Skip to content
Part 10 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

“Maryam!” ta kira sunana a hankali.

Ni ma a kasalance na amsa, lokaci daya kuma Ina zama gefen gado muna fuskantar juna.

“Ke ce abokiyar shawarata, (ta shiga labarta min hirarsu da Madina, ba ta san na ji komai ba,ta rufe da) me kika fahimta a nan kaina ya kulle sosai. Kar matarnan ta illata min yaro, ina tsoron yan siyasar nan Maryama. Har yanzu Azeez bai san wani abu so ba, ba sonta yake ba. Kuma me ya sa sai Azeez? Bayan Azeez ba shi da komai, bai ajiye ba, bai ba wani ajiya ba. Sai kai! Ina! DA MAGANA “

“Gawa ta rike mai wanka”na karasa mata karin maganar tata.

“Ƴan siyasar nan duk abin da zasu yi sai da dalili, kar bokonta ne ma ya ba ta wani nakalin, take son yin amfani da yarona.”

Ajiyar zuciya na sauke hade da guntun murmushi sannan na ce “Ba na jin za ta cutar da shi Aunty, da gaske son shi take yi.”

“Maryam! Ke yarinya ce, amma yan siyasar nan abun tsoro ne.”

“Addu’a ce kawai mafita, ni da ke mu dage da yin ta, in Sha Allah, Allah zai yi zabin abin da ya fi alkairi.”

“Je ki nemo wayarki.” ta yi maganar kamar mai rada.

Lokacin da na sakko basa falon, dama ban yi tsammanin samunsu ba.

Tun da naga Sim dina guda biyu a kan gado na san Ya Azeez ya dauke min waya, lokokin mirror na bude hade da watsa su ciki.

Gefen gado na zauna, ina auna yadda zan ji, idan aka ce yau ake daurawa Ya Azeez aure, bama wannan ne kawai problem din ba, yadda za ta dauke shi zuwa wata kasa shi ne damuwa. Saboda ta rufe duk wata kofa da nake ganin za ta iya zame min sauran damar da zan bi wajen ganin cewa ni ma na cika burin da ya dade a zuciyata. 

Ta ya zan rayu babu Ya Azeez a gefena, ni ko ba zai ce min komai ba, kawai dai in rinka ganin shi yana gilmawa, hakan yana kwantar min da hankali.

Na jima a zaune kafin na mike zuwa toilet na dauro alwalar Isha’i, saboda zuwa lokacin goma har ta wuce.

Bayan na idar da sallahr ma zaune na yi kan sallayar, ni kaina ba na ce ga abin da nake tunani ba. 

Shadaya na tuna ban ba Dog abinci ba, da sauri na nufi kitchen , na hada mishi abincin.

Lokacin da nake sauka entrance ne na tuna da duwatsun da na ga Aunty Adama na jerawa jiya, da sauri na kai idanuna wajen, amma ban gansu ba.

Dog yana jin motsina ya tashi “Ga abincinka” na yi maganar hade juye mishi a cikin kwanon da ake sanya mishi.

Yadda yake kallo na, sai naga kamar ya fahimci raina babu dadi.

Ba na cikin yanayin da zan yi mishi abin da nake mishi idan na kawo mishi abinci.

Dalilin da ya sanya ni juyawa na fice, daidai lokacin kuma motar Ya Azeez ta shigo gidan.

Tsaye na yi har ya fito daga cikin motar ya nufo wajen da nake tsaye.

“Kin ba shi abincin ne?” Abin da ya fara tambaya kenan.

Na amsa mishi da kai, wannan ya sa ya nufi hanyar shiga part din Aunty.

Bayanshi na bi, zuciyata na ta fada min, in fada mishi abin da na tsara a cikinta.

Ku san a tare muka shiga falo ni ce na ce “A kawo abinci ne?”

