Skip to content
Part 7 of 25 in the Series Cikin Baure by Hadiza Isyaku

Kallon ta Abbas ya cigaba da yi, lokaci ɗaya kuma yana murmushin da shi kansa ya san yaƙe ne, don ko kaɗan bai ji daɗin yadda ta yi ƙerere a gabansa tamkar sandar rake ba, sai dai ya danne rashin jin daɗin saboda ya fahimci ɗanyen kan yarinta na ɗibar ta, uwa uba kuma ga ƙarancin wayewa a tattare da ita.

“Hmm”, ya faɗa a ransa tare da ɗauke kai ya dubi waya, fita ya yi daga Tiktok ɗin ya rufe data, ƙasan ransa kuma yana jin duk ba daɗi, a je wayar ya yi a hannun kujera sannan ya dubi Asma’u, cikin son ɓoye ƴar damuwar da ta haifar mashi a rai ya tambaye ta “Babu gas kika ce ko?”

Taƙaitaciyyar amsa ta ba shi cikin sautin da kai ka ce tilas aka yi mata “Eh babu”, tana rufe baki ta ɗauke kai tana hararar gefe, “Okay”, ya faɗa, a ƙasan ransa kuma yana ta yaƙin dakatar da dariyar da ke shirin kufce mashi, don ko kusa bata iya fushi ba, ta wani ɓangaren kuma bai kamata ya maida fushinta wasa ba, sai dai duk da haka ya ƙuduri niyyar gyara mata kuskuren ƙereren da ta yi a gabansa, don ba haka ake magana da miji ba.

Hannunta da ta riƙe ƙugu da shi ya jawo ya ce “Toh madam zauna, sai mu san abin yi,” jim ta yi kamar ba zata zauna ba, cewa ya yi “Ko sai na zaunar da ke?”

Sanin ƙaramin aikinsa ne zaunar da ita ɗin ya sa ta wurga mashi kallon sama da ƙasa tare da zama gefenshi, zaman shi ma ya gyara suna fuskantar juna, duban ta ya yi a tsanake ya ce “Yanzu tukunna ma, wannan fushin duk na miye?”, ya ƙarashe maganar yana kallon ɗan ƙaramin bakinta da take ta tsukewa.

Tafarfasar da zuciyar Asma’u ke yi ce ta tunzura ta faɗin “Fushin na komai ne”, lokaci ɗaya kuma ta janye hannunta da yake shirin ruƙowa, sosai amsar da ta ba shi ta dakar mashi zuciya, shiru ya yi gami da ƙure ta da kallon mamaki, shi kam bai yi zaton a irin wannan lokacin Asma’u zata yi mashi haka ba, duba da yadda ya faranta mata rai da sabuwar waya, bai san babu wani abu da zai yi mata wanda idan ta kalle shi zata rangwanta mashi ba, saboda tsanarsa ta riga ta gama ginuwa a zuciyarta.

Zuciyarsa a dagule ya sake tambayar ta “Komai kamar me?”

Shiru ta yi tana ta cika da tumbatsa, cikin sanyin murya ya sake cewa”Ki yi mani bayani sai in baki haƙuri”, don fushinta ba ƙaramar baraza ba ce a gare shi.

A gadarance ta ba shi amsa “Ai komai a bayya ne yake”, saboda yanayin da ta ga ya shiga ba ƙaramin girman kai ya ƙara mata ba.

Raunanan idanunsa ya ɗan lumshe gami da faɗin “Koh?”, ta ce “Eh”, ya ce “Toh shikenan, ni dai kawai na san na ce ki cire photo a WhatsApp, kuma ni bana ɗaukar wannan a matsayin laifi, don ba zan juri wasu su gane mani fuskar mata ba”

A ranta ta ce “Ni ma wannan ban ɗauke shi a matsayin laifi ba, aure na da ka yi kafin na cimma burina shi ne laifinka, kuma na rantse sai na yi maka hukuncin da zaka rabu da ni ba tare da ka sani ba”, a zahiri kuma “Hmm!” kaɗai ta iya cewa.

