Kallon shi nake daga sama har kasa, ban ga alamun jini ko tashin duka a jikinsa ba, kuma dama abin da nake gudu kenan. Ko ba komai na dan ji dadi, duk da yadda na ga idonsa daya na gefen dama jini ya kwanta.
Yadda ya kara tamke fuska yana kallona ne ya sanya ni janyewa hade da ba shi hanya ya wuce.
Kamar 5mins da shigarsa dakin na bi bayansa, a tsorace na ƙwanƙwansa.
Cikin murya da ke cike da ɓacin rai ya ce “Waye?”
A tsorace na ce “Ni ce.”
“What again?” ya kuma tambayata, ba tare da ya yi min iznin shiga ba, duk da kofar a bude take.
Idan har yana cikin daki baya rufe kofa, Sai dai ya, dan turo ta kadan, alamun baya daki shi ne a ga kofarshi a rufe.
Na dan tura kofar kadan yadda zan samu damar ganinsa sosai. Zaune yake gefen gadonshi, idanunsa zube a kofar dakin fuska a daure
“Dama Aunty ce, ta ce idan ka dawo in tambaye ka me za a dafa ma.”
“Liar!” Ya fada a tsawace hade da mikewa tsaye.
Na yi saurin ja da baya tsorace, na dauka dukana zai yi.
“Sau nawa zan fada miki ki daina shiga harkata, just leave me, I said stay away from me, ke kurma ce.” Ya kai karshen maganar tashi hade da jan dogon tsokin da ya tabbatar min da irin haushina da yake ji.
Take zuciyata ta karye, burina in kyautata mishi, so nake ya rika samun farin ciki koda ta bangarena ne. Tun daga lokacin da ya canja zuwa yadda yake yanzu, babu wanda yake raba ya ji dadi, na shiga goge hawayen da ke sakko min. Duk yadda na so sai ta muryata, sai da ta bayyana kukan da nake yi, cikin muryar kukan na ce”Ya Azeez wlh ba na so, ni ba na son wannan sabon halin naka, da ba haka kake ba, why are you changing your habit, please Ya Azeez don Allah ka koma halinka na da.” kuka sosai nake yi, kukan da nake yin shi daga ko wane lungu da sako na zuciyata. Har ga Allah ba na son yadda Ya Azeez ya canja.
Kallona yake kamar TV, kafin daga bisani ya ce” Ba dai za ki daina shiga harkar tawa ba ko? Please get out, kafin in sauke bacin raina a kanki. “
Har zuwa lokacin da na juya da zummar barin wurin kuka nake yi mai sauti.
“Mtsswww! “ya ja dogon tsaki tare da fadin” Zo nan dalla”
“Mtsswww! (Ya kuma jan wani tsokin) Kin wani bi kin takura min, ina ruwanki da rayuwata, haba da Allah” ya ci gaba da mita lokacin da nake tahowa.
“Me kuka dafa?”
Cikin muryar kaka na ce “chips ne”
“Me ye shi?” Har lokacin muryarshi akwai alamun bacin rai.
“Irish da ƙwai.” na kuma ba shi amsa cikin kuka
“Shi ne wani chips. Mtsww!” ya kuma jan tsokin a karshen maganar shi.
“Akwai?”
Wannan karon kai na jijjiga mishi alamar akwai tare da goge guntayen hawayena.
Wani dogon tsokin ya ja, kamar ba zai magana ba, Sai kuma ya ce “Dalla can wai me ye za ki zo kina wani yi min kuka ne, wlh zan wanke ki da mari and you know me”
A hankali na rage sautin kukan, dalilin da ya sa ya ce “Kawo min Irish din da tea, ki sanya min Ovaltine .”
Kai na kuma jijjigawa alamar to.
“Ki wanke hannunkin nan, kar ki sanya min majina dalla” cikin daga murya ya yi maganar, saboda yadda na kusa shiga kitchen.
Ban amsa ba, amma kuma na ji shi sarai, kuma ko bai fada ba, ina kiyayewa fiye da kiyayewa ma a duk abin da zai ci. Na san baya son kazanta kamar dai Aunty. To ai jini baya karya.
A falon na cimmashi zaune a 3sitter,wannan ya sa na aje babban tiren a gaban shi, na shiga hada mishi tea din yana kallo na, duk da lokaci zuwa lokaci yana jan dogon tsoki, tsokin da na rasa dalilin yin shi.
Bayan na kammala hada mishi tea din, dakina na koma hade da tsayawa saitin window ina kallon yadda yake cin abincin a nutse.
Kan 3sittern ya kwanta bayan ya gama , ba jimawa bacci ya dauke shi.
Sai da na tabbatar baccin shi ya yi karfi, kafin na fito da sanda zuwa dakin na shi, komai a gyare amma hakan bai hana ni, sake sabon gyara ba.
Da canja mishi bedsheets na fara, na kara gyara mishi closet na shi, sannan na shiga toilet nan ma na kalkaleta fes.
Fresheners na fesa mishi masu sanyin kamshi, saboda shi ba ya son turaren wuta.
