba. Tabbas ya yi ganganci ba ƙarami ba na rabuwa da ita, amma ba komai, tunda akwai sauran igiya ɗaya a tsakaninsu zai dawo da ita.
“Ta wace fuska ma zan fuskanci Aisha?”, tambayar da ya yi ma kansa bayan ya gyara kwanciyarsa a kan kafaɗa, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da cije leɓe, duba da irin muguwar taren da ya nuna ma Aishar, gabansa ne ya faɗi, dan ya san da wahala ta iya sauraron sa.
Wata irin matsananciyar kewar ta da ta yaransa ce ta sake game mashi jiki, a hankali ya lumshe idanunsa da suka yi mashi nauyi, haƙiƙa da Aisha zata kula shi, toh da ya faranta mata ita da ƴaƴanta fiye da zato.
Yana cikin wannan yana yi ne wayarsa ta shiga ruri, yana dubawa ya ga Sani ne, sai da ya ja tsaki sannan ya ɗaga kiran, saboda a yanzu ya tsani Sani saboda shi ne silar haɗa shi da alaƙaƙai.
A taƙaice suka gaisa, daga can cikin wayar Sani ya ce “Ya Hajj kana ina?”, Nas ya ba shi amsa da ina gida”, Sani ya ce “Ok idan ka fito dan Allah mu haɗu”, Nas ya san maganar, amma sai ya ce “Wani abu?”, Sani ya ce “Eh”, Nas ya ce “Ok, ka saurare ni.”
“Toh” kawai Sani ya ce, ya katse kiran, tsaki Nas ya sake ja, sannan ya aje wayar, ya san batun duk na Asma’u ne, shi kuma ya yanke ma ransa sakin ta, dan ya gama karanta ma kansa wasiƙar jakin yadda zai tunkari Aisha, sanna yana jin a jikinsa zai same ta a ɓagas.
Da yamma liƙis ya biye ma zuciyarshi ya nufi unguwarsu Aisha, sai dai tun shigarshi layin tsoro ya kama shi sakamakon hango wata jibgegiyar mota da ya yi a ƙofar gidansu, “Kaddai motar can wurin Aisha ta zo”, da hanzari ya basar da wannan zancen na zuci tare da sa ma ransa ƙwarin guiwa, lakkarsa a sake ya ƙarasa ƙofar gidansu Aisha da motarsa.
Gefe ya raɓa ta shi ya fito, aikuwa suka yi ido huɗu da Aisha a gaban wannan mota tana dariya. Yadda Nas ya ɗimauce sakamakon bugawar da zuciyarshi ta yi, ya ɗauka girgizar ƙasa ce a ke.
Itama Aishar gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa har ta nemi duk wani farinciki dake ranta ta rasa, dan rabon ta da ta ga Nas tun ranar da ya sake ta, ko yaransa ma sai dai ya yi masu aike, ko kuma ya je can makarantarsu idan yana son ya gansu.
Shi kuwa Barrister Kabeer, wanda shi ne masoyin Aisha na haƙiƙa tambayar ta ya yi “Waye wannan ya shiga gidanku?”, bata ɓoye mashi komai ba ta ce “Tsohon maigidana ne?”, gabansa na faɗuwa ya ce “Me ya kawo shi gidan ku?”, amsa ta ba shi da “ina na sani”, cewa ya yi “Ko dai so yake ya maida ki ne?”, Aisha na lura da firgicinsa ta ce “Allah ya kyauta, idan na koma mashi kai kuma fa?”, jikinsa a mace ya ce “A’a uban yaranki ne fa”, shiru ta yi, saboda bata ma son maganar, dan a yadda son Barrister Kabeer ya shiga ranta bata ji zata iya son Nas, yara ne dama take mawa, kuma yanzu suna wurinta, kai ko da Nas zai karɓe yaran ma, toh ba damuwarta ba ne in dai zata haifi wasu a tare da Barrister.
Barrister kuwa suna hira amma idonsa na ƙofar gidansu Aisha, fitowar Nas kawai yake so, amma fin rabin awa bai fito ba, ko da ya ji shi shiru, sai suka yi bankwana ya tafi, saboda hirar da suke ta dena armashi, daga shi har Aishar ba cikin nutsuwa suke ba.
