Bayan ta fita tsakar gidan kai tsaye wurin dazu ta kuma nufa, ta shiga bankada ko wace fulawa, tana tona ko ina.
Hankalinta kaf yana a kan kokarin ganin ta samu kwalbar, shi ya sa ba ta sauraron komai.
Ta yi saurin ja da baya hade da wani tsalle, cikin rudaddar murya ta ce “Na shiga uku maciji. Hammawa!!” ta shiga kwalawa Hammawa kira da karfi.
Ya amsa daga can cikin dakin ta dora da “Ka taho da sanda wlh maciji na gani”
Bai ɓata lokaci ba ya dakko wata katuwa gora ya nufo wurin a guje.
Sai iya duban shi bai gan shi ba, ita kuma ta kafe a kan lallai ta ga macijin nan, Sai idan wani wuri ya shige.
Dole ta baro wurin a tsorace ta dawo dakin cikin laluben mafita.
Jagwab ta zauna gefen gado, zuciyarta cunkushe, idan har ba a ga wannan kwalbar ba, dole ta je Maiduguri da kanta a kara hado mata wata. Tun kafin Aisha ta haihu.
Ta mayar da ganinta kan wayarta da ke vibration
Kamar ba za ta daga ba, sai kuma ta daga gaf kiran zai yanke.
“Gana!” ta fada kai tsaye
“Adama!” ita ma Gana ta kira sunan ta
“Labari mara dadi Adama, Alhaji Bukar ya sake ni.”
Aunty Adama ta gwalo ido hade da buga kirjin ta, ba ta yi tsammanin jin wannan sakon ba, Alhaji Bukar din da ko uwar shi ba ya yi wa biyayya irin yadda yake wa Gana, shi ne zai sake ta.
“Saki dai namu wannan da namiji ke wa mace?”
Cike da mamaki Aunty Adama ta tambaya
“Wlh shi Adama, Sai kin ga darun da muka sha jiya, ya ce sai in bar mai gida, wai shi aure zai yi. Babu irin rokon da yaran nan basu yi mishi ba, a kan ya yi hak’uri in zauna amma ya ce bai yadda ba. Wai ni Bukar ya kora, Hmmm!” ta karashe maganar cike da jin zafi
Jiki a mace Aunty Adama ta ce” To yanzu kina ina? “
” Ina nan gidan Bilya, shi ma matarshi ta ce wai ba za ta zauna da ni ba, kin san ba shiri muke da ita ba. “
” Ƙundun ubannan! Ita Falmata ta ce ba ta zama da ke, to don ubanta sai ta tafi gidan ubanta ai. “
Baki bude Gana ta ce” kin manta yadda ta shanye Bilyan, yanzu haka ya nemo min haya, har an fara kai kayana ma”
“Oh ni Adama!” cike da mamaki ta yi maganar, irin abun ya zo mata a ba za ta, ba ta taba irin wannan abun zai faru da Gana ba.
“Ai ki bar su kawai, jira nake komai ya natsa, daya bayan daya za su gane kuskurensu, musamman Bukar, har gida sai ya zo ya duka yana neman gafara ta.”
“Dole kam ki dauki mummunan mataki a kansu. Musamman ma Bukar din. Ai in fada miki ni kaina Gana ina cikin tashin hankali” Aunty Adama ta rufe da maganar da ke damunta.
Daga can Gana ta ce “Menene?”
Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce ” kwalbar nan da na binne, ko kin san an tone ta”
Gana ta hangame baki kamar tana gaban Aunty Adama, cikin matsanancin mamaki ta ce “Adama Allah Ya hada ki da hatsabibiyar kishiya, ita ma a tsaye take”
“Kamar nonon maza kuwa” Aunty Adama ta cafke, ta kuma dorawa da “Wannan karon Gana, ban ki Aisha ta mutu ba wlh, ta zame min kashin wuya, amma zan amayota, ina nan zuwa cikin satin nan. Saboda dazu Huzaima ma ta kira ni wai maganar auran mijinta ya tashi. Ke abubuwa sai damalmalewa suke. Anya ba hannu aka sanya mana ba? “
” Ni ma na fara tunanin hakan, Sai dai kin shigo mun karasa tattaunawa. “
” To shi kenan sai na shigo din. “cewar Aunty Adama hade da yanke kiran.
