Skip to content
Part 25 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

“Aunty! Aunty!! Aunty!!!” Haka ya rika kwala mata kira daga inda yake tsaye, Sai kuma ya juyo hade da fisgar hannuna, muka fice daga cikin dakin a tare.

Da sassarfa muka rika haura stairs din, har zuwa lokacin da ya tura kofar dakin hade da kiran sunan Aunty.

Ta sauke wayar da ke kunnenta lokaci daya kuma ta ware idanunta a kanmu

Cikin wani irin yanayi mai kama da firgici ya ce “Kin san me yarinyar nan take fada kuwa?”

“Me ta fada?” Cewar Aunty tana kallonmu

Ya juyo da kallon shi zuwa kaina ya ce “Maimaita abin da kika fada min.”

Na tabe baki da niyyar kuka, tsawar da ya daka min ce ta hanani yin hakan.

“Please. Ba fa fada ba ne Abdul’azeez, bi ta a hankali mana” Aunty ta fada a tausashe, kafin ta ce “Me ta fada maka, fada min kai ina ji.”

Ya zame hannunsa da ke cikin nawa, tare da tattara hankalinshi a kan Aunty ya shiga labarta mata abin da na fada mishi, Ya rufe da “Wai har ni ma kama nake mata da Zombie, ni fa!” ya nuna kanshi da yatsa, da alamun bacin rai a fuskarshi.

Aunty da ta nutsu shiru tun da ya fara maganar ta ce “But this is serious issue Azeez, bai kamata ka ji haushi ba”

“Amma Aunty ni za ta ce ina mata kama da Zombie”

“please get out, I want to talk to her please” Cewar Aunty hade da nuna mishi kofar fita

Ya fice rai a bace, ita kuma ta juyo zuwa inda nake tsaye ta ce “Zo nan Maryam!” na karasa kusa da ita, Sai ta karasa janyo ni na zauna gefen ta.

“Abin da ya fada gaskiya ne?”

Na daga kai alamar eh. Ina share hawayen da suka gangaro min

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali hade da furta “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un”

Duk mu ka yi shiru, kafin ta katse shirun namu da fadin “Tun yaushe kenan wannan ya fara?”

A hankali na ce “Wajen wata biyu kenan.”

“Amma me ya sa ba ki fada min ba?”

“Ba na son tayar miki da hankali ne.”

Duk mu ka yi shiru, ta kara katse shirun namu da fadin “Daga yau ki dawo dakina da kwana da duk wasu al’amuranki, sannan zan sanar da Hammah”

Na jinjina kai alamar na fahimci maganar tata

“Kina yin addu’a kuwa?”

Na dan yi shiru kamar ba zan amsa ta ba, Sai kuma na ce “Ina yi”

“Ki kara yi kin ji”

Na jinjina kai alamar to.

“Tashi mu je dakin na ki?” ta karashe maganar hade da mikewa tsaye.

Tana gaba ina bin ta a baya mu ka rika sauka stairs din.

A main palour muka cimma Hammah tare da Ya Azeez, da alama magana mai muhimmanci suke yi.

Ganinmu ya sanya su mayar da hankalinsu a kanmu.

” Zo nan Maryam!” cewar Hammah yana kallo na

Gabana ya rika wata irin faduwa har zuwa lokacin da na karaso wajen shi na duka kan gwiwata.

“Auntynki ta fada miki abin da na fada mata?”

A tsorace na shiga girgiza kai alamar a’a

“To ni yanzu zan fada miki, Bandi ya nemi auranki, kuma na amince mishi”

Kamar ana tsittsinka min jijiyoyin jikina haka na ji maganar, yayin da bakina ya rufe ruf, duk da so nake in cewa Hammah ni ba na son Uncle Bandi.

“Wai Hammah lafiyarka kuwa?” cewar Aunty idanunta a kanshi

“Na yi abu sabanin na lafiya ne?” shi ma ya tambaya idanunshi a kanta.

“To amma haka ake aure fisabilillahi. Haka kawai sai ka bayar da yarinya, tana so ko ba ta so. Ya kamata a tambaye ta ai. Kuma yanzu ma ba ta aure muke ba, ta lafiyarta muke yi.” cewar Aunty rai a bace.