A soro Aisha ta yi kiciɓus da Nas zai fito, gabanta na wata irin faɗuwa ta raɓa ta gaishe shi, cikin raunin murya ya amsa, ta juya zata shige gida ya dakatar da ita da faɗin “Aisha na bar saƙo a faɗa maki, ina roƙon ki dan Allah ki yi nazari kafin ki yanke hukunci.”, hannayensa sama yana roƙonta ya ƙarashe maganar, kasa magana Aisha ta yi, sai dai “Uhm” kawai, saboda ta fahimci inda rauninsa ya dosa, cikin gidan ta shige ta bar shi nan tsaye a soro, shi kuwa mamakin kyawun da dirin da ta ƙara ne ya tsuma shi, bai san sadda ya ce “Allah ka san na tauye haƙƙoƙin wannan baiwa taka da yawa, ina roƙonka da ka sa ta yafe mani, kuma ta saurare ni”, motsin da ya ji kamar za a fito ne sai ya tafi.
Hajiyarsu kuwa kasa motsawa daga inda take ta yi, mamaki kawai take yadda Nas ya saduda tun ba a je ko ina ba, dan har ƙwalla ya yi mata wurin neman afuwar gallazawar da ya yi ma ƴarta, hannunta riƙe da haɓa ta ce “Allah mai iko”, domin alamu sun nuna ruwa ya daki babban zakara.
A cikin wannan yanayin ne Aisha ta tarar da ita a ɗaki, tambayar ta Aisha ta yi “Me ya kawo wancan mutumin?”, ajiyar zuciya Hajiyarsu ta sauke, kafin daga bisani ta bata amsa “Haƙuri ya zo bayarwa, tare da neman bikon ki koma ɗakinki”, Aisha ta san dama za a rina, tunda bata cuce shi ba, fuskarta ba annuri ko kaɗan ta ce “Aikuwa ya makaro, dan na rantse ko sama da ƙasa za su haɗu ba zan koma gidansa ya kashe ni ba.”
Hajiyarsu ta ce “Saman da ƙasan suna wurinsu ma ba zaki koma ba, dan idan maye ya manta, har a lahira uwar ɗa ba zata manta ba.”
Ba Hajiyarsu Aisha kaɗai ba, duk wanda ke da alaƙa da ita a familinsu basu goyi bayan maganar komawar ta a gidan Nas ba, asali Babansu Aisha birki ya taka mashi a ranar da suka haɗu a Masallacin Jumu’a “Nasiru ka dena wahalar da kanka game da Aisha, dan ba zata koma gidanka ka sake gigita ta ba”, a marairaice Nas ya ce “Dan Allah a taimaka mani ko dan yara”, wani mugun kallon Babansu Aisha ya yi mashi “Ai Nasiru time off! Ka gama wasa da damarka, kuma da ka san da yara, da baka sake ta ba”, Nas ya buɗe baki zai sake wata magiyar ya dakatar da shi, tare da nuna mashi haƙuri shi ne kawai mafita, dan haka ya yi ta kansa, Aisha ma ta haɗu da rabonta, Barrister da aure ya zo, dan haka ba za su hana shi ita ba saboda shi. A taƙaice dai cikin ƙunar rai Nas ya tafi, dan buƙatar shi bata biya ba.
A ranar ne bayan Magrib kuma suka yi mahaɗa da Sani kan batun Asma’u, aikuwa maimakon su fahimci juna, sai gashi sun yi uwaka ubanka, dan Nas da bakinshi ya ce Sani ne ya liƙa mashi Asma’u, shi kuma Sani haushin bai mori ko sisin Nas ba a dalilin Asma’u ya ce “Ka ji mani Nas, kai yaro ne da za ka ce na liƙa maka ita, ka sani ban maka dole ba, ko ka zauna da ita, ko ka bar ta a gidansu duk ɗaya ne a wurina.”
Cike da haushin wannan magana Nas ya ce “Haka ka ce?”, Sani ya ce “Eh”, a tunzure dama Nas ya ke, cewa ya yi “Jira ka gani”, yana rufe baki ya zagaya gaban motarsa ya ɗauki biro da pepper ya rubuta saki ɗaya ma Asma’u, Sani da ko kallon motar bai yi ba bare ya san wainar da ya toyo a ciki ya ji ya ce “Karɓi, tunda ba tilas ka yi mani ba, toh na sake ta saki ɗaya”, bai jira sake jin wata magana daga baki Sani ba ya shige motarsa, fizgarta ya yi tare da baɗe Sani da ƙura.
Kamar Sani zai haɗiye zuciya ya mutu, yanzu wannan ita ce sakayyar da Nas zai yi mashi, “Na rantse da Ɗaa ka yi Nasiru”, yana rufe baki tari ya sarƙe shi a dalilin wannan ƙura da ya shaƙa, da ƙyal ya ƙarasa gida, saboda tarin kamar ya kashe shi. Halima na jin yadda suka yi da Nas ta ce “Allah ya ƙara, kwaɗayi mabuɗin wahala ai”, duk tijarar Sani, amma ya kasa ce mata komai, sai ma bajewa da ya yi kan gado yana ta maida numfashi, ƙasan ransa kuma yana ta zullumin yadda zai tunkari Aunty da takardar sakin Asma’u.
