Skip to content
Part 31 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

A kidime na ce “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un yaushe?”

“Yanzu wai.” ta amsa ni a sanyaye

“Aunty wai mutuwa dai irin wannan, wacce na sani?” na yi tambayar mamakance

Ba a mamakin mutuwa, amma ni kam na yi mamakin mutuwar Aunty Adama, kodayake ba iya mamaki kawai na yi ba, har yanzu ma ban gama yarda ba.

Daga ni har su Yafindo duk mu ka yi cirko-cirko a tsakar gida cike da jimami

Jiki ba kwari Aunty ta koma daki, Sai na bi bayan ta

Tsaye na cimmata ta kalli gabas, fuskarta na bayyana tashin hankalin da take ciki

Juyowa ta yi sosai tana fuskantata kafin ta ce “Maryam duniya na ba ni tsoro, idan mutuwa ba ta zama wa’azi ga al’umma ba, babu wani abu da zai zame musu wa’azi na kasa yarda Mamansu Huzaima ta rasu. Kai jama’a Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!”

Ni dai bakina ya mutu, ba na jin ko mutuwar mahaifiyata ta girgizani kamar ta Aunty Adama, kodayake lokacin ba ni da wayau amma wannan mutuwa kam ta yi min bazata

” Aunty za ki je? “na tambaya dakyar kamar mai koyon magana

” Dole. In Sha Allah gobe zan tafi. “

Fuska na narke tare da fadin” Ni fa? “

” Ki yi hak’uri Maryam, Hammah ya ce kar ki shiga gidan nan yanzu. Ba na son wani abu ya kara samun ki kuma. An samu dakyar kin warware. “

” Amma Aunty a nan ba zan ji dadi ba”

“Na sani. Ki yi hak’uri, ga Bingel nan, ke ce kin ki sakin jiki da ita. Da yanzu kun saba.”

“Ita da ba ta zama” na kuma fada a shagwabe

“Ki yi hak’uri na ce”

Maganar da Baffa ke yi a waje ne ya sanya ban kara cewa komai ba.

Shi ma jimamin mutuwar Aunty Adama yake da kuma maganar tafiyar Aunty gobe.

Tun daga wannan lokacin ba iya mu kadai ba, gidan ma babu wanda ya kara sukuni, kamar dai a nan aka haifi Aunty Adama.

*****

GANA

Misalin karfe sha daya na safe ta dakko wayarta lokaci daya kuma tana mita “Adama ba za ta canja hali ba, dama idan har ka ga kiranta, to tana cikin matsala ne, da zarar ta samu mafita shi kenan. Har kiranta na yi ba ta daga ba amma ko ta biyo.”

Jin wayar ta shiga ne ya sa ta katse mitar da take yi.

“Ina mai wayar?” ta yi saurin tambaya, saboda yadda ta ji namiji ya daga

“Mai wayar Allah Ya yi mata rasuwa”

Ta yi saurin sauke wayar a kokarinta na tantance lambar da ta kira

Ganin lambar Adamar ne dai ta mayar da wayar a kunnen ta hade da sanyata a hands free ta ce “Me ka ce?”

“Cewa na yi mai wayar Allah ya yi mata rasuwa.”

“Ban gane ta mai wayar ta rasu ba, kai kana ina?”

“Ina cikin mota.” ya kuma amsawa

“To ita me wayar fa?”

“Ita ma tana cikin motar.”

“To ba ta wayar.” cewar Gana a hanzarce.

“Na ce miki Allah Ya yi mata rasuwa.”

“To wai a motar ta rasu?”

“Eh. A nan cikin tafiya muka lura kamar ba ta numfashi, ana taɓa ta Sai a ka ga ta rasu”

Ta rufe bakin da ta bude kafin ta ce “Rasuwa, mutuwa fa kenan kake nufi. Kana nufin wai Adama ta mutu, mutuwa irin wacce ba a dawowa?”

“Wlh kam, har ma an sanar da mijinta” mutumin ya amsa.

“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!” Cewar Gana hade da yanke wayar, ta zuba mata ido tana kallo, ta kasa gasgata abin da ta ji

“Adama ta rasu?” ta kara maimaitawa a hankali.

“Kai a’a wlh” ta fada hade da kara kiran lambar Aunty Adama

Mutumin dazu ne dai ya kara dagawa

“Ba wata mace a kusa da kai” Abin da ta fada kenan ba tare da ta amsa sallamar shi ba

“Akwai”

“To ba ta wayar”

“Don Allah da gaske mai wayar nan ta rasu?” Aunty Adama ta tambaya

“Eh wlh. Dama tun da aka fara tafiya ta dukar da kanta da mu ka ga abun ya yi yawa ne, shi ne aka taba ta, sai kawai mu ka ga ta fadi”

“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un”! “

Cewar Aunty Adama hade da yanke kiran, kai tsaye wayar Karima ta kira. Ƴar Aunty Adama ta fari.

