Zaman da Asma’u ta yi don chat ɗin bai mata daɗi ba, kasantuwar jikinta bai iya ɗaukar sanyin da ke ratsa ƙafufunta yana shiga cikin jikinta, naɗe kafafuwan ta yi a kan kujerar one seater da take zaune, lokaci ɗaya kuma ta lulluɓe kaf jikinta da marron Hijab, farinciki fal a ranta ta yi zaman hakimai a kan kujerar sannan ta yi playing saƙon Khadija da ke naɗe cikin sauti. Farko amsa sallama ce Khadija ta yi, sannan ta ɗora da “Masha Allah Tawan! Ki ce Abbas ya ƙaraso da ke a duniyar gizo, toh Allah ya sa Alkhairi kuma ya tsare maki”, bakin Asma’u washe ta ce “Amiin” a fili, sannan itama ta danna voice button, don duk da bata taɓa yin WhatsApp ba, amma ta ga yadda ƙawayenta ke yi.
“Amiin ƙawas, godiya nake”, abin da Asma’u ta faɗa kenan, fitowa ta yi daga contact ɗin Khadija ta shiga na Sailuba duk da ita bata zo WhatsApp ɗin ba bare ta yi mata reply akan sallamar da ta yi mata. Dp ɗin contact ɗin ta buɗe mai ɗauke da ƙayataccen hoton Sailubar da ta ɗauka cikin jar doguwar rigar atamfa, sosai dp ɗin ya ɗauki hankalin Asma’u har ta ji tana son itama ta ɗora nata hoton.
Ɓangaren status ta koma, nan ma ta ci karo da status ɗin family and friends ɗinta sun ɗaura mabanbantan pics da vedios, babu kuma wanda bai ɗauki hankalinta ba, sai dai rashin media ko ɗaya a wayarta ya hana ta ɗora nata, ga shi bata iya saving status ba bare ta yi copy and paste.
Dawowar Khadija online ce ta ƙara mata karsashin WhatsApp ɗin, hira sosai suka cigaba da yi ta manyan ƙawaye, a nan Asma’u ta buƙaci Khadija ta sanya ta a groups, don WhatsApp ɗin ya ƙara mata armashi.
Voice Khadija ta yi mata da “Okay, akwai kuwa hots groups na matan aure, bari zan bada contact ɗinki ayi add, ko don ki ƙara samun hanyar faranta ran Abbas.”
Asma’u na jin voice ɗin ta ɗan tsuke fuska, domin maganar Khadija ta fama mata mikin ƙiyayyar Abbas, cikin raɗaɗin maganar ta yi mata reply ta hanyar typing da “Ashe ma hanyar da zan faranta ran Abbas”, sticker mai ɗauke da dariya Khadija ta turo mata kafin ta yi mata typing da “Eh mana tunda mijinki ne”, Har cikin ran Asma’u ba daɗi ta ce “Su miji manja, kin manta zaman wucin gadi nake a gidan, lokaci kawai nake jira in tada hargitsi ya rabu da ni?”
Sosai maganar Asma’u ta ba Khadija mamaki, flushed emoji ta turo mata, sannan ta yi mata typing da “Asma’u kin kuwa san me kike faɗa?”, amsa Asma’u ta bata da abin da ke ranta dangane da Abbas, inda ta ce “Na sani mana, ke zan iya rantse maki ban ɗauki Abbas miji ba, duk wata soyayya ko hidima da yake mani ina kallon su kawai a matsayin wahal da kansa”, sticker mai hoton wata mata riƙe da haɓa Khadija ta sake turo mata, daga bisani ta rubuta mata “Toh Allah ya kyauta maki, ni dai ba ruwana.”
Dariya Asma’u ta tura mata “Da ruwanki kuwa, tunda ba ki da kamata, ni ma ba ni da kamar ki.”
