Skip to content
Part 15 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Shigowa ta gidan ke da wuya Dog ya fara haushi alamun oyoyo, yayin da Monkey ke ta tsalle gami da yar ƙara alamun murnar ganina.

Duk da I’m not in good mood haka nan na yada zango a wajensu, na shasshafa jikinsu sannan na wuce apartment dinmu.

Sau biyu kacal na buga kofa Aunty ta bude tare da fadin “Dama Ina kokarin kiranki ne fa.”

Na murmusa kadan tare da fadin “Sai gani.”

Muka karasa falon a tare, haka kuma muka zauna a taren, tana tambayata Ya Azeez. Na ba ta amsa da ya wuce. Haka ta shiga tambayata abin da ya faru a wurin taron. Inda na rika ba ta labarin duk abin da na gani. Na rufe labarin da mika mata bags din da Ya Naseer ya ba ni.

Ledar farko wando n jeans fari, da shirt light blue, Sai facing cap fara, a bayan rigar an rubuta Yola Connect Daga kasa aka yi logo na Instagram, haka ma aka rubuta jikin facing cap din.

Daya bag din Kuma take away ne mai dauke da kaza daya, Sai juice din D’jino wanda na tabbatar daga Cameroon aka yo odarshi.

Ta mike tsaye, kasancewar zuwa lokacin an yi sallahr magriba, har zuwa lokacin bakinta bai yi shiru da yabon kayan ba, wannan ya sa na ji dadi sosai. Saboda ta yaba wani abu daga Ya Azeez. 

Lokacin da take hawa stairs din da zai kai ta dakinta ne ta juyo hade da fadin “Ko kin san mutuminki ya shiga dakin Hammah ya debar mishi kudade masu yawa, ba ma na Nigeria ba, na waje.”

Ido na gwalo cike da mamakin abun sannan na ce “Yaushe ya dauka?”

“Sai Allah. Dazu Hammahn yake fada min, kuma ya ce min ya kira Azeez din bai daga ba.” ta kai karshen maganar hade da juyawa zuwa saman.

Na sauke hannuna daga kan habata, tare da bude hand bag dita na zaro wayata na shiga kiran layin Ya Azeez. Gab za ta yanke ya daga kiran

“Kana ina? “na tambaye shi jin bai ce komai ba, tun da ya daga kiran.

“Mene ne? “

Muryarshi ta nuna sai da ya daure fuska sannan ya yi tambayar.

“Don Allah kar ka zo gida yanzu, Hammah yana neman ka. “

“Me ya sa yake nema na? “ya tambaye ni da alamun  sake murya kadan.

“Ni ma ban sani ba, amma dai kar ka zo.”

Tsoki kawai ya ja tare da yanke kiran

Da haka na mike zuwa dakina na yi alwala tare da canja kaya na gabatar da sallar magriba, jin an kiran sallahr isha’i ya sanya na yi sannan na mike zuwa kitchen.

Naman kazar na raba biyu, na aje rabi, rabin kuma na tafi kaiwa Dog tun da Aunty ta ce ba za ta ci ba.

Ina tsaka da ba shi naman ne motar Ya Azeez ta shigo, ya fito hannunshi rike da Ledar da aka raba wurin taron, yayin da yake sanye da jar riga bakin wando, tun kafin ya karaso wajenmu kamshinsa ya riga shi zuwa, Monkey da Dog suka yi masa oyoyo, duk take away din kazar ya mikawa dog, yayin da ya zubewa Monkey ayaba tuta guda ya juya, kala bai ce min ba.

Sai da na gama yi wa su Dog komai na al’ada, sannan na juya zuwa daki.

Misalin karfe tara na dare ina duba littafina na ji tashin muryar Hammah, wannan ya sa na fito a hanzarce, rike yake da gefen wandon Ya Azeez cikin daga murya yake fadin “Where is the key, tell me where did you get the key?” duk lokacin da bai amsa ba, ya kan kai mishi duka da murtukeken hannunshi, dukan da nake jin shi a kaf jikina.

Yadda ya kara kai mishi wata masga ne ya sanya ni fadin “Hammah sorry please. Don Allah ka yi hakuri” a tsorace na yi maganar yayin da muryarta take rawa alamun zan yi kuka.

Sai a lokacin ne Aunty da ke can tsakiyar stairs din dakinta ta ce “To ai ya ki ba shi key din.”

Cikin kuka na ce “Ya Azeez don Allah ka ba shi key din.”

“Wlh Abdul’azeez idan ba ka ba ni key din ba, yau za ka yi bacci a prison ne, that your terrorist friends, you will go and meet them there”

Na karasa matsowa kusa dasu cikin kuka na ce “Don Allah Ya Azeez ka ba shi key din, ka ga jini na zuba, ka ji ciwo.”

Aunty da ke sama ta yi saurin sakkowa, da alama ba ta san da ciwon ba, sai da na fada

“Ina ka ajiye key din?” ta tambaye shi tun kafin ta karaso inda suke

“A Ina ka aje key din na ce?” cikin tsawa ta yi kara maimaita tambayar, ganin bai amsa ta da farko ba.

