Skip to content
Part 17 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Duk windows din na rika bi ina lekawa, amma ba na ganin komai, saboda an rufe glass din window ta ciki, na sauka kasa cike da takaicin yadda ban samu damar ganin cikin dakin ba.

Shiru na yi tare da nazarin shawarar da zuciyata ta kawo min, wani bangaren na fada min in karba, wani kuma na hana ni.

Daga karshe dai na karbi shawarar, na nufi inda nake tunanin samun dutse, cikin sa a kuma na samo irin mai kankarar nan, a hankali na shiga kwankwasa glass din bayan na hau kujerar, daga can gefe na samu nasarar fasa glass din kadan.

Na yi saurin saka idona kwaya daya cikin dakin, cike da mamaki nake karewa dakin kallo, akwai tarin alkur’anai sun kusa sittin, sai tarin carbi, da ya tasarma dari. Dukkansu an zubesu ne a kan wata tabarmar kaba, wacce ke shimfide a cikin dakin.

Sai wasu korai irin na fulani guda biyu, an rufe su da faifai. Yayin da aka dora wasu fararen tsakuyoyi a kai .

Sai kuma wasu manyan faifai guda biyu, an cika su da farin yashi, an dora wasu tsakuyoyi a kai.

Bayan na babu komai a cikin dakin, a sanyaye na sauka, zuciyata cike da tambayoyin da ban san amsarsu ba.

“Me ye amfanin wadannan kayan a wajen Hammah?” “Su Aunty sun san halin da yake ciki ko ba su sani ba?”

A hankali na zauna kan kujerar, kafin in nemo amsar tambayoyin na ji ana kwankwasa kofa. Tunanina ya zama gaskiya, domin Hammawa ne tsaye a kofar waje.

Tun kafin ya shigo ciki ya ce “Wallahi Maryam masu naman nan basu fito ba, wai sai zuwa yamma.”

“Shi kenan, bari in dafa mishi indomie” na yi maganar hade da karbar kudin.

Ina shiga babban falo na jiyo karar wayata da ke daki, da sauri na nufi dakin, gab za ta tsinke na daga kiran, ba tare da na gama tantance bakuwar lambar ba. “Ki fito ina kofar gidanku?” Abin da aka fada kenan lokacin da na daga kiran.

Jin muryar mace ya sanya ni sauke wayar ina kara karewa lambar kallo, saboda an yanke kiran. “In fito kina kofar gida, wacece wannan din?” na tambayi kaina bayan na maimaita abin da ta fada min, yayin da lokaci daya kuma nake nazarin muryar kamar na taba jin ta.

Baki na tabe hade da daukar zumbulelen hijab dina onion color mai haske na sanya, sannan na nufi gate, cike da tunanin wa zan gani.

Tun da na bude kofar fita na hango wata dankareriyar mota baka, mai dauke da tinted glass. Ban ji tsoro ba, saboda na san zai wahala a zo har kofar gidanmu a cutar da ni.

Isa ta daf motar ya yi daidai da sauke glass din driver side, kyakkyawar fuskar Salma me cike da kasaita ta bayyana, ta rika bi na da kallo daga sama har kasa, kafin ta yi min alamun in zagaya in shigo da kanta. Na yi kamar yadda ta bukata, sai da na lalleka motar na tabbatar babu wani abu na cutarwa a zahiri sannan na zauna.

“Me ya sa kike nema na?” ta yi maganar cike da izza kuma a hankali. Sai na fara tunanin ko duk Salma haka suke ne, saboda da yawan Salmomin da na sani haka suke komai cikin takama, har da Salmar kwana casa’in, wacce ita sunan kawai ma aka ara mata ta hau, amma an shimfida mata irin characters din Salmomin zahiri.

Ni ma sai na ari irin basarwarta na ce “Saboda kina son Ya Azeez, ko ba gaskiya ba ne?” na kai karshen maganar tare da kallon fuskar ta, ta dan yi shiru kafin ta ce “Gaskiya ne ina son shi.”

“Yanzu yana ina?” Na tambaye ta da kwarin gwiwata, saboda so nake na fada mata wani labari sabo game da shi, da ba ta san da shi ba, ga mamakina sai na ji ta ce

“Ya je Amerika, daga nan suka wuce Dubai.” ta fada min cikin siririyar muryarta kamar ba ta son maganar.

Daga yadda ta yi amfani da ‘suka’ na tabbatar ta san tare da Madina suka tafi, shi ya sa na gyara zama da niyyar fada mata abin da na san ba ta sani ba, kuma idan ta ji shi yanzu duk izzarta sai ta razana ta. “Amma kin san idan sun dawo za a daura musu aure.”

Ta yi wata irin zabura tare da fadin “What?” “yadda kika ji” na kuma arar kasaitarta.

“No! No!! This will not happen, ba zai taba faruwa ba. Haka ta rika fada cikin tashin hankali, yayin da ni kuma wani dadi ya lullubeni ganin na samu abin da nake so.