“Aisha. Yanzun kam ana maganar so ne, Bandi yana da wata damuwa ne?”

“Ko yana da damuwa Hammah ko ba shi da ita, ya kamata a ji ra’ayin yarinya?”

“Ra’ayi kuma, ni ne zan bi ra’ayinta kenan?”

“A maganar aure hakan ba laifi ba ne, Ya kamata a ji ta bakinta, ba kawai ka dauki yarinya ka ce ka bayar da ita ga mutumin da basu taba wata magana ta soyayya ba”

“Kina ta maganar soyayya Aisha. Kina sona lokacin da kika aure ni. Please mu fadi gaskiya.”

“Wancan lokacin daban.”

“A’a! Duk mune gaskiya.” cewar Hammah yana girgiza kai

“Ni dai a tambayi yarinya idan tana so”

“Bayan kin gama zuge ta ” Hammah ya fada cikin fushi.

Ta kara matsowa sosai kusa da inda nake a duke ta ce “Ni ba zuga ta ba, amma kuma ba zan bari a yi mata dole ba. Ga Maryam nan ka tambaye ta, idan tana son Bandi ina goyon bayan hakan dari bisa dari, idan kuma ba ta so, to maganar gaskiya ba za ta aure shi ba. Sai dai kuma idan iyakata za a nuna min ta ba ni ce na haife ta ba. “

” To ai kin ji, kin ji irin halin na ku na mata, ba damar mutum ya yi abu sai kun canja mishi ma’ana. Aisha ko ke ce kika haifi Maryam na ce ga abin da nake so ta yi kin isa ki hana ne? Ke da ita duk karkashin ikona kuke.” Cewar Hammah yana kallon Aunty.

Falon ya yi shiru kamar ba kowa, kafin Hammah ya katse shirun

“Shi kenan zan yi abin da kike so, but you have to know that a nan inda muke komai zai kare. Idan Maryam ba ta son Bandi, to a nan din inda muke za ta fada min wanda take so. Idan ba haka ba zan aura mata Bandi”

“Wai Hammah lafiya kuwa? Ya haka?” cikin yanayi na mamaki Aunty ta yi maganar

Jin bai amsa ba ta kuma cewa “Aure haka da gaggawa, ba shiri.”

“Waye ya yi gaggawar? Ina tunanin mun yi maganar nan da ke tun watanni biyu baya. Ko Maryam din ba ta isa aure ba ne?”

Jin ba ta amsa shi ba ya mayar da hankalinsa kaina tare da fadin “Ke! Kina son Bandin ne?”

Kan Aunty na fara dora idanuna, na mayar kan Ya Azeez wanda ya yi tsaye kamar zane. Kafin na sauke a kan Hammah wanda dama ni yake kallo.

“Ina jin ki.”

Na kwaɓe fuska kamar zan yi kuka kafin na shiga girgiza kaina, alamun ba na son shi

“Ki bude baki ki yi min magana” cewar Hammah a tsawace

Na dan ja baya cike da tsoron shi, lokaci daya kuma na fashe da kuka.

“Ki yi magana ba kuka.” Aunty ta fada da alamun fada-fada, ba kuma fada ba.

Cikin kukan na ce “Ni ba na son shi”

Hannayenta ta watsa tare fadin “Period”

“Ba kya son shi?” Hammah ya kara tambaya ta

Na daga kai alamar eh, lokaci daya kuma Ina sharce hawayena.

Ya gyara tsayuwarsa tare da fadin “Na ji ba kya son shi, kuma na yarda ba zan aura miki shi ba, amma bisa sharadin a nan inda kika fadi ba kya son na shi, a nan za ki maye gurbinshi da wani.”

“Hammah…” cewar Aunty da sauri, shi ma cikin saurin ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yana fadin

“Aisha your mouth kept please, just watch it”

“Amma…”

“I said watch it!” cikin tsawa ya yi maganar.

Wannan ya sa dole ta yi shiru.