Sai da aka kwana biyu kana ya je gidan Aunty ya basu saƙon Nas, hannun Aunty na karkarwa ta buɗe takardar ta fara karantawa, bayan ta gama ne ta buga uban tagumi “Oh ni Habiba, mun ga ta kanmu.”
Sani da ke tsaye gefenta ya ce “Wallahi kada ki sanya kanki cikin damuwa saboda wancan matsiyacin da bai san darajar ɗan Adam ba”, Aunty ta ce “Ai ni abin ne ke ɗaure mani kai Sani, a ido kamar mutumin arziki, ashe mugun gaske ne”, Sani ya ce “Wallahi kuwa”, nan ya kwashe duk wani baƙin halin Nas, da irin baƙin maƙonsa, da kuma irin wahalar da ya gana ma Aisha duk ya faɗa ma Aunty, Aunty ta ce “Kuma Sani ka san da haka, shi ne kuma ka haɗa Asma’u da shi?”, Daburcewa ya yi, ya nemi soka ma zancen wuƙa.
Aunty na lura ta ce “Hmm Allah ya kyauta!”, shirun da Aunty ta yi ne ya ba Sani damar miƙewa, “Bari dai in je Aunty, komi kenan zan dawo”, saboda ya gama ɗaure kansa, baki Aunty ta ɗan taɓe kafin ta ce “Toh shikenan.”
Yana tafiya ta iske Asma’u da ke jiyo su a ɗaki “Ga takardarki in ji Nas, kuma dama shirye nake da aikawa, dan ba zan yadda da auren ƙunci da tsumulmula ba wlh.”
Asma’u da tunanin yadda zata koma ma Abbas ya fara shagaltar da ita ta ce “Alhamdulillah, na huta da masifa, mutumin can saura ƙiris ya kashe ni da ƙunci.”
Baƙinciki bai bar Aunty ta sake magana ba, sai ma ficewa ta yi tabar Asma’u sagale da pepper a hannu.
Tunanin yadda zata koma ma Abbas ta shiga yi, sai dai sanin abu ne mai wahala ya iya saurarar ta ya kusa sanya ta kuka, domin irin azabar da ta gana mashi kare ba zai ci ba.
Lamo ta yi kan kujera, kamar wadda aka umurta ta ɗauki waya ta kira Abbas, aikuwa har ta tsinke ba a ɗauka ba.
Bata daddara ba ta sake kira, sai ji ta yi Khadija ta ɗaga “Malama lafiya kike kiran mijina?”, wani irin takaici ne ya ƙume Asma’u, yau ita ake yi ma gorin miji.
Kashe wayar ta yi tare da komawa ta kwanta, kuka mai tsuma zuciya ta riƙa yi, a ranta kuma ta yi ta addu’ar Allah ya yafe mata, dan duk abin da ke faruwa da ita, ita ta ja ma kanta.
Khadija kuwa ba ƙaramar kiɗima ta yi ba akan kiran da Asma’u ta yi ma mijinta, dan ta san yadda Abbas ya so Asma’un, tsaf zai iya koma mata.
Abbas na shigowa ɗakin ya ganta rai haɗe, cike da kulawa ya zauna gefenta a kan kujera, a tunaninsa ko cikin ne ke damunta dan saura wata biyu ta haihu “Babyn baby! Me ya faru?”, ya faɗa tare da sumbatar kumcinta, sai da ta shasshaɓe fuska kamar zata yi kuka sannan ta ce “Ba kai ne ba”, idanu ya ɗan zaro “Ni, me na yi?”, wayarsa da ke kusa da ita ta ɗauka, dialer ta shiga tare da nuna mashi kiran Asma’u, gabansa ne ya faɗi, dan ba tun yau Asma’u ke kiransa ba, kawai dai bai taɓa ɗagawa ba ne, dan bai da lokacinta.
Fuskarsa a murtuke ya ce “Asma’u ce silar fushin?”, kai ta ɗaga “Eh, meye haɗinka da ita.”
Da ace Abbas zai iya magana, da ya ce “Ƙauna ce sila”, toh bai da wannan ikon, saboda Asma’un ta zubar da ƙimarta a idonsa.
Cikin son kare kansa ya marairaice “Ba ni da haɗin komai da ita Deejah, kawai dai tana kirana ne, sai dai ban taɓa karɓa kiran ba”, take zuciya da bata da ƙashi ta ce ma Khadija “Wata rana zai ɗaga ai”, musamman yadda ta ga jikinsa ya yi sanyi, cewa ta yi “Toh bana son tana kira mani miji.”