*****
GEMBU
Yau Asabar kuma shi ne ya kama satinmu daya da zuwa Gembu, zuwa lokacin kam duk wasu kananan ciwo ni dai ba na jin su. Saboda magani aka yi min ba na wasa ba. Har da na kariya wanda aka dafa nama na rika cin shi da allura, kai wasu magungunan ma ban san an yi su ba
Ya Azeez ne kawai shi bai shan duk wani magani da za a ba shi, shi kam bai yarda ba shi da lafiya ba ma.
Kamar yanzu ma da muke zaune jikin garu, Baffa na daga kofarshi zaune, hira muke sosai wacce duk a kan Azeez ne.
“Abdul’azeez akwai sihiri sosai a jikin shi, mun yi iya wanda za mu iya, saboda wani abun kam ba zai karyu ba, musamman da ba ya son shan magani. Sai dai mu bi shi da addu’a” cewar Baffa cikin sanyi
Yafendo ta ce “Ai ko makaho ya lalubi Audu ya san da magana a lamarin shi.”
Yagoggo ma ta ce “Ni ba tun yanzu ba ma, nake zargin haka, tun wani zuwa da suka yi. Na dai yi shiru ne.”
“Kin san mutanen birni su dai su ci abinci mai dadi su yi bacci, basu neman maganin tsarin jiki” Baffa ya kuma fada sannu a hankali.
Na mike a hankali na nufi Bingel wacce take kwance shanu za ta kai su wurin cin abincinsu.
“Yau dai zan bi ki.” na fada Ina kallon yadda take kora shanun cikin kwarewa.
Ta yi murmushinta mai kyau kafin ta ce “mu je mana”
Monkey na kwanto hade da rike igiyarshi mu ka jera.
Karon farko da na shiga cikin dajin da tsaunukan da ke guroje
Akwai sanyi da tarin tsaunuka da kasa wacce kai tsaye ba zan iya kiranta yashi ba.
Akwai bishiyoyin fiya wanda na wuni ci hade da shan madarar shanu.
A zuciyata na ce dole su yi kyau, gari ba zafi ga kuma nono ana sha mai kyau da tsafta
Bamu dawo ba sai yamma, a nan mu ka taras da Ya Azeez, yau ya ga dama ya leko mu
Lokacin da mu ka iso tsaka gidan sosai ne na ga Hammah ya fito daga dakin Baffa, sosai na yi mamakin ganin shi. Gabana ya yi irin faduwar da yake yi a duk lokacin da na gan shi.
Da sauri na yi kasa ina gaishe shi, ya amsa hade da tambayata jiki, na amsa mishi da na ji sauki.
“Ya su Aunty?” na kuma tambayarshi kaina a kasa
“Tana lafiya, tare mu ka fito da ita ma, za ta je Maiduguri”
Yadda ya mayar da hankalinshi kan Baffa wanda ya fito daga cikin daki ne ya sanya ni mikewa, tun da ma can gaisuwar ce kadai ke hada mu.
Ku san a tare mu ka shiga daki dakin da Aunty take da Ya Azeez.
Zaune take cikinta ya dan fito amma ba sosai ba.
” Dan madara, yau a nan za ka kwana ne?”
Ta fada cikin tsokana.
Bai amsa ba, ya zauna a kan katifa.
“Ko kudin sun kare?” ta kuma tambaya idanunta a kanshi.
“Ni gida zan tafi, Hammah zan bi.” ya amsata yana ɓaɓɓata rai
“Ai ka yi ma kokari.” ta yi maganar hade da dauke idanunta daga kanshi zuwa kaina.
“Sunana ne ya fito cikin wadanda suka samu tsallake zagayen farko na gasar zanen da na ce miki mun yi a Abuja. Kuma sun ce next week suka son ganinmu, za su yi mana bita kafin mu yi jarabawa”
“Allah Ya bada sa a”
“Amin.” ya amsa yana kallona, kafin ya ce “Kin ji sauki kenan. Wannan yarinyar ta zama problem wlh.”
“Me ta yi?” Aunty tambaya da sauri
“me ye ma ba ta yi ba.” ya amsa hade da mikewa ya nufi kofar fita
“Ina monkey?” ya yi tambayar daidai lokacin da ya saka kanshi waje
“Ga shi can a waje.”
“Kar ku kara fitar min da abu zuwa daji.”
Kafin in amsa shi Aunty ta yi caraf ta ce “To dajin bakonshi ne, bare ko kace bai saba ba.”
