Idanun likitan cikin nata ya bata amsa da “Yeah, kina da juna biyu Madam.”
Tamkar wadda aka tsikara ta miƙe gami da dafe ƙirjinta dake luguden faɗuwa ta ce “Na shiga uku ni Asma’u”, a yadda ta ƙarashe maganar kai ka ce faɗowa ƙwayoyin idanunta zasu yi saboda tsananin firgici.
A tarihin rayuwar Asma’u,ba a taɓa yi mata baƙin albishir irin wannan ba, domin tsananin tsanar da take ma Abbas, ta sa ta ƙyamar haɗa iri da shi, sannan har ila yau cikin ya ƙara tazara a tsakanin haɗuwarta da Nas, wadda mafarkin ta ya zame mata jiki, don ko a yau aurenta da Abbas ya mutu, toh dole ta yi zaman iddar haihe ciki, uwa uba kuma ga rainon ‘dan da za haifa har zuwa zayaye, wanda ‘karanci shekara biyu ne, ga shi ita kuma bata ‘ki ta bude idanu ta ganta a gaban Nas a matsayin mata ba. Kuka mai bayyane da tashin hankalin dake cike da ranta ta fashe da shi, a daidai lokacin da ta dafe goshi da hannunta na dama.
Abbas da likita kuwa tuni sun yi nisa a mamakin wannan firgicewa tata, musamman Abbas da bai san lokacin da murnarsa ta koma ciki ba. Kusan a tare suka miƙe gami da kallon juna, sannan a taren suka juya akalar ganinsu a kanta, cikin tsananin kullewar kai likitan ya ce,
“Subhanallah, Malama lafiya?”. Abbas kuwa gabansa na wata irin faɗuwa ya janye mata hannu, jefo mata irin tambayar likitan ya yi “Asma’u lafiya?”, duk da zahirinta ya nuna cikin da aka yi mata albishir ne silar shigarta wannan hali.
Gabaɗayansu ba wanda ta ba amsa, sai dai “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”, da take ta furtawa, dafa kafaɗarta Abbas ya yi da hannunsa da ke ta rawa, muryarsa a sanyaye ya ce “Asma’u”, A fusace ta janye kafaɗarta tare da ƙara ƙaimi wurin kukan da take, sake ruƙo ta ya yi, kamar zai yi kuka ya tambaye ta “Asma’u wannan duk na miye dan Allah, ko cikin ne bakya so?”
“Ban sani ba”, ta faɗa gami da fizge kafaɗarta a karo na biyu.
Kai likitan ya girgiza tare da sauke ajiyar zuciya, shi kam rabon da ya ga irin wannan tun wani saurayi da wata budurwa da suka zo wurinsa a lokacin yana aiki a Ningi, ko su kansu basu yi irin wannan firgicewar ba duk da alamu sun nuna cikin da ke jikin budurwar ba ta hanyar aure aka same shi ba, zuciya ce ta fara ɗarsa mashi tambayar anya wannan cikin ta hanyar aure Asma’u ta same shi?, “Calm down Asma’u”, ya faɗa cikin sigar lallashi.
Ko kusa bata ji me ya ce ba, dan a lokacin ne itama ta dubi Abbas a fusace ta ce “Ka cuce ni Abbas, kuma ba zan taɓa yafe maka ba.”
Cikin fushi Abbas ya kawar ma likitan da zargin da ke ta maimaituwa a ransa ya ce “Kamar ya na cuce ki? Ina ce ke matata ce ta sunna wadda kuma ko hannunta ban taɓa riƙewa ba sai bayan aure”. Yadda ya ƙarashe maganar yana nuna ta ne ya fassara musu mugun takaicin da maganarta ta ƙumsa mashi.
Wannan fusata ce kuma ta sa likitan dakatar da shi tare da yi mashi alamun ya zauna, tamkar Abbas zai yi kuka ya bi umarnin likitan, cikin hasalar da yake ciki ce ya furta “Lallai Asma’u, kin ce wani abu kema”, yana kai maganar ƙarshe ya cije leɓe, ƙuri ya yi ma system da kuma takardun da ke a kan teburin likitan, wanda a baɗini ba su yake kallo ba, tunanin muhallin da zai aje abin da Asma’u ke cikin yi yake, har ta kai ga itama ta zauna bisa ga umarnin likitan ba tare da ya sani ba.
