Skip to content

Cikin Baure | Babi Na Biyu

4.8
(4)

<< Previous

Kara goge fuska na yi da hijabi gami da shanye idanuna ta yadda Nas zai gan su da annuri idan na yi arba da shi. Sai dai kash! Ban ankare da takun da na ji ba nashi bane sai da babbar ‘yarsa mai suna Salma ta bude kofa, Sanye take cikin uniform na islamiyya mai ruwan blue.

Ba don na so ba na sakar mata murmushi lokacin da ta dube ni da girmamawa ta ce “Ashe Aunty Asma’u ce”, a takaice na ce “Ni ce kuwa”, kasan raina kuma cike da taikaicin faduwa kasa ba nauyin da na yi, domin har ga Allah ban tsammaci ba Alhaji Nas ne zai bude mani kofa ba.

Cikin salon cusa kai na sakalo kafadarta duk da shekarunta ba za su wuce goma ba, cikin gidan muka nufa, lokaci daya kuma muna magana kamar dama mun saba da juna.

A matsakaicin farfajiyar gidan muka hadu da Aishar Nas, fuskarta dauke da fara’a ta tarbe ni, inda ta ce “Amarya ce da kanta?”, ni kuwa ban so ta ambaci amarya ba, domin kalmar zata iya hana sakona isa wurin mijinta, koda yake ta baya ta raggo, katin bikina da na kawo mata fa?, a raina na ce “Allah ka iya mani”, tare da sakar mata murmushin ya’ke. Idanuna akan Salma lokacin da ta nufi falo na gaishe da Aishar, bayan ta amsa ne ta yi mani iso nima a kayataccen falonta da ke fitar da kamshi mai sanyaya da zuciya.

Zama ta yi tana fuskantar kujerar da nake zaune, a wannan karon ma ban so haka ba, domin zata hana ni kashe kwarkwatar ido a falonta da maroon and golden colours suka kawata komai na cikinsa.

Bayan mun gaisa ne na shiga tambayar kaina “Na ba ta katin ko kada na bata?”, amsar da ta fi kwanta mani a rai ita ce kawai na ba ta, tunda ban shaku da ita ba bare na fada mata wani abun daban, kuma a yanzu haka idanunta na akan katin da nake ta murza yatsana babba da manuni a gefensa.

Tasowa na yi na mika mata katin, kafin ta karba hadaddiyar wayarta dake gefenta ta dauki ruri, sosai wayar ta birge ni, nan na kara tabbatar da mijinta na ji da ita, don ko shakka babu shi ya siya mata ita, karbar katin ta yi sannan ta dauki wayar. Amsa kiran ta yi, ni kuma bayan na koma wurina da zama na daura idanuna a bakin dakakken lace dinta peach, wanda aka kawata flowers din jikinsa da purple colour.

Jin ta gama wayar ne na maido dubana gare ta, a lokacin kuma katin take karantawa a kasan ranta, inda ni kuma na shiga karanta kyakkyawar fuskarta domin na banbance wanda ya fi kyau a tsakanin ni da ita.

Ita din bakar bafullatana cewadda rayuwar jin dadi ta kara fito da asalin kyawunta. Ni kuma Asma’u buzuwa ce fara da rayuwar talauci ta disashe haskena, a yanzu kam ta fi ni kyau, amma idan Allah ya hada ni aure da mijinta na san sai na yi mata fintinkau a kyau.

Ina shirin rokon Allah ya ba ni mijinta ko ta wane hali ne ta dakatar da ni da fadin” Ashe bikin ya zo?”, murmushi mai sauti kadai na yi tare da dan noke kai alamun jin kunya, dorawa ta yi da “Allah ya sanya Alkhairi”.

A gaggauce cikin raina na ce “Ba Amiin ba”, don bana bukatar albarka ko ya take a cikin aurena da Abbas.

Murmushi na sake yi tare da maida hankalina ga duka yaranta da suka karaso tsakiyar falon a cikin shirinsu na Islamiyya. Suma din tubarakallah suna da kyau kamar mahaifansu.

