Skip to content
Part 1 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

BISMILLAH RAHMANIR-RAHIM

Adamawa State Nigeria
10:00 PM

Dougirie (80 units) na daya daga cikin manyan ugunwanni da mazauna cikin ta suka ci, suka kuma tayar da kai. Unguwa ce da ta hada manyan mutane, yankasuwa, manyan ƴan boko, da kuma manyan ƴansiyasa, tun daga kan gwamnoni, yan majilasu da sanatoci.

Manyan-manyan gine-gine da ke unguwar na daya daga cikin abin da ya kara kawata manyan titunan da suka ratsa kusan ko wace center.

A ko wane lokaci unguwar ta kan kasance shiru babu hayaniya, bare yanzu da agogo ya nuna karfe 10:00 na dare cif-cif.

Daidai lokacin Hamman Adama ne tsaye a cikin falon shi na kasa, hannayenshi du biyun goye a bayan shi, yayin da fuskar shi ke nuna tsananin bacin ran da yake ciki, bacin ran da ya sanya hancinsa kara budewa hade da dagawa sama.

Tsaye yake ki-kam kamar an zana daya, idanunsa da suka canja kala zuwa ja, ya kafe su a kan kayataccen lallausan rug carpet din da ke shimfide a tsakiyar falon.

Da sauri ya daga kai zuwa inda ya ji an taba kofar, kamar dama abin da yake jira kenan.

Saurayi ne dan kimanin shekara 27-28 ya shigo, sanye yake cikin farin wando Jeans da kuma farar shirt cotton mai guntun hannu wacce ta fito da dunkulallen jikinsa da ya sha gyme.

Tun kafin ya ce wani abu, cikin kakkausar murya Hammah ya ce “Where is my car key? ” ya kai karshen maganar ta shi hade da mika mishi dogo kuma jibgegen hannunsa.

Jin shiru bai yi magana ba kuma bai yi alamar yin maganar ba , cikin daga murya ya kuma cewa “AZEEZ! I’m talking to you, I said where is my car key?”

Wanda aka kira da AZEEZ din ya shiga shafa tarin bakar sumarsa wadda take fitar da wani kamshi mai dadin shaka.

Kafin ya ankara Hammah ya sauke mishi manyan yatsunshi a kan fuskar shi, marin da ya sanya shi saurin kifawa hade da tsaida duk wasu na’urori na jikinsa, ba yau ne Hammah ya fara marin shi ba, amma har yanzu ya kasa sabawa da marin nashi.

Ya nuna shi da murtukeken yatsanshi, lokaci daya kuma cikin hucin da ke nuna tsananin bacin ran shi ya ce “AZEEZ wlh kwanciyar hankalinka shi ne ka kai ni inda ka sayar min da mota, because na san ka siyar. Just let’s go!” ya kai karshen maganar hade da nuna mishi kofar fita.

Azeez wanda ya ji wani dummm! Lokacin daya kuma duhun da ya mamaye masarrafar ganin shi ya rika yayewa a hankali, kafin ya gama tantance komai, Hammah ya hankadashi da karfi zuwa waje, Hammahn kuma ya rufa mishi baya a zafafe.

Daga yadda suke sauka a kan entrance din za ka tabbatar da yadda zuciyarsu ke zafi, ku san a tare suka isa farfajiyar da aka jera motocin reras kamar na sayarwa. Yayin da yake hasken da ke farfajiyar gidan kamar rana, ya kara kawata su.

Da wani irin karfi Hammah ya bude kofar hade da tura Azeez front seat, zayawa ya yi driver seat ya shiga tare da fisgar motar, suka fice kamar walkiya, bayan da maigadin ya bude musu kofa.

Jiki ba kwari na sake labulen windows, lokaci daya kuma na ja jiki a mace zuwa kan kujera, zamana da sauke nannauyar ajiyar zuciyata ban san wanda ya riga wani ba.

Tun daga lokacin da Hammah ya shigo gidan dazu da yamma zuwa yanzu hankalina yake a tashe, ko Azeez da ya dauki motar ba na jin ya kai ni tashin hankali.