Komai bai ce ba ya karasa ficewa.
“ke kina son saka kanki a hidimar Azeez, shi kuma bai san abun arziki ba”
Ni dai zama na yi hade da manna bayana jikin garu ba tare da na ce komai ba.
“Maryam me kike biye min game da Hammah?”
Na yi saurin dagowa ina kallon ta, yayin da gabana ke wata irin faduwa.
Yadda ta zuba min idanune ya sa na ce “Ba komai”
“Karya kike yi” ta yi saurin tare ni.
Na yi kasa da kaina ba tare da na ce komai ba.
Ita kuma ta gyara zaman ta muna fuskantar juna sosai tana fadin “Fada min duk wani abu da kike sani na sirri game da Hammah. Komai nake son sani”
Na lashi busassun laɓɓana ba tare da na ce komai ba.
“Zuwa yanzu kam Maryam kin nuna min ba ni ce na haife ki ba, ni kuma jin ki nake yi kamar ƴar da na duka na haifa, ashe ke a wurin ki ba haka ba ne. Tsawon lokaci kina ta min boye-boye. Kin kyauta. Kin nuna min ban hada komai da ke ba. Hammah shi ne naki, to ga shi can ai, gobe zai koma sai ki shirya ki bi shi”
Na waro ido cike da tsoro, yayin da furucinta ya daga min hankali.
Idanuna suka kawo ruwa, cikin rawar murya na ce “Wlh Aunty kallon uwa nake miki, ba ni da wata uwa a yanzu da ta wuce ki. Hammah bai yi min abin da kika yi min ba, don Allah ki daina fadin irin wannan maganar.”
“Ta ya ba zan fada ba. Na dauka duk lokacin da kika ga wani abu sabo ni ce wacce za ki fara fadamawa, Sai ga shi abubuwa da yawa sun faru ba ki tana fada min ba.”
“Ba na son hankalinki ya tashi ne”
“Yanzu da ba ki fada min ba, kwance yake?”
Na girgiza kai alamar a’a
Duk mu ka yi shiru kamar ba kowa dakin.
Kafin ta katse shirun namu da fadin “Mutum sai Allah! Ban san lokacin da Hammah ya shiga kungiyar asiri ba, ban kuma san ko tun wane lokaci ba. Tsawon lokaci yana ciyar damu da haram. Ba dole mu yi ta ganin bala’i kala-kala ba.”
Baki na hangame ina kallon Aunty, kamar ba zan tanka ba, Sai kuma na tambayi abin da ke cin raina na ce” Kungiyar asiri kuma? “
Harara ta watso min kafin ta ce” yau kika fara sani?”
Ban amsa ba, kuma ban janye Idanuna daga kan fuskarta ba
” Shi ne ya fada Aunty? “
” Da bakinshi kuwa. “yadda ta amsa ne ya tabbatar min da gaske take.
Mamaki hade da tambayoyi ne ta a zuciyata.
“Me ya faru, me kuma ya sa Hammah da kanshi ya ce shi dan kungiyar asiri ne. Yaushe ya fada? Kuma a ina? Dazu da na gan shi babu wata alamar nadama ko tashin hankali a kan fuskar shi. Kodayake shi da Auntyn duk gwanaye ne wajen iya danne damuwa.”
“Je ki yi sallah, ki zo mu yi magana, ni ke ce abokiyar shawarata, tun da ke ba ki yi da ni”
Jiki a mace na nufi kofar fita, har zuwa lokacin mamakin maganar Aunty nake yi.
Ba ni da wata cikakkar nutsuwa haka na yi sallahr, ina kan sallayar a ka kawo min madara mai zafi da pepesoup din naman zabo.
Madarar kawai na iya sha, amma naman ko dandanashi ban yi ba.
Ina kan sallayar Ya Azee ya shigo, yadda ya yi tsaye a tsakiyar dakin ne ya sa na ce “Kana son wani abu ne?”
“Za mu wuce ni da Hammah yanzu”
“Cikin daren nan?”
“Ai kin san ba zan iya kwana a nan ba” karshen maganar tashi ta yi daidai da fitar shi
“To Allah Ya tsare hanya, Sai mun taho”
Ko ya amsa min ban ji ba, ni ma sai na mike tsaye , baki na kuskure kafin na kabbara sallahr isha’i.