Skip to content
Part 14 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Aunty Adama

Dogon tsoki ta ja, jin yadda ta kwashe tsawon wuni tana kiran lambar Gana ba ta shiga ba, yanzu kuma ta shiga amma ba a daga ba, karo na biyu ta kuma turawa lambar kira, Sai ta nuna mata busy, wannan ya sa ta dakata da kiran, ta san Gana din na kokarin kiranta ne

Ba jimawa kiran ya shigo wayar tata.

“Ina kika shiga ne?” tambayar farko da Aunty Adama ta fara jefa mata, ko sallama babu.

“Kin kira ni ko?”

Cikin rashin jin dadi Gana  ma ta tambaya.

“Har ban san iyaka ba.”

Aunty Adama ta amsa ta.

“Wutarmu ce ta samu matsala, Sai da na bayar da wayar caji.”

“Haba shi ya sa na yi ta kira ba ta shiga.” cewar Aunty Adama, haɗe da gyara zama alamun za ta yi magana mai muhimmanci.

Bari mu leka Azeez da Maryam

Azeez & Maryam

Kamar yadda ya ce in shirya  misalin hudu da rabi na yamma na fito cikin kwalliyar da ni kaina sai da na burge kaina, doguwar riga (Abaya) irin mai yar ciki da ta Saman nan, ta ciki din fara ce Kal, mai armless din hannu, yayin da ta saman ta kasance light ash, Sai aka yi ma gaban kwalliya da wasu irin design na farar flowers.

Madaurin da ke tsakiyar ma Ash ne, shi ne na yi amfani da shi wajen daure tsakiyar kamar yadda ake daure  belt, hakan sai ya  fitar min da siffar madaidaicin jikina, yayin da na yi rolling din veil din ya fitar da doguwar fuskata sosai.

Farin takalmi mara tudu na yi amfani da shi tare da farar hand bag, ban cika ma fuskata kwalliya ba, amma sosai ta yi kyau musamman yadda powdern ta kwanta lumui a kanta.

Sansanyan kamshi ne ke fita daga jikina, a haka na taka zuwa saman Aunty, ta bi ni da kallo, hade da fadin “Ma Sha Allah, sosai kin yi kyau Maryam.”

Murmushin jin dadi na yi kafin in yi magana aka turo kofar, Ya Azeez ne, na kasa dauke idona daga kanshi, tabbas Ya Azeez dan gaye ne da iya tsara kwalliya, amma ta yau zan iya cewa ta sha bam-bam da ko wace kwalliya da na ga ya taba yi.

Kwalliyar suit ne rigar ciki fara Kal mai dogon hannu, Sai ya dora top  baka, irin bakin nan mai sheki, yayin da baƙin wandon ya hadu da bakin takalmin da ke kafarsa cover.

Sumar nan ta sha gyara tare da fitar da kamshi mai dadi, hannunsa agogo ne golden mai shegen kyau, Sai ya yi min kama da irin samarin Ethiopian nan da muke gani a wakokin yan Ethiopia.

“Tubarakhallah Ma Sha Allah. Duk kun yi kyau” Aunty ta kuma fada cike da jin dadi wannan ya sa ya mayar da kallon shi kaina muka hada ido, Sai ya tamke fuska kadan, ni kuma na fadada fuskata da murmushi. Don sosai ya yi kyau, abun farin cikin kuma shi ne tare zamu fita.

“Azeez magriba ta yi maku a gida.”

Bai ce komai ba, amma idanunsa yana kan Aunty wacce ta yi maganar.

Kudi ta miko min “Idan ma ba zai kawo ki ba, ki samu abun hawa ki dawo.”

Na karbi kudin tare da fadin “Toh.”

Shi kuma ficewa ya yi daga dakin, yayin da Aunty ta ci gaba da jaddadamin idan na ga abun da bai gamshe ni ba in taho gida.

Ni kam da to kawai nake amsa mata, damuwata kar Ya Azeez din ya tafi, ya ce ya fasa zuwa da ni.

Lokacin da na fito daga kofar babban falon, na hangi motarshi fake, Sai da na sauke ajiyar zuciya kai tsaye ta jin dadin bai tafi ya bar ni ba,  na tunkari wajensu dog tare da manna siririn farin glass dina. 

