Skip to content
Part 28 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Na sauke ajiyar zuciyar da ban san dalilinta ba, kafin na juya cikin gidan.

Inda na iske Malam yana ta hidimar hada magani a wani koko, gefe na samu ina kallon yadda yake abu cike da kwarewa kuma a nutse.

Kamar hoto haka na rika kallon shi, har ya gama hade-hadenshi, ya dago yana kallo na fuskar shi dauke da murmushi ya ce “Ko ke ce za ki gaje ni?”

Na mayar mishi da murmushi ba tare da na ce komai ba

Ya nufi wata rumfa ya dakko gora mai dan girma da karamin koko ya ce “Kina zuwa dibar ruwa?”

Na girgiza kai alamar a’a

“Yau za ki fara to” ya yi maganar hade da aje gorar kusa da ni.

Na mike hade da daukar gorar na bi bayan shi.

Yana gaba ina bin shi, wata irin kaunar tsohon nake ji, kauna irin ta ƴa da uba, jin sa nake kamar mahaifina, yana da cikar kamala da kwarjini.

Shekarunsa basu boye kyawunshi ba, farin gashin da ya baibaye masa fuska sai ya mayar da shi kamar wani Balarabe.

Wurin dutsen nan mai zubar da ruwa muka isa, na tsaya daga gefe saboda ni ba na son in ga ruwa da yawa, duk da wannan ba wani fadi gare kuma wucewa yake hakan bai hana ni jin jiri ba.

“Matso mana!” ya fada yana waiwayena

Na matso kadan yadda zan iya kallon kasan ruwan. Farin yashi ne a kasa mai hasken gaske da duwatsu manya da kanana farare.

“Nan muke shan ruwa mu da dabbobinmu.”
Ya fada lokacin da yake debo ruwa da kokon yana zubawa a cikin gora.

“Baya karewa?” Na tambaya a hankali

Ya shiga girgiza kai hade fadin “Bai taba karewa ba, kuma bai taba rage zuba ba”

Jin furucinshi ya sa na kara matsowa sosai na ce “Baffa daga ina kuma yake fitowa ya zubo nan?”

“Allah shi kadai ya sani” ya ba ni amsa lokacin da yake mikewa tsaye.

“Ba a taba fadawa ba kuma?”

Ya zubawa ruwan ido kamar yana karantar wani abu kafin ya ce “Ba na ce ba. Amma ana yin shekaru sama da goma ba a fada ba.”

Na dauki ruwan kamar yadda naga suna yi, muka fara tafiya, yana karamin haske a kan abubuwan ban al’ajabi da ke tattare da ruwan.

Bayan mun isa gidan na sauke ruwan, na karbi tabaryar da Yafendo ke daka. Ita kuma tana tsokanata wai zan karbe musu miji daga zuwana

Wunin ranar sai nake ji na kamar an karbo ni daga hannun ƴan kidnappers, komai a sake nake yin shi ina ji na wata mai ƴanci.

Bingel ba ta dawo gidan ba sai bayan la’asar, dama hankalina duk yana gun ta, damuwata Kar Ya Azeez ya dawo bai ga monkey ba ya rika ball da ni.

Yanzu kuma da na ganta da monkey din Sai hankalina ta kara kwanciya ko ba komai bai ɓata ba ya dawo.

Da dare Aunty ta kira ni zuwa bayi, ina tsaye ta kifa wata ƙwarya ta ce in hau kan kwaryar in yi wanka

Duk da akwai duhu hakan bai hanani kwalalo mata ido ba ina fadin “Aunty idan ta fashe fa?”

“Ni ma na fadi wannan, ya ce ba za ta fashe ba, ni ma a kan irin ta na yi kuma babu abin da ta yi.”

Yanzu kam mamaki ne ya hanani magana

Ta kai bakin kofar fita na ce “Aunty wai Ya Azeez fa?”

“Wannan ne zai zauna a nan, yana cikin gari, kila gobe ko jibi ki gan shi”

A zuciyata na ce “Ya Azeez Sam baya son wahala, shi dai kawai aji dadi yauwa.”

Bayan fitar Aunty ne na hau kan ƙwaryar da BISMILLAH ji nake kamar za ta dare.

Abun mamaki na ji kamar na hau Dutse, tun ban saki jikina ba har na saki jiki na yi wanka da ruwan maganin sau bakwai kamar yadda Aunty ta shaida min.

