Dog nake ba madara a cikin kejinsu, yayin da monkey yake taya shi lasa da ƴantsalle-tsallenshi.
Motar Ya Azeez ta shigo gidan, ya fito sanye da sport wear farare, kai tsaye wajenmu ya doso.
Bayan ya gama shafa jikin dog ne ya ce “Yau ma bai ci abincin daren ba?”
Na kalli inda abincin yake na ce “Bai ci ba.”
“Why?” cike da damuwa ya yi maganar.
“I don’t know.” Ni ma na amsa jiki a sanyaye.
Ya isa wurin abincin ya shinshina kamar yadda ko wane lokaci nake shinshina abincin idan bai ci ba
Ya ajiye gefe yana fadin “We have to see the doctor. I will take him to hospital.”
Ni dai ban ce komai ba, ya fice daga cikin cage din.
Lokacin da na dawo Aunty ce kawai zaune a falon, tana taba wayarta, shigowata ce ta sanya ta mayar da hankalinta a kaina.
Na zauna kusa da ita ina kallon abin da take kallo.
Status din Aunty Huzaima take kallo, ni ma sai na taya ta kallon, inda Aunty Huzaiman ke bayanin yadda ake yin Masar shinkafa, da yake chef ce.
Muna tsaka da kallon ne Ya Azeez ya fito sanye cikin golden yellow din riga shirt da farin wando. Kamshinsa mai dadi ya cika falon.
Tare muka aje idanunmu a kanshi.
“Ta shi ki dakko mayafinki mu je asibitin”
Ya yi maganar idanunsa a kaina. Ban dauka da ni zai je ba, shi ya sa ban yi kokarin shiryawa ba tun farko.
“Me za a yi asibitin?” Aunty ta tambaya idanunta a kaina
“Dog za mu kai ya ga likita?”
Baki bude Aunty ta ce “Ni Aisha! Karen za a kai asibiti?”
“Ba ya son cin abinci ne” Ya Azeez ya amsata a hankali
“Shi ne saboda rashin aikin yi za ku dauke shi ringidi-ringidi zuwa asibiti. Sai ka ce wani ɗa, idan bai ci ba kanshi ya yi ma wa ba”
Dukkanmu bamu ce komai ba, Ya Azeez ma kofar fita ya nufa, ni ma sai na shiga daki na canja kaya zuwa riga da siket din atamfa na dora karamin mayafi
“Sai mun dawo Aunty” na fada lokacin da na iso falon
Baki ta tabe kafin ta ce “A dawo lafiya.”
Cikin cage din na same shi yana canjawa dog sarkar wuya.
Bayan ya gama ne ya ja dog din zuwa waje, take monkey ya fara kuka, daman na san za a rina, monkey ya tsani a fita da dog shi a bar shi.
“Mu tafi da shi don Allah”
Na fada a marairaice lokacin da yake kokarin fita
Ya ɗan ja siririn tsoki sannan ya ce “Matsalarshi barna, baya zama shiru.”
“Ni zan kula da shi”
“Ki fito da shi.” ya yi maganar lokacin da yake ficewa gabadaya daga cikin kejin.
Na nufi monkey wanda ya yi zugum, kamar ya san a kanshi muke magana.
Na kwanto shi tare da kama kunnen shi na dan ja kadan ina fadin “Ka nutsu, ban da rashin ji, da kyar na samu ya ce a tafi da kai”
Ya dauke hannuna daga saman kunnenshi yana kallo na.
“Ka ji ai” na katse mishi kallon da yake min.
Idanunshi ya shiga kyakkyaftamin, ni kuma na ja sarkar da ke jinkinsa zuwa waje.
Lokacin da muka fita farfadiyar gidan ne na hango Ya Azeez ya bude back seat dog ya yi tsalle ya shige. Da muka isa monkey ma Irin tsallen ya yi ya zauna kusa da Dog ya yi wani zugudi ya nutsu.
Sai abun ya ban dariya, ban san lokacin da na tuntsire da dariyar ba, lokacin da nake daidaita zamana a cikin motar.
Ya juyo yana kallo na, na dauka zai ce wani abu ne, sai bai ce koman ba.
Duk lokacin da na wai ga back seat na ga yadda monkey ya nutsu yana ta kyakkyafta idanuwa sai in ji dariya ta kama ni.
Muna cikin tafiyar ne na ji an janye dankwalina, ko ban tambaya ba, na san monkey ne, zatona ya zama gaskiya lokacin da na waigo ya ga na gan shi sai ya dankwafa min dankwalin ya koma ya zauna. Na zare mishi ido alamun kar ya kara.
Shi kuma ya shiga kyakkyafta min ido.
Haka ya rika damuna , baya taba komai sai ni, Sai ya bari na saki jiki ya tuge min dankwali, wani lokacin ya ba ni salin-alin, wani lokacin kuma sai dai in kwace shi da karfi, mui ta kokawa. Ya Azeez ci kanku bai ce mana ba, har muka isa asibitin.
Mu muka fara fita, sannan dog, donkey kam dama bai nuna alamar zai fito ba, shi ya sa muka rufe shi, tare da sauke mishi glass kadan.