Yadda na yi tsammani haka ne ya faru, tsugune na gan shi gaban dog yana ba shi abinci haɗe shafa gashin jikinsa, wannan ya sa na tsaya daga wajen cage din ina kallon su, har zuwa lokacin da ya kammala ya fito zuwa wajen motar shi.

Ni ma sai na shiga da zummar yi wa dog sallama Kamar yadda na saba duk lokacin da zan fita.

A nutse nake tahowa inda yake warming din fara Kal din motar da ta sha wanki, na shiga na zauna da Bismillah, wannan ya ba shi damar jan motar a hankali ya fice daga gidan.

Tun da muka dau hanya komai bai ce min ba, tukinshi kawai yake yi cike da kwarewa, yayin da ni kuma nake shakar daddaɗan kamshin shi da ya cika motar.

Lagon Villa muka yi wa tsinke, tun daga yadda na ga motoci fal a farfajiyar, na tabbatar mutane sun fara zuwa.

Kamar yadda na ga ya fita bayan ya yi parking haka ni din ma na fita ina gyara zaman gilashina.

Ga mamakina sai na ji ya riko hannuna, wannan ya sa jikina ya mutu sai na rika bin shi salo-salo kamar sakarya har zuwa lokacin da muka shiga dakin taron wanda bai yi min kama da Nigeriata ba, saboda yadda aka tsara shi.

Sansanyan kida na tashi mara hayaniya, yayin da mutanen wurin duk suke a nutse cike da kasaita.

Haka na rika bin su da kallo daya bayan daya har zuwa lokacin da muka zauna a kujerar da nake expecting an tanade ta ne don mu.

Zamanmu ba jimawa abokan Ya Azeez suka rika zuwa miko gaisuwa, abin da ya ban mamaki shi ne yadda bai sake fuskarshi ba, duk da dama bai faye sake fuska ba, amma na yau kam daban.

A hankali na rika gane fuskokin mutanen da ke wurin da yawansu celebrity ne na Instagram.

Ina tsaka da raba idanu ne Ya Naseer ya iso wurinmu.

“I want talk to you AZ”

Shi ne abun da ya fara fada, da wani irin yanayi a kan fuskarshi wanda na kasa fassarawa.

Bai dago ba ya amsa da “ina jin ka”

“let go outside” cewar Ya Naseer

“I’m not going anywhere Naseer, Kawai ka fadi abin da kake son fada.”

“Me ya sa ka zo da Maryam wurin nan?”

Wannan karon kam ya dago kai ya kalle shi, yayin da fuskarshi ta bayyana mamakin tambayar da Ya Naseer din ya yi mishi.

“I’m asking you”

“Ban sani ba.” ya amsa shi a fusace.

“Ni na sani, saboda Salma ko? But why Maryam?” zan iya samo maka wata ba Maryam. “cewar Ya Naseer a fusace.

Abun Sai ya ba ni mamaki, me ya sa yake fada da jin haushi a kan na zo nan din, kodai wurin ba kyau.

Wacece kuma Salma, da ta dalilin ta na zo nan.

“I will take her home now, ba ta dace da wannan wurin ba.” Ya Naseer ya katse min tunani da maganar shi.

“Try it Naseer! I said try it”cike da bacin rai Ya Azeez ke maganar, lokaci daya kuma ya daga gefen rigarshi, karamar bindigarshi ta bayyana, ya sauke rigar tare da fadin” I will shoot your leg, if you try this nonsense for me “

Gabana bai koma daidai Ya Naseer ma ya daga rigarshi tashi bindigarshi ta bayyana sannan ya ce” I will shoot your heart “ya yi maganar hade da nuna zuciyarsa da yatsansa.

“I’m not joking “cewar Ya Azeez

“I’m not too”Ya Naseer ma ya mayar mishi da amsa.

Zuwa lokacin na tsorata sai nake gani kamar kowa ma a wurin yana da bindiga, what if fada ya kacame fa, kowa ya fitar da bindigar shi, gabana ya yi wata irin faduwa, da na tuna irin tashin hankali da zai faru.