“No” ya amsa min lokacin da yake yin hanyar dakinshi

Sai na tsinci kaina da mai bin bayan shi, gab zai shiga dakin ne ya waigo tare da tambaya ta “Lafiya”

Shiru ban amsa ba, kamar yadda rashin amsa ta ba ta hana shi bude kofar da ya yi niyya ba, ni ma ba ta hanani bin shi cikin dakin ba.

Gefen gado ya zauna yayin da yake zare kambas din da ke kafarshi, bayan ya zare kambas din ne ya ce “, Wai me ya faru?” wannan karon sai da ya hade fuska sosai.

Ajiyar zuciya na sauke, sannan na ce “Ya Azeez da gaske auranta za ka yi?”

“Wacece?”

Ya yi tambayar tamkar bai fahimci tawa tambayar ba

“Ita Madinan?” na ba shi amsa idanuna a kanshi. Wanda na tabbata da hankalin shi a kaina yake zai hango tsantsar soyayyarshi a cikinsu.

Dogon tsoki ya ja sannan ya ce “You! You!! Za ki fara kuma, ina ruwanki ne?”

Ya zuba min idanunsa da suke cike da bacin rai “Dalla Malama fitar min a daki, wane raini ne wannan, har za ki zo ki tasa ni gaba, da, wata nonsense question” a tsawace ya yi maganar,

wannan ya sa na fashe da kukan da tun dazu nake son yin shi ya ki zuwa, kila shi ya sa ya taho da karfi Ina gab da fita daga corridor da ya hada dakinshi da babban falon na ji muryarshi yana fadin “Ke dalla tsaya.”

Tsayawar na yi, tafukan hannuna a kan fuskata yayin da sautin kukana ke fita a hankali. 

“Ki rufe min bakinki, kafin Aunty ta jiyo kukanki ta fara fada, and kin san ba na son wannan fadan nata.” 

A hankali na rika rage sautin kukan nawa har na yi shiru, har zuwa kuwa yana tsaye ya tasa ni a gaba, idanunsa a kaina. 

Ganin na yi shiru gabadaya ya ce “Better.” daga haka ya koma dakin shi.

Bayan shiga ta daki bisa gado na fada na yi kukana da Sai da ni da kaina na gamsu cewa ya ishe ni, kafin na mike zuwa falo, a hankali na bude kofa, so nake in ga ko Aunty Adama ta kara jera duwatsun nan amma ban gani ba.

Ina kokarin komawa daki ne, na ji Hammah ya bude kofar shi alamun fitowa zai yi.

Wannan ya sa na manne kaina a jikin pillar ta yadda ba zai ganni ba.

Wajen Hammawa mai gadi ya dosa, ban san me suka ce ba, na ga dai Hammawa ya mike zuwa dakinshi na masu gadi, Hammah kuma ya rufe kofar hade da zare key din, kafin ya bude wani extra daki da yake jere da na maigadin, amma akwai yar tazara kadan a tsakaninsu ya shige.

A daidai lokacin kuma Dog ya fara haushi, ban san me ya sa Dog yake wa Hammah haushi ba, idan dai ka ji haushinshi ko da rana ne, to Hammah ne ya shigo ko Aunty Adama.

Ina son in fito daga inda nake boye , kuma Ina jin tsoron kar ina fitowa Hammah ya ganni, wannan dalilin ya sa na kara a matse jikina.

Yau ne, gobe ne Hammah yana neman kwashe awa a daya a cikin dakin, zuwa lokacin kuma kafafuna sun fara gajiya, duk lokacin da na yunkura da zummar shiga daki, wata zuciyar sai ta fada min, ai ya dade yanzu zai fito.

Ina ta tsaye a wurin har na ji taba kofarshi alamun zai fito, dalilin da ya sa na kare manne kaina.

Wutar gidan ya kashe gabadaya, wannan ya sa Dog ci gaba da yi mishi haushi, a cikin duhun na ga kamar yana wanka a tsakiyar gidan, amma ban tabbatar ba, duk da Ina jin saukar ruwa kadan.