Ya dago yana kallon Auntyn fuskar nan a cunkushe sannan ya ce “Yana cikin mota” daga haka ya kwace kanshi daga rikon da Hammah ya yi mishi zuwa dakinshi.

Na sauke ajiyar zuciya, ko ba komai dai hannun Hammahn ba zai kara sauka a kan lafiyayyen jikinshi ba.

Dama na san idan har Aunty ta sanya baki zai fadi inda Key din yake, sabannin Hammah da idan zai kashe shi ba fada zai yi ba.

Hammah da Aunty suka fice a tare, ni kuma na nufi dakin Ya Azeez din.

Lokacin da na shiga zaune yake a gefen gado ya dukar da kanshi, yayin da jinin ke diga a hankali daga gefen kanshi inda ya ji ciwo.

“Get out!” cikin wata irin tsawa ya yi maganar tun kafin in gama shigowa cikin dakin.

Na yi saurin ja da baya a tsorace. Yayin da na zubawa jajayen idanuna nawa idanun.

“I said get out!” ya kuma fada tare daga hannunsa yana nuna min hanya.

Na kuma ja baya saboda yadda na ga ya mike tsaye a fusace. Ya rika sauke numfarfashi kamar wanda ya ci gudu a filin tsere kuma ya zo na daya.

“Zan wanke ma ciwon ne dama.”

“Ban so” ya fada daidai ina dire maganata.

Ya ja dogon tsoki haɗe da nufo kofar fita, wannan ya sa na yi baya da sauri, na dauka dukana zai yi, sai kuma na ga ko kallo na ma bai yi ba, ya nufi kofar falo.

Dakin na shi na dawo, na shiga gyara inda ya bata da jinin. 

Sai da na gyara  dakin tsab, sannan na koma dakina.

Karatun ma gagara ta ya yi, lamarin Ya Azeez kawai nake juyawa, na rasa dalilin da ya sa yake sata, da kuma yadda yake ya n watsi da duk wata hanya da za ta zama cibiyar ta gabanshi. 

Shi dai kawai ya dau wanka, ya hau babbar mota, ya yi rayuwa ta jin dadi. 

Abun da kuma yake kara ba ni mamaki da lamarin shi, shi ne yadda iya gida kawai satar shi ta tsaya, idan har zai shigo gidan to dole sai ya samu abun a dauka. Haka na ci gaba da tsinto abubuwan ban mamaki, tsoro, alamar tambaya a lamarin shi har bacci ya dauke ni. 

Cikin bacci na rika jin haushin dog ba kakkauwa, saboda ko wane irin bacci nake ba dog ba, ko monkey ne ya yi Yar kararsa sai na ji.

Da sauri na fito falo tare da nufar window na bude labule, gabana ya yi wata irin faduwa saboda ganin inuwar Hammah yana wanka a tsakar gida.

Na sake labulen da sauri na koma kan kujera  jagwab na zauna.

Zuciyata cunkushe da son sanin ma’anar wankan Hammah a tsakar gida, kuma a tsakiyar dare.

Dog bai tsagaita da haushi ba, Sai da Hammah ya kunna wutar gidan alamun ya gama abin da yake yi.

Ni ma jiki na ja zuwa dakin, bayan na tabbatar Hammah ya shige dakinshi, ta hanyar leka tsakar gidan. Tunani kala-kala, tambayoyi kala-kala dankare da zuciyata.

Na yi zugum a gefen gado bacci ya ki zuwa, kuma na kasa yin karatu, Sai dai in ta bude littafin ina rufewa, tunani cunkushe a zuciyata, rashin sanin halin da Ya Azeez yake ciki, dalilin Aunty Adama na jera duwatsu, da kuma wankan Hammah a tsakiyar gida, sune abubuwan da suka cika zuciyata fal, na mike tsaye da zummar jaraba sallah, cikin ikon Allah kuma sai zuciyata ta rage cushewar, a kan sallayar bacci ya dauke ni.

Ban jima sosai ba Aunty ta tashe ni sallah, ina idar da sallahr game da Azkhar din safe na wuce kitchen.

Misalin 8:30am Aunty ta fita, ni kuma 9am daidai na fito don zuwa makaranta kasancewar ba a yin komai sai revision Monday zamu fara Exam.

Tun da na fito na hango Hammah tsaye tare da Hammawa, cikin shiga mai kyau, mai kuma nuna cewa shi din ya tara, ya ci ya koshi ya kuma tayar da kai.

Yayin da Dog ke ta zuba haushi daga cikin kejin yana kallon Hammah.

Gani na kuma sai ya juya haushi na shi zuwa kaina yana kallona,  ganin Hammah tsaye sai na ki zuwa wajen dog din duk da yadda ya tsananta haushinshi saboda yadda ya ga na wuce su ba tare da na leka na yi musu sallama kamar yadda na saba ba, idan zan fita.

“Sannu da fitowa Hammah” na fada lokacin da na zo saitinsu bayan na duka

“Yauwa Maryam, za a tafi makarantar ne?”

