Ta rika hada stairs din bibbiyu ta rika hadawa ko nauyin cikin jikinta ba ta ji
Isar ta falon ke da wuya ta rarumi Maryam zuwa jikinta hade da jijjigata tana kiran sunanta.
Yadda ta ga jikin nata ne ya sanya ta canja shawarawa zuwa tofa mata addu’a.
Yayin da Hammah ya iso falon hade da tsayawa a kansu kamar zane yana kallon su.
Azeez ma ya turo kofar falon ya shigo hankalinsa a kan su Aunty.
“Me ya same ta, na ji kamar kararta?”
“Ban sani ba, ni ma karartan kawai na jiyo” Aunty ta ba shi amsa cikin yanayi na ban tausayi.
Ya duko daidai saitin fuskar Maryam din yana ganin yadda take sauke numfashi, Sai kuma ya mike hade da sanya hannunshi a aljihu, kamar ba zai ce wani abu ba sai kuma ya ce “Ya kamata a yi wani abun a kan yarinyar nan gaskiya.”
Cikin fada-fada Hammah ya ce “To me za a yi mata? Me ye kuma ba a yi mata ba? Maganin nan yi ake yi, ana kuma kan yi. Ba dai ta ce ita ba ta jin magana ba, kuma ta iya leke-leke.”
Cikin rashin fahimta Aunty ta ce “leke-leken me ta yi?”
“Ita ai ta sani”
Daga haka ya yi hanyar barin falon.
Ta raba Maryam din da jikinta, ta kwantar da ita a kan tiles din tana kallon Azeez.
“Me ta yi?”cewar Aunty tana kallon Azeez
” I don’t know. Yaushe za ku je Gembun? “
Ya canja hirar tasu
” Ban sanya time ba har yanzu. “
” Idan ba damuwa jibi ki shirya sai in kai ku, amma kai ku kawai zan yi “
Cike da mamaki take kallon shi, saboda ba ta yi tsammanin jin haka daga gare shi ba.
Ba ta kai ga ba shi amsa ba, na bude ido ina kallon su.
Na yunkura dakyar na zauna ina kara kare musu kallo, kamar yau na fara ganinsu
” Sannu. “Ya Azeez ya cike da tausayawa.
Kai na daga alamar amsawa.
Aunty ma ta aiko min da tata sannun, na motsa bakina a hankali na ce” Yauwa”
Duk muka yi shiru, Sai Ya Azeez da ya wuce zuwa dakinshi.
Aunty ta gyara zama sosai tana fuskantata kafin ta ce “Maryam fada min gaskiya, wane leke-leke kika yi, ya ja miki ciwo?”
Na waro idanuna da suka sha ciwo, ina fadin “Ni ban leka komai ba”
“Ba za ki fada min gaskiyar ba kenan?”
Kwal-kwal na yi kamar zan yi kuka na ce “Ni ban san me na leko ba”
Ta yi shiru hade da, kallo na, alamun da ya nuna min ta yi nisa cikin tunani.
“Me ya sa Hammah ba ya nuna tausayin halin da kike ciki sosai to? Ba tun yanzu na yi noticing wannan ba Maryam, yana magana a kan ciwonki ne kawai bayan ni na yi mishi magana. And dazu ya ce wai leke-leken ki ne ya ja miki, kuma ya ce ke din kin san komai. “
A dan tsorace na ce” Allah Aunty ni ban san komai ba”
“To me ya sa ya ce kin sani?”
Na watsa hannuwa sama alamun ni ma ban sani ba
“Maryam!” ta kira sunana a hankali.
Na juya sosai ina kallon ta.
“Tsawon zamana da ke, ba sai na fada miki ina da damuwa, na san kin sani, koda ba du ba na san kin san wasu…”ta dan tsagaita hade da mayar da numfashi, kafin ta dora
” Shekarata ku san 30 kenan da aure, kawayena akwai masu jikoki, amma ni ki kalli, yaro daya Allah Ya ba ni, shi ma kuma ga yadda yake, kin san ko su wannan kadai ya isa ya dame. Bayan duk wannan tsawon shekarun sai ga ciki ya bayyana gare ni, cikin da kullum yake sanya ni a fargaba, ban sani ba ko ajalina ne na dauka, in mutu in bar Azeez a halin da yake ciki akwai tashin hankali.