Haƙuri Abbas ya bata da kalmomin da bai san bata buƙatarsu a wurinsa ba, kuma ya yi haka ne don a zauna lafiya, amma ba don ya gamsu cewar ya yi mata laifi ba. Maganar yin ƙerere a gabanshi kuwa cewa ya yi “Kin ga ni ma ban ji daɗin yadda kika yi tsaye a gabana kina maganar Gas ba”

Ita kam dama neman abin da zata zaƙalƙalo mashi take, don bata so wutar ta mutu a ƙanƙanen lokaci ba, tamkar abokinta ta dube shi “Toh daga kwance kake so na yi maka maganar ko yaya?”, kai ya girgiza sannan ya ce “A’a ranki ya daɗe, a matsayina na mijinki ne nake son ki fahimci bai kamata ki yi mani magana a haka ba, kuma a bar maganar ma tunda bata yi maki daɗi ba, amma don Allah ki gyara”, ya rufe baki kenan a ka maido wutar Nepa, bai bari ta ce wani abu ba ya ce “Yauwa kin ga an maido wuta ma, ta shi ki haɗa mana breakfast, kafin anjima na karɓo maki gas ɗin”

Kamar zata tashi sama ta fice daga ɗakin, “Allah ya kyauta” ya furta a fili, tambayar kansa ya shiga yi “Shin irin wannan ƙuruciyar ce ta Asma’u ake cewa sai na yi haƙuri da ita ko kuwa dai wannan halin na daban ne”, domin sati huɗu kenan da aurensu, amma bai san wani jin daɗi na musamman daga gare ta ba, saɓanin yadda abokansa ke ba shi labarin farincikin da suke samu a wurin amarensu, waɗanda kusan tsararrakinta ne, wasu ma basu kai ta shekaru ba.

Bai da ta cewa dangane da tambayar da ya yi ma kansa har sai ya gama tantance halinta, cigaba da kallon Tik tok ɗinsa ya yi saboda bai son damuwa ta samu mazauni a zuciyarsa.

Daga can kitchen kuwa da tulin baƙinciki Asma’u ta haɗa breakfast, fuskarta kuma bayyane da abin da ke ranta ta ɗauko ta kawo mashi, har a lokacin kuma yana zaune a kan kujerar da ta bar shi, yana ganin ta ya faɗaɗa fuskarsa tamkar bata ɓata mashi rai ba, “Har kin gama?”, ya tambaye ta tare da karɓar tiren da ke ɗauke flask da cups gami da kayan tea ɗin.

“Umm!” kaɗai ta ce, sannan ta koma kitchen ta ɗauko plate mai ɗauke da soyayyen ƙwai, tana ajewa ta buɗe plate ɗin sama “Ƙwan dai ya ƙone”, ta faɗa tana kallon shi, duban cikin plate ɗin Abbas ya yi ya ga yadda ƙwan ya yi ƙonewar da ba lallai ne ya iya cin sa ba, ita dama can bata iya soya ƙwai ba, sai dai rashin iyawar na yau ya fi na kullum, kallon ta ya yi “Ai dama ragowar dankalin kika soya mani”, kamar zata cije shi ta ce “Toh da wace wutar zan soya maka dankalin?”, kai Abbas ya jinjina “Yes, na tuna ba gas, kuma wutar nepa ba tabbas.”

Ba tare da ta ce komai ba ta juya, ruƙo hannunta ya yi “Ina zaki je, ga breakfast kuma?”, a ƙufule ta ta juyo”Baka lura da na mutum ɗaya ne ba”, Tabbas Abbas bai lura ba, da ba zai tanka mata ba, don ya fahimci tana buƙatar ya bata space ta sha iska, “Okay” ya faɗa tare da sakar mata hannu.

Bedroom ta shiga ta kwanta a gefen gado, ƙasan ranta kuma tana jin kamar ta kurma ihu, “Allah ka raba ni da Abbas, don bana ƙaunar zama a gidansa”, addu’ar da ta yi kenan a ranta, lokaci ɗaya kuma ta rumtse idanu tamkar mai bacci. Abbas kuwa damuwar rashin breakfast ɗin Asm’u bata bari ya yi nasa breakfast ɗin ba, don daƙyal ya iya shan rabin cup na tea, ƙwan kuwa dama bai ciwuwa, haka ya kwashe komai ya maida kitchen, cikin ransa kuma yana takaicin rashin iya girkin ta, abokansa ma sai dai a can gidansu Abeeda ta girka ya kai musu, gudun kunyata.

Ruwan zafi ya dafa ya yi wanka, yana dawowa ɗakin kuma bai tanka mata ba sai da ya tabbatar da ya gama shirin fita sannan ya zo gaban gadon “Madam fita zan yi”, daga kwancen ta ce “A dawo lafiya”, cike da tsokana ya ce “Ba rakiya?”, banza ta yi da shi, bai kuma cewa komai ba ya fice ɗakin yana dariyar yaƙe, kitchen ya biya ya ɗauki clynder gas.