Sosai ya yanke ƙauna da samun damar yin murnar wannan ciki, dan sai yadda wadda cikin ke jikinta ta yi da shi, shi tsoron shi ma kada ta yi sanadin zubewar cikin, don babu wata alama dake nuna tana son shi, gaban shi na ci gaba da faɗuwa ya yi magana a ransa “Ita ɗin banza, da mun yi shari’a kuwa”. Saboda burin shi ya ganshi da ɗa ko ɗiya shi ma.
Ya yi nisa a cikin magana da zuciyarshi likitan ya dakatar shi ta hanyar faɗin “Abbas”, a ɗan firgigi ya dube shi “Na’am Doctor.”
Ita kuwa dogara guiyawun hannunta ta yi akan taburin likitan da ke gabansu, lokaci ɗaya kuma ta rufe fuskarta da tafukan hannyayenta, tunanin makomar da za ta jefa cikin da tun a take ta yi ma lakabi da alakakai ta fara, sai dai bata yi nisa ba itama likitan ya datakar da ita ta hanyar ambatar sunanta “Asma’u”, kasa amsawa ta yi, sai dai shesshekar kuka, janye mata hannaye Abbas ya yi “Magana ake madam”, saboda baya son ta yi ma wani irin tsiyar da take mashi a gida.
Sosai hawayen da ke malala a kumatunta suka ƙara dulmiyar da su a mamaki, har ta kai ga office ɗin ya yi shirun da baka jin sautin komai sai na AC, wani irin mugun kallo Abbas ya watsa mata, wanda irinsa ne na farko da ya taɓa yi mata, asali ma ita bata laifi a wurinsa, amma rashin gwada murna da samuwar gudan jininsa ya haifar mashi da matsanancin jin haushin ta.
Likitan ma duk da hawayen da take bai fasa yi mata maganar da ya yi niyya ba, cikin sanyin murya ya tambaye ta “Asma’u me ya sa bakya murna da kyautar da Allah ya ba ki?”, amsa ta ba shi a ranta “Saboda ta biyo ta hannun wanda bana so”, a zahiri kuwa shiru ta yi tare da sake rufe fuskarta, Abbas ne ya amsa mishi tambayar da dai-dai abin da ya ke ranta “Saboda bata son cikin likita.”
Murmushin yaƙe kawai likitan ya yi, don shi ma ya fahimci haka, cigaba da magana ya yi, “Asma’u ba zan tambaye ki manufar wannan firgicin naki ba, don ba hurumina bane, amma zan baki magana a kan ki sani haihuwa rahama ce, kuma babu mutumin da baya son ta musamman Musulmi, saboda Manzon Allah SallaLlahu alaihi wa Sallam ya ce ku yi aure ku hayayyafa don in yi alfahari da ku a ranar alƙiyama, ko ke bakya son Annabi SallaLlahu alaihi wa Sallam ya yi alfahari da zuri’arki.?”
Maganarsa ta ƙarshe ce ta ɗan kadar mata da gaba, cikin muryar kuka ta ba shi amsa “Ai ni ba haihuwar ce bana so ba”, sake tambayar ta likitan ya yi “Idan ba ita ba ce bakya so ba meye na ɗaga hankali maimakon murna?”, shiru ta yi, nasiha mai ratsa zuciya ya yi mata, inda ya nuna mata akwai tarin mutanen da ke neman haihuwa da komai nasu, amma basu samu ba, don haka gode ma Allah ya kamata ta yi ba butulce masa ba. Sai dai duk girman wannan nasiha da ya yi mata bata ɗauki komai ba a ciki.
Juyawa ya yi wurin Abbas da jikinsa ya gama la’asar, magana ya ba shi wadda zata kore zargin da ya san labudda sai ya ɗarsu a zuciyarsa, inda ya ce “Ka san mata na tsoron cikin fa, musamman da ya kasance na fari, saboda haihuwa na da ƴar wahala, don haka ka lallaɓa ta har wannan tsoron ya fita a ranta”, da ƴar dariya ya ƙarashe maganar, dan Abbas ya gazgata zancensa.
