Skip to content
Part 12 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ba karamin dadi na ji ba, lokacin da na ga motar su Aunty ta shigo, ko ba komai za a katse abin da ke faruwa a cikin wancan dakin.

Motoci hudu ne suka shigo a tare ta Aunty, Hammah,  da kuma Aunty Adama dukkansu apartment din Aunty suka yi wa tsinke, wannan ya sa na bi bayansu.

Dukkansu fada suke wa Ya Azeez na shirin fita da shi bindigar da ya yi, tare da yi mishi fadan sanin mutanen da zai yi mu’amala dasu, da kuma nesanta kanshi da irin ƴan’iskan garin nan.

Ba jimawa su Ya Naseer da Mubarak ma suka shigo, gidan dai ban yanke da mutane ba, Sai wajen shadaya na dare.

Zuwa lokacin tuni zazzabi ya rufe ni, abinci da na gama ma, ko iya ci ban yi ba, ga kunne na da yake min wani irin azabar ciwo.

Wanshekare da safe haka su Aunty suka kafa sintirin zuwa police station, yayin da ni kuma cikin karfin hali nake ayyukan gida, kula da Ya Azeez da kuma su Dog, kodayake shi ma Ya Azeez din hankalinshi yana kansu na kan su Dog din. 

Kayan dubiyar da Madina ta rika kawowa har tsoro suka rika ba ni, ga wata shagwabawa ta musamman da take wa Ya Azeez, har da su mota ta ce za ta canja mishi wai idan ya ji sauki, kullum tana yawon zuwa gidan mu.

Kamar za ta mayar da shi ciki, a, zuciyata na ce ba banza ba, samari ke son manyan hajiyoyi su yi wuf dasu. Saboda idan har yadda Madina ke ba Ya Azeez kulawa haka ma sauran Hajiyoyin ke ba masoyansu kulawa, lallai akwai matukar wahala ga budurwa ta samu kansu

Kwana uku maganar case din su Ya Azeez ta mutu, aka tura yaran da suka yanke shi gidan gyaran hali, aka kuma shata musu layi tsakaninsa da Kb. Sai lokacin komai na gidan ya fara daidaita, kuma a lokacin ne Aunty ta lura da ramar da na yi, da kuma yadda ban ji sosai, shi ya sa ta ce da safe in shirya mu je asibiti, tun da ba makaranta nake zuwa ba, zamu fara exam ne.

Da misalin karfe tara na safe, zaune nake a falo sanye da doguwar riga pink color, na zagaye fuskata da veil din rigar, hankalina yana kan TV, duk da ba komai nake ji ba, amma na kan gane abun da suka fada da motsin labbansu.

Ba iya TV ba, ko a zahiri da haka nake gane abin da mutane suke fada,  idan aka yi magana a hankali ba na ji, idan kuma aka yi da karfi damuna yake, ba na son abu mai ƙara sam.

Ban  ji ƙarar knocking ba, sai kawai na ga kofar ta bude, yanzu Aunty ba ta rufe kofa, saboda ni ce mai kokarin budewa, kuma yanzu ba kunnen jin ƙarar knocking din.

Ya Azeez ne ya shigo, jikin shi sanye da kayan sport, na tabbata ya je motsa jiki ne, ledar da ke rike a hannun shi ya dora kan cinyata ba tare da ya ce komai ba ya nufi dakin shi.

Na janye idona daga kallon da nake bin shi da shi tare da sauke ajiyar zuciyar da ban san dalilin yin ta ba.

Ledar na bude, mamaki ya kashe ni ganin kwalin iPhone, ai da sauri na ɓare kwalin tare da zaro wayar cike. 

Ido hade da baki na bude, lokaci daya kuma na mike na shiga taka rawar da ban san na iya ta ba.

“IPhone!” na fada tare da kama habata alamun mamaki, na kuma kwaso wata rawar ina jujjuya wayar.

“Da alama lafiya ta samu.” muryar Aunty ta katse ni.

Na yi saurin dakatawa da rawar da nake yi, amma kam fuskata a washe take, bakina har kusa da kunne.

Ta karaso inda nake tsaye tana fadin “Me muka samu?” da yanayin motsin labbanta na gane abin da ta fada.

Wayar hannuna na mika mata, lokaci daya kuma Ina fadin “Ya Azeez ne ya ba ni yanzu.”

“Ahh! Lallai the real definition of gobarar titi.” ta fada dan daga murya yadda zan ji.

Na kuwa washe baki, cike da tsokana ta ce “Ke ɓarauniyar zaune shi na tsaye.”

