Daga kwancen da nake na rika bin shi da kallo, sanye cikin fararenn kaya riga da wando cotton masu taushi na gaske, sosai ya kara canjawa, jikin nan subul, ga wata kiba ta ban sha’awa, gashin kan nan ya kara baƙi hade da cika, kamshinshi mai dadi ya cika falon.
Ya dauke idanunshi daga kaina zuwa kan Aunty wacce ta janye tagumin da ta yi tana bin shi da ido har zuwa lokacin da ya zauna kan kujerar da ke fuskantarta yana dan murmushi kasa-kasa.
“Allah Ya shiryeka Azeez” cewar Aunty cikin yanayin da ke nuna sarewa.
Jin bai yi magana ba ta kuma cewa “Azeez ace ƴan’uwarka kamar Maryam da take kaunarka da gaskiya, ba ta da lafiya, a dangi har da ban yi tunanin zuwanshi ba ya zo ya duba yarinyar nan, amma ban da kai, ka kyauta na gode da wannan.”
Ya kai kallon shi kaina kafin ya mayar kan Aunty a hankali ya ce” Ina Abuja fa”
Cikin zaro ido ta ce “Abuja kuma? Yin me?”
Ya shafa tarin sumarsa sannan ya ce “Competition na je a kan zane-zane?”
Tabe baki ta yi cikin rashin muhimmantar da zancen tare da fadin “Har tsawon wannan lokacin?”
“Eh.” ya amsa a takaice
Bakin ta kuma tabewa ba tare da ta ce komai ba
Shi ne ya ce “Wai ita me ya same ta, ta zama haka?” ya yi tambayar idanunshi a kaina
Aunty ta juyo zuwa inda nake kwance tana bi na da kallo kafin ta ce “Ba ta da lafiya har yanzu.”
Ya rika kallona ba tare da ya ce komai ba, kuma fuskarshi ba ta labarta min abin da ke cikin zuciyarshi ba.
Ni dai sosai ganin shi ya faranta raina, na ji duk wata damuwata ta ragu. Har wani karfi na ji hade da kuzari.
Aunty ta mike zuwa kan stand ta dakko tissue hade da goge jinin da ke kan hannuna, ta mayar min da drip din, sannan ta wuce zuwa kitchen.
“Sorry!” cewar Ya Azeez a hankali
Na daga kai alamar na ji.
“Kina shan magani kuwa?”
Na kuma daga kai alamar eh
“Me ke damunki haka to, ko ba kya cin abinci?”
Wannan karon shiru na yi ban amsa shi ba. Saboda ban san me zan ce ba.
Ya mike tsaye da zummar tafiya Aunty ta fito hannunta rike da karamin bowl.
“Aunty wai wannan tana shan magani kuwa?” Cewar Ya Azeez yana kallon Aunty
Cike da damuwa ta ce “Tana sha, ciwon ne bamu San ma irin shi ba, magani yi ake amma duk a banza, wlh na fara tsorata Abdul’azeez.” Cike da mutuwar jiki ta karasa maganar, wanda ya sa na jikin Ya Azeez ya saki sosai.
Falon ya yi shiru, Sai Aunty da ta zauna a inda ta tashi dazu, hade da aje bowl din da ke hannunta mai dauke da kankana da kuma ayaba.
“To me aka ce yana damunta? Ya kuma tambaya a sanyaye
” Sai Allah. Kowa da abun da yake fada, muna nan dai muna ta magani har zuwa lokacin da za a dace. Amma kam ina cikin damuwa hade da tashin hankali, duk lokacin da na kalli yadda Maryam ta koma, ji nake kamar akwai laifina, ban rike amanarta ba.”
Ta kai karshen zancen hade da sharce hawayen da suka gangaro mata
Falon ya kuma yin shiru, idan ka dauke gunshekin kukan Aunty.
Ya Azeez kuma yana tsaye kamar fol.
“Na fara tunanin tafiya da ita Gembu wurin Baffa, ko za a dace” Cewar Aunty cike da jimami
Kai ya shiga jinjigawa alamun gamsuwa tare da fadin “Tunani mai kyau. Saboda wannan abun ya yi yawa”
Duk suka yi shiru, kafin Aunty ta ce “Kun bar ni da kiwon biri, bari in kai masa abinci” ta kai karshen maganar hade da nufar kofa.
Falon ya rage daga ni sai Ya Azeez wanda ya zuba hannayensa du biyun cikin aljihu, yayin da fuskarsa ke nuna alamun zurfi cikin tunani.