Sosai Abbas ya ji daɗin wannan bayanin, domin ya rage mashi zafin raɗaɗin da ke ranshi. Magunguna likitan ya rubuta musu, karɓar takardar Abbas ya yi tare da godiya.
Tunda kuma suka fito office ɗin likitan ba wanda ya tanka ma wani, a yadda suke tafiya a ware ma ba kowa ne zai gane tare suke ba, don shi ya yi gaba, ita kuma tana biye da shi a baya.
Saƙe-saƙen zuci ne ke ta maimaituwa a ransu, ta ɓangaren Asma’u cewa ta yi a ranta “Na rantse sai na ɓarar da wannan cikin”, shi kuwa Abbas ya rasa me kuma ke kada mashi gaba, duk da nutsar mashi zuciya da likita ya yi. Cikin wannan yanayi suka isa a parking space ɗin asibitin, anan kuma suka taras da wasu matasan ma’aurata zasu shiga motarsu da ke ɓangaren hagun da mashin ɗin Abbas yake, kallo ɗaya zaka yi musu ka san sabon aure ne kuma suna matuƙar ƙaunar juna, dan a kan idanunsu mijin ya buɗe ma matar mota ta shiga, sannan ya ɗan duƙa yana yi mata magana cike da kulawa.
Wani irin ƙunci ne ya ƙara mamaye ma Asm’u zuciya, duk da tana samun fiye da irin wannan kulawar a wurin Abbas, sai dai rashin kasancewar Nas ne ya hana ta gamsuwa, asali ma gani take kamar ba wani abin da take mora a daɗin aure. Ta wani ɓangaren kuma auren mai mota na ɗaya daga cikin manyan burikanta na rayuwa, shi ya sa take matuƙar ji da Nas a ranta.
Satar kallon mutumin ta yi lokacin da ya ɗago yana dariya tare da rufe murfin motar, gani ta yi ya miƙa ma Abbas da ke kan mashin hannu sun gaisa, sannan ya shiga motarsa.
Abbas bai lura da kallon ƙurillar da take yi ma ma’auratan ba “Mu je” ya faɗa bayan ya tada mashin ɗin, kamar zata maƙure shi ta hau, tana daidaita zama ya ja suka tafi gida.
Gabaɗaya kuma rikicewar tunani ta sa Abbas ya manta da siyen magunguna sai da suka shigo layin gidansu,”Ya Salam” ya furta cikin zuciyarsa, suna isa ƙofar gidan ya buɗe mata ta shiga, sannan ya juya karɓo maganin.
Bedroom Asma’u ta yi tsinke tare da faɗawa kan gado, Cikin jajanta ma kanta ta ce “Wayyo ni Asma’u ya zanyi”, lokaci ɗaya kuma ta fashe kuka mai ƙarajin gaske. Abbas na dawowa ya tsinkayi tashin wannan kukan a tsakar gida, da hanzari ya ƙarasa cikin bedroom ɗin bakinsa na faɗin “Asma’u lafiya?”, duk da ya san sanadin kukan.
Ko da ba ƙiyayya a tsakanin su da wahala a wannan lokaci ta iya bashi amsa, bare kuma a yanzu da take jin kamar ta raba shi da ranshi dan ta huta da baƙincikin rayuwa a gidanshi.
Sosai wannan kuka ya ƙara ɗimauta zuciyar Abbas, hawa ya yi kan gadon tare da ɗago kafaɗarta “Asma’u me ya sa kike son tarwatsa mani zuciya?”, fizge kafaɗarta ta yi da ƙarfi ta koma, ɗago ta ya yi a karo na biyu ya ce “Asma’u sam hakan bai dace ba, ki tashi ki faɗa mani damuwarki ko na samu sauƙi a raina.”