Fuska na kyabe tare da fadin “Kai Aunty!”

Dariya ta yi lokacin da take miko min wayar, ni kuma na nufi wajen TV domin sanya caji.

“A nan za ki sanya cajin? To ina mai tabbatar miki kika sanya wannan wayar caji a nan, to ba ta ki ba ce, saboda wanda ya ba ki, zai dauke abar shi ya sayar.”

Ta kai karshen maganar lokacin da take mika min key din dakin ta.

Da gudu na haura saman, don wani irin karfi nake ji, duk ciwon kunnen nan ban jin shi.

Cike da farin ciki muka isa asibitin specialist, Aunty ce ta shiga ta fita har na samu ganin likitan kunne .

Bayan shigar mu office din tambaya ta farko da ya fara jefo min ita ce “Me ya sa kunnen yake ciwo?”

“Haka nan.” Na amsa mishi.

Ido ya zuba min kafin ya ce “Haka nan kawai, ba faduwa kika yi wani abu ya buge ki ba, ba kuma dukanki aka yi a wajen ba, ba wani abu mai tsini kika yi amfani da shi a kunnen ba?”

Na juya ina kallon Aunty kamar a wurin ta amsar tambayoyin da aka yi min suke.

“Wanne ne daga ciki, so that mu san ya za mu yi treating naki?”

Na kuma kafe Aunty da ido, wannan ya sa likitan ya ce “Ko za ki dan bamu wuri Hajiya.”

Ya karasa maganar cikin dariya. 

Baki ta kyaɓe tare da fadin “Dukanta aka yi, ba ta son in sani ne.”

Wannan ya sa hawayen da nake ta kokarin rikewa tun dazu suka sauko.

Cikin kuka na ce “Ai bai gani ba ya mare ni.”

“Ta ina aka taba mari ba a gani ba?” ta tambaye ni cike da bacin rai.

“Shi kenan dai na fahimta” cewar likitan a lokacin da ya mayar da hankalin shi kan wata takarda yana rubutu.

“Shi ga wancan dakin ki jira ni.” ya min maganar hade da nuna min dakin da hannunshi.

Na mike zuwa dakin lokaci daya kuma in sharce hawayen da ke bin kuncina.

Ban jima a ciki ba ya shigo tare da yi min scanning, a tare muka fito, ya rubuta mana magunguna, sannan ya ce bayan sati daya mu dawo.

Tun da muka fito Aunty ke fada, yayin da nake ta ba ta hak’uri a kan ni dai kar ta yi wa Ya Azeez magana don Allah, na yafe mishi.

Wannan ya sa da ni da Ya Azeez din ta hade mu gaba daya taita zazzaga fada a cikin mota, muna zuwa junction din unguwarmu ta Parker motar hade da umurtata in fita, ita wurin aiki za ta koma.

Ledar magunguna ta mika min, keyn dakinta da kuma 1k ta mashin.

Ni kaina na ji dadin yadda ta sauke nin, saboda ko ba komai zan huta da fadan da take yi, kafin ta kai min duka. Duk da abu ne mai wahala a wajenta, tana da fada kam, amma ba ta faye duka ba.

Wurin wani mai nama na tsaya, na sayi na 500, na karasa wurin mai fruit na sayi ayaba ta 300,kafin na tare keke zuwa gida.

Kai tsaye wajensu Dog na nufa, na basu oyoyo sannan na wuce ciki.

Dakina na wuce tare da kwaso Sim dina na haura dakin Aunty.

Cikin mintuna talatin na gama saita komai na wayar, abin da yake a zuciyata shi na fara yi, wato lekawa Instagram.

Update din Ya Azeez na rika bibiya, har zuwa lokacin da na zo kan wani video wanda ya ja hankalina sosai, sanye yake da farin wando kal, wanda ya hadu da farin kambas din da ke kafarsa, bakar riga cotton wacce ta kwanta a kosasshen jikinsa, tarin bakar sumarsa mai kama da ta matasan Ethiopia ta kara fito da kyan kwalliyar tashi.

Da wani irin tako na(slow-motion) yake sakkowa daga kan wani kayataccen stairs, har zuwa parking space, Inda aka yaye ma wata hadaddar farar moto rigar jikinta, da wani irin yanayi na isa, ya bude kofar motar ya shiga, daidai nan videon ya kare, na maimaita kallon videon ban san ko sau nawa ba,  ya ja hankalina kamar yadda ya ja hankalin mutane, saboda yana da viewers fiye da 10k,yayin da ya samu tsokaci mai yawa.