“Karima! “

Cikin kuka Karima ta amsa

“Innalillahi die Wa’inna IlaihirRaji’un! Da gaske dai Adama ta rasu. Kina ina yanzu? “

Cikin kuka Karima ta ce” Ina cikin mota”

“Har kin tafi kenan?”

“Eh.” Karima ta amsa

“Ke kadai ce?”

Karima ta kalli maigidanta wanda yake zaune kusa da direba kafin ta ce “Ni fa Abban Nana ne”

“Kina ji na Karima, idan wayarki akwai kara ki rage, ina son fada miki wani abu ne.” Cewar Gana kamar mai raɗa.

“Ina jin ki.” Karima ta fada idanunta a kan maigidanta.

“Idan kin isa gida. Ki shiga bedroom din Adama ki daga gadon ta, za ki ga wani wuri ya nuna alamar kamar an taba bude shi”

Karima ta shiga jinjina kai tana kara tattara nutsuwarta a kan maganar Gana

“To ki tona wurin nan, ki tabbatar kin tona shi, saboda akwai kokon kan jaki da na mutum da ta binne”

Cike da tsoro Karima ta waro ido, tuna ba ita kadai ba ce a motar sai kawai ta ce “To!” hawaye na gangaro mata

Gana ta yanke wayar cike da tashin hankali.

Ita kam tuni ta fara nadama a kan abin da suka aikata. Mutuwar Adama babban wa’azi ne a wurinta.

Mutuwa ba ciwo ba hatsari sai dai kwatsam.

“Subhnallah!” ta fada a bayyane.

Lokaci daya kuma ta juya zuwa cikin bedroom dinta da niyyar fitar da duk wani tsubbu, sannan kuma ta yi shirin tafiya Yola.

*****

Misalin karfe bakwai da rabi na dare gawar Aunty Adama ta iso Adamawa sunshine.

Hammah, Azeez, Bandi da wasu makotan Hammah guda biyo ne suka tarbo gawar Aunty Adama

Daga lokacin ne kuma zuriyar Aunty Adama ta rika sauka.

Zuwa karfe sha daya na dare duka ƴaƴanta biyar sun sauka a gidan.

A lokacin kam su kadai ne ba kowa.

Misalin karfe daya na dare Karima ta kwatsa musu maganar da Gana ta fada mata

Hankalinsu ba ƙaramin ta shi ya yi ba.

A cikin daren suka dage gadon suka shiga tona rami daidai saitin da suke tsammanin a nan aka a binne kokon kan da Gana ta fada

Gawar Aunty Adama a gefe kwance yayin da yaranta biyar ke ta faman gini, idan wannan ta gaji sai ta ba wannan.

*****

Aunty Aisha ba ta iya jira gari ya waye ba, misalin karfe sha daya ta baro kauyensu zuwa guroje, daga nan ta hau motar Yola.

Shi ya sa karfe 9am daidai mai keke ya aje ta kofar gida.

A lokacin kofar gidan a cike yake, wannan ya kara tabbatar mata da lallai Adama ta rasu.

Farfajiyar gidan ma a cike, mutanen unguwa da kuma ƴan’uwan Hammah da na Aunty Adama.

Haka ta rika ratsasu har zuwa dakin Aunty Adama.

Tura kofarta ke da wuya ta ci karo da gawarta nade cikin likafni, wannan ya tabbatar mata da an riga an gama hadata sallah kawai za a yi mata, saboda akwai maza ma guda hudu a cikin dakin, ta san kuma masu daukar gawar ne

Gana, su Aunty Karima sai wasu ma fi kusanci da Adaman ne a cikin dakin.

Su Karima kam an ci kuka an yi gwaɓe-gwaɓe

Ta rabe a hankali ta ba mazan hanya lokacin da suke fita da gawar.

Su Huzaima suka kuma fashewa da kuka hade da rungume junansu.

Sosai ta ji tausayinsu ya kamata, basu saba da kowa ba sai mahaifiyarsu, da ita suke tonawa suke kuma rufewa.

Sunan sun yi aure amma kamar ita ce ke musu zaman auran, duk wasu matsalolinsu ita ce ke magance su. Su basu san su magance matsala da kansu ba.

Basu rainata ba, amma dukkansu babu mai shiga harkarta, iyakacinsu da ita gaisuwa idan sun hadu, saboda sai su zo su tafi ma ba ta basu shiga sashenta ba.

Idan dai sun hadu a tsakar gidan zasu gaishe ta.

Dama-dama Huzaima suna ɗan ɗasawa da Azeez, ita kam wani lokaci ta kan leko ta tambayi ko yana nan.

Bayan ita kam babu mai tambayarta Azeez.

Dole su yi kuka, saboda zasu sake sabuwar rayuwa, rayuwar da babu mahaifiyarsu a cikin ta.

Ita ta gaishesu hade da yi musu ta’aziyya suka amsa cikin kuka.