Da shi da banza duk ɗaya, dan bata taso ba, sannan kuma bata dena kukan ba. Jikinsa a mace ya sauka daga kan gadon, sai da ya kalle ta sannan murya a raunane ya ce “Na gode sosai Asma’u, ni dai Allah ya sani ban cutar da ke ba, don haka bani da haƙƙi a kan kukan da kike”, yana rufe baki ya juya ya fice daga gidan, a daidai fita layin gidansu ya ga Zulaiha zata je gidanshi, faɗa mata ya yi ta koma, Asma’u bata da lafiya, yanzu bacci take.
Zulaiha na komawa gida ta faɗa ma Ummansu Asma’u bata da lafiya, Abbas na gidan Block ɗinsu kiran Ummansu ya shigo a wayarsa, sai da ya dubi amininsa Abdull da suke a kan benci ɗaya sannan ya amsa kiran da sallama, daga can ta ce “Abbas me ya samu Asma’u?”, amsa ya bata “Zazzaɓin ne Umma, kuma da sauƙi”, fatan ƙaruwar sauƙin ta yi mata, sannan ta katse kiran.
Aljihun gaba ya maida wayar, sannan suka cigaba da magana da Abdull akan halin da ya baro Asma’u, wanda ya kasa binnewa a ranshi har sai da ya labarta mashi, gabagadi Abdull ya tambaye shi “Anya kuwa yarinyar nan tana son ka?”
Da sauri Abbas ya dube shi “Kamar ya tana so na?”, Abdull ya ce “Ka yi mamakin tambayar ko?”, kai Abbas ya jinjina tare da ‘dan cije lebe “Sosai ma”, Abdull ya ce “Na daɗe da karantar yanayinka Abbas, na fahimci ba wani sosai kake jin daɗin zama da ita ba, ko da kuwa bata cutar da kai, toh kuma baka samun kulawar da ta dace a wurinta, don ko kusa jikinka bai nuna ka yi sabon aure ba, asali ma sai rama kake saboda tunanin da ya aure ka ba tare da ka sani ba.”
Sosai maganar Abdull ta sa Abbas nazarin rayuwar shi da Asma’u, tabbas abin da Abdull ya faɗa gaskiya ne, amma bai danganta shi da rashin so, sai da ya hade gululun da ya tokare masa zuciya sannan ya dubi Abdull “Gaskiya ne maganarka, amma na fi danganta zamantakewa ta da Asma’u da ƙarancin wayewa ba kiyayya ba”, Abdull da ya san idanun ƴan mata yanzu a buɗe suke ya ce “Asma’un ce ke da ƙarancin wayewa? Kai dai ka binciki matsayinka a zuciyarta, don wannan kukan da take saboda an ce tana da ciki ba banza ba.”
Da ace Abbas bai mutu a kan son Asma’u ba, da tuni ya gano abin da Abdull ke son nuna masa, sai dai duk da haka jikinsa ya yi sanyi, mafarin gabaɗaya hankalinsa ya karkata zuwa gida, duban Abdull ya yi “Ka ga bari in je gida”, sosai Abdull ya lura da sanyin jikinshi, amma sai ya basar ya ce “Ya kamata dai.”
Sallama suka yi, Abbas ya hau mashinɗinsa ya nufi gida.
Asma’u kuwa falo ta dawo kan kujera bayan ta gama kukan, kwantar da kanta ta yi bayan kujerar ta lumshe idanu, tambayar ba zata ce zuciya ta jefo mata,inda ta ce ”Yaushe na yi sakaci har ciki ya shige ni”, tunawa da a ƴan kwanakin da suka shude ta sake ma Abbas fiye da zato ne ya ba ta cikakkiyar amsar tambayarta, don haka ta ƙudiri ya gama ganin farin fuskarta ta hanyar faɗin “Ka ci taliyar ƙarshe Abbas, na rantse sai na gasa maka azabar da dole ka rabu da ni, kuma wannan cikin ko da bala’i sai ya fita jikina.”