Ya juyo kaina, cikin muryar da ke nuna alamun rashin wasa ya ce “Maryam fada min wanda kike so, idan ba haka wlh zan daura miki aure da Bandi nan da sati biyu. Ina son ki yi aure ne, ba na son ki kara wata daya a gidan nan, saboda wasu dalilai nawa. Fada min wa kike so? “

Shiru na yi saboda ban san me zan ce mishi ba. Ni da ban taba yin saurayi ba, wa zan kama

“Ina jin ki.” ya katse min tunanina

Wani shirun na kara yi, shirun da ya dauke mu wajen mintuna goma

Inda ya katse shirun da fadin “a take uwarki ta ce ba ta amince da Bandi ba, kuma kika goya mata baya. Ni ma kuma a take na yi rantsuwar a kan sharadin da na ba ki. Matukar ba ki amsa shi a take ba, to zan yi abin da na fada miki tun farko”

Yana gama fadin haka ya juya zuwa kofa, da sauri na mike na bi bayan shi hade da kiran sunanshi.

Bai amsa ba amma ya dakata daga tafiyar da yake yi

“Don Allah Hammah ka yi hakuri”

“Na yi hak’uri ai, amma matukar kafata ta fita daga falon nan, wlh bakin alkalaminki ya bushe”

Na kuma juyowa ina kallon sashen dasu Aunty suke tsaye kamar an dasa su.

Idanuna na lumshe saboda wani tunani da na yi.

Da alama wannan ita ce hanya daya ta cikar burina, kodai in samu abin da nake so, ko kuma a fasa hadani da Uncle Bandi.

Na bude Idanun a kan Hammah wanda yake kallo na.

Na ta ka a hankali zuwa kusa da shi. A hankalin kuma na ce “Ina da wanda nake so.”

Komai bai ce min ba, Sai kallo na da yake yi.

Kamar mai raɗa na ce “Ya Azeez nake so” na kai karshen maganar cikin zubar hawaye, yayin da gabana ke wani irin bugu.

Cikin wani murmushi da na rasa ma’anar shi Hammah ya ce “Kin ji to Abdul’azeez take so” ya yi maganar yana kallon Aunty.

“Wane Abdul’azeez din kuma?” da hanzari Aunty ta yi tambayar hade da takowa inda muke

“Na nan gidan” Hammah ya amsa ta har zuwa lokacin murmushi bai gushe a kan fuskar shi ba

Cikin kidima Aunty ta ce “Amma ba ki da hankali Maryam. To ba gara Bandi din ba ma, kin san ina ya dosa, amma Azeez mijin aure ne. Mutumin da bai aje ba, bai ba kowa ajiya ba. Sai shirme kawai. Shirmen ma na banza da wofi.”

Sosai Hammah ya fashe da dariya kafin ya ce “Tun da ta ce Abdul’azeez din take so magana ta kare Aisha. Ni na rasa ma ina kika dosa. Kin ce ba kya son Bandi, yanzu ma Abdul’azeez din kin ce ba kya so”

“Ni fa ba Bandi ne ba na so ba, ba na son dai a aura mata wanda ba ta so.” cewar Aunty tana kallon Hammah

“To yanzu kuma ta fadi wanda take son kin ce ba ki yarda ba.” Hammah ya fada cikin dariya.

Irin dariyar nan da ke kular da mutum.

Da alama kuma Auntyn ta ƙulu, cikin bacin rai ta ce

“Azeez bai cancanci ya zama mijin Maryam ba, ba na fata ta auri miji irin Azeez. Ni na san ba ta son shi. Matsawar da ka yi ne ya sanya ta ce shi.”

“Oho kuma.” In ji Hammah lokacin da yake tunkarar kofar fita.

Bayan ya fita ne ta juyo inda nake tsaye tare da fadin “Ba ki da hankali, ko ce miki aka yi Abdul’azeez ne mijinki ai har kotu za ki iya kaiwa a kwatar miki hakkinki, bare ke ki zabe shi da kanki, in don maganar Hammah ne ki bari ni zan lallashe shi. Amma kam ba za ki kare da auran Azeez ba.”

“Ni ma ban tashi aure ba, gara ma ki matsa mata ta janye maganarta gaskiya. Ni babu wata yarinya da zan aura.” karon farko da Ya Azeez ya yi magana cike da bacin ran da ban taba gani a fuskarshi ba

“Kai da Allah can! Kai ka samu Maryam a matsayin mata ai ka more, wlh kai ke da barka, ita kam sai dai a yi mata jaje.”