Bamu jima ba muka ga likita, Ya Azeez ne ya yi mishi bayanin matsalar dog, shi kuma ya shiga bincikarshi da taimakon Ya Azeez, saboda dog ba ya da sabo sam. har da wani abun awo ya yi amfani, ni dai ina ta kallon ikon Allah.
Bayan ya gama ne ya kalli Ya Azeez ya ce “A binciken da mu ka yi lafiya ƙalau yake gaskiya.”
“To me ya sa ba ya cin abincin?” Ya Azeez ya tambaya
“Kila ko ya gaji da cin kalar abincin , ko kuma yana tsoron wani abu.”
“Wani abu kamar me?” Ya Azeez ya yi saurin tambaya.
“Kila ko ana dukanshi, ko kuma yana jin tsoron mai ba shi abincin.”
Wannan karon Ya Azeez bai ce komai ba, sai idanu da ya zuba min. Likitan ya dora da
“Idan kuma ba a kwance shi, a rika kwance shi ya dan rika zagayawa, Idan da hali ma a rika fita da shi waje. Ko kuma ka yo mishi aure”
Tsakanin ni da Ya Azeez ban san wa ya riga kallon wani ba, a tare kuma muka dauke idanunmu mu ka mayar a kan likitan wanda ke ɗan murmushi. Likitan ya dora,
“Su ma dabbobi kamar mutane suke, suna da sha’awa, musamman idan suna ci suna koshi, ka kalli karen kan nan ma Sha Allah kamar zaki, dole ya bukaci mace, idan da ace ta macen kare ce ma, hana ku bacci za ta yi da kuka”
Ni dai aje kai na yi a kasa kamar tunkiya, ji nake kamar tona rami in shige
“Shi kenan doctor, za mu yi waya, yanzu ba maganin da za a bamu?” Ya Azeez ya yi maganar lokacin da ya mike tsaye hannayensa zube cikin aljihu
“Babu wani magani, kawai dai a rika kokarin canja mishi abinci, ba abinci kala daya ba.”
“Ok to mun gode”
Ya yi maganar yana mikawa likitan hannu, zuwa lokacin tuni na kai kofa, shi ya sa har na isa wurin motar su basu karaso ba.
Monkey Yana ganina ya zaro hannunshi tsakanin glass din da aka bude, na kama hannun na rike gam, yay ta ja na ki saki, yadda yake ta kokarin fito da kanshi ta tsakanin glass din da yadda yake kokarin kwace hannunsa shi ne ke ban dariya, shi ya sa nake yin ta silently har Ya Azeez ya karaso.
“Ke ce ke koya mishi rashin ji kenan?”
Na saki hannun monkeyn tare da fadin “A’a”
“Ba ga shi na gani ba, tun da muka taho yake son ku yi abun da kuka saba”
Wannan karon komai ban ce ba, illa murmushi da na yi.
Bayan mun dauki hanyar gida ne, Ya juyo yana fuskantata, cikin alamun muhimmantar da zancen da zai yi ya ce “Wa kike tunanin yana maltreating na dog?”
Na yi shiru alamun nazari kafin in ce “Gaskiya ba na ce ba.”
“Ko Mamansu Huzaima?” ya tambayar idanunsa a kaina.
Na shiga girgiza kai tare da fadin “Ai Aunty Adama ko sashen da Dog yake ba ta isa ta raɓa ba, tsoronshi ma take ji.
Ya jinjina kai alamun gamsuwa da magana ta kafin ya ce” To ko Aunty ce? “
Kan na kuma girgiza tare da fadin” Aunty ba za ta yi maltreating na shi ba”
“Ba fa ta son shi kin sani” ya kuma jaddadamin
“Du da haka” Ni ma na karfafa amsata ta farko.
Duk muka yi shiru, kamar ba zai kara magana ba sai kuma na ji ya ce “To ko Hammawa ne?”
“Ba zai yi ba shi ma”
“Hammah ne?” ya kuma tambayata
Na yi shiru ina nazarin tambayar ta shi, tabbas Hammah ya tsani dog, ba ya son ganin shi, saboda haushi da yake mishi, amma kuma ba, zai iya dukan dog din ba, bai isa ma ya je kusa da shi ba.
“Shi ne ko?” ya kuma tambaya ta
Bayyanannar ajiyar zuciya na fitar kafin in ce “I don’t think so?”
“Why?”
“Saboda Hammah da Aunty duk basu isa su je kusa da dog ba”
“To idan basu ba waye, ke ce?”
Na zaro ido ina fadin “Wlh ni ban taba dukanshi ba, kuma a tambaye shi a ji ga shi nan” na juya baya ina kallon dog wanda yake zaune yana kallon mu
Tsoki kawai ya ja ba tare da ya kara cewa komai ba.
Gefen hanya muka tsaya ya siyo wa dog nama monkey Kuma ayaba, Amma bai basu a cikin motar ba.