Kamar 10mns, ya kunna wutar, wannan ya kara tabbatar min da zargina a kan wanka ya yi. Saboda daidai wurin da ya tsaya a jike yake.

Maigadi ya bude, sannan ya shige dakin shi, sai a lokacin Dog ya yi shiru.

Jiki a sabule na shiga dakina, me kuma hakan ke nufi? Me ya sa Hammah ya rufe maigadi a daki? Me ya yi a cikin waccan dakin tsawon awa daya? Me ya sa ya yi wanka a tsakar gida?

Da wannan tunanin na zauna gefen gadona, yayin da zuciyata ta cika da son sanin me ye a cikin dakin da Hammah ya shiga. Dama ni ban taba ganin an bude dakin ba.

Agogon da ke jikin bangon dakina na kalla, karfe uku na dare har da mintuna biyu.

Zuciyata duk a yamutse take, cike da tunaninka barkatai, a haka na yi alwala na hau kan sallayata, abin da ya fi damuna shi na fara gayawa Allah wato maganar auran Ya Azeez da Madina, kafin sauran bukatu suka biyo baya.

A kan sallayar bacci ya dauke ni, ba jimawa kuma na ji Aunty na buga kofa, wannan ya tabbatar min asuba ta yi.

Bayan na tabbatar mata da na tashi, toilet na shiga tare da dauro alwala.

Shidda saura muka hadu da Aunty a cikin, daga, yadda take yi komai na fahimci ba ta da kuzari, da alama maganar jiya na cin ta, bugu da kari ga yawan hammar da take yi, wannan ya kara tabbatar min ba ta yi baccin kirki ba.

“Kin ga wayar ta ki kuwa?” ta katse shirun da ya mamaye kitchen din.

Kai na girgiza alamar a’a

“Azeez ya dauke kenan?”

A, hankali na ce “Ban sani ba, amma na ga simcard din”

Wani murmushi ta yi mai kama da kuka tare da fadin “Ya dauke din kenan. Allah Ya shirya”

“Amin” Na amsa.

7:30am na gama shirina cikin gogaggun uniform dina, yayin da kamshi mai dadi yake fita a jikina, kai tsaye falo na fito, na wuce dining inda muka shirya abun kari, tea na hada mai kauri, a hankali nake sipping tare da yankar soyayyan kwan da ke gefena.

A haka Aunty ta sakko cikin shiri ta same ni, kan dining na bar ta, na nufi wurin Dog domin duba yadda ya kwana.

Dakin da Hammah ya shiga jiya na zubawa ido, sosai ina son sani me ye a ciki, sannan me ya sa ya dade a cikin shi.

Kallona na mayar daidai saitin wurin da ya yi wanka jiya, kafe wurin na yi da ito, kamar ina, jiran fitowar wani abu, mintuna kusan biyar na bata, sannan na nufi wurin Dog, da alama ya kosa in karaso, saboda ya kasa zama wuri daya a cikin kejin, Sai tsalle yake tare da dan karamin kuka yana kallo na, wannan ya sa na kara daga kafa zuwa wurin na shi.

Ina budewa kuwa sai ya yo kaina, na yi saurin ja da baya ina fadin “Stop it please, kar ka taba ni dog kayana zasu baci, farare ne.”

Burki ya ci, amma har zuwa lokacin bai daina kukan da yake nuna ya ji dadin ganina ba.

Wurin da yake cin abincin na wanke, na juye mishi madara, dayan kuma na juye mishi indomie da kwai wacce ta sha nama, sannan na, wanke wajen sanya mishi ruwa na zuba mishi ruwan.

Duk yana tsugunne yana kallo na, Sai da na ce mishi “Oya come and eat”

Tinkis-tinkis ya taso zuwa wajen, na shiga shafa farin gashinshi, tun ina mamakin yadda yake jin maganar mutane zuwa yanzu kam har na saba, ko harararshi na yi ganewa yake yi, Allah Ya sa ni ina kaunar Dog, duk inda na tafi hankalina yana wajen shi.