“To me ya sa za ta ce ni? Ni dai ba zan aure ta ba”

“Ita ma Allah Ya kyauta ta aure ka.”

Ya tako a fusace zuwa inda nake tsaye ina kuka ya nuna ni da yatsa tare da fadin “Tun wuri ki je ki janye abin da kika fada, idan ba haka ba, wlh za ki yi danasani.”yana gama fadin haka ya fice a fusace

Yayin da Aunty ke ta aika mishi da zagi da baƙaƙen maganganu.

Duk gidan sai ya rikice a kwanakin, tsakanin Hammah da Aunty ba dadi, saboda ta ce ba ta san maganar aurena da Ya Azeez ba.

Shi kuma ya ce ita ra sani, wannan abun ba karamin yamutsa hazo yake yi ba.

Ni a bangarena rashin lafiyata ce ta fi damuna ba maganar aure ba, saboda har ga Allah zabina kenan auran Ya Azeez, kuma ba na fatan Hammah ya sauka daga kan wannan bigiren.

Ban damu da yadda Ya Azeez ya yi mana yaji ba, ni dai fatana Allah Ya ban lafiya.

saboda tun daga lokacin da na dawo dakin Aunty da zama ciwo ya yi worst, har suma nake yi, aiki kam dole Aunty ta dauki leave ga cikinta da yake ta kara girma.

Ni kam ko makiyina ya kalle ni ya san cewa ina jin jiki.

Ku san kowa a dangi sai da ya zo gaishe ni, hatta su Aunty Huzaima sai da duk suka zo.

Aunty Adama duk kiyayyarta gare ni kullum sai ta shigo duba ni.

Magani kam babu kalar wanda ba a yi, wani lokaci abu ya yi sauki, wani lokaci kuma ya karu.

Hammah ma yana bakin kokarin shi kudin magani ko nawa ne zai biya.

kashi da fata ne kawai suka rage a jikina sai jijiyoyi.

Wasu masu maganin sun ce Mayu ne suka kama ni, wasu kuma suka ce gamo na yi, ko wanne da irin abin da yake fada.

Ni kam ko me suka ce ma zan iya yarda, saboda abubuwan da nake gani sun wuce hankali, wasu su ban tsoro wasu kuma ko tsoron ma basu ba ni, saboda na saba da ganinsu.

Kamar yanzu ma da nake kwance a falo da Ledar drip a hannuna, Aunty kuma na kitchen tana girki.

Ido biyu ba wai bacci nake yi ba, na ga wani katon zakara jawur, bakinshi duk jini ya faso bangon falon ya fito.

Na rika kallon yadda yake tunkaro ni, bakinshi na digar jini.

Na kwadawa Aunty kira lokacin da na ga ya fisge drip din da aka sanya min.

Tsakanin rufe bakina da fitowar Aunty ban san wanda ya riga wani ba.

Ta duka saitin kaina tare da fadin “Maryam, me ya faru?”

Cikin muryar rashin lafiya na ce “wani zakara ne ya fisge drip din, kin ga ya diga min jinin bakinshi a hannuna.”

Ta lumshe ido cike da damuwa tare da fadin “Ki rika addu’a Maryam don Allah. Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Ni Aisha wane irin abu ne wannan. Allah ka kawo min saukin wannan abu.”

Ni dai kallon ta kawai nake yi ba tare da na ce komai ba. Ta shiga tofa min addu’o ‘I kamar yadda ta saba

Saboda ni dai ko wace addu’a ma ta bace min, dama-dama idan wani yana yi a zahiri ina iya bin shi, amma ni kadai ban iya tuna komai.

Jagwaf na ga ta zame ta zauna a kasa, zuwa lokacin na fahimci hankalinta a matukar tashe yake. Damuwa karara ta bayyana a kan fuskarta.

Kamar daga sama Ya Azeez ya turo kofar falon ya shigo. Rabon da ya zo gidan kusan wata daya kenan, tun ranar da na ce ina son shi.

<< Da Magana 24Da Magana 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×