Bayan na fito kai tsaye dakin kwananmu na dosa na yi shirin bacci.

Na fi awa biyu da kwanciya bacci ya ki zuwa, idona a bushe, har Aunty ta shigo ta yi bacci ni ban yi ba.

Kamar wasa har asuba ban runtsa ba, ban san cutar rashin bacci cuta ce babba ba sai da same ni.

Da safe na tashi kamar wata yar sholi, kowa biyu – biyu nake kallon shi

Ga baccin ina ji, amma ko na kwanta ba zai zo ba, tun ina iya boyewa har Aunty ta fahimci akwai abin da ke damuna.

Shi ya sa duk wani motsi nawa a kan idonta.

Motsi kadan za ta ce “Me kike ji yanzu?” wani lokaci in ba ta amsa wani lokaci kuma in yi shiru.

Baffa na shigowa gidan ta fada mishi, abin da na sani kawai shi ne Baffa ya kama kaina ya rike da karfi yana daga nan ban san me ya faru ba.

Ashe daga nan faduwa na yi, na ci gaba da fadin

” Jira Baffa, ni ma dalibarka ce, kuma kawar ƴar ka Aisha tun tana yarinya”

Baffa ya ɗan sassauta da rike min kan da ya yi ya ce “Me ya sa kika shiga jikinta?”

“Ban shiga jikinta ba, taimako na zo yi. Tun lokacin da kake da almajirai nake zaune a nan gidan, Idan Aisha ta zo karin karatu sai in biyo ta, shi ya sa duk karatun da ta iya ni ma na iya. Tare mu ka yi sauka, ban, taba cutar da kowa ba bare ita.

Bayan na yi sauka sai mahaifina ya dauke mu daga nan zuwa wani tsuburi, mu ka rika ibada hankali kwance. Sai dai ni na kan kawo ma ziyara ba tare da saninka ba, in duba lafiyarka.

Ba kai kadai ba, har da Aisha, ita ma ina kai mata ziyara.

Na san tana da matsala ba tun yanzu ba, Sai dai ba na iya taimakawa saboda wadanda suke da alhakin matsalar sun fi karfina. Haihuwar da ba ta yi ba banza ba ne, an yi mata asiri ne, da wasu duwatsu, ana jera duwatsun ne a kofar dakin Aisha duk ranar girkinta, idan har da wadannan duwatsun mijinta ba zai iya shiga ba.

Na so kwashe su, amma akwai baƙaƙen jinnu da ke gadinsu har safiya.

Sai ranar da Maryam ta fita da duwatsun mijin Aisha ya samu damar shiga dakin har ya kusance ta a karo na biyu, kuma ta samu wannan cikin na jikinta.

Shi kuma Abdul’azeez, asiri aka yi mishi yake yin abin da yake yi, sannan wannan cikin na jikinta an yi mishi asirin a binne shi a cikin kwalba, Sai dai Biri ya tona kwalbar kuma Maryama ta jefa ta cikin fulawowi, har yanzu kwalbar na cikin fulawar, idan kuma har wanda ya yi asirin ya gani zai kuma binne ta. Idan har ba a yi hanzarin dakkota an fasa ba, Aisha za ta haifi yaro ko yarinyar da ta fi Abdul’azeez lalacewa.

Zan dawo, zan dawo wani lokacin..”

*****

AUNTY ADAMA

Ba ta san Aisha ba ta gidan ba sai da aka kwana uku, sannan Hammah ke fada mata ta tafi Gembu.

Hankalinta ba karamin tashi ya yi ba, ta san waye mahaifin Aisha, babban mutum ne da Allah Ya ba sani ta bangaren malamta.

Shi ya sa duk yadda ta so ta kori Aisha daga gidan ta kasa.

Duk abin da za ta yi wa Aisha da zarar ta je garin abun ke karyewa, wani abun ma ba ya kamata

Abu biyu ne ta yi nasara a kan ta, su ma sai da ta sha bakar wahala ta bi hanya mai kaya, hanyar da ko yaranta basu san ta bi ta ba.

Daga Allah sai ita, sai kuma Gana.

Hankalinta ya kasa kwanciya da tafiyar tata, fatanta kar su je su wargaza mata duk shirin da ta yi tun kafin Aishar ta haihu.

Da sauri ta mike ta nufi hanyar da za ta fitar da ita waje.

Kai tsaye kuma ta tunkari wajen da ta rufe kwalbar da Malaminta ya ba ta.