Ƙarar tsayawar mashindinsa ce ta katse mata zantukan da take, miƙewa ta yi ta koma bedroom ta kwanta, don bata kaunar ganin shi kusa da ita, sai dai ta gudu bata tsira ba, yana shigowa kai tsaye bedroom ya nufa tare da hayewa kan gadon, cike da kulawa ya ɗago mata kai ya ɗora a kan cinyarsa, kamar a bin tsiya ta maida kanta a kan pillow, dubanta ya yi kamar maraya “Bakya son nan ɗin”, hannunsa na nuni da cinyarsa lokacin da ya ƙarashe maganar,
Idanunta a rufe ta ce “Eh bana so”, kai ya ɗan gyaɗa “Toh shikenan, amma kin sha maganin kuwa?”, amsa ta ba shi “Ban sha ba”, ya ce “Saboda me?”, ta ce “Saboda bana ra’ayi.”
A hankali ya lumshe idanu domin haɗiye dafin da ya game mashi zuciya a dalilin wannan gadararriyar amsar da ta ba shi. Shi kam yau ya ga ta kanshi duk da ba wannan ne farau ba a irin gwalishewar da take mashi.
Cikin dakiya da son maida komai ba komai bane ya duƙar da kansa saitin fuskarta har tana jin numfashinsa, sumbatar ta ya yi a kumcin ya kuma ce “Ok toh Asmy, duk lokacin da kika yi ra’ayin don Allah ki sha, ko dan babyna da ke jikinki”, yana janye kanshi ta sa hannu ta goge inda ya sumbace ta, murmushin yaƙe ya jefe ta da shi lokacin da ya sauka daga kan gadon.
Falo ya koma ya kwaso magungunan da kuma abincin da ya karɓo mata gidansu yanzu da ya shigo unguwar, kan stool ɗin gadon ya aje mata su, ba tare ya sake kula ta ba ya fito ɗakin, kan plastic chair ya zauna a tsakar gida. Saƙawa da kwance yadda zai lallaɓa ta ya shiga yi, duk da ya fahimci akwai wani abu a ƙasa, sai dai tsananin son da ya ke mata ya makantar da shi ganin wannan abin, a ransa ya ce “Allah ga ni gare ka”, don baya iya misilta damuwar da ke ransa.
Yana nan zaune aka fara kiran la’asar, alwalla ya yi sannan ya koma ɗakin. Filon da Asma’u ke kwance ya ɗan buga a hankali “La’sar ta yi, ki daure ki tashi ki yi sallah.”
Yana tafiya ta fito itama, jirin yunwa da kuma zazzaɓi na ɗibar ta ta shiga banɗaki ta fito, daƙyal ta yi alwala ta koma falo ta zauna, wayarta dake gefenta ta ɗan latsa, missed call ɗin Aunty ta gani har biyu, kiran number ta yi ta sa handsfree, bayan Aunty ta ɗaga ne ta tambaye ta “Asma’u ya jikin?”, sai da ta matse hawayen da suka cika mata idanu sannan ta ce “Da sauƙi”, daga can Aunty ta ce “Madallah, kun je asibiti ko?”, ɗaga kai ta yi kamar suna gaban juna “Eh mun je” da ajiyar zuciya ta ƙarashe maganar, Aunty na ji ta ce “Kukan me kike?”, amsa ta ba ta da “Aunty ban da lafiya sosai”, lallashinta Aunty ta yi, bayan Asma’u ta tsagaita kukan Aunty ta tambaye ta “Me kike so na aiko maki da shi?”, dan ta san tatsuniyar gizo bata wuce koki. Tun da Asma’u ta fara rashin lafiya bata jin ra’ayin komai sai kwaɗon tuwon ruwa, don haka ta faɗa ma Aunty shi take so, Auntyn kuma ta yi mata albishir da nan da kwana biyu Nafisa zata kawo mata, ta kuma ce duk abin da take so ta yi ma Maman Abbas magana, tana da yaƙinin za a kawo mata, “Toh” kawai ta ce, amma ko buƙatar abu zata kashe ta ba zata iya yin magana gidansu Abbas a kawo mata ba, duba da marabar da take nema da ɗansu. Suna gama wayar ta mike ta yi sallah dakyal, a kuma kan abin sallar ta zame kan ta kwanta.