‘Yarta ta biyu mai suna Amrah ce ta karbi katin “Mom katin bikin waye?”.
Harara ta bata maimakon amsa “Ba a gaida mutane sai tambayar gulma?”.

Kusan a tare suka gaishe ni, bayan na amsa musu ne na dubi Amrah da ke duba katin, yadda take karantawa cikin in’ina ne ya tabbatar mani da ba sosai ta iya karatu ba. Sosai nake son yarinyar, saboda duk cikin su ita kadai ta biyo babanta, kuma ganin ta ne ya tunatar da ni abin da ya kawo ni gidan.

Salima ce na ga ta yi gaba bakinta na fadin “Ku fito mu jira Abba a waje”, nan na fahimci yanzu shi ma gogan zai fito, don tun a bakin layi na ga motarsa.

Sai da Aisha ta kara gyara ma sauran yaran biyu hijabi, sannan suka fice tare da Amrah.

Tashi Aishar itama ta yi ta shiga bedroom dinta, inda tunda na shigo nake jiyo motsi a can, muryar Nas na ji yana magana, sai dai ban san me yake cewa ba, gira na dage tare da kara daidaita nutsuwata.

A tare suka fito, shi yana gaba ni ita tana baya, shi din yana da kwarjinin da duk sadda na ganshi sai gabana ya fadi.

A daburce na gaishe shi, ba tare da ya kalli inda nake ba ya amsa cikin jin kai “Laafiya lau”.

Ficewa ya yi daga falon, har a lokacin kuma Aisha na biye da shi, ni kuwa bakincikin yadda ya amsa mani da kuma kuma kishin rakiyar da Aishar ta yi mashi ne suka turnuke mani zuciya, ban san sadda na mike nima na fita ba, ina cikin zura takalma Aisha ta dawo cikin gidan, “Ba dai tafiya ba”, ta fada tana kallon fuskata da ke kicin-kicin , ce wa na yi “Aikuwa dai”, ta ce “Ko ruwa baki sha ba?”, kai na girgiza “A’a nagode”, fatan Alkhairi ta kara yi mani tare da tabbacin zata zo bikina idan ta samu dama.

A gaggauce muka yi bankwana na fice gidan, can na hangi Nas ya kusa isa inda motarsa take, cikin sauri na rika tafiya, sai dai lokacin da na je dab da motar har ya ja yaranshi sun tafi, tsaye na yi ina kare ma bayan motar kallo, bangare daya kuma idanuna na fitar da hawayen bakinciki, don alamu sun nuna zan sha wahala a kan farautar soyayyarsa, jiki ba kwari na kama hanyar gidanmu, cikin raina ina ta addu’ar neman sassaucin Allah akan tsaka mai wuyar da so ya jefa ni.

Haka kwanakin bikina da Abbas suka cigaba da matsowa, ‘yan uwa na kusa da na nesa sun zaku ranar bikin ta zo, ni kuwa duk na fice hayyacina, don tamkar ranar mutuwata na dauki ranar daurin aurena.

A daren biki bayan mun gama bridal shower ni da kawayena ne na tafi gidan mahaifina, kasantuwar a can za’a dauke ni zuwa dakina, don haka ban san adadin mutanen da suka je taya Aunty murnar aurena ba.

A ranar walima nake tambayar makwabtanmu Aishar Nas ta zo?.

Suka ce ba su gan ta ba jiya da yau, ban ji komai ba, sai ma na yi fatan Allah ya sa bata ba mijinta katin bikin ba.

Yanzu dai gani a dakina, inda nake tababar anya soyayyar Alhaji Nas zata bari na zauna lafiya da mijina..?

Batun gaskiya! Ba soyayyar Alhaji Nas kadai ba, hatta shi Abbas din ta bangarensa bana tunanin tsaurin ra’ayi irin nasa zai bari mu zauna lafiya, domin shi mutum ne wanda bai damu da sharholiyar duniya ba, duk wani abin da ba za’a ribaci lokaci a cikinsa ba da wahala ya halarce shi. Ko hidimar bikinmu da aka yi ba inda ya halarta bare kuma abokansa, ni da kawayena ne kadai muka yi ta fadi tashi wurin hada party kamar bikin diyar roba, hakan kuwa ba karamar tsanarsa ya kara mini a zuciya ba, duk da dai shagalin bikin ba da son raina aka yi shi ba.