Ke kadai ce kike yi min kamar ƴa ta gari a wajen iyayenta, ke ma yanzu ga ki kwance tsawon watanni uku, babu makaranta ba ki iya hasala komai, na kasa gane tsakanin ke da Azeez wanne zan ce gara shi. Azeez da lafiyar shi ba ta amfana min komai sai bakin ciki, ko ke da kike kwance cikin jinya. “
Sosai tausayinta ya kama ni, nake jin kamar in tashi in ce mata na warke.
Ta mike tsaye fuska a jagule tana fadin” Za mu je Gembu in Sha Allah jibi. “
Na daga kaina alamar na ji abin da ta fada.
Har ta fara hawan stairs din sai kuma ta dawo falon hade da kama ni, ta na fadin” Mu je sama, ba na son zaman ki ke daya. “
A hankali muka rika hawa stairs din kamar tana koya min tafiya.
Tun daga wannan lokacin Aunty ke ta shiri, duk wani abu da ta san zamu bukata sai da ta sanya mana shi cikin kayan tafiyarmu.
Ya Azeez kam bamu kara kara ganinshi ba, Sai daren da zamu tafi ya shigo gidan wajen sha biyun dare.
Ana idar da sallahr asuba, muka dau hanya, ni da Aunty ne a baya, Ya Azeez da donkey a gaba, saboda cewa ya yi dole da shi za a tafi.
Wani abu da ya rika ban mamaki shi ne, muna fitowa daga gidan sai na rika jin kamar ana warware min wani kulli a jikina.
Jikina duk ya wani saki kamar ba nawa ba.
Motar kuma shiru, dama Aunty da Ya Azeez ba wata hira kirki suke ba, hirarsu ba ta tsawo sai ta koma fada.
Bare yanzu da kowa ranshi ba dadi, kowa da abin da ke damunshi.
Tafiya ce mai nisan gaske mu ka yi kafin muka isa Gembu, daga nan muka dauki hanyar rugarsu Aunty.
Ba dai mu isa ba sai 9pm, zuwa lokacin dukkanmu a gajiye muke likis.
Da madara mai zafi aka tare mu, kafin aka kawo mana piya da ayaba.
Bayan mun ɗan taba ne mu ka yi wanka hade da ramuwar sallahr da aka biyo mu.
Ni dai bacci na yi sosai babu mafarkin komai ko jin tsoron komai, saboda ban san ma lokacin da Aunty ta kwanta ba, suna hirarsu ta yaushe gamo.
Bayan mun karya da safe na zuwa kan wani dutse da ke bayan dakin da kwana ina kara karewa garin kallo
Na dauka a kasashen waje ne kawai ake samun irin wannan yanayin, ashe a Nigeria ma akwai.
Yanayin garin kadai ya isa ya gusar da kananun matsaloli da sanya mutum cikin Nishadi.
Daga inda nake zaune ina iya hango wasu tarin Duwatsu da masu kyau, wanda ruwa yake kwarorowa ta tsakaninsu.
Daga samansu kuma bishiyoyi ne manya da kanana, masu fure da marasa fure, ba sai an tambayi irin ni’imar da wurin zai bayar ba, musamman yadda kasan yake shimfide da kananun ciyayi kore shar gwanin sha’awa.
Daga kasan Dutsen ma fili ne kare kallon ka, shi ma shimfide da ciyayi masu kyau.
Shani farare Kal, mul-mul dasu suna ta kiwo hankali kwance.
Sai yanzu ne na tuno da wayata na rika addu’ar Allah Ya sa Aunty ta zo min da ita.
Kamshin da na ji ya tabbatar min Ya Azeez na tsakiyar gidan ko ma kusa da ni.
Na juya da sauri, can kusa da dakin Baffa na hango shi fuska cuskune
“Ko me aka yi mishi kuma oho?” na fada a zuciyata ina kallon Bingel da ke mika mishi wani ƙaramin koko da ke hannun ta.
Na ji dadin yadda bai kalle ta ba, ita da kokon
Bingel kyakkyawa matashiyar budurwa ce, fara tas da Allah Ya azurtata da komai na cikar mace
Wayewa da ilmin zamani ne kawai ta rasa. Idan ban da yaren fulatanci babu abin da take ji.
Na kasa dauke idona a kansu har zuwa lokacin da Ya Azeez ya bar wurin Aunty kuma ta fito daga dakin Baffa zuwa wani dakin daban.