Khadija tana yi mashi halaccin da ko me take so zai iya yi mata, cewa ya yi “An gama Deejah, Insha Allahu Asma’u ba zata ƙara kira ba.”, A take ya garƙama duka numbers ɗin Asma’u a black list, sannan ya shiga WhatsApp ya yi blocking ɗinta, daga ƙarshe kuma ya goge duka numbers ɗin a wayarsa.
Bayan ya gama wannan ne ya rungume matarsa, cikin tausasa murya ya ce “Bana son fushi, ki kwantar da hankalinki kin ji, ba Asma’u da ta cutar da ni ba, a duniyar nan kaf ɗinta bana jin akwai macen da zan iya saurara idan ba ke ba matata”, maganganu masu cike da zallar so ya yi ta faɗa mata har ta sauko, aikuwa sai da ta sumbace shi sannan ta ce “Ina son ka mijina”, martani ya maida mata, daga nan suka nufi bedroom, duk da tsohon cikin amma Khadija sai da ta kusa sumar da shi da kulawa…
Shi kuwa Nas ba wanda bai tura ba a danginsa kan a sanya baki Aisha ta koma, amma Aisha da mahaifanta suka ƙi amincewa. Barrister kuwa tuni ya turo magabatansa a ka fidda ranar aure, dan sha’anin Nas tsoro yake ba shi.
Baƙinciki kuwa kamar ya kashe Nas a ranar da aka ɗaura auren Aisha da Barrister. Mafarin da ya ga ba Sarki sai Allah, sai ya koma ma Asma’u, ita ma dama jiransa take, dan ta fidda rai da samun Abbas, tana komawa kuwa suka dasa gasa juna.
Aisha kuwa tuni burinta na samun soyayya ya cika, dan kuwa Barrister ya bata cikakken ƴancinta na ƴa mace, kan kace me ta zama wata hamshaƙiya saboda zagaye duniya da suke. Ɓangaren ƴaƴanta ma kula suke samu a wurinsa kamar shi ya haife su.
Khadija kuma ta haihu, ta haifi kyakkyawan yaro kamar babansa, an sanya mashi sunan mahaifin Abbas. An sha shagali kuwa kamar ba gobe.
Asma’u kuma yanzu baƙincikin rashin haihuwa ne damuwarta, wanda ake zargin Nas ɗin ne bai da lafiya, aikuwa kullum cikin kuka take, musamman idan ta tuna wulaƙancin da ta yi ta zubawa lokacin da ta samu cikin a gidan Abbas, wanda za a iya cewa mugun halinta ne ya kashe ɗan.
“Allah na san sakamakon butulcin da na yi maka ne nake karɓa, ina roƙonka da ka yafe mani, sannan ka bamu zaman lafiya da fahimtar juna ni da mijina”, wannan ita ce addu’ar da Asma’u ta lazimta, saboda ta fahimci rashin kunya ba za ta fisshe ta ba, saboda Nas walki ne daidai ƙugunta. Cikin ikon Allah kuwa sai ga shi addu’arta ta karɓu, duk wani rikici sun rage shi, yanzu har zama suke ita da shi su ɗan tattauna matsalolinsu tare da magance su.
Hakan kuma ba ƙaramin daɗi yake musu ba, saboda zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki.
Sannan yaran Aisha ma kusan kullum suna gidan, har sun shaƙu sosai da Asma’u, saboda suna ɗebe mata kewa. Aunty ma hankalinta ya kwanta, dan ta dena jin mugun labari a wurin Asma’u.
Batun rashin haihuwa kuwa shi suka sa gaba, yanzu dai sun fantsama neman magani. Sai mu ce “Allah ya sa mu dace baki ɗaya Amiin.”
Tammat bi hamdillah.
A yau 17-3-2023 na kawo ƙarshen wannan littafi na CIKIN ƁAURE, ina roƙon Allah ya amfanar da mu da abin da ke ciki; kuskuren da na tafka kuma Allah ya yafe mana Amiin.
Da fatan kuma Fans na wannan littafin za su gafarce ni bisa ga jinkirin da a ka samu a kammala littafin, da fatan za ku karɓi uzurina.
Taku ce a har kullum, Hadiza Isyaku (Maman Mu’azzam da Abdallah).
Masha Allah gsky book din nan yayi dadi sannan kuma mun dauka darasin da ke ciki……. Allah ya saka da alkhairi ya kara basira
Amiin ya Allah, Nagode sosai Sis