Da wannan tsana da ke ta mamayar zuciyata ne nake hasaso rayuwar aurenmu mai cike da kuna, domin ji nake ba zan iya faranta ran Abbas ba saboda ban yi shirin zaman aure da shi ba. Yadda nake ta sa’ka irin gubar da zan lasa mashi ce take ta bayyana a fuskata, domin an ce labarin zuciya a tambayi fuska.

Hakan ya sa kawayena da ke cike da bedroom suna jiran ango da abokansa zaulaya ta, saboda shirun nawa ya yi yawa, daya daga cikinsu mai suna Sailuba ce ta ce “Uhm! Su Asmy zullumi ya sa an yi jugum”, dariya sauran suka kwashe da ita saboda sun fahimci inda maganarta ta dosa, Sa’adatu kuwa ta ce “Ba dole ta yi jugum ba, yau zata ji abin da muke karantawa a novels ai”, gabadaya dakin suka kwashe da wata dariyar.

Ni kuwa dariyar yake kawai nake, don akwai kamshin gaskiya a maganar kawayena. Sosai kuwa hada zullumin yadda zan kasance da Abbas a wannan dare, kara tunzura zuciyata ta yi har na fara tambayar kaina “Anya ma zan yadda Abbas ya kasance tare da ni a matsayin mata?”, don hakan daidai yake da rusa tanadin da na yi ma Alhaji Nas, saboda har na fara tsara yadda zan kashe aurena da Abbas din.

Kafin na samu amsar tambayar da na yi ma kaina ne Khadija dake zaune a gefen gado ta jefo mani wata tambaya, kasantuwar dakin ya rage daga ni sai ita, “Wai wannan shiru-shirun na lafiya ne Asma’u?”, domin gaskiya ba haka kawayenmu suke ba, duk wadda aka yi ma aure kusan sai ta fi kawayenta zakewa a daren walima, saboda duk maitar auren muke.

Take tambayarta ta ‘bubbugar mani da hawaye masu kaurin gaske, cikin muryar kuka na rada mata “Kadija bana son Abbas aka aura mani shi”.

Baki bude ta cigaba da yi mani kallo mai dauke da tsantsar mamaki, sai dai kafin ta yi magana muka ji muryar daya daga cikin kawayenmu na fadin “Ga ango nan fa”, tana rufe baki kuma muka ji takun dawowar su ciki.

Da sauri ta mike tare da sa hannayenta biyu ta share mani hawaye, lokaci daya kuma ta jawo mayafin dake kaina ta rufe mani fuska.

“Angunan sun shigo?”, ta tambaye su cikin sigar basarwa a lokacin da suka shigo dakin. Sailuba ta ce “Ango ne kadai ai, kuma gashi can suna magana da kanwarsa a waje”.

Jin wannan magana ya sa na dan ji saukin faduwar da gabana ke ta yi, don da alama ba yanzu Abbas zai shigo ba tunda ba abokansa.

Kamar daga sama muka ji sallamar shi, su kuwa tuni dama Khadija ta ce su rage hayaniya. Cikin bedroom din ya shigo tare ta tsayawa a bakin kofa. Khadija da ta fi su sanin shi ta yi magana cikin sigar zaulaya, inda ta ce “Ango ka sha kamshi”,

Dariya na ji ya yi tare da fadin “Kawayen Amarya ashe baku tafi ba?”, Sailuba kuwa ta yi karaf ta ce “Ai muna nan sai mun siyi baki”.

Ba kawayena da ke ganinsa ga da ga ba, hatta ni da fuskata ke rufe da mayafi na ji alamun dariyar yake ce Abbas ya yi gami da fadin “Lallai”.