Asma’u na jin tashin mashinɗinsa ta ce “Ɗan wahala, na rantse ka yi bankwana da farinciki madamar muna tare”, tashi ta yi zaune gami da jingina bayanta da kan gado, wayarta da ke a gaban filow ta ɗauka ta shiga WhatsApp, nan ta ci karo da reply ɗin Khadija a kan status ɗin da ta ɗora, inda ta ce “Tubarkalla, lallai Abbas ya iya kiwo.”

Da Khadijah ta san yadda Asma’u ke ji dangane da Abbas da bata ce mata haka ba, Sticker mai ɗauke da fushi ta tura mata “Don Allah ki dena yi mani maganar Abbas”, tsokanar ta Khadija ta yi “Daga na faɗi gaskiya?”, wata irin ƙwafa Asma’u ta yi a fili sannan ta rubuta mata “Ba wata gaskiya, balbela da farinta aka ganta”, Khadija ta ce “Koh?”, Asma’u ta ce “Eh”, dariya kaɗai Khadija ta tura mata chat ɗin na su ya tsaya. Ta so ta ɗan bibiyi groups ɗinta amma yunwa da ƙunci suka hana ta, fitowa ta yi a WhatsApp ɗin ta kira number Aunty, don da ta ji irin wannan yanayin ita take kira ko sauran ƴan’uwanta. Bugu biyu Aunty da ɗaga kiran, bayan sun gaisa ne Asma’u ta marairaice “Aunty yaushe zaku zo ɗin?”, daga can Aunty ta ce “Wai lafiya ne kike ta matsawa mu zo?”, zuciyar Asma’u a karye ta ce “Ba komai Aunty, kawai na yi kewarku ne”, sassauta murya Aunty ta yi “Insha Allah muna nan tafe ranar Lahadi, tunda dai sauran bukukuwan dangi ma sun lafa”, sosai Asma’u ta ji daɗi, hirarsu ta uwa da ɗiya suka cigaba da yi, bayan sun gama wayar ne Asma’u ta fito, ruwan tea kaɗai ta sha, saboda bata buƙatar komai, gyaran gidan ta shiga yi, cikin ƙanƙanen lokaci ta gama ta koma ɗaki ta kwanta, domin tunanin Nas a tsanake.

Ta ɓangaren Abbas kuwa yana zuwa wurin refiling gas ya ji shi da muguwar tsada, amma saboda bai son damuwar Asma’u haka ya ciri kuɗi ya bada aka sanya mashi, ragowar kuɗin da ke aljihunsa kuma ya yi cefanen ɗanyar kuɓewa.

Asma’u kuma bata shan ɗanyar kuɓewa tun fil azal, Abbas kuma bai sani ba, haka ta yi tuwon bata ci ba, Abbas na dawowa bai tambayeta ta ci ko bata ci ba, don tun da safe ya fara sarara mata.

Yunwar safe da ta rana suna haɗe mata ta fara bin kujera da kwanciya, isa da gadararta kuma sun hana ta tashi ta girka wani abu, sai can gab da la’asar da ta ji zata mutu ta miƙe ta girka taliyar hausa da manja ta ci, tana yin la’asar baccin gajiyar yunwa ya cika mata ido, duk da ba a son baccin yamma, amma haka ta miƙe ƙafa a kan doguwar kujera ta yi ta shirgar bacci.

Aikuwa tun bayan falkawarta idanuwanta suka ƙeƙashe, tana gabatar da sallar magarib da isha’i ta ɗauki waya ta cigaba da karatun novels, kuma ko da Abbas ya dawo abinci kaɗai ta ba shi ta dasa karatun.

Ta ɓangaren shi kuwa kamar ya yi kuka, lokacin da ya kamata a ce matar shi na kusa da shi amma ba haka ba, tashi ya yi daga falon ya koma bedroom ya kwanta don ba zai iya jurar banzatar da shi ɗin da ta yi ba “Oh ni Abbas”, ya faɗa tare da gyara kwanciyarsa a kan kafaɗa, ya so bacci ya ɗauke shi, amma ƙuncin zuciyarshi ya hana, zaune ya tashi ya jingina bayansa da kan gado yana jiran shigowarta, ganin har goma ta buga bata shigo ba ya fita falon, samun ta ya yi hankalinta kwance tana duban waya, daga tsayen da yake ya dube ta “Asma’u wai me kike da waya?”, cikin jin haushin ya katse mata karatu itama ta dube shi “Karatu nake”, tambayar ta ya yi “Na me karatun?”, ta ce “Na novels.”