A takaice dai da kunci suka karashe wannan wuni ita da Abbas, duk da kokarinsa na ganin ta dayaye, amma ta ƙi, abinci da magani kuwa ba wanda ta ci, saboda bata ma jin yunwar, sai dai ko kusa ba ƙarfi a jikinta.
Cikin dare tana ta juye-juye ƙishirwa ta taso mata, yunƙurawa ta yi ta tashi zaune, Abbas da ke lura da duk wani motsi nata ya tashi zaune shi ma “Ko zaki sha ruwa?”, kai ta ɗaga alamar “Eh”, tunda ta fara rashin lafiya yake shigo mata da ruwa, kan stool ya miƙa hannu ya ɗauki jug da ƙaramin kofi ya tsiyaya mata ruwan, da hannunsa ya bata, ba musu ta sha, saboda a yanzu duniyar ta mata ƙunci, zafin da jikinta ke yi ma ya ishe ta, bare ta yi mashi wulaƙanci, tana gama shan ruwan ya taimaka mata ta kwanta, sannu ya cigaba da yi mata duk da bata amsawa. Haka dai suka kwana ba tare da ɗayansu ya yi baccin kirki ba.
Washegari da kanta ta nemi magani, don ita kaɗai ta san azabar da ta sha cikin dare, sai dai batun ƙudirinta na ƙin wannan ciki yana nan daram, don ba wata maganar arziki tsakaninta daAbbas.
Ta ɓangaren shi kuwa ya ɗaukar ma ransa cusa mata son wannan cikin da kulawarsa, da rana yana dawowa ya same ta kwance a kan kujera, ɗan duƙawa ya yi ya ce “Asma’u tashi kisha magani”, taimaka mata ya yi ta tashi zaune, da kanshi ya bata magunguna ta sha, zama ya yi gefenta ya ɗan riƙe hannunta, sassauta murya ya yi “Asma’u, rashin walwalarki tsakanin jiya da yau ya sa jikina yin sanyi, sai nake ganin kamar saboda cikin dake jikinki ne, ko dai bakya murna da cikin ne”, janye hannunta ta yi ta dube shi “Dama ta ya zan yi murna da shi?”, duk da ba alamun wasa a maganarta, amma shi sai ya yi dariya gami da faɗin “Rashin murna da shi fa kamar bakya son shi ne”, ta ce “Eh”, ya ce “Bakya son cikin?”, ta kuma cewa “Eh”, ya ce “Bakya sona kenan!”, gajeren murmushi ta yi wanda ya kasa gane ma’anar shi, dariya ya yi, gami da sake ruƙo hannunta, “Asma’u idan bakya so na ai ban san ya zan yi ba”, a ranta ta ce “Gwara kuwa tun wuri ka san abin yi”, a zahiri kuma guntuntun tsaki ta ja, lokaci daya kuma ta yamutse fuska, wanda hakan ke nuna surutunsa na hau mata kai, ɗan basarwa ya yi kamar bai lura ba, zayyana mata irin son da yake mata ya shiga yi, ita kuwa da shi tatsuniya duk ɗaya.
Haka wannan wuni ya kusa shuɗewa Abbas na ta nan-nan da ita, ita kuwa sai muguwar sakayyar gwalishewa take mashi, burinta kawai ya bar gidan ta ɗauki waya saboda ta ɗan ji sauƙi.
Da yamma liƙis ya yi shirin fita, zama yi a gefen gado yana kallon ta, a lokacin ita kuma tana kwance “Asma’u fita zan yi”, ran ta sal ta ce “Da dai ya fi”, hannunta dake cikin nashi ya ɗan matsa da ƙarfi ya ce “Da alamun kin gaji da zamana a gidan ko”, ɗan rumtse idanunta ta yi, alamun ta ji zafin matsar da ya yi mata.
Dariya ya yi gami da faɗin “Ragguwa kawai, me ye cikin wannan matsar idan aka haɗa da zafin haihuwa”, ɗan kwantowa ya yi, wanda hakan ke nuna baya son fita.