Sai da ya shanye madarar tas ya koma kan indomien sannan na fito, ina fada mishi zan je school, ka kula da kanka, and I’m going to miss you.

Ya dan yi ƙaramin haushi kadan, wannan yake tabbatar min da ya ji maganata kuma ya amsa.

Lokacin da na shigo falon Aunty ce tsaye tare da Ya Azeez, da alama taso shi ta yi, kuma fadan da kullum yake cewa baya so, shi ne take mishi.

Shigowa ta ce ta sanya ta yin shiru, shi kuma ya nufi hanyar dakinsa fuska a tamke.

“Abdul’azeez!”ta kira shi da daurarrar murya

Ya juyo yana kallon ta, amma bai amsa ba.

“Daga nan zuwa yamma nake son, kodai ka dawo ma da Maryam wayarta da ka dauko ko ka sawo mata sabuwa. Tun da kai ka zama cinnaka ba ka san na gida ba, na dauka Maryam ta fi karfin ka taba kayan ta.”

Ta karashe maganar tana juyowa kaina “Dakko jakar ki mu tafi ke kuma.”

Daga haka ta fice, na mayar da kallo na kan Azeez wanda ya tamke fuska fiye da dazu.

Kunnuwana biyu na kama hade da narke fuskata alamun ya yi hak’uri.

Wata jibgegiyar harara ya aiko min, hakan ya sa na juya dakina da sauri don dakko jakata.

A hanya ma ni da Aunty kowa shiru, da alama dukkanmu mun yi nisa a tunanin abubuwan da muke kallo a matsayin matsalarmu ko masalaharmu.

A school ma haka na wuni, don ma revision ake mana zamu fara exam, amma kam na wuni zuciyata ba dadi, ga rashin baccin da ban yi ba jiya, wannan ya haddasa min wani irin ciwon kai mai zafi.

Yau na riga Aunty dawowa, saboda ina sauka kofar gate din gidan ana kiran sallahr la’asar.

Kamar ko wane lokaci kai tsaye wurin Dog na zarce, shi din ma ina kallon shi yana haushi hade da tsallen murnar ganina.

Hankalina kaf a kan Dog din ne, shi ya sa ban ga kowa/komai ba sai Dog din.

Kamar daga sama na ji wani abu ya yi tsalle a gabana, yana kokarin kwace ledar Biscuit din da nake budewa Dog.

Wata irin gigitattar kara na saki, lokaci daya kuma na watsar da ledar Biscuit din da jakata na yo kofar fita a guje.

A kokarina na fita waje ne, na gabje goshina da karfen da aka gitta a jikin kofar, ban damu ba, kokarina kawai shi ne in fita. Amma na kasa fitar, kuma har zuwa lokacin ba daina sakin gigitattar karar ba.

Ga Dog yana taya ni da wani irin haushi da ke nuna ni da shi muna neman taimako.

Kamar daga sama na ji an fisgo ni, an kuma rungume ni tsam, wannan ya sa na fara nutsuwa kadan, har zuwa lokacin kuma Dog bai fasa haushin da yake yi ba.

“Dog stop it!” Ya Azeez ya fada cikin tsawa, lokaci daya kuma ya tura ni baya ya nufi wurin da Dog din yake.

Sai a lokacin ne na ga abin da ke faruwa, wani dan madaidaicin biri ne a can saman waya ya yi tsuhu, alamun a tsorace yake, yayin da Dog ya kasa ya tsare, ya hana shi zuwa wajena ko taba kayana da na watsar a kasa, ta hanyar haushi da barking din da yake yi.

Ya fara rage haushin na shi hade da nufo inda nake ya kuma tare ni (irin kar dai wani abu ya same ni) . Har zuwa lokacin yana kananun haushi kadan.