“Okay, toh ki zo ki kwanta, da safe sai ki ƙarasa”, nuna mashi ta yi bata jin bacci, bata ankare ba kuwa ta ji ya saɓe ta, sassauta murya ya yi yana duban ta, “Mu je toh ki karanta mana, ni ma bana jin baccin”, bai dire da ta ko’ina ba sai kan gado, ɗan rungumo ta ya yi daga zaunen da suke “Yauwa karanta ƙwarai, ni ma ina son novels Asmy”, ya yi mata wannan dubarar ne don kada ta ɗauki abin da zafi, sai dai miskilanci da tsanar sa basu bari ta karanta ba, dole ta ajiye wayar suka kwanta. A wannan dare kuma sai da ya kusa kuka sannan ta ba shi haƙƙinshi na mijinta, shi ma ba dan ya wadatu ba ya haƙura.

Batun zuwan su Aunty kuwa bai san da wannan magana ba, da yamma ya je gidansu Ummansu.

ke tambayar shi “Me ka shirya ma surukan naka?”
“Surukai kuma?” ya tambaye ta shi ma tare da zama a kan jarkar ruwa.

Daga kan tabarmar da take zaune a ƙofar ɗakinta ta ce “Eh mana, jiya mun haɗu da Halima ta ce Gobe Lahadi zasu zo, ko ba ka sani ba?”, Sai da ya danne mamakin ƙin faɗa mashi da Asma’u ta yi sannan ya wayance “Na san da zuwansu Umma, kawai da farko ne ban fahimce ki”, gyɗa kai ta yi “Ayya”, tambayar ta ya yi “Umma toh me za a yi musu?”, cewa ta yi “A’a ka je kai da matarka ku yi tsarin da kanku”, ta yi haka ne don bata son shiga haƙƙin surukarta, Abbas ya san muddin ya sakar ma Asma’u ragamar abincin watsa shi zata yi, lallaɓa Ummansu ya yi akan dai ta shirya musu, itama ta san Asma’u bata iya girki ba sai ta amince zata yi musu Fankasu, inda kuma Abeeda zata je can ta taya Asma’u su yi miya.

Abbas na fita daga gidansu ya wuce kasuwa ya siyo cefane mai rai da lafiya, yana zuwa gida ya jibge shi a bakin kitchen, ɗaki ya samu Asma’u riƙe da waya tana ibadar, “Asmy uwar waya”, ya faɗa tare da zama gefenta, murguɗa mashi baki ta yi, ya ce “Sorry” yana dariya.

Leƙa fuskar wayar ya yi “Wane littafi ne kike karantawa?”, miƙa mashi wayar ta yi “Ni ba karatu nake ba”, cikin ranta tana godiyar Allah, don tsaf zai ce ta karanta mashi.

Shi ma ya ji daɗi da ya ga ba karatun bane, fita ya yi daga ɗakin ya kira ta “Asmy”, tana fitowa ta ga uban cefane, tun kafin ya yi magana ta tambaye shi “Wannan cefanen fa?”

Idanunsa a kan cefanen ya ce “Na miyar da za a yi ma su Aunty ne”, da mamaki ta dube shi “Kai ma ta faɗa maka zasu zo ne?”, kai ya ɗaga mata “Eh”, lokaci ɗaya kuma ya ruƙo hannunta “Na san kin san da zuwansu, me ya sa baki faɗa mani ba”, zare hannunta ta yi “Ai na san zata faɗa maka shi ya sa”, murmushi kawai ya yi. Faɗa mata ya yi a gidansu za a yi fankasu, ita da Abeeda kuma zasu yi girkin miyar, da yake bata ƙaunar danginsa su raɓe ta sai ta ce ita zata yi miyarta, nuna mata ya yi aikin na da yawa ai, kafewa ta yi a kan ba sai Abeeda ta zo ba, shi ma ya kafe a kan sai ta zo, aikuwa sai ta fusata ta ce “Kawai har miyar ma ka kai can gidanku a yi”, ya daɗe da fahimtar bata son danginsa, shi ya sa ba me zuwa gidan, haɗe fuska ya yi “A’a sai dai a kwaso maki sauran girkin ki yi, kin ga kin hutar da su da wahala”, shiru ta yi, don ta san ba zata iya ba, tabbatar mata ya yi da Abeeda zata so.

Haka kuma aka yi, cefane kaɗai Asma’u ta gyara da yankan alayyahu, amma duka aikin miyar Abeeda ta yi, tunda kuma Abeeda ta shigo gidan sau ɗaya suka yi magana, saboda Asma’u sai shan ƙamshi take, Abeeda kuma ta fi ta jin kai, don haka kowa ya cigaba da sabgarsa.