Juyawa ya yi ya fita, su kuwa tuni jikinsu ya yi sanyi, Sailuba ce dai uwar magana, duban su ta yi ta ce “Anya wannan bakin zai siyu kuwa?”.
Wata wadda murar da take ta hanani gane muryarta ta ce “Da wahala kam”.

Muryar Abbas muka ji a falo yana kira Khadija, daga nan inda take ta ce “Ni Khadijar?”, ya ce “Eh, don Allah magana nake son mu yi dake”.

Kallon juna duk wanda ke beroom din suka yi, Khadija na fita Sailuba ta bude baki zata yi magana, ina jin wadda ke kusa da ita ta dan bugo ta alamar ta yi shiru, saboda muna jiyo muryar Abbas a tsakar gida.

‘Kus-‘kus suka cigaba da magana, ni kuwa zafin da ke raina bai bar ni ma na ji me suke cewa ba. Ba’a fi minti biyar da fitar Khadija ba sai gata ta dawo, cikin murya mai dauke da mutuwar jiki ta ce musu “Toh yan siyen baki sai a maida kudin a jaka, ango ya ce bai zo da abokansa ba, don haka ku tashi mu kara gaba”.

Sosai wannan magana ta daki zuciyata. Ni Abbas zai tozarta ma kawaye?, A fusace na dage mayafina na kuma ce “Kamarya bai zo da abokai ba, ko yana nufin shi kadai ya shigo?”, Khadija da ta san wutar kinsa dake ruruwa a raina ce ta inginza ni faɗin haka ta ce “Ya ce su abokansu basa rakiyar ango, saboda hakan bai dace ba wai”, tana rufe baki ta karasa yafa mayafinta gami da daukar jaka.

Zan sake wata magana Sailuba ta toshe mani baki, cikin taushin murya ta ce “Kin ga mu ba bakin tsanani bane, mijinki yana da gaskiya, wurin siyen bakin nan ana abubuwan da basu da ce ba, don gabadayanmu mun shaida haka, don haka kada ki ji komai”.

Kamar zan yi kuka na ce “Haba Sailuba, wannan cin fuska ne kawai Abbas ya yi muku”.

Kusan a tare suka ce “A’a”, sosai suka nuna mani hakan bai wani bata ransu ba, duk da na san fada kawai suke. Jiki ba kwarin da suke ta hada kayansu ne ya tabbatar mani da haka, bayan sun kimtsa ne suka dafa ni tare da yi mani bankwana, ina murmushin ya ke na ce “Sai yaushe?”

Sakina ta ce “Sai mun fidda rana”, don Al’adar kawayenmu bayan biki suna haduwa su zo gidan Amarya. Fitowa suka yi in banda Khadija, gam na rike hannunta na ce “Abbas ya tozarta ni”, kai ta girgirza “Ki yi hakuri, zamu yi magana a waya kafin na dawo”. A gaggauce ta rika lallashina, inda ta nuna mani da in cire batun kiyayyar Abbas a raina tunda ga shi har mun yi aure. Jin ta kawai nake har ta gama ta tafi, amma kiyayyar Abbas tuni ta samu mazauni na dindindin a zuciyata. Musamman da ya ja mani abin faɗi a wurin kawayena, don ko rantsuwa na yi ba zata zama kaffara ba sai sun yi ta yawo da ni a gari suna cewa na auri miji dan ‘kabalu, saboda haka muke ce ma samarin kawayenmu masu tsaurin ra’ayi.

Ko da yake, ina jin zafin zubar da ajin da Abbas ya yi mani ne kawai don yana shi, da a ce Alhaji Nas ne ba zan ji haushi ba, a bangarena ma ba zan yi gigin kawo kawayena ba don mugun kishinsa nake.

Motsin Abbas na jiyo a zaure yana rufe gida, don ba wata tazara ce a tsakanin dakina da zauren gidan ba.

Na tabbata da ina son Abbas zan yi farinciki da shigowar sa, amma da yake bana son shi sai nake jin kamar gudu daga gidan.

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

1 thought on “Cikin Baure | Babi Na Biyu”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.