Ajiyar zuciya na sauke mai nauyi tare da lumshe idanuna, Ya Azeez cikakken namiji a zahitamce, wanda ya hada duk wasu siffofi da mace ke so, madaidaicin kyawu, jiki mai kyau, iya kwalliya, kuruciya, ga kuma kudi, musamman yadda Madina ta rike mishi kan maciji shi kuma yake wasa da bindin.

Kullum kara fasowa yake da zafafan abubuwa, zan iya cewa a kaf duniyar Instagram Don AZ shi ne ake magana, yayin da wasu ke amfani da sunanshi wajen bude account a TikTok da sauran kafafen sada zumunta na zamani

Na dade ina kallon videon  na shi cike da shauki, kafin na shiga kitchen don girka mana abincin rana.

Lokacin da na fito da dustbin ne zan kai bola na yi kicibis da Madina a tsakar gida, yayin da Hammawa ke biye da ita hannunshi rike da manyan ledoji, na san kayan kwalam da makulashe ne, Sai turarurruka, maya-mayai shafawa na kai da na jiki, da kuma na wanke takalma.

Kai ta dauke min, kamar yadda ni ma na dauke mata nawa kan na mayar da shi inda Aunty Adama ke parking din motarta.

“Waccan matar wurin wa take zuwa ne a gidan nan?” Aunty Adama ta tambaye ni lokacin da nake kokarin juya sharar da ke hannuna.

Kamar ba zan amsa ba, Sai kuma na ce “Wajen Ya Azeez take zuwa?”

“Me ya sa take zuwa wajen shi?” ta kuma tambayata.

Wannan karon kam na dago kaina hade da saka kwayar idanuna cikin nata kafin na ce “Ban sani ba” daga haka na wuce abu na

Aiki kawai nake yi, amma hankalina gabadaya yana dakin Ya Azeez inda Madina ta shiga ta yi shiru kamar an aiki loma zagayar wuya.

Ni kaina ban san lokacin da na ganni a tsakiyar dakin ba.

Madina da ke kwance kan sofa ta mike zaune tare da fadin “Lafiya?”

Idanuna na watsa mata sannan na ce “Ba wurin ki na zo ba”

“To wanda kika zo wajen na shi bacci yake yi” daga haka ba ta sake ko kallo na ba, ta koma kan sofar ta kwanta.

Na kai kallo na kan Ya Azeez da yake kwance sambal kan lafiyayyen gadon shi, da ya Sha mashimfidi mai laushi, baccinshi yake yi hankali kwance.

Wannan ya sa na juya zuwa kofa.

Ban samu nutsuwa ba, Sai da suka bar gidan misalin karfe hudu yamma, ni hakan ya fi min dadi ai, kazantar da mutum bai gani ba tsafta, zuwan ta gidan sai da ta tayar min da ciwon kunne, ciwo yake sosai, shi ya sa na kwanta lamo kan kujera, har zuwa lokacin da Aunty ta dawo aiki.

Da dare ma haka ya hanani bacci, na shiga zarya tsakanin falo da dakina, ga wani zazzabi mai kwankwatsa kashi da nake ji a jikina.

Misalin karfe sha biyu na dare azaba ta sanya ni fitowa falo, na isa wurin window na tsaya tare da yaye labulen ina kallon tsakar gidan mai dauke da hasken nepa kwanyar kamar rana. 

Ban jima da tsayuwa ba, kofar Aunty Adama ta bude,  Aunty Adama ce ta fito zuwa kofarmu, inda ta shiga jera duwatsun nan, wadanda na fahimci ba ta jera su sai ranar da Aunty ta karbi girki.

Sai da na ba ta kamar 30mns da shigewarta part din ta, sannan na bude kofa a hankali na fito.

Addu’o’i kala-kala na rika tofe duwatsun dasu, kafin na yi Bismillah na kwashe su duka, kitchen na yi wa tsinke tare samo farar leda na zuba su a ciki na kulle, na aje su inda  ni din ce kawai zan iya ganinsu.

Koda na koma daki sai bacci ya gagare ni, kadan in fito ko Aunty Adama ta biyo sawun ajiyar ta. 

Haka har misalin karfe hudu na asuba, inda na riski Aunty Adama duke gaban entrance din Aunty tana laluben ajiyarta

Tsaye na yi ina karanta tashin hankalin da ke kan fuskarta, ta hasken da ke haske min fus karta. 

Safa da marwa kawai take, har zuwa lokacin da ta hak’ura ta koma dakinta. 

Ni ma jiki a mace na koma dakina, saboda zuwa lokacin wani irin bacci nake ji.

<< Da Magana 11Da Magana 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×