Sam ba na son abin da zai taba Azeez, yana matukar ba ni mamakin yadda Azeez ke sata, mutumin da ya taso cikin zallar arziki , bai rasa komai ba, amma ko bera a wajen batun sata sai dai ya zauna wurin Azeez ya dauki darasi.

Duk boyen da za ka yi wa kudi, ko kayan kudi, Sai idan Azeez bai zo wurin ba, idan har zai zo sha Allahu sai ya tono su, hancinsa kamar yana jin kamshi kudi.

Da sauri na mike jin takun sakkowar mutum daga kan stairs din da ya ratsa falon, kafin in yi wani yunkuri tuni sautin muryarta ya karade falon, “Ina za ki je? Tsaya!”

Cak! Na tsaya har zuwa lokacin da ta karasa sakkowa “Azeez din ya zo?”

Kamar munafuka haka na daga kai alamar Eh, lokaci daya ina cin karamin yatsana na dama.

Saboda na san ta san ya zo, kawai tana son tabbatar ma da kanta zargin da take min na zuwan Azeez din ne ya hana ni bacci

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ba tare da ta ce min komai ba.

Hakan ya ba ni damar sulalewa, tun da Allah Ya taimake ni ba ta yi fada ba.

Aunty

Da kallo ta bi Maryam har ta shige dakinta, wasu tagwayen ajiyar zuciyar ta sake saukewa lokaci daya kuma ta nufi kujerar da Maryam din ta tashi ta zauna.

A matsayinta na uwa, ba sai ta zauna ta bayar da labarin irin, kunci, daci, zafi, bakin ciki da bacin ran da take ciki ba gami da Azeez, a matsayin shi na ɗa daya tilo da ta mallaka tsawon shekarun auranta 27.

Azeez bai nemi komai ya rasa ba tun tasowarshi bai san babu, bare ace ko shi ne ke sanya shi sata, komai ya bukata yana samu, amma hakan bai hana shi yin sata ba. Za ta iya cewa da za a bayar da sarautar sarkin satar Nigeria to tabbas Azeez ya cancanta. Dadinta daya baya fita waje, satar tashi iya gida ce, idan har zai shiga, ba zai fita hannu banza ba, dole sai ya samu abun dauka. An yi maganin, an yi addu’ar, duk shekara sai ta je Saudiyya kuma Azeez na daya daga cikin manyan addu’o’inta, amma har yau shiru, Sai kamar abun ya yi sauki, Sai kuma ya dawo.

Ko yaushe ne addu’arta za ta karbu? Allah Ya sa ba sai bayan ranta ba, saboda tana son ganin ranar da za a aje abu Azeez ya gani kuma bai dauka ba.

Maryam

Bayan shiga ta daki, gefen gado na zauna jiki ba kwari, yayin da na sanya ƙaramin yatsana a cikin bakina ina cizawa kadan-kadan, wannan yana daya daga cikin dabi’a’una, duk lokacin nake cikin dogon tunani, tsoro, rashin gaskiya, damuwa, neman mafita ko kuma bacin rai.

Ban taba ganin mai sa’a gami da hanzarinn sata irin Ya Azeez ba, da ace Gambu mai kidan barayi zai dawo duniya, Sai ya rasa kirarin da zai yi wa Ya Azeez a bangaren sata.

Ya kai makura wajen iya sata, kamar yana yi da aljanu.

Ban San ya yi nisa harkar har haka ba, Sai dazu da Hammah ya zo yana hucin wai an dauke mishi mota, sosai abun ya ba ni mamaki, saboda ko mai kamar Azeez ban gani ya shigo gidan ba, amma yadda maigadi ya tabbatar da shigowar Azeez har da yadda ya fita da motar babu ta yadda za a yi in karyatashi.

Fatana dai Allah Ya sa motar ba ta yi nisa ba, saboda duk abin da Azeez ya dauka, Sai dai mai shi ya yi addu’ar Allah Ya ba shi wani. Kuma ga shi a wannan karon Hammahn ya dauki zafi da yawa, kila hakan baya rasa nasaba da motar sabuwa ce. Amma na tabbata jikin Ya Azeez zai fada mishi.