Tabbas ƙawancensu ya wuce misali, kuma a cikin ƙawancen sukan faɗa ma juna gaskiya, don haka take Khadija ta yi ma Asma’u voice da “Asma’u ki dawo hayyacinki, samun miji kamar Abbas sai an tona, don haka ki yi ma kanki ƙiyamullaili ki koya ma kanki son shi, tunda kin ga yana maki ƙaunar da ba ma kowace mace ke samun irin ta ba”, sosai ta ankarar da Asma’u illar gangancin da take son yi, ta hanyar nuna mata ƴanmatanci da zawarci duk gaibu ne, wanda babu wanda ya san haƙiƙaninsa sai matan dake a gaban iyayensu, babban misali ta buga mata da kanta, inda ta bata labarin yawo da hankalin da saurayinta ke ta yi mata, kullum ba wata tsayayyar magana, kuma ba don bata da siffar da zai aure ta bane, kawai don ya ga tana masifar son shi.
Asma’u kam ta yi nisa a tsanar Abbas, don haka bata jin kira, taƙaicetacciyar magana ta yi ma Khadija “Toh nagode. Ki yi adding ɗina a groups ɗin, hada na novels idan akwai.”
Khadija ta san Asma’u bata ji nasiharta ba, kawai dai bata son jan maganar ne gudun ɓacin rayuwakansu, a taƙaice itama ta ce “Toh”, tare da sauka.
Asma’u ta ɗauka a take zata ganta a groups, don haka ta yi ta zuba idanu, sai da ta yi kusan minti goma tana jira, amma shiru. Saƙo ta aje ma Khadija “Malama ya na ji shiru?”. Previous chat ɗinsu da Khadija ta bi, aikuwa maganar faranta ran Abbas ta yi mata tsaye a rai, a tsiwace ta yi magana a fili, inda ta ce “Ran Abbas ɗin ya daɗe bai yi fari ba”, sauka ta yi daga WhatsApp ɗin don ya mata shiru. Jujjuya wayar green colour ta shiga yi, lokaci ɗaya kuma tana yi mata kallo mai cike da birgewa dan ta cire cover, a ranta ta ce “Ina ma Alhaji Nas ne ya siya mani ita, da ya ga godiya ta musamman.”
Maida cover wayar ta yi, lokaci ɗaya kuma ta kwantar da kanta a bayan kujera tare da lumshe idanu a hankali. Duniyar tunanin Nas dake sanya ta farinciki ta lula, a zuciya ta hango gashi nan yana shirin fita cikin shigarsa ta omo blue ɗin boil, tunga ya ja a bakin ƙofa ya na yi mata kallon so da ƙauna, daga zaunen da take a kan royal bed ɗin ɗakinsa ta murguɗa mashi baki, hannu ya kai a kunnensa ya ce “Tuba nake chair lady.”
Sosai wannan tunanin ya nishaɗantar da Asma’u har ta yi murmushi mai sauti ba tare da sani ba, “Ina sonka Nas”, ta faɗa cikin sambatun haukan da soyayyar Nas ɗin ta haifar mata. A cigaba da tunanin bogin ta hango ta kwantar da kanta a gadon bayan Nas, saboda har ta yafe mashi laifin da ya yi mata, a hankali Nas ya zare mata hannaye dake zagaye da shi, juyo da ita ya yi suna fuskantar juna, lakatar hancinta ya yi kafin ya tambaye ta “Me kike so na yi miki tsaraba?”, ta buɗe baki zata ce “Ice cream” kenan sallamar Abbas ta dakatar da ita, jikinta a tsume ta buɗe idanu don ba ƙaramar mutuwar jiki tunanin Nas ke sanya ta ba.
Idanunta da suka ƙanƙance ta sauke ma Abbas dake tsaye a bakin ƙofa tare da amsa sallamarsa, ji ta yi ina ma tunanin Nas ɗin ne na zahiri ba ganin Abbas ba.