Ku san a tare muka shiga, ta yi saurin juyowa tare da fadin “Maryam”
Na amsa lokacin da muke zama a tare.
“Daga zuwanmu har kin ji sauki”
Kadan na murmusa ina fadin “Alhamdulillah”
“To ciwon naki ko a gidanmu yake?”
Wannan karon murmushi na yi mai sauti ba tare da na ce komai ba
Ita ce ta kuma cewa “To abun ne ya ban mamaki, muna gida ciwo kullum ba sauki, kullum gaba-gaba ya ƙwaryar roro, amma muna zuwa nan shiru, wannan abu da magana”
“Me ya sa Ya Azeez ke ɓata rai?” na canja salon hirar tamu
Baki ta ta e sannan ta ce “Abun bacin rai wuya yake mishi, dama ai, haka fuskar ta shi take kullum. Wai fa daga Baffa ya ce bai tafiya sai da auran Bingel.”
Gabana ya fadi ras, na rika kallon Aunty ba ko kyaftawa, yayin da kunne na ke jin maganarta kamar saukar aradu
“Ni wlh da Baffan ma zai yi mishi haka da na ji dadi, to idan ba a kauyen ba, birni kam wace mai hankali ce za ta auri Azeez? Sai dai ko irin su Madinan. Ita yanzu kin ga ai ta yi ta kanta.”
Kafin in yi magana Ya Azeez ya dago labulen hade da dora kwayar idanunshi a kaina ya ce” Ki zo”
Jiki ba kwari na bi bayan shi har zuwa dakin Baffa
Yana zaune kan sallaya hannunshi rike da carbi, kanshi nade da rawani fari.
Na kuma gaishe shi cike da girmamawa, ya amsa yana tambayata ya jiki.
Na amsa da Alhamdulillah.ina jin sauki
“Allah Ya kara sauki”
“Amin.” na amsa.
Shiru ya da ratsa dakin kafin ya ce “Aisha ta yi min bayanin ciwon ki, shi ya sa na ce ki zo, mu ga ko akwai abin da za mu iya taimakawa. Sai dai akwai abubuwa masu sarƙakiya a lamarin ki Maryam”
Jin na yi shiru ya ce “Fada min me kike ji, ko kike gani?”
Na gyara zamana hade da rattaba mishi duk abin da nake gani
Ya shiga jinjina kai alamun ya fahimce ni “Kamar an yi miki ture ne” ya fada a hankali kamar mai rada.
“Ta shi ki je, za mu yi magana da Aishar.”
Na mike a nutse zuwa tsakar gidan, inda kowa ke ta sabgar shi.
Daga can nesa na hango Monkey a daure, dalilin da ya sanya ni canja akalar tafiya ta zuwa wajen shi.
Mun dade ba mu gaisa ba, mun dade ba mu yi nishadi ba, na dade ban ba shi abinci ba. Shi ma ya dade bai ci abinci daga hannuna ba
Tun da ya hango ni yake tsalle, da ɗn kukan murna, saboda a mota bai ga fuskar yi min kiriniya ba a lokacin da muke zuwa.
Ina zuwa dab da shi kuwa ya yi tsalle tare da fadawa jikina, ya haye kan kafadata.
Na sauke shi kasa ina shafa gashin jikinsa, Sai ya kuma yin tsalle ya kara haye ni
Na sauke a karo na biyu ina ƴar dariya “Don you miss me?” na fada ina ci gaba da shafa shi.
Na dakata da shafa shi ina kallon Bingel da ta koro shanu, cikin harshen fulatanci na ce mata “Ina za ki je”
“Kiwo” ta amsa min da fulatanci.
“Ga dan rakiya”
Ta yi dariya jerarrun fararen hakoranta suka bayyana “Ya taho” ta kuma amsa min.
Na shiga kwance Monkey na mika mata igiyar.
Na dauka za ta ji tsoro sai na ga caraf ta rike i
giyar ko a jikinta
“Ba kya jin tsoro?”
Na tambaya da sauri
“Birin zan ji tsoro? Da an jima za ki gansu sun zo shan ruwa, har da manya-manyan ko za ki kara” cikin dariya ta yi maganar.
Na mayar mata da dariyar sannan na ce “Ba na so, wannan ya isa kuma ki kular min da shi”
Da kai ta amsa min, sannan ta bi shanunta wadanda suka dan yi mata nisa.