Na rika rarraba idanuwa cikin hall din, inda wasu ke ta shan soyayyarsu da yammantansu wasu kuma suna cin abinci, wasu kuma suna tattaba wayoyinsu.

Kwayar idona ta sauka a kan wata matashiyar budurwa wacce ke sanye da bakin wando dogo  irin pencil din nan, farar shirt ta mata long sleeve mai santsi, kanta kuma kananan kitson attach wanda ta matse da wani madauri mai kyau, kunnenta da wuyan sanye da siririyar sarka silba, kafarta kuma farin takalmi ne flat mai igiya. A kwalliya irin ta zamani to tabbas ta yi kyau, duk da fuskarta babu heavy make up, Hakan bai hana farar fuskar tata kyau ba.

Fara ce sosai, jikin nan a goge kamar ba ta daga tsinke.

Kai tsaye wajenmu ta doso, wannan ya sa na daidaita nutsuwata hade da komawa na zauna, yayin da Ya Naseer ya bar wurin lokacin da ta karaso.

Kujera ta janyo haɗe da zama wannan ya ba ta damar fuskantar Ya Azeez, wanda har zuwa lokacin fuskar shi ba ta gama warwarewa daga daurewar da ya yi mata ba, a lokacin da suke sa-in-sa da Ya Naseer.

Ni ma zama na yi, lokaci daya kuma zuciyata na fada min ko ita ce Salman

“Azeez!” Ta Kira sunanshi da wata irin murya ta yangayu cike da yanga.

Bai kalle ta ba da kuma hakan bai sanya ta fasa fadin abin da ta yi niyya ba.

“I’m here just because of you, and you know that. I’m so eager to see this day. Ranar da kwayar idona za ta hadu da ta ka. Why have you done this to me?”

Da wata irin kissa da kisisina take magana, yayin da ko wane harafi take fitar mishi da tajweed, wannan ya sa na gane akwai sauran aiki a gabana, idan har Ya Azeez zai rika haduwa da irin wannan, to ni kuma me zan yi mishi da zai burge shi. Da kaina na ba kaina amsa da babu.

Maganar da ya yi ce ta maido da hankalina wajen su

“What did I do?”

“Ba ka yi komai ba?” ta tambaya a hankali.

Maimakon ya amsa, sai ya mayar da hankalinshi kan taba wayar da ke hannun shi.

Hakan ya sa na zunguri kafarshi ta can kasan table din da muke zaune.

Cikin sa’a  ya dago kai muka hada ido.

Fuska na narke kamar zan yi kuka. Kowa da baiwar da Allah ya yi mishi, ni kam Allah ya yi min baiwar iya shagwaba, kuma na san tana tasiri sosai a kan shi, wani lokacin, wani lokacin kuma sai dai in Sha kwada, shi ya sa ma nake son jaraba ta a wannan karon saboda ba ni da komai sai ita. 

“Me ye?” ya tambaye ni fuska a daure 

Na kara narke fuskar sannan na ce “Ruwa zan sha” 

Da ido ya yi min nuni da ruwan da ke gabanmu. 

Na kuma shagwabe fuska ba tare da na ce komai ba. 

Hararar da ya aiko min da ita ce ta sanya ni fadin “Ni ba zan iya sha a nan ba, mutane sun yi yawa.” 

Kanshi ya dauke daga kaina zuwa kan wayarsa, yayin da ni kuma na langabe kai tare da kafe shi da idanuna wadanda kadan suke jira hawaye ya fita. 

A hakan nake satar kallon reaction din Salma, wacce ta nuna kamar ba ta san abin da yake faruwa ba, wayarta kawai take tabawa.

Wannan ya tabbatar min da cewa ita din ba wawuya ba ce a waye take. 

Kamar 2-3 min muna a haka, kafin ya mike haɗe da daukar robar ruwa daya ya nufi hanyar fita ba tare da ya ce komai ba. 

Ni ma mikewa na yi da zummar bin bayan shi, lokacin da muke hada ido da Salma, ba zan iya fassara irin kallon da ta yi min ba, ba harara ba ce, kuma ba kallon sama da kasa ba ne, ba kuma na warning ba ne. Wani kallo ne me kama da, mu zuba mu gani.