Ni da kaina na ba kaina maki dari bisa dari, saboda yadda dakin ya kara kyau, musamman yadda gadon ya yi lukui cikin fari kal din bedsheets mai taushi.
Kitchen na koma ina nazarin abin da ya kamata in dafa mishi da rana. Ganin ban tuna komai ba ya sa na koma daki hade da jiran farkawarshi in ji zabin shi.
Bacci ya yi sosai, saboda bai farka ba, sai biyu saura ina kallon shi ta window yana ta mika irin ta mai tashi bacci, kafin daga bisani ya lalubi wayar shi dake gefen shi ya tura aljihu tare da ficewa daga gidan gabadaya ko dakin da na sha wahalar gyarawa bai leka ba. Takaici barkar shege.
Bacin rai ya sa ko abinci ban nema ba har Aunty ta dawo, ko hutawa ba ta yi ba muka shiga kitchen girkin abincin dare, misalin karfe shidda muka gama, kuma tun daga lokacin nake zuba idon shigowar Ya Azeez amma shiru kamar an aiki loma zagayar wuya, har bacci ɓarawo ya sace ni ban ji shigowarshi ba.
*****
Misalin karfe tara na safe, na ji buga kofa, na ajiye takardar jamb dita wacce ba na gajiya da kallo, tun daga lokacin da Aunty ta kawo min ita.
“Waye?” na fada hade bude kofar.
Yau kwana biyar kenan rabon shi da gidan, sanye yake cikin kananun kaya lemon green masu taushi, hannunshi na dama rike da gorar ruwan faro.
Kamshinsa mai dadi ya cika wurin “Ina kwana na fada a hankali.” Maimakon ya amsa min, tsoki ya ja hade da raɓa ni ya shige ciki.
Kai tsaye dakinsa ya dosa, dalilin da ya sa ni ma na wuce nawa dakin, saboda na san idan har yana son wani abu zai yi magana.
Kamar wacce aka tsikara haka na fito zuwa falon, abun mamakin da na gani ne ya sanya ni saurin komawa cikin sanɗa, tun da bai ganni ba.
Ya Azeez ne ke kokarin kwance katuwar tv plasmarmu da ke cikin falo.
Da wani irin hanzari na dauki wayata ina lalubar Aunty, a fili nake fadin “daga Aunty, don Allah ki daga Aunty, yi sauri ki daga, wayyyo! Aunty daga mana” magana nake hade da zagaye tsakar dakin nawa kamar mai dawafi
Kamar tana jin abin da nake fada ta daga kiran, tun kafin ta ce wani abu na ce “Aunty! Yi sauri ki zo gida, ga Ya Azeez na kwance miki plasmar babban falo.
“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Gani nan zuwa, gani nan yanzu in Sha Allah.”
Na yanke kiran hade da lekawa falon kadan, har yanzu tsugunne yake kansa tsaye yake kwance tvn kamar wani mai gyara, ko kuma tashi.
Zagaye daki nake yi ina fadin “Yi sauri Aunty, don Allah ki yi sauri ki zo.”
Har zuwa lokacin da Ya Azeez ya yi nasarar kwance Tvn ya fita falon da ita Aunty ba ta karaso ba, abin da ya kara daga min hankali.
Falon na fito tare da bude kofar a hankali ina lekensa, yana kokarin sanya Tvn a motarshi, mai gadi kuma ya budewa Aunty kofa ta shigo.
Wani irin dadi na ji, har wata ajiyar zuciya na sauke mai sanyi.
Ko parking mai kyau ba ta yi ba, ta bude motar ta fito ba tare da ta rufe ba.
Kai tsaye Ya Azeez ta dosa, wanda ya yi kamar bai ganta ba, saboda tuni ya saka TVn a back seat. Shi kuma ya shiga front seat.
Kofar na bude hade da fitowa na tsaya kan entrance ina kallon su hade da jin abin da ke faruwa.
Murfin kofarshi take kwankwasawa hade da umurtarshi ya fito amma fir ya ki fitowa, har zuwa lokacin da ta fara daga murya alamun ranta ya fara baci.
“Bude min kofa in dauki Tv ta Azeez.”
Sai a lokacin ya sauke glass din motar. Ban san me ya ce ba, amma na ga bakin shi ya motsa alamun magana, kila shi ya sa Auntyn ta daga murya tare da kwadawa Hanmawa maigadi kira ta ce “Dakko abu ka bige min kofar nan in dauki Tv dita.”
Ya Azeez ya fito da sauri hade da dannawa motar locked, cikin kurari yake magana “Wlh idan ka taɓa min mota, sai na farkeka da wannan wukar.” ya kai karshen maganar ta shi da zaro wata wuka a ƙugunshi,yar karama ce amma yana danna wani abu sai ta koma doguwa, tana wani irin kyalli kamar madubi.
Wani irin tsoronshi ya kama ni, kuma na san ba ni kadai ba, har da Hammawa da ya kwakkwalo mishi ido daga inda yake tsaye.
Ganin Aunty ta nufi Ya Azeez gadan-gadan rai bace, ya sanyani saurin saukowa da gudu, Aunty ita ce Uwata ita ce ubana, ta nuna min ko wane irin gata a duniya, ba zan so wani abu ya same ta ba.