Wayata da ke kasan filo na janyo hade da duba time, karfe 11:15pm agogon ya nuna min, har zuwa lokacin babu Hammah bare Azeez.

Yadda na ba za madauka sautina ko wane bangare na gidan shi ya janyo mini jin karara shigowar motar Hammah.

Da sauri na mike zuwa falon, cikin sa’a, Aunty ta tashi, wannan ya ba ni damar sakewa sosai na nufi window da ke hasko min tsakar gidan kaina tsaye.

Daidai lokacin da Hammahn ke rufe kofar motar, cikin sauri na dafe kirjina saboda faduwar da ya yi, a zahiri kuma na ce “ina ya baro Ya Azeez sannu din?”

A hankali na saki labulen da na rike, yayin da ilahirin jikina ya yi sanyi, har zuwa lokacin maimaita tambayar da ke damuna nake yi, ban damu da babu mai ba ni amsa ba.

Ji nake kamar in nufi sashen Hamma na tambaye shi ina ya baro Ya Azeez, sai dai na san ba zai taba amsa min ba, kila ma ya kwakkwadoni musamman yadda ran san nan yake a bace.

Kuma dama shi ba mai sakin fuska ba ne, kullum a hade take kamar yaki ya riga shi kofar gida.

Na jima a tsaye kafin daga bisani na zabi komawa dakina. kwanciya kawai na yi, amma babu wani abu mai alamar bacci a idona, damuwata kawai shi ne in san ina zan Ya Azeez ya ke? An samu motar? Wane hali yake ciki?

Bacci bai dauke ni ba sai hudu saura, bacci mai dauke da mafarkai kala-kala, a cikin mafarkina ne na ji Aunty na kwankwasa min kofa, wannan ya tabbatar min biyar ta yi.

Da kyar na yunkura zuwa kofar, na shaidawa Aunty na tashi, daga nan kuma toilet na wuce, wanka na fara yi da ruwa mai zafi, saboda wani irin ciwo da jikina ke yi, tamkar na yi dambe da manyan aljanu a cikin dare, ga wani irin nauyi da kaina ya yi min, kamar an kwada min rodi, wani dummmmm nake ji.

Ban daga daga kan sallayar ba, Sai da na idar da Azkhar, sannan na nufi kitchen, inda nake ta jiyo buruntun Aunty, Irish take ferewa, bayan na gaishe ta, Sai kawai na shiga wani aikin gadan-gadan.

Duk aikin da muke yi, hankalin na kan lamarin Ya Azeez, ina son tambayar Aunty ina tsoron amsar da za ta ba ni.

Dole na ja baki na yi gum.

Misalin karfe takwas muka kammala komai, Kunun gyada mai shinkafa, black tea, chips Sai Kuma normal tea da bread da Kwai.

Ni na karasa gyara kitchen din, yayin da Aunty ta koma sama don yin shirin fita aiki.

Sai da na kammala gyara ko ina, hade da gogewa na kunna turaren wuta, kamshi mai dadi ya gauraye tangamemen falon da aka kayata shi da kayan alatu masu daukar hankali.

Komai na Aunty daban ne,kamar mai aljanu tsabta haka take, za ka iya farkawa cikin dare ka ji ta tana mopping, ba ta son Datti ko kadan, kominta kal-kal

Shi ya sa ba ta da mai aiki ko daya, Sai ni da nake taimaka mata, ni ma zama da ita, dole na zama yadda take, Hausawa dama sun ce zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai, kullum cikin kalkale-kalkale nake, wuni nake goge can, share can, gyatta can, ba na ko gajiya.

Sai da na kammala gyare dakina tsab, sannan na nufi falo, inda nake jiyo karar cups, wanda ya tabbatar min karyawa Aunty ke yi.

Tun da na fito ta kafe ni da idanu har na karaso wurinta, wannan ya sa na rufe fuskata da tafukan hannuna ina siririn murmushi, saboda na san duk lokacin da Aunty ke ma wani irin wannan kallon, yana nufin tuhuma.