Tun daga nesa gabanta ke faduwa, saboda yadda ta ga kamar an tone wurin.

Ta daga kafa sosai ta isa wurin, hannayenta biyun ta rike kwankwaso dasu kamar maburki kafin ta ce

“Na shiga uku ni Adama! Kar dai an tone min kwalbar nan?”

Ta yi maganar a bayyane kuma a kidime.

Daga inda take tsaye ta kwaɗawa Hammawa kira.

Ya rugo a guje zuwa inda take, cikin yanayin basarwa ta ce “Me kake nema ka tona wannan ramin?”

Ya ja baya da sauri hade da daga hannuwanshi du biyun sama ya ce “Ni! Wallahi ban tona rami ba.”

“To waye ya tona?”

Ya matso sosai yana leka ramin da kasa ta kusa cikewa ya ce “To sai Allah, amma ni kam ba ni ba ne, ban ga kuma wanda ya tona ba”

“Je ka” ta fada cike da jin haushin shi, kamar dai ya amsa laifin tona ramin

Ta rika bin tsawon katangar hade da laƙa ko wane sako, amma ko irin kwalbar ba ta gani ba.

“Na shiga uku! Ni ba ta garin nan ba yaƙi ya ci kwartuwa” ta fada cike da sarewa.

“Aisha mayya ce ita da ubantan nan wlh. Ya aka yi suka san na binne kwalbar nan. Ina ma ace shi ne malamina, don da alama yana da ilmi sosai”

Tana tafiya hanyar part din Aunty take maganar.

Tsaye ta yi a kofar part din tana kallon kofar shiga kamar tana jiran fitowar wani.

Daga bisani kuma ta juya zuwa part dinta, cikin rashin sanin abun yi.

Tun da ta fara taka stairs din ta rika jin karar wayarta alamun kira na shigowa

Dalilin da ya sa ta kara sauri kamar mai shirin tashi

Tana isa kiran na yankewa, tana duba miscalled din ne kiran ta kara shigowa.

Ta daga tana fadin “Huzaima, ya aka yi?”

Daga can bangaren Huzaima ta ce “Momy maganar auran Baban Junior ta kara tashi, yanzun nan ya bar gidan nan, har yana ce min wai idan zan iya zama in zauna, idan ba zan iya ba ga hanya, har kudin mota zai ba ni”

Aunty Adama ta ja tsoki kafin ta ce “Don Allah Huzaima ki bar in ji da abin da ke damuna. Ina na fada miki yadda za a yi, kika ce min ke a’a, Sai yanzu ki dame ni, ki jira zuwa an jima za mu yi waya, yanzu ina wani abu ne”

Ba ta jira cewarta ba, ta yanke kiran, cikin da kunar zuciya take fadin “Dama an ce mai ƴaƴan mata baya rufe kofa. Yara mata hidimarsu karewa take ne, ga shi Allah ya ba ni su har biyar. Kuma ko wacce da kalar matsalarta, a haka idan ka gansu sai ka ga kamar duka kenan, amma matsaloli na nan cunkushe a ɗuwawunsu.”

Tana masifar tana kiran layin Malam directly, kiran Gana a yanzu duk bata lokaci ne a wajen ta

Yana daga kiran suka gaisa ta dora da abin da ya sa ta kira shin” Malam, na fada ma uban matar nan hatsabibi ne na rubutawa a takarda. Kasan Fulani akwai asiri, bare na Gembun nan da suka tashi a kan dutse. To wlh kwalbar nan mai laya an tone ta daga inda na binne ta. Kuma na san shi ne zai turo aljanun kan dutse su tone ta”

Cikin tsawa Malam ya ce “Me kike son fada min. Jira-jira-jira Ina zuwa” ya yi maganar cikin yare.

Ganin ya yanke kiran, Sai ta bi wayar da kallo, kamar shi ne a gabanta.

Kamar mintuna biyar ya kira ta, bayan ta daga ya ce “Kina ji na ko Adama?kwalbar nan tana nan a cikin gidan nan ba a fita da ita ba. Saboda haka ki fita yanzu ki bincika ko ina za ki gan ta. Idan ma cikin dakinta ne, ki san yadda za ki yi a shiga ciki a binciko ta”

“To. Yanzu kam zan fita in kara dubawa.” Lokacin da take ba shi amsar har ta kai kofar fita daga bedroom din.

Matar J ✍🏻

<< Da Magana 27Da Magana 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×