“Eh.” na amsa har zuwa lokacin ina duke

“Allah Ya taimaka.”

“Amin” na kuma amsa shi tare da mikewa na nufi hanyar fita, yayin da kunnuwana ke dakko min maganar Hammawa inda yake cewa “Wallahi Alhaji, karen can mutum biyu ne kawai ke rabarshi a zauna lafiya, fada gare shi sosai, shi ya sa ma ba a bude shi, idan ka ga an bude shi, to Yallaboi Azeez ne ko Maryam.”

Har na fice Hammah bai ce komai ba, duk da na so ya ce din, wace irin magana ake yi a kan karen, me ya ce a kan karen, amma idan na dawo makaranta zan tuntubi Hammawa.

Azeez

Tun da ya bar gidan dakinshi na hotel ya nufa, kuma bai damu  da ya tsayar da jinin da ke bin gefen fuskarshi ba, ya haye gado ya yi kwanciyar shi,  misalin 8am  ya tashi, a lokacin ne ya yi wanka brush, tare da rama sallahr magriba jiya da kuma isha’i, sannan ya yi sallahr asuba. 

Yana zaune kan sallaya Anwar ya turo kofar ya shigo cikin shirin fita aiki

“Morning bro” ya fada bayan ya shigo dakin sosai.

“Morning” Azeez ya amsa shi a hankali.

“I’m going to work, and Madina ta ce a fada ma tana zuwa, ta kira wayarka ba ka daga ba.”

Bai amsa ba, hakan ya sa Anwar ya ce “Na wuce”

“be right back” Ya fada a hankali 

“Thank you.” cewar Anwar lokacin da yake jan handle din kofar, suka yi kicibis da Naseer wanda yake kokarin shigowa dakin Azeez din, hannunshi rike da laptop, a tsaitsaye suka gaisa Anwar ya wuce, shi kuma ya shigo cikin dakin sosai.

Gefen gado ya zauna tare da dora laptop din Shi akan cinya yana fadin “Azeez come see something please”

Harara Azeez din ya aiko mishi da ita.

Naseer ya yi dariya kafin ya ce “Wai abin da ya faru jiya?  na kai ta gida ne saboda ba na son ganin ta a wurin, dalla ta zo  ka gani.”

Bai ce komai ba, amma ya mike zuwa inda Naseer din yake zaune.

Table ya janyo tare da dora laptop din sannan ya yi playing din wakar.

Azeez ya zubawa laptop din ido yana kallon yadda wata kyakkyawar budurwa ke rawa a wata waka ta Ethiopia

“What? “ya tambayi Naseer cikin rashin fahimta.

“Da wa ta yi ma kama? “

Ya yi shiru alamun tunani kafin ya ce” I don’t know “

Naseer ya kara playing din wata wakar tare da fadin” Yanzu fa “

“I don’t know “

Naseer ya dan ture shi kafin ya ce” Ba ta ma kama da Maryam? “

“Which Maryam? “

“Maryam di ta mana”

“Oh do you have a Maryam, I don’t know her?” cewar Azeez lokacin da yake tashi tsaye.

Kafin Naseer ya yi magana Madina ta turo kofar wannan ya sa ya fice daga dakin.

Sai da ta rufe kofar sannan ta karaso cikin dakin tare da rungume Azeez  kamshi shi mai dadi ya ratsa kofofin hancinta, dalilin da ya sa ta manna mishi kiss a wuya bayan ta cire face mask da ke fuskarta.

Kafin ta janye jikinta daga na shi, tare da zaunar da shi gefen gadon ita ma ta zauna

“I have a gist” Bai Amsa ba amma ya kalle ta, wannan ya sa ta ce

“A kaf duniya, ka zabi Kasar da kake son zuwa I will take you there.”

Ya ɗan yi shiru kamar ba zai ce komai ba, Sai kuma ya ce “America”

“your last choice”

Ya jinjina kai alamar eh.

“So, ni kuma zabina shi ne Dubai. I will take you there. “

Yadda bai yi murna ba ne ya sa ta ce “What is wrong with you?”

Ya ɗan nisa kadan kafin ya ce “just.”

“Are you sure?” ta tambaya cike da kulawa

“I’m very sure” ya amsa ta, duk da shi kanshi ya san yana jin wani abu mara dadi, wanda bai san ko menene ba.

Duk suka juya zuwa kan mirror inda wayar shi ke vibration alamun shigowar kira.

Madina ta mike zuwa inda wayar take, ta dakko hade da zubawa sunan da ke kan screen din ido Maryam Aunty

Ta mika mishi kiran, kafin ya daga kiran ya tsinke, Sai ya jefar da wayar gefen shi, lokaci daya kuma yana sauraron maganar Madina.

“Azeez idan mun dawo daga tafiyar nan, mu yi aure don Allah, hankalina zai fi kwanciya, amma yanzu kullum cikin tashin hankali nake.”

Uffan bai ce mata ba, kuma dama ta san ba lallai ya yi maganar ba, kamar yadda ba zai iya saba umarninta ba.

Wannan shi ta nema, kuma ta samu.

<< Da Magana 14Da Magana 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×