Su Aunty kuwa su biyar suka zo, ita da matan babansu biyu, sai ƙanwar mijinta, da Kausar, wadda itama yayar Asma’u ce da suke ɗaki ɗaya. Murna wurin Asma’u ba a magana.

Da aka kawo abinci kuwa suka yi ta santi, Matar babansu Asma’u ta ce “Wannan girki ya yi daɗi, ke kika yi shi Asma’u?”, Asma’u bata ji kunyar Abbas ba ta ce “Eh”, Aunty ta ce “Anya kuwa”, don ta fi kowa sanin Asma’u bata iya girki ba, Sauri Abbas ya yi “Ita ta yi shi Aunty”, duban shi Asma’u ta yi tana dariya, a kaikaice ya ɗaga mata gira yana dariyar shi ma.

Bayan sun gama cin abincin aka dasa hira, har Abbas ya yi mamakin surutun Asma’u wanda bai taɓa zato ba. Fita ya yi domin Asma’u ta gana da danginta, aikuwa suka sa ta gaba wurin nasiha, Aunty ta ce “Indai kika bi Abbas, ina tabbatar maki da zaki ji daɗin rayuwa”, saboda wayar da kaɗai ya chanja mata ta tabbatar masu da Abbas zai faranta ran ƴarsu, ita kuwa duk abin da suke faɗa jin su kawai take, salon kissar ma da suka koya mata sai dai ta ajiye su, duk ranar da ta auri Nas zata gwada mashi. Kayan mata kuwa a take sai da aka bata wasu ta sha, sauran kuma suka ce ta adana.

Abbas na dawowa kuma aka haɗe su aka ƙara yi masu nasiha a kan su zauna lafiya, domin dukkansu sun yi sa’a.

Har gidansu Abbas su Aunty suka je tare da Asma’u, can ma sun ga tarba ta musamman. Da zasu tafi kuwa Abbas da mahaifiyarshi suka haɗa musu sha tara ta arziki.

Bayan tafiyarsu ne Abbas ya riƙo hannun Asma’u suka dawo gida, tun a tsakar gida ya rungumota ta baya, “Miye haka?” ta tambaye shi tana son haɗe rai, cusa kansa ya yi a wuyanta “Baki ji Aunty ta ce mu riƙe juna ba”, sosai maganarsa ta bata dariya, cikin ɗakin suka koma, nan ya buƙaci ta yi mashi surutun da ta yi ma su Aunty, ƙin yi ta yi, aikuwa ya matse ta yana mata cakulkuli, dariya kuwa hada sarƙewa ta riƙa yi, sosai ya ji daɗin haka, cikin taushin murya ya ce “Haka nake so kullum mu kasance, amma ba kya sake mani fuska, me ya sa?”, shiru ta yi tana kallon shi, don idan amsar da ke ranta ta fito fili to sai zuciyar shi ta buga, cewa ya yi “Don Allah ki lamunce mani mu riƙa irin wannan rayuwar ta nishaɗi, ni kuma na maki alƙawarin fita zarra a cikin mata”, sosai kuwa a wannan lokacin ta lamunce mashi, tun a falo suke farinciki, har suka koma bedroom. Ana kiran magarib suka fito, wanka Abbas ya fara, bayan ya kimtsa ya nufi masallaci, ita ma ta yi. Da Abbas zai dawo ya siyo musu nama da ice cream saboda ba abinci, suna gama ci ya yi mata maganar koyon girki, aikuwa ta ce ba zata je ba, ya ce “Toh Abeeda ta zo ta koya maki”, ta ce “Sai dai idan na yi girkin ka zubar”, barin maganar girkin ya yi, suka cigaba da kallon News a ƴar ƙaramar Tv ɗinta dake manne a bango.

A ƴan kwanakin nan kuma Abbas yana samun sassauci a wurin Asma’u, don ta fara jin daɗin abubuwan da yake mata, amma har a ranta idan ta ce tana son shi ta yi ƙarya, saboda mafarkan Nas da ke ta addabar ta, wanda har rubuta sunan Nas din a jikinta take tana gogewa. Ana cikin wannan yanayin kuma ta fara zazzaɓi, lallaɓa ta Abbas ya yi suka je asibiti, doctor na duba result ɗinta ya miƙa ma Abbas hannu “You did it Abbas, tana da juna biyu.”

Cikin wani irin tashin hankali Asma’u ta riga Abbas magana “Na shiga uku, ciki doctor?”

Wannan littafin kyauta ne a wurinku, likes, comments and share ne kadai tukuicin da zaku bani.

<< Cikin Baure 6Cikin Baure 8 >>

1 thought on “Cikin Baure 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×