“But me ya sa kika fada min wannan ma? ” Ta jefo min tambayar da ban tanadi amsarta ba a cikin agendern haduwarmu. “Saboda ba na son ki ji kwatsam!” Na ba ta amsa tare da fatan Allah Ya sa ta gamsu, Salma tana da wayau sosai, ko don tana karatun lauyanci oho.

“Thanks” Ta fada a sanyaye, wannan ya sa na san tattaunawar tamu ta zo karshe, shi ya sa na bude kofar da niyyar fita, amma ta dawo da ni ta hanyar janyo min hijab kadan, ta dora min bandir din kudi a kan cinya ta.

Girgiza kai na yi tare da fadin” Ba ki da abin da za ki biya ni”.

Sai ta yi murmushi mai dauke da izza, ni kuma na fice, daidai kuma lokacin motar Aunty Adama ta shigo layin.

Gabana ya fadi, saboda na san ta ga fitowa ta daga motar, kuma ga shi Salma har ta daga glass ta juya kan motar ta zuwa hanyar fita daga layin.

Ta babbar kofa na shiga cikin gidan, saboda Hammawa bai rufe kofar ba, daga budewa Aunty da ya yi.

Tun da ta fito take kallo na, irin kallo na tuhumar nan. “Waye ya sauke ki a mota, ina kuka je?” Ta jefo min tambayar idanunta ƙur a kaina.

Cike da tsoro na ce “Ban je ko ina ba, ba kuma namiji ba ne, Salma ce”

“Wacece Salma?”

A tsoracen na kuma cewa “Budurwar Ya Azeez ce, ta zo tambayata Azeez ne, amma wallahi babu inda na je, ki tambayi Hammawa”.

“Budurwar Azeez!”

“Eh” na amsa da sauri na dauka kara tambayata take, ashe mamaki take yi. “Yar wane gari ce?”

“Ya Naseer ya ce min yar Mubi ce, kuma babanta shi ne shugaban majalisar jahar nan” na yi mata dogon sharhi a kokarina na son ganin ba ta daura min jakar tsaba ba.

Aya ba ta kara digawa ba, ta yi hanyar part din ta.

Ni ma sai na yi namu, bakina cike da addu’ar Allah Ya sa kar Aunty Adama ta yi min wani kullin a wurin Hammah, shi ne abu ma fi kankanta a wurin ta.

Ko da ta tabbatar ta shiga dakin ta, sai ta janyo wayarta, bugu daya a can bangaren Gana ta daga.

“Kin ta fi wurin nan?”ita ce tambayar farko da ta fara jefawa Gana.

“Ban je ba tukun, na kira shi ya ce in bari sai nan da karfe biyu”

Aunty Adama ta sauke ajiyar zuciyar jin dadi. “Na gode Allah da ba ki je ba. In fada miki baya ce ta haihu.”

Daga can bangaren Gana ta ce “Bayan wa? Me ya faru?”

“Wallahi kamar na sani na dawo gida yanzu, aiko na hadu da wata zukekiyar mota a kofar gida, wai diyar dan majalisar jahar nan ce ta zo neman Abdul’azeez, don Allah ki ji bala’i”.

Cike da kakabi Gana ta ce “wannan yaron ban da wannan kaddarar ta shi ta shashanci, kila har gwamna Adamawar ma watarana zai yi”

“Na ga alama, saboda haka ta maganarki, a ja masa layi da ko wace irin mace, a cire masa sha’awa kwata-kwata, sannan wannan Salmar da Madinan farraƙu nake son a yi musu don ubansu. Sannan a koro min su daga Dubai din idan so samu ne kar su kara kwana biyu Gana”

“An gama” cewar Gana, tana taya kawarta jin zafin abin da ke shirin faruwa. “Sai na ji ki.” Aunty Adama ta fada hade da yanke kiran.

*****

Yau Litinin da ya kama kwana uku da fashe gilas din dakin sirrin Hammah, kuma kwana uku da haduwata da Salma, kwanaki ukun da nake wuni da kwana a cikin zullumi, kullum shiru nake yi in ji wani abu ya faru.

Musamman bangaren Hammah da kullum sai ya kai wa dakin nan ziyara, kuma ya yi wanka a tsakar gida, ina sanin hakan ne ta hanyar haushin da Dog yake yi mishi.

Bayan fitar Aunty zuwa wurin aiki dakin Ya Azeez na shiga, na gyare shi tsab, tare da fesa mishi room freshener sannan na fito zuwa dakina, da zummar goge kayana tun da babu aikin da zan yi.

Na goge kala biyu, na ji ana kwankwasa kofa, sai da na zare iron din, sannan na nufi kofar.

Cike da wani irin farin ciki, ɗoki gami da murna na ware idona kan Ya Azeez wanda yake sanye da shirt mai santsi fara tas mai dogon hannu, bakin wando mai santsi shi ma, sai cover baki, necktie shi ma baki, bayan shi goye da jaka baka irin ta matafiya,

Ban son lokacin da na yi tsalle na fada kan shi ba, ina ihun murna, shi ma cike da dokin ya rungume ni, fuskarshi ta kasa boye jin dadinshi sai murmushi yake.