Cikin siririyar murya na ce “Yanzu fa zan ci abincin, na tsaya gyara dakina ne.”

Tabe baki ta yi, kafin ta yi magana aka yi knocking kofa.

Da sauri na nufi kofar hade budewa, gabana ya yi wata irin faduwa, ko maganar Hammah na ji sai gabana ya yi irin wannan faduwar.

Sanye yake da shadda gambari blue Wacce ta sha dinkin babbar riga, kansa sanye da blue hula, kafarsa Sanye da bakin takalmi cover wanda ya sha mai.

A tsorace na duka gefe, hade da gaishe shi, ya amsa min lokacin da ya nufi dining.

Dakina na wuce, amma ban rufe kofar ba, saboda na san dole sai an yi maganar Ya Azeez, ni kuma ina son ji.

Bayan sun gaisa ne na ji Aunty ta ce “An samu motar?”

“Eh. Amma tana Maiduguri, wai yaron nan miliyan goma kacal ya siyar da motar nan”

Baki bude Aunty ta ce “Motar miliyan hamsin din?”

“Wlh. Ai yaron nan ya kai terror.”

“Yana ina yanzu?” Aunty ta kuma tambaya.

“Yana police station. But na ce su sake shi. Amma su jira in je”

“To kudin fa?”

“Zan bayar da miliyan goman in karbi motar.”

“Kai za ka bayar da miliyan goman Hammah? Me zai hana a matsi Azeez din ya bayar da na wurin shi, idan ya so a rage asara.” Aunty ta fada idanunta a kan Hammah.

Cikin rashin muhimmantar da zancenta ya ce “Kin ji ki, a tunani ki ko miliyan daya za a samu a wajen Azeez, the only thing I want is my car, and I got it, so ba ni da wata matsala kuma. I’m going, ana jirana.”

“Allah Ya kiyaye hanya, a dawo lafiya.” Cewar Aunty da wata kalar muryar da na kasa fassarawa.

Kan kujerar da ke gaban mirrorna na zauna, lokaci daya kuma Ina nazarin maganganun Hammah.

“Me yake damun Ya Azeez ne? Daga jiya misalin karfe biyu na rana zuwa goma na dare shi ne har ya kashe 10 million, million fa ban dubu ba.” Na yi maganar a zuciyata hade da jinjina lamarin

“Maryam!”

“Na’am!” Na amsa da sauri lokaci daya kuma na nufi falon inda nake jiyo muryar Aunty.

Jakar hannun ta na karba, hade da bin bayanta lokaci daya kuma Ina sauraron abin da take fada

“Ina jin kawai ba sai kin yi abincin rana ba, tun da Sai 4pm zan dawo, ki nemi abin da za ki ci da rana.”

“Toh!” na amsa lokacin da nake bude wuta mata murfin motarta hade da aje mata Jakarta a kan seat.

“Idan Azeez ya shigo gidan nan, ki kama kanki, kin san dai halinsa.” ta yi maganar hade da nuna ni da yatsa.

Shiru na yi ban ce komai ba.

“Ina kara fada miki, wlh kar ki shige mishi idan ya dawo, saboda Hammah ya tafi station, kuma yana zuwa za a sako shi, duk da ba lallai ya zo nan din ba, so ina fada miki ne, in case Koda zai zo.”

Wannan karon kai na jinjina alamun gamsuwa.

Na juya da zummar komawa ne, na ga Aunty Adama ta bude kofar ta ta fito , shirye tsab cikin wani tamfatsen Lace blue hade da digon fulawoyi pink, pink din gyale tan yafa, sosai ta yi kyau.

“Ina kwana? “

A ciki ta amsa min, kamar ko wane lokaci, ban damu ba, saboda hannun hagu ba bakon kazanta ba ne.

Kamar 30mins da ta tafiyar Aunty na ji ana knocking, sosai gabana ya fadi lokacin da na bude kofar na ga Ya Azeez tsaye ya kalli, hannayensa zube a cikin aljihun wandonsa Arewa fuskar nan a hade.

Matar J.

Da Magana 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×