Lokacin da muka isa gida Hammah na shirin fita, ganinmu sai ya fasa shiga motar ds ya yi niyya har mu ka fito a tamu motar
Dog kuwa ganin Hammah sai ya fara sana’ar ta shi ta haushi.
Cike da bacin rai Hammah ya ce “Wato Azeez ba dai za ka daina daukar min kudi a daki ba ko?”
Bai jira cewar Ya Azeez din ba ya dora”kar ka sake ka ce min ba kai ba ne, saboda camera ta nuna min Kai. Ina ka kai min kudi masu yawa haka Azeez. Saboda Allah me za ka yi da wadannan kudin masu yawa haka?”
Yadda Hammah ya karasa maganar sai na ji sosai ya ba ni tausayi, da alama wannan karon Ya Azeez ya guma mishi, ma fi munin gumawa.
Motar da ya fasa shiga dazu, ita ya shiga yanzu, Sai da ya zo saitinmu ne ya ce” Kar in dawo in samu karen nan a gidan nan, idan ba haka ba zan sanya a kashe min shi wlh”daga haka ya fice daga gidan.
Mu ka kalli juna ni da Ya Azeez, ni furucinka Hammah na karshe ne ya ba ni tsoro.
Ya Azeez kuwa cikin cage ya mayar da su dog, sannan ya ce min in sanya ido a kan abincinshi fiye da can baya.
Kai kawai na daga ina kallon yadda ya nufi bangaren Aunty Adama duk da ya san tana ciki ba ta fita ba. Ko me zai yo oho?
Dakin Aunty na fara yi wa tsinke, kwance take ganina bai sa ta tashi sai dai ta ce “Na dauka gado aka ba ku”
Na yi dariya hade da ficewa na ja mata kofar.
Har na doshi dakina kuma sai na fasa shigar na nufi kofar fita, ganin Ya Azeez yana kokarin bude kofar Hammah ya sa na nufi wajen kaina tsaye.
Ina tsaye har ya bude kofar ya shiga ni ma sai na bi bayan shi, cike da mamaki nake kallon yadda yake disconnecting cctv cameran da Hammah ya sanya, bai dauke shi wani lokaci ba ya kamalla. Sannan ya juyo yana kallo na”Idan ya dawo ki fada mishi kin ji ko”
Na lashi labbana da suka bushe ba tare da na ce komai ba,
“Ina zuwa.” ya fada hade da yin hanyar waje.
Bayan fitarsa ne na tuna, ni ma fa ina da case da dakin Hammahn, cikin sauri na haura saman, na shiga tattaba handle din kofofin Ko wacce a kulle, ta dakinshi ce kawai a bude, tsaye na yi a tsakar dakin bayan na shiga, ina kare mishi kallo, tangameme ne kamar dai nasu, bambancinsu kawai shi ne wannan na Hammah, don haka shirin dakin maza aka yi wa dakin, waccan kuma na mata ne.
Na nufi durowar mirror cikin sauri na janyo ta na shiga bincikawa, ina cikin binciken ne Ya Azeez ya shigo.
Da sauri kuma a tsorace na mike tsaye ina kallon shi kamar zan cinye shi da idanuna
Ya dauke idanunshi daga kaina tare da nufar durowar kayan Hammah, wata loka ya bude, sai ga hannun shi dauke da tarin wasu keys masu yawa.
A matukar tsorace na bi bayan shi, har zan wuce sai kuma na fasa na kutsa kai dakin da na ga ya bude ya shiga.
Baki na bude tare da kwalo ido saboda abin da na gani.
Jakukkuna ne irin na Ghana must go sun fi talatin, dukkansu shake da kudade na different countries, ban taba ganin garin kudi haka ba sai a ranar.
Daya daga cikin Ghana must go din ya dauka, tare da miko min key din yana fadin “Idan kin gama ki mayar da keys din inda kika ga na dakko su”
Kamar wata wawiya haka na mika hannu na karɓi keys din, na bi shi da idanuna har ya bacewa ganina.
Na sauke ajiyar zuciya haɗe da juyawa ina kallon cikin ɗakin, “Ina Hammah zai ka wadannan kudaden? Dole Ya Azeez ya rika sata yana shan sharafinsa, kudi kamar a dakin buga su. Yanzu wasu na can yau ko kudin da zasu sa yi abinci basu da shi, amma ga tarin kudi a nan kamar zasu yi magana”
Hannun na sanya a kasalance na janyo kofar tare da sake key din ta na murza.
Kamar in mayar da key din in fita daga sashen sai kuma na tuna, ba lallai in kara samun irin wannan damar ba. Na rika bin duk kofofin ina gwada musu key, duk wacce ta bude sai in leka in ganewa idona, kofa ta farko da na bude wani store shake da kayan gona, dangin Masara, shinkafa, wake, gyada da kuma dawa. Sun fi buhu dubu biyu, ni ban san ranar da aka shigo da su ba ma, haka na kulle kofar na shiga ta gabanta, nan kuma kayan electric ne sabbi dukkansu cikin kwali, kofar na rufe hade da bude ta gaban ta.
Na yi saurin sake handle din, gabana na irin wata faduwa…