Wannan ya kara ba ni damar kare masa kallon irin cikar da ya yi a sati daya da ban gan shi ba.
Tausayin kaina ya kama ni, a yadda na koma din nan na san Ya Azeez ya fi karfina, da lafiyata ma yana ganin ni din ba ajin shi ba ce bare yanzu da na zama kashi da rai.
Juyowar da ya yi ne ya sanya ni janye idona cikin sauri zuwa wani sashen.
Ya tako zuwa saitin kaina hade da dukawa, wannan ya haddasa min mutuwar jiki duk da ina fama da ciwo.
“Bayan ba na nan, su Nasir sun zo gidan nan?”
Na girgiza kai alamar a’a
“Da gaske?”
Na daga kai alamar eh.
“Na ji dadi” ya fada a hankali bayan ya yi shiru na ƴan dakiku.
Mikewa tsaye ya yi tare da mayar da hannayensa cikin aljihu.
“Ba na son su ga Aunty da ciki, shi ya sa duk na ci ubansu, mu ka ɓata”
Na ɗan murmusa kadan, hade da juyar da kaina gefe, ban san me ye matsalarshi da cikin Aunty ba, shi da za a yi wa ɗan’uwa ko yar’uwa.
Shigowar Auntyn ce ta sanya shi nufar hanyar kofar dakin shi.
Misalin karfe biyar na yamma, zaune muke a falo mu uku, ni, Aunty da kuma Ya Azeez.
Kamar kullum sanye da nake da doguwar riga, bayan Aunty ta taimaka min na yi wanka.
Doguwar riga ita ce kawai take rufa asirin ramar da na yi.
Kuzarina yau na daban ne, saboda zuwan Ya Azeez, har tsokanata Aunty ke yi, wai ganin Ya Azeez ya sa na ji sauki.
Yanzu ma idanuna a kanshi, sanye yake da bakin wando bakar riga, da bakar facing cap wacce ya juya, yayin da kafarshi ke sanye da fari ƙal din cambas. Kankana yake sha a hankali hade da tattaba wayarshi, Aunty ma wayar take tabawa, ni ce kawai shiru illa raba ido da nake tsakaninsu su biyun da kuma tv wanda karatun alkur’ani ke fita a hankali.
Turo kofar da aka yi ne ya sanya mu juyawa zuwa kofar, Hammah ne tare da Aunty Adama, da alama ita daga aiki take, shi kuma daga commitment din Shi.
Ya Azeez ne ya fara dauke kanshi ya mayar kan abin da yake yi, ni da Aunty kuma muka shiga gaishe su.
Aunty Adama ce kawai ta ce min ya jiki.
Na amsata da sauki, kafin ta juya zuwa kofar fita, Hammah kuma ya shiga tambayar Ya Azeez yaushe ya dawo.
Kamar ba zai amsa ba ya ce “Jiya”
“Wannan Shekarar ba za ki je umrar ba ne Aisha, azumi yana ta karatowa, ban ji kina batun ba.”
Cewar Hammah yana kallon Aunty, lokaci daya kuma yana zama a kan kujerar da ke fuskantarta
Ni ta fara kallo kamar ni zan amsa tambayar, kafin a sanyaye ta ce
“Ba na jin zan je”
“Saboda ciki wai? In don shi ne ai ba damuwa, idan kin haihu a can ma ni ina so”
Yana maganar ina kallon Ya Azeez wanda ya yi kicin-kicin da fuska kamar Hammah na fadin wani mummunan sako.
Sosai ya ban dariya, Sai dai kawai ban yi ba.
“Ba don ma haka ba, ina son zuwa Gembu ne” cewar Aunty tana kallon Hammah
Cike da mamaki ya ce “Gembu kuma, ina sai bayan sallah kike zuwa, me ya sa yanzu, ga kuma yanayin jikinki sannan tafiya ba kusa ba”
Sai da ta ja numfashi sannan ta ce “Saboda Maryam, ina son zuwa wurin Baffa da ita, ko akwai taimakon da zai yi mana”
Hammah ya mayar da hankalinshi kaina, na yi saurin yin kasa da kai, kamar munafuka.
Da yanayin ko-in-kula ya ce “Allah Ya kiyaye hanya, a motar haya ko ta gida za ku dauka a samu direba?”
“Ga Azeez nan, tun da ya dawo ai sai ya kai mu” cewar Aunty tana kallon Ya Azeez din
“Wa! Ni! Gaskiya ku nemi direba, ni ba zan iya zuwa wannan garin ba, ba laifi idan a jirgi”
Cikin fada Aunty ta ce “To sai ka je Abdul’azeez, wurin ƴan’uwan nawa ne kake kyamar zuwa?”