Shi kuwa sai da ya ƙare ma tsakar ɗakin dake hargitse da kayan da suka yi breakfast kallo sannan ya shigo, bai kuma yi mamakin ganin shi haka ba, don ya san zalƙin wayar ba zai barta ta iya komai ba a yanzu, zama ya yi a hannun kujerar tare da faɗin “Madam har yanzu kina nan?”, hannunsa a kan cinyarta ya ƙarashe maganar, a hankali ta janye mashi hannu don ji take kamar ƙaya ya ɗaura mata “Eh, yanzu nake shirin tashi”, ta faɗa a kasalance, duban ta ya yi a tsanake kafin ya ce “Kamar ma bacci kike ji”, girgiza kai ta yi “A’a”, cewa ya yi “Amma idanunki sun nuna haka”, karɓar wayar da ke hannunta ya yi, rage contrast ɗin wayar ya yi, don a tunaninsa ko hasken screen ne, miƙa mata ya yi sannan ya ce “Hasken waya na taɓa idanu, ki riƙa ragewa”, cewa ta yi “Toh”. Ya lura da ba wata walwala a tare da ita, mafarin ya tashi daga kan kujerar, sai da ya faɗa mata wake da lettus na can tsakar gida sannan ya wuce bedroom. Yadda ya bar shi a hargitse, haka shi ma ya tarar da shi. a wannan karon ma uzuri ya yi mata, don sabuwar waya musamman ga wanda bai taɓa riƙe ta ba sai a hankali. Gyaran ɗakin ya shiga yi, saboda idan ya bar ta da shi toh zata yi rana wurin girki, ga shi har goma da rabi.
Yana gamawa da ɗakin ya fito tsakar gida, nan ma sai da ya rage mata wasu ayyukan sannan ya yi shirin fita.
Kitchen ya same ta tana jera plates da cups a kan kitchen-wear, cike da ƙaunar ta ya rungumota ta baya tare da cusa kansa a wuyanta yana shaƙar ƙamshin jikinta “Asmy fita zan yi”, ya faɗa cikin tausasa murya, wani irin baƙinciki ne ya turnuƙe zuciyar Asma’u, musamman da ƙamshin turarensa da ta tsana ya game kitchen ɗin, ita kam da Abbas zai kyauta mata, da ya dena shige mata, zame jikinta ta so yi, amma ta kasa saboda irin riƙon da ya yi mata “A dawo lafiya”, ta faɗa a taƙaice, don so take ya rabu da ita, cewa ya yi “Allah ya sa, amma ki gama girki da wuri, don ba zan daɗe ba”, kai ta gyaɗa “Toh”. Ta ɗauka da ya zare hannunsa tafiya zai yi, kawai sai ta ji ya yi mata irin juyowar da zuciya ta hasko mata Nas ya yi mata suna fuskantar juna, “Tsarabar me zan miki?” Abbas ya tambaye ta, tambaya ita ma ta jefo ma kanta “Ko ya ji zancena na ɗazu?”, lokaci ɗaya kuma gabanta na wata irin faɗuwa, ƙuri ta yi ma fuskarshi tare da haɗe yawun tashin hankali, shi kuwa yadda ta kafe shi da idanun ne ya yi tasiri a kansa “Kin yi shiru?”, ya faɗa cikin murya mai kama da raɗa, murmushin yaƙe ta yi “A’a bana son tsarabar komai”, ɗan zaro idanu ya yi “Anya; Har ice cream ɗin bakya so?”
Cikin yanayin firgici Asma’u ta lumshe idanu, tare da kwantar da kanta a ƙirjinsa “Ina so”, ta yi haka ne domin ta samu sassaucin figicin tabbacin ya ji sambatunta na ɗazu, shafar bayanta ya yi “Okay sweet heart”, ɗago da fuskarta ya yi gami da sumbatar lips ɗinta “Ina son ki Asma’u”, ya faɗa hannunsa tallabe da kumcinta.
“Ni kuma bana son ka”, ta faɗa cikin ranta, lokaci ɗaya kuma tana kallon fuskarsa mai ɗauke da sajen dake ƙara masa kyawun da ita bata ganinsa.
Abbas ya ji daɗin yanayin da suke ciki, ba don neman na Maggi ba, da ya tsaya gidan kawai don su kasance a haka. Sun ɗauki ɗan lokaci a kitchen ɗin, kafin daga bisani ya tafi.
Asma’u kam cike da ruɗani ya barta, tariyar tunaninta da Nas ta shiga yi har ta gane ba inda ta yi magana a fili sai lokacin da ta ce “Ina son ka Nas”, kuma a lokacin tana da yaƙinin Abbas bai dawo ba, kuma koda ya dawo toh sautin bai yi tashin da zai ji ba, “Toh idan ma ya ji sai me?” ta faɗa a fusace, tare da sauke hannayenta dake harɗe a ƙirji, fitowa ta yi daga kitchen ɗin tana ta sababi a ranta, domin zuciyarta ta fara ƙeƙashewa, bata ƙi ba ma Abbas ɗin ya ji ko ya ga abin da zai tabbatar masa da ba ƙaunar sa take ba.