Na sauka daga jikinsa tare da zare jakar bayan sa, ina fadin “Sannu da zuwa Ya Azeez, we missed you”

“I missed you too”
Ya fada yana yar dariya, na yi gaba zuwa dakinsa na aje masa jakar tare da fadin “yaushe ka dawo?”

“jiya.”

Na langabe kamar zan yi kuka ina fadin “shi ne sai yau muke ganinka”

“Da dare ne sosai na sauka” ya fada lokacin da yake zare takalmin kafarsa

“Me za a kawo ma?”

“That indomie and kayan ciki, I missed them”

Na yi dariya tare da ficewa zuwa kitchen, na san marinating din kayan cikin yake so a yi mishi, Sai da na hada komai sannan na koma dakina na kira Aunty na shaida mata zuwan Ya Azeez.

Indomien na fara gamawa na kai mishi, lokacin yana bayi, na dawo na ci gaba da gugata, amma har lokacin zuciyata wasai, wani irin dadi nake ji, kamar an biya min hajji.

Ba jimawa Aunty ta iso, abun mamaki sai ta rungume Ya Azeez cike da farin cikin ganinsa, haka nan sai na ji hawaye na zubar min, shi ne kawai yaronta a duniya ina ma ace Ya Azeez ya dabi’antu da dabi’u kyawawa, lallai da Aunty ta yi mishi duk wani abu da yake so a duniya, tana kawar da kanta ne a kan wasu lamuran na shi saboda dabi’unshi da ba ta so.

Hammah ma ya yi farin cikin dawowarshi, kamar yadda Aunty ta rungume shi haka ma Hammah ya rungume shi lokacin da suka hadu.

Ni kadai ya yo ma tsaraba, dogayen riguna kala uku masu kyau, baƙaƙe guda biyu sai fara daya, hade da set uku da hand bag dinsu, na ji dadin tsarabar nan ba kadan ba, na yi tsalle na yi murna sosai.

Bayan dawowar Ya Azeez gida abubuwa suka ci gaba da tafiya cikin nasara, abu daya kawai ke daga min hankali shi ne maganar auran Ya Azeez da Aunty ta ce za a yi idan sun dawo, inda kawai na ji dadi shi ne ba Salma ba Madina, tsawon sati biyu da dawowarsu babu wanda ya yi maganar Madina kuma ita din ma ba ta zo gidan ba. Sai dai mu ganta a TV tana faman campaign.

Wannan ya sa na fara tunanin ko dai Salma ta yi abin da nake so ne? Idan ya tabbata Salma ta yanke alakar Ya Azeez da Madina to ni na fi kowa farin ciki, saboda na fi tsoron karo da ita fiye da Salma.

Misalin karfe shida na yamma ina daure tuwo a leda a kitchen, Aunty kuma tana marinating kayan ciki Hammah ya shigo, fuskar nan a haɗe saboda ko gaisuwa ta bai amsa ba. Ya shiga fada “Aisha zan ci mutumcin Abdul’azeez a gidan nan, me yake nema a can dakin da ya sa ya kashe min glass, ban yi muku iyaka da dakin can ba?”

Aunty ta kalle ni, ni ma na kalle ta, cikin zuciyata ina fadin sai yau ya gano na fasa mishi glass din kenan, ga shi ya dorawa Ya Azeez laifin.

“Da yaushe to ya fasa glass din, na ga ba ya wuni a gidan ma bare kwana tun da ya dawo, sai ma ya yi kwana uku bai shigo gidan ba.” cewar Aunty a tausashe.

“Ki dai fada mishi, wallahi ya fita a idona kuma ya dauke min wancan dan iskan karen daga gida” ya kai karshen maganar hade da juyawa sai kuma ya tsaya yana kallon kofar fita daga falon kafin ya ce “yauwa zo nan, dama kai nake nema”

Tsakanin ni da Aunty ban san waye ya riga wani fita daga kitchen din ba, na zubawa Ya Azeez ido wanda yake sanye cikin kayan ball, lemon green, hatta socks da takalmin kafarshi lemon green ne, daga bayan rigar an rubuta ‘Azeez 10’

Hammah ya rika matsawa inda Ya Azeez din ya tsaya yana nuna shi da murtukeken yatsanshi tare da fadin “Uban me ka aje can dakin da ka je dauka har kake fasa min glass?”

Ya hade fuska ba tare da ya ce komai ba. Cikin tsawa da tsananin fushi Hammah ya ci gaba da cewa “karo na farko kuma na karshe da za ka hada harkarka da dakin can, saboda dakin can is outbound to all of you” ya kai karshen maganar hade da juyowa yana kallon mu.

Ya kuma dorawa da “kashedi na biyu, kar ka kara zuwa wajen Engineer Bashir ka ce na ce ya ba ka mota, kashedi na uku Azeez ba na son zaman karen can a gidan nan, ka fitar min da shi daga gida.”

Daga haka ya fice daga falon a fusace, sai a lokacin na sauke bayyanannar ajiyar zuciya tare da kallon Ya Azeez da ya juya da niyyar fita rai a bace.

<< Da Magana 16Da Magana 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.