Kamar zata yi kuka ta Jujjuya kanta akan filo “Dan Allah ka rabu da ni in huta”, har a cikin ranta bata yi haka dan shagwaɓa ba, amma hakan sai ya ƙayatar da shi, ɗan turo baki ya yi shi ma, lokaci ɗaya kuma ya shanye idanu, cikin sigar shagwaɓa shi ma ya ce”Toh madam, bari na tafi tunda kora ta kike.”
Wani irin bambarakwai ta ji, wai namiji da sunan (Mom), duk da ƙayatarwar da na shi salon ya yi, amma daga kwancen ta taɓe baki “Tooo! Baka dai yi kyau ba”, ido ya zaro “Ko?”, ta ce “Eh”, ya ce “Toh shikenan, amma fa ke naki salon ya yi kyau, idan na dawo zaki koya mani irin shi”, shiru ta yi dan ta fahimci bai ji daɗi ba.
Miƙewa ya yi sannan ya tambaye ta “Me zan siyo maki idan zan dawo?”, amsa ta ba shi da “Bana son komai”, kai ya gyaɗa “Ok.”
Gidansu ya nufa, inda ya samu Ummansu da ƙannenshi ƙumshe a ɗaki saboda sanyin da ake sararawa, zama ya yi kan hannun kujerar dake kusa da ƙofa, gaishe da Ummansu ya yi “Ina wuni”, amsawa ta yi daga gefen gadon da ta ke zaune tare da tambayar shi “Ya Asma’un?”, ya ce “Da dauƙi”, ta ce “Tana dai cin abinci ko?”, dan ta san wani laluayin bai barin cin abinci. Faɗa mata ya yi “Tana ɗan ci”, ta ce “Toh da sauƙi tunda tana ci”, hira suka cigaba da yi hadda ƙannensa da duk sanyi ya sanya su ladabi, bai tashi tafiya ba sai ƙarfe shida saura, ya miƙe kenan Abeeda ta dawo daga aiken da Ummansu tayi mata.
Bayan sun gaisa ne ya ce “Yauwa Abeeda, dan Allah shara da wanke-wanke zaki yi Asma’u gobe idan Mai duka ya kai mu”, a tsiwace ta ce “Kam, sai dai ciwon ya kashe ta”, baki ya buɗe “Kai Abeeda, dan Allah”, buga cinya ta yi “Na ce fa ba zan je ba, saboda ba ragi a tsakanina da mai girman kai”, Ummansu na ji, amma bata ce masu kanzil ba, dan ta daɗe da fahimtar shi kanshi Abbas ɗin ba wata daraja yake da ita wurin Asma’u ba, bare kuma danginsa, jira kawai take ya faɗar damuwarshi da bakinshi.
Lallaɓa Abeeda ya yi akan ta je, “Toh” kawai ta ce dan bata son gardamar ta yi tsayi. Bayan tafiyarshi ta ce ma Ummansu “Wallahi ko ciwo zai kashe ta ba zan je ba Umma”, kai Ummansu ta girgiza “A’a, zuwa dole”, kamar Abeeda zata yi kuka ta ce “Umma toh sai in je, yarinya ƙarama ta yi ta wani sha mani ƙamshi”, ko kusa Ummansu bata son su fahimci ta san halin Asma’u, dariya ta yi “Toh ita da gidanta dole ta sha ƙamshi”, nan dai ta maida abin wasa, duk da sauran yaran ma sai faɗin baƙin halin Asma’u suke.
Abin da Asma’u ke so kenan, don so take dangin Abbas su tsane ta, ta haka ne zasu taya ta hurar wutar neman saki a wurin Abbas.
A can gidan kuwa tuni Asma’u dauki waya, da shigarta WhatsApp ba inda ta yada zango sai Group ɗin su na ƙasaitattun Mata, don group ɗin suna yawan magana a ciki.
Tambayar da ke ranta ta jefe masu “Dan Allah wa ya san maganin zubar da ciki?”, kankace me kuwa ta samu mabanbantan amsoshi, wanda mafi yawa nuna mata illar kuskuren da take shirin yi suka yi.
Inda wata ta ce “Ke ki gode ma Allah ma kin samu, mu kuma mu ce me?”