Idan tana cikin fushi ta fi yin aiki cikin sauri, don haka cikin ɗan lokaci ta ƙarasa aikinta har ta ɗaura girkin shinkafa da wake. Wayarta ta ɗauko a ɗaki ta dawo tsakar gida ta zauna kan ash ɗin plastic chair, WhatsApp ɗin dai ta koma, aikuwa sai ga groups guda uku sun bayyana a screen ɗinta, “Godiya nake Dije” saƙon data a je ma Khadija kenan, a fili kuwa dariyar murna ta shi ga yi don hakan har ya wanke mata damuwar da ke ranta.
Group ɗin Novels ne a sama, kuma shi ne ya ɗauki hankalinta, don sauran tunda Khadija ta jingina su da faranta ran Abbas suka fita ranta.
Aikuwa a sa’a ta shiga Group ɗin mai suna Home of Hausa Novels, domin wani novel ne mai suna Kishiyar Katsina ta ci karo da an turo shafukansa har guda goma.
Sosai sunan Novel ɗin ya ɗauki hankalinta, shafi na uku ne a sama, shi kuma ta fara karantawa, yadda ta ga soyayyar Khamis da Maryam a cikin shafin ne ya sa ta bin sahun shafukan, har ta gano shafin farko, don ta fi son fara karatun littafi daga farko. A farkon ne kuma ta fahimci kafin Maryam, a kwai uwargida mai suna Aisha.
Yadda labarin ya yi mata armashi ne ya mantar da ita wakenta dake ta tafasa a kan gas, sai da ta je shafin da Maryam ta fara girki ne ta tuna da nata girkin, aikuwa a hanzarce ta tashi ta shiga kitchen, ƙasa-ƙasa ta ga wutar gas ɗin na ci, ɗan ƙara wutar ta yi, amma ta ga sam ta ƙi ƙaruwa “Ba dai gas ɗin ya ƙare ba”, ta faɗa a fili tare da miƙewa tsaye, agogon wayarta ta duba, ƙarfe ɗaya daidai, bata wani damu ba saboda tana da hot plate, kuma ga wutar Nepa, a kan cabinet ta aje wayar, sannan ta jona hot plate ɗin a socket, maida tukunyar ta yi a kansa, sannan ta wanke shinkafa ta zuba.
Fitowa ta yi ta dasa karatun daga shafin da ta tsaya. Ba ita ta tashi ba sai da ta ji girkin ya fara ƙauri, da sauri ta koma kitchen ɗin ta sauke girkin.
Asma’un da duk nawarta ƙarfe biyu ta gama komai, hatta wanka da sallar azuhur duk ta yi, amma sai ga shi waya ta kai ta har biyu da rabi ba tare da ta gama komai ba, sauƙinta ma shaguɓe ne Abbas ya yi mata cewar zai dawo da wuri, don baya son ta shantake akan waya.
A gaggauce ta yanka lettus, sannan ta yi wanka da sallah. Make-up mai ɗaukar hankali ta yi, sannan ta ɗauko baƙar jallabiyar ta mai kyau ta cikin lafe ta saka gami da yafa ƙaramin gyalen jallabiyar a kai. Duk wanda ya ga haɗuwarta a lokacin zai yi tunanin saboda mijinta ta yi, sai dai ita a ranta ba haka bane, ta yi kwalliyarta ne don ta ɗauki Pics ɗin da zata ɗaura a status.
Gaban dressing mirror ta tsaya tana duban kanta, sosai itama ta birge kanta, ji ta yi ina ma Nas ya bayyana a bayanta su ɗauki pics ɗin a tare, kai ta girgiza don waɗannan mafarkan na Nas na taɓa mata zuciya, musamman idan ta tuna soyayyar ta ɓangare ɗaya ce. Cike da hope ɗin wata rana za su kasance a tare ta ɗauki wasu pics ɗin a gaban mirror.
Fitowa ta yi falo da nufin ɗaukar wasu, sai dai tana jin ƙarar mashin ɗin Abbas ta fasa, maida wayar ta yi a jikin charge sannan ta koma bedroom ta zauna a gefen gado.