Ban San lokacin da hawayen kaunarshi suka shiga gangarowa a idona ba, na duka hade da mamutse zuwa kirjina, ji nake kamar in huda kirjina in saka shi ciki, yau kam iya kauna ya nuna min, rumgume yake tsam a kirjina yayin da idanuna ke zubar da hawaye, hannayena kuma suna shafa lafiyayyen gashin shi, wannan bai sa ya nutsu ba, rabin hankalinsa yana kan Ya Azeez, wanda yake yi wa Biri fadan abin da ya yi. Shi kuma birin ya yi zumu, irin yana sauraron nan.

“Sakko ka ba ta hak’uri” ya yi maganar cikin tsawa.

Tsakanin kai karshen maganar ta shi, da durowar birin ban san wanne ya riga wani ba.

Abun mamaki Dog Sai ya hana shi karasowa wurina ya tare shi.

Sai da Ya Azeez ya ce “Ba wani abu zai yi mata ba Dog, hak’uri zai ba ta” sai a lokacin ne ya rage haushin, kuma still bai ba shi damar zuwa kusa da ni ba.

Daga nesa ya kwanta hade da dukar da kanshi wai in yi hakuri.

Cikin muryar kuka na ce “Ta shi na yi hak’urin, amma kar ka sake min haka.”

Hammawa da ke leken abin da ke faruwa daga wajen cage din ya kwashe da dariya, sannan ya ce “Fetel kin faye tsoro, walahi na dauka karen nan ne ya cije ki ko maciji.”

Ni dai uffan ban ce ba, Sai idona da nake ta mitsittsika, ina kuma kallon Biri, wanda ya tashi ya koma can saman waya yana kallo na.

Sai a lokacin Ya Azeez ya ja dogon tsoki tare da fadin “Kin faye tsoro wlh. Haba da Allah, Kamar wacce ake kwakulewa ido da ranta.”

Kafin in ba shi amsa motar Aunty ta shigo, wacce dama horn dinta ya sanya Hammawa barin wurinmu yana dariya.

Kai tsaye wajenmu ta dosa, daga wajen cage din ta tsaya tare dafa dogayen karafan da ke kofar tana kallo na kafin ta ce “Yau ma marin na ki ya kara yi ko?”

Kai na girgiza alamun a’a

“To fada za ki yi, ko kashe ki ya yi Maryam aka dawo da ke duniya aka tambaye ki shi ne ya kashe ki, za ki ce a’a.”

Ya Azeez na kalla, wanda ya hade fuska ba tare da ya ce komai ba.

“Waye kuma ya kawo Biri ni Aisha?” ina jin sai a lokacin ne ta ga Birin.

Yadda ta ga ina kallon Ya Azeez ne ya sa ta ce

“Kai ne ka kawo mana Biri kuma. Lallai ga ma’anar karin maganar tsugunne ba ta kare ba, an siyar da kare an sawo Biri. Wannan kam ba ma a sayar da karen ba, aka kawo birin.”

Duk muka yi shiru daga ni har Azeez din, yayin da Birin ke ta kallon Aunty kamar ya san maganarshi take yi.

“To bari ka ji, saboda na fahimci kamar ba ka da hankali, idan ba layi aka ja ma ba, gobe zan iya, dawowa in samu kura ko zaki a gidan nan. To wlh Azeez Kar ka kara kawo mana komai, nan din ba gidan zoo ba ne, Idan sha’awar kiwon dabbobin kake yi, to ka bude gidan zoo ba gidanmu ba.”

Daga haka ta juya ta nufi hanyar shiga part din ta.

Na langabe kai ina kallon shi, harara ya watso min sannan ya ce “Dalla fita ki ba mutane wuri.” ya rufe da tsokin nan na shi.

Dog na zubewa Biscuit a gaban shi masu yawa, sannan na tillawa Monkey (haka na ji Ya Azeez na kiran sunan shi) ragowar na ledar, take ko ya cafe, ya fara ci.

Ni kuma na fice rungume da jakar makarantata.

<< Da Magana 9Da Magana 11 >>

1 thought on “Da Magana 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×