“Ni ba kyama nake ba, kawai dai ya cika nisa ga hanyar ba kyau.”
Ya amsata a hankalinsa a kan wayarsa
“Ko bayan duniya ne sai ka je wlh, ka ji ma na rantse ma,”
Dariya Hammah ya fashe da ita, hade da mikewa ya nufi stairs din da zai sada shi da dakin Aunty yana fadin “I don’t know why, ba kwa shan Inuwa daya da Azeez, na same ku gwanin sha’awa amma kuma har fadan ya zo”
Uffan dai Auntyn ba ta ce ba, ta bi bayan shi, yayin da Ya Azeez ma ya nufi kofar fita rai bace.
*****
AUNTY ADAMA
Gyalenta ta warware hade da ajiye shi kan hannu kujera, ta zauna dakyar alamun akwai gajiya a tare da ita.
Wayarta ta lalubo hade da kiran lambar aminiyarta Gana, ba jimawa Gana din ta daga.
Bayan sun yi gajeruwar gaisuwa ne Aunty Adama ta dora da “In fada miki sai ga ɓarawon yaron nan ya dawo.”
Cike da madaukakin mamaki Gana ta ce “Ki bari don Allah”
“Wallahi! Da dai kin ga gidan shiru hankalinmu kwance.”
“To ya kika ga yanayin shi?” Gana ta tambaya cikin zakuwa
“Ai kin san shi kamar kare yake, tsinuwa ba ta sanya shi komai sai kaurin bindi. Ya yi fresh abun shi”
“Kai Adama?”
“Da gaske”
Duk suka dan yi shiru kafin Gana ta katse shiru da fadin “Amma ai ba wata macen ya samu ba ko?”
“To idan ma ita ya samu Gana ina ruwana, ya je can yay ta bin matan ma har ya kwaso jaraba, idan ma aikin da aka yi na raba shi da matan bai yi ba.”
Kafin Gana ta ce wani abu Aunty Adama ta dora
“In fada miki ciki yana nan yana ta kaburi. Kuma wannan kwalba dai na binne ta, har na kosa ma ta haihu, yaro ko yarinyar su girma. Saboda wannan karon ban yi saunancin da na yi a kan Azeez ba, ga shi nan abun ya shafe ni, ba dama in aje abu Azeez ya gani bai dauka ba. Shi ya sa wannan karon na ce a yi mana katangar karfe da shi.”
Daga can bangaren Gana ta yi karamar dariya tare da fadin” Ba ki da kirki Adama”
Ita ma siririyar dariya ta yi kafin ta ce “Ga mara mutumci nan Aisha. Ta san irin wahalar da na sha da mijina har ya kawo matsayin da yake yanzu. Ta zo ta shigar min hanci da kudundune, tun da ta ki koruwa, kuma Hammah baya iya yi mata wulakanci, Sai bakin cikin ƴaƴan nata ya kashe ta ai. Wlh idan har da raina Aisha ba za ta haifi ɗa mai albarka ba. Irin Abdul’azeez za ta yi ta haifa, ba makaranta ba kasuwa, ga sata kamar ɓera.”
Suka yi dariya a tare kafin Aunty ta kuma cewa” Ita ma yarinyar da ke sanyata farin cikin tana nan ita gawa ita ba gawa ba. Na fada miki dai zan zo karshen watan nan, kafin a fara azumi, za ki sha labari “
” To Allah Ya kawo ki. “Gana ta amsa daga can bangaren.
Kafin ta kara cewa wani abu, karamar wayarta ta yi kara, wannan ya sa ta yanke wayar da suke da Gana tare da fadin” Ina zuwa.”
MARYAM
Falon ya rage saura ni kadai sai karatun da ke tashi a hankali.
Haka nan sai na ji gabana na faduwa kamar ana kallo na ta wani wurin.
Dalilin da ya sa na shiga waige-waige kamar mara gaskiya.
Har zuwa lokacin da idona ya hango min abin da nake tunani ko tsammani.
Na tsurawa halittar mai kama da kyankyaso ido, yayin da ita kuma ta shiga canja min kala zuwa abubuwa daban-daban. Har daga karshe ta canja zuwa katon kadangare irin mai jan kan nan ta yo kaina gadan-gadan.
Ƙwala kara na yi mai karfi daga nan kuma ban san me ya faru ba.