Abbas kuwa kai tsaye bedroom ɗin ya shigo, tun daga bakin ƙofa haɗuwarta ta fizge shi, “Masha Allah” ya faɗa yana mai zama a gefenta, kafe ta ya yi da idanu yana mata kallon so, tafukansa cikin nata ya ce “Madam kin yi kyau.”
Ita kuwa tamkar zata haɗe rai ta ce “Nagode”. Sun ɗan jima zaune yana ta yaba kwalliyarta, kafin daga bisani ya ruƙo hannunta suka fito falo, da wayarsa ya yi musu hotuna, duk da bata saki fuska ba amma ta yi kyau sosai. Miƙa mashi wayarta ta yi “Ka tura mani pics ɗin”, karɓa ya yi yana ƴar dariya, “Ok, je ki kawo mana abinci tukunna”, zama ya yi ƙasan carpet, ita kuma ta fita ta kawo musu abincin.
Abbas na kai lomar farko a baki ya ji ƙaurin girkin, haɗiye wa ya yi sannan ya dube ta lokacin da ta ta kai spoon a baki “Madam gikin ya yi daɗi, sai dai akwai ƙauri kaɗan.”
Murmushin jin kunya ta yi, suka cigaba da cin abincin, suna gamawa ta kwashe komai ta kai kitchen, falon ta dawo ta zauna gefensa a ƙasan “Ka tura mani?” ta tambaye shi, don burinta pics ɗin su iso wayarta ta ɗaura a status.
Sai da ya ɓata kusan seconds goma yana kallonta sannan ya ce “Yanzu zan tura ranki ya daɗe.”
Aikuwa yana tura mata ta tashi daga kusa da shi ta koma kan kujera, kallon pics ɗin ta shiga yi, inda shi kuma ya riƙa kallon ta don suna fuskantar juna, sosai yake ƙaunar ta, da a ce zata sakar mashi ruhi da jikinta, da ya bata kulawar da bata taɓa zato ba. Daga ƙasan carpet ɗin ya riƙa janta da hira, sai dai duk abin da yake faɗa bata fahimtar sa, saboda hankalinta na wurin tunanin pics ɗin da zata saka wanda ya fi kyau. Shi kuwa bai lura da ba ta surutansa take ba, saboda dama bata cika sa baki idan yana magana ba.
Kiran sallar la’asar ɗin da aka fara ne ya sa shi tashi, dubanta ya yi “Bari na je masallaci, daga can kuma zan wuce wurin sana’ata.”
Ta kuwa ji daɗin haka, fuskarta ɗauke da walwala ta ce “Ok, a dawo lafiya”, cewa ya yi “Allah ya sa”. Alwala ya fita ya gabatar, sannan ya fidda mashinɗinsa ya tafi.
Sallar Asma’u itama ta gabatar, sannan ta buɗe data, dp ɗinta ta chanja, inda ta ɗora hotonta wanda take ita kaɗai, a status ta koma ta ɗora wani pic ɗin sannan ta cigaba da karanta littafin Kishiyar Katsina, littafin kuma na mata daɗi ne idan ta kalli Khamis a matsayin Nas, sannan kuma ta kalli kanta a matsayin Maryam, inda Aishar Nas ta maye gurbin Aishar Khamis.
Salon kissar Maryam ma na ƙayatar da ita fiye da zato, alƙwali ta ɗaukar ma ranta in dai ta auri Nas sai ta linka irin abin da Maryarm ke yi ma Khamis.
Haka dai ta wuni zungur riƙe da waya. Abbas kuwa da shirin taka mata birki ya dawo, saboda pics ɗinta da ya ga ta baza a status, sai da ya bari sun gama cin abinci sannan ya ce “Asma’u “, amsawa ta yi tare da dubansa daga kan kujerar da take inda suke fuskantar juna “Photonki nake son ki cire a dp”, ya faɗa ba tare da alamun wasa a maganarsa ba.
kallon baka isa ba ta yi mashi, lokaci ɗaya kuma ta ce “Saboda me?”, amsa ya bata da “Saboda ina kishinki”, shiru ta yi na wucin gadi, kafin daga bisani ta ce “Toh mi ye a ciki, na ga dai ba wasu maza ke da contact ɗina ba.”