Sannan ta shiga gaishe da sauran mutanen cikin dakin, su ma suka amsa hade da yi mata sannu da dawowa.

Gana ta dora da “To a yafi juna dai Aisha. Adama dai kin ga sa’i ya yi. Don Allah a yi hakuri a manta baya, a yi hakuri a yafi juna”

Cike da jimami Aunty ta ce “Ai ba ta yi min komai ba.”

“Duk da haka dai, zama na shekara da shekaru dole a saɓa ma wani”

“Haka ne kam” mutanen da ke dakin suka fada gabadaya

“Na yafe mata, Allah Ya yafe mu ba ki daya”

“Amin Ya Rabbb!”mutanen da ke dakin suka kuma fada cikin jimami.

Aunty kuma ta gyara zamanta a cikin dakin zuciyarta a karye, duniya zancen banza har yanzu ta kasa yadda Mamansu Huzaima ta rasu.

Ba ta baro dakin ba, Sai da yan kai ta suka dawo.

Kafin ta karasa part din ta, Sai yanzu ta rika jin ina ma ta taho da Maryam ko ba komai za ta gyara musu part din nasu, ita kam ga gajiya ga nauyin ciki ba ta jin za ta iya.

Haka nan ta daure ta fara gyara dakinta, Sai kuma gasu Adda Halima sun shigo, da Adda Faɗi, sune suka taimaka mata ta gyara sashen tsab, a kuma bakinsu ne take jin wai an fitar da kokon kan mutum da na jaki a dakin Aunty Adama

A firgice ta ce “In ji wa?”

Suka sassauta murya kafin suka ce “Abin duniya ɓoyuwa yake yi Aisha. To a bakin kawarta wannan yar Maidugurin muka ji. Tana isowa babu abin da ta fara tambaya sai kun fitar da kokon kan jakin nan da na mutum din da na ce muku ku fitar kuwa. Take fadawa yaran”

Aunty da ta saki baki ta rufe tare da fadin “Waye ya saka mata kokon kan?”

“Yo wa zai saka mata? Ita ta tona rami ta binne abun ta saboda neman duniya, kawartar kuma Allah Ya matsi bakinta ta fada, shi ya sa yaran suka tura ta daki ai basu barin ta fito waje, kamar ta ruɗe.” cewar Adda Faɗi

Adda Halima ta dora da “Ai Adama ta zuba mulki gidan Hammah, babu mai raɓarshi daga ita sai yaranta, duk macen da ya auro Adama sai ta kore ta. Ke ce kawai kika fi karfinta. Ke ma din ba ta bar ki haka nan ba, tun da ga shi nan daga haihuwa daya sai yanzu Allah Ya kawo wani rabon”

“Ai tana can dai yanzu tana girbar abin da ta shuka, yaranta sai kuka suke. A zuciyata na ce dama ku kuka ya kama ba mu ba, ba ta bar ku kun rabi kowa ba sai ita, to ga shi ta tafi ta bar ku damu da kuka raina din. Matar nan fa ko zuwa mu ka yi gidan nan to ba ɓangarenta ba sai dai na Aisha. Wlh Halima da ana zuwa lahira a yo leke a dawo, yau kam da na gwada lekawa na ga yadda mala’iku suka tari Adama “

Adda Halima ta tuntsire da dariya, yayin da Aunty ta murmusa kadan tare da fadin” Don Allah Halima ku bar maganar nan. Ba a shiga tsakanin bawa da ubangijinsa. Sai ku ga Allah Ya gafarta mata duk wasu laifukanta, kuma fa wannan ma zato ne ko hasashe kila ba gaskiya ba ne”

“Zato kuma Aisha! Wannan kam ba zato, matar da aka ciro kokon kan mutum a dakinta, to komai ma za ta iya aikatawa.” cewar Adda Faɗi.

Aunty ta yi shiru cikin Nazarin maganganunsu, har yanzu ba ta yarda da an fitar da kokon kan mutum a dakin Adama ba, to me take da shi, amfanin me yake mata?

Idan har wannan maganar ta tabbata to ba ta san da kalar mutanen da ta kwashe tsawon shekaru tana rayuwa dasu ba, Hammah daga shi sai Allahnshi ya san abin da yake aikatawa. Ita kuma wannan an ce ga abin da aka fitar a dakinta.

Anya za ta ci gaba da zama a gidan nan kuwa, duk da Baffa ya ce mata ta hak’ura ta zauna, saboda Hammah ya tabbatar mishi da ya yi nadama abubuwan da ya aikata.

“To idan karya yake fa?” ta tambayi kanta da kanta

“Zan sanya wa duk wani motsi na shi ido, da zarar na gano abin da ban fahimta ba, zan kama gabana” ta kuma fada a cikin zuciyarta

Ta mayar da hankalinta kan su Adda Faɗi wadanda suke goge kujerun dining, ita ma sai ta haura sama domin samun damar watsa ruwa.

<< Da Magana 30Da Magana 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×