Wannan ya kara tabbatar min da cewa lallai ta san kanta ba ballagaza ba ce, mace da ta san kanta ba ta nuna kishinta a gaban kishiya dannewa take yi.

Sosai akwai aiki a gabana, ko wane bangare ba sauki, Madina kudi da iya tarairaya.

Salma kuruciya, wayewa, budewar ido, kyau, ga kuma kudi saboda daga ganin kura ba sai an, tambaya ba, za ta ci akuya.

A jikin mota na cimmashi, isowa ta wurin ke da wuya ya mika min robar ruwan hade da aika min da harara.

Ban damu ba, saboda abin da nake bukata in yanke igiyar da ta hada zamansu da Salma, kuma na yi hakan. So raina fes.

Jingina na yi da motar kamar yadda ya jingina, tare da balle murfin robar na shiga shan ruwan a nutse.

Sauke robar ruwan daga bakina ta yi daidai da shigowar kira a wayar shi.

Ba bukatar in tambaya, na san da Madina yake waya.

Ya tura wayar aljihu lokacin da ya gama amsa kiran tare da fadin. “mu je”

Lokacin da muka isa hall din kowa na gabatar da kanshi ne, wanda ya fi burgeshi a Instagram, abin da ya fi son ci da sauransu.

Wannan gabar sosai ta yi min dadi tare da nishadantar da ni, yau ga ni ga celebrity din Instagram na yola mata da maza.

Lokacin da layi ya zo kan Ya Azeez ne, Ya Naseer ya zo ya janye ni zuwa wajen hall din.

Kai tsaye wajen motarsa ya dosa, ya bude motar tare da umurtata in shiga yayin da yake aje ledojin da ke hannunsa a  back seat.

Bayan ya fice daga wurin ne na ce “Wani abu ba zai faru ba idan ya dawo ya ga ba na wajen?”

Na yi tambayar cike da sanyin jiki.

“Ba zai yi komai ba.” ya ba ni amsa hankalinsa a kan tukin da yake yi.

Na sauke numfashi a hankali kamar ba zan kara cewa komai ba, Sai kuma na jefo mishi tambayar da ke zuciyata.

“Wacece Salma da na ji kana cewa na zo wurin nan ne saboda ita?”

Wannan karon ya juyo tare da zuba min idanunshi wadanda suke dauke da wani abu da ya sa na janye nawa idanun.

“Wacce ta zo wurin AZ, kuma ita ce abokiyar takarar Madina, tana matukar son shi. Babanta shi ne shugaban majalisa jiha. “

Na jinjina kai cike da mutuwar jiki, jin ita ma Salma kudi ba matsalarta ba ne, koda yake dama na ga hakan a jikinta tun da na dora idanuna a kanta.

“To me ya sa ni ya zo da ni nan?” na kara tambayar Ya Naseer. 

“Saboda ba ya son Madina ta gan shi tare da Salma.” 

“Kenan ni shamaki ce ga bacin ran Madina?” na tambayi kaina, wani abu na yi min daci a zuciya, da na san don wannan Ya Azeez zai ce in yi mishi rakiya, karon farko da na ƙi yi mishi abin da yake so. 

Da ran Madina ya yi haske gara na ba Salma Daman kasancewa da Ya Azeez. 

“Yaushe za a ta shi taron?” na yi tambayar ina kallon Ya Naseer. 

“Na san yanzu ma sun ta shi” ya ba ni amsa a takaice. 

Siririn tsoki na ja a zuciyata, na so ace taron bai tashi ba, ta yadda Salma za ta samu damar kebewa da Ya Azeez. 

Ban kara cewa komai ba, har zuwa lokacin da Ya Naseer ya yi parking a wajen gate tare da mika hannun shi ya tattaro ledojin da ya ajiye a back seat ya miko min yana fadin “Shi ne abin da za a raba, ga duk wanda ya halarci taron.” 

“Na gode” na fada lokacin da na bude kofar na fice zuwa cikin gida. 

<< Da Magana 13Da Magana 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×