Tunda ta fara maganar yake kallonta har ta kai ƙarshe, cewa ya yi “Duk da haka dai ki cire, status ɗin ma don ko kin cire masu YO da GB sai sun gani, don haka da ya fita kada ki sake sakawa”, bai bari ta ƙara magana ba ya miƙa hannu “Ba ni wayar na cire dp ɗin a yanzu”, don alamu sun nuna bata ji maganarsa ba, ɗauke kai ta yi “Ka bari zan cire”, tana rufe baki ta miƙe da wayar ta nufi bedroom.
Zuciyarsa cike da zafin gardamar da ta yi mashi ya raka ta da idanu, lallai yadda yake kishinta ko da tsiya sai ta cire dp ɗin, don ko da ƴan’uwanta ne baya fatan su gane mashi ita, bare wasu can, duk da bai tunanin kafin su yi aure tana kula wasu samarin bare har su samu contact ɗinta.
Bedroom ɗin shi ma ya koma, samu ya yi har ta kwanta, takowa ya yi gaban gadon “Ba dai fushi ba ko?”, ya tambaye ta cikin son maida komai ba komai bane, duk da yana jin raɗaɗi a ransa.
Banza ta yi tamkar ba da ita yake ba, kamar zai yi kuka ya ce “Asma’u kina ji na fa”, Ɗago da kanta ta yi daga kwancen “Toh me kake so na ce, photo ne na ce zan cire, don haka ka rabu da ni.”
Tunda suka yi aure bata taɓa yi mashi makamancin haka ba, duk da shu’umcin da take mashi, mamaki fal a ransa ya cigaba da kallon ta, zuciya iya wuya ya ce “Toh ki tashi ki cire yanzu”, cikin ranta ta ce “Na rantse ba zan cire ba”, a zahiri kuma ta sake yin shiru. Asma’u ta samu ƙwarin guiwar yi mashi taurin kai bisa ga wutar son Nas da ke ta ci a ranta, wadda karatun novel ɗin da ta yi yau kaɗai ya rura mata, yanzu kuwa bata jin akwai sauran ragi ko ragowa a tsakaninta da Abbas, musamman da yake shirin takura mata a kan abin da ke faranta mata rai.
A nashi ɓangaren ma neman ragowar dake tsakaninsu ya yi ya rasa, saboda baya son gardama, ɓangare ɗaya kuma ga tsananin kishinta da yake, sai dai taushin hali irin nashi bai bari ya biye ma zuciyarsa da ke zuga shi ya karɓe wayar da tsiya ba, sai dai ya yi mata barazana, aikuwa da yake tana son wayar sai ga shi ta ba shi ya cire.
Falo ya koma ya zauna, cikin ransa yana nadamar saurin siya mata waya, don tun ba a je ko’ina ba alamu sun nuna ba zata bari su zauna lafiya ba, sai shaɗayan dare ya dawo bedroom ɗin ya kwanta, ya so jure kwanciya a can gefe amma ya kasa, dolensa ya dawo a jikinta ya kwanta.
Ita kuwa wannan haushi bai bari ta gaishe da shi da safe ba, shi ma ɗin bai damu ba, don ya san hanyar da zai bi har ta huce daga fushin da take.
Ta so ta ɗauki gaba da shi, amma rashin gas ya yi mata tsiya lokacin da zata haɗa musu breakfast, ga shi kuma ba wutar Nepa. A falo ta same shi zaune yana kallon short wa’azin Malam Aliyu Rasheed a Tiktok, ƙerere ta yi a gabanshi tare da faɗin “Ba bu Gas.”
Ko kusa bai ji me ta ce ba, don hankalinsa ya tafi a kan vedion, dubanta ya yi “Me kika ce?”
A ƙufule ta ce “Na ce ba Gas.”
Wannan littafin na cikin ɓaure tamkar kyauta ne, tukuicin da kaɗai zaku bani shi ne yin mani LIKES, COMMENTS & SHARE idan labarin ya ƙayatar da ku, ta hakan ne Manhajar bakandamiya zasu biya ni abin da zan samu damar suburbuɗo maku littafin a kan lokaci.
Ga waɗanda basu da account a bakandamiya ku yi koƙari ku buɗe, zaku samu ɗinbin ilimi a manhajar.
Masha Allah