Wata kuwa cewa ta yi “Dan Allah cikinki ko ‘dan gaba da Fatiha ne ne ki haƙura da shi, idan ya so bayan kin haihu sai ki kai ɗan gidan marayu”. Wannan magana ta ƙona zuciyar Asma’u, a fusace ta ce “Ke kam baki iya magana ba, ni cikina ɗan halak ne, dan sai da aka shafa Fatihar sannan ubansa ya mallaka mani shi”, waccan matar ta ce “Au, kuma shi ne zaki ha’inci ubansa ki yi mashi asara? Toh ki rufa ma kanki asiri ki bar cikinki, dan wasu na can na nema.”
Sauran ƴan group ɗin kusan sun goyi bayan matar, sai dai sun nuna mata bai kamata ta faɗa ma Asma’u haka ba.
Ita kuwa da ta ga za a cinye ta ɗanya sai ta rufe data ta kwanta kan kujera zuciyarta cike da ƙunci, cikin ƙanƙanen lokaci kiran Khadija ya shigo, daga kwancen da take ta ɗaga kiran “Asma’u meke damunki ne?”, abinda Khadija ta fara fa’da kenan, saboda ta ga hatsaniyar.
Kuka Asma’u ta fashe da shi “Khadija me ya sa ba zaki fahimce ni bane, bana son Abbas, bana ƙaunar haɗa iri da shi”, kasa magana ta yi saboda kukan da ya ci ƙarfinta, hakan ya sa Khadija faɗin “Ya isa haka, gobe Insha Allah zan shigo kawai.”
Washe gari tun wurin ƙarfe shaɗaya Khadija ta zo, lokacin kuma Abbas nan, sosai shi da Asma’u suka yi murna da zuwanta, cike da farinciki ya dube ta tun kafin ta zauna akan kujera “Haba Khadija ba zuwa ba aike.?” Haƙuri ta ba Abbas akan karatun da ta fara ne ya hana ta fita, fatan Alkhairi Abbas ya yi mata sannan ta zauna suka gaisa.
Fita ya yi ya basu wuri, Khadija ta dubi Asma’u dake hakimce kan kujera ta ce “Sannu hamshaƙiya mandiya”, sosai ta ba Asma’u dariya, gaisuwar yaushe gamo suka yi, sannan suka dasa hira.
Suna cikin hirar ne Abbas ya dawo, tun a tsakar gida ya jiyo shewar Asma’u, cike da jin daɗi ya shigo falon, duban Khadija da ke gyara mayafi ya yi “Yau kam na ji daɗin zuwanki Khadija, saboda madam ta saki jiki.”
Dariya kawai Khadija ta yi, Asma’u kuma sai ta bi shi da ƴar harara, bedroom ya shiga tare da kiran Asma’u, sai da ta murguɗa baki sannan ta amsa, kai Khadija ta girgiza mata alamar ta bari hakan bai dace ba, “Ke” ta faɗa, wanda ke nuna Khadija ta rabu da ita.
Samun Abbas ta yi tsaye yana jiran ta, fuskarsa cike da annuri ya ce “Idan kina nishaɗi kin fi kyau”, ƙoƙarin riƙo ta ya yi, sai ta ja baya “Ka manta? ” ta nuna ƙofar falo, kai ya jinjina “Okay Khadija ko?”, shiru ta yi, ɗan matsowa ya yi “Ƙaunarki sa wa take na manta da kowa Asmy”, murmushin da iyakarsa kumci kaɗai ta yi, da dai ya ga taƙi ba shi haɗin kai sai ya faɗa mata fita zai, “Okay” Kaɗai ta ce, gami da juyawa zata fita, riƙo ta ya yi “Me zan siyo maku toh.”
Amsa ta ba shi “Ka siyo mana alala”, sannan ta fice, bayanta ya biyo, suka taras Khadija na waya.
Zama Asma’u ta yi, shi kuma ya fita. Bayan Khadija ta gama wayar ne ta nade kafarta daya akan kujera, maida dukkan nutsuwarta ga Asmu’u da suke fuskantar juna sannan ta jefo mata tambaya “Asma’u, me ye nakasun Abbas da kike neman maraba da shi…?”
am okay
am okay ina fatan alkhairy.