Kafin in karasa tuni ta isa wajen shi, cikin murya mai dauke da madaukakin ɓacin rai take magana “Ni farke ni Azeez, idan ba ka farke ni ba, ba ka kaunar Allah. Na ce ka farkeni don ubanka.”
Ta karasa maganar tana matsawa sosai gaban shi.
Daidai lokacin na iso, na shiga jan ta baya ina kuka,ita kuma tana kwacewa zuwa inda yake tsaye yana huci.
Key din hannun shi ta fisge, tun kafin ta isa ta yi unlocked din motar, ta shiga kiciniyar dakko Tvn amma ta kasa. Wannan ya sa ta dago murya tana kiran Hammawa “Zo ka dakko min, Idan ya haifu don Allah ya farkeka.”
Sai da ta yi wa Hammawa tsawa sannan ya taho a tsorace yana kallon Azeez, wanda yake tsaye yana ta huci kamar zai yi aman wuta.
A tsora ce ya fiddo TVn hade da kinkimarta zuwa hanyar da za ta sada shi da falon Aunty, har zuwa lokacin bai daina kallon Azeez ba, har tuntube yake yi.
Key din Aunty ta jeho mishi, ta bi bayan Hammawa.
Wurin key din na nufa, na dauka hade da komawa inda Ya Azeez din yake na mika mishi, maimakon ya karbi key din sai ya kawo min warta, cikin ikon Allah na goce, ganin ya kara nufo ni, na kwasa da gudu, Sai ko ya biyo ni, yana fadin “Sai na ci ubanki wlhi, yar iska, ai ke ce kika fada mata. Ko saunawa zan fada miki ki daina shiga harka ta, yau sai na yi maganinki” karshen maganar ta shi ta yi daidai da saukar katon takalmin kambas din shi a kan mazaunaina.
Karar da na saka ya sanya Aunty juyowa, ni kuma daidai lokacin na shiga kwanar backyard din flat din Hammah a guje, Ya Azeez na bi na.
Duk lokacin da na waiga na ga yana bi na da wuka tsirara, ai sai in kara speed, Ni kaina ban san na iya gudu ba sai ranar.
Da yake flat din Hammahn jere yake da na Aunty sai na jima ban kai karshe ba, bare in shawo kwanar da za ta kawo ni entrance din Auntyn.
Shiga kwanar tawa ke da wuya, mu ka yi karo da Aunty, ashe taro mu ta yi ta nan, duk yadda take cewa in tsaya, kin tsayawa na yi, a dari na wuce ta, kuma a darin na shige cikin falon, wanda na yi sa’ar kofar a bude.
Garam! Haka na mayar da kofar na rufe hade da danna key, jikina wani irin rawa yake yi, ban taba ganin tashin hankali irin wannan ba, mutuwa na gani tsirara.
Juyawar da zan yi Sai na ga Hammawa mai gadi tsaye, ban saurareshi ba, na kuma nufar dakina a guje, key na sanya bayan na shiga, still na kara shigewa toilet na danna key, da ace ramin toilet din ma zai ishe ni shiga tabbas da ciki na kutsa.
Kirjina na dafe, yayin da Numfashina ke wani irin gudu, ji nake hancina ya yi kadan wajen shaka da fesarwa, shi ya sa na bude bakina, na rika fesar da iska da karfi, ko ina jikina rawa yake yi. Lokaci zuwa lokaci na kan ce “Wayyo Allahna! Na shiga uku!”
Azeez
Kafin ya karaso kwanar Aunty ta shigo, wannan ya sa ya rika rage speed din gudunshi, har zuwa lokacin da ya tsaya cak yana mayar da numfashi.
“Ba ni wukar nan!” ta fada hade da mika mishi hannu tana haki, saboda ita ma a guje ta taho.
Ya shiga jujjuya wukar a hannun shi yana kallon ta kafin ya ce “Ba fa tawa ba ce.”
“Ko ta uban waye ka ba ni, tun da bushewar zuciyarka, har ta kai za ka iya kashe mutum Azeez.”
“Ni fa kawai ina tsorata ta ne.”
“Karya kake yi wlh. Ba ni wukar nan. Ta Yi maganar hade da kama hannunshi ta zare wukar sannan ta ce” To ta fi.”
Daga haka ta koma kwanar da ta fito, ta bar shi nan tsaye.
Har ta kule bai dauke idon shi daga wurin da ta bi.
Takaici uku duk a sanadiyyar Maryam, Ya dauki Tv ta sa an karbe, an karbe wukar shi, abun haushi da takaici shi ne bai samu ya doke ta ba.
Lallai Allah Ya taimake ta, da ace yau ta shiga hannunsa, da yanzu ba wannan labarin ake yi ba, saboda sai ya zubar mata da hakora, sai dai a sanya mata na roba,idan Allah Ya sa ta yi tsawon kwana.
Hannunsa ya sanya du biyun ya shiga yamutsa tarin sumar shi da wani irin yanayi na bacin rai. Kamar karamin yaro haka ya shiga bubbuga kafafunshi kafin ya yarfar da hannayensa tare da fadin “Oh My God!”