Skip to content
Part 32 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Haka gidan ya rika karbar ƴan gaisuwa har dare, zuwa lokacin Aunty ta kara gajiya tibis ga wani irin ciwo da bayanta yake yi, haka nan take yin komai cikin karfin hali

Misalin karfe 8:30pm Azeez ya hauro zuwa dakinta, tun da ta iso sai yanzu ta gan shi, ba ta san ma yana gidan ba.

Kallo daya ta yi mishi ta fahimci akwai yunwa a tare da shi

Ya zauna gefen gadon, Sai ma ya kwanta gabadaya ta baya, duk kafafunsa a kasa.

“Me ya faru? Kai da ba ka iya gaisuwa ba.” ta fada cikin tabe baki

Ya mike zaune tare da fadin “Aunty dama haka kabari yake?” yadda ya nutsu alamun firgici suka bayyana a fuskarshi ne ya sanya Aunty tattara hankalinta a kanshi tare da fadin “A ina ka gani kai?”

“Tare da ni aka saka Aunty Adama fa. Wlh na kasa cin abinci na ji tsoro”

Murmusawa kadan ta yi kafin ta ce “Haka yake Azeez, kuma a nan mutum zai zauna tare da ayyukan da ya aikata a duniya alkairi ko akasin hakan, har ranar da za a tashi duniya. To waye ya san ranar? Wa ya san ko kwana nawa zai yi a kabari kafin a tashi duniyar? Idan ka aikata alkairi za a fadada ma wannan kabarin idan kuma ka aikata sharri Allah zai umurce shi da ya kara matse ka. “

” Kai!! “ya yi saurin fada.

” Da gaske. “ta amsa mishi, ba ta taɓa ganinshi cikin nutsuwa irin yau ba.

” Shi ya sa ka ga kullum ina ta fada don dai kawai ka zama na gari Azeez, ba wai don ba na sonka ko son takura ma ba. Ba na son dai ace yau ga shi ka karbi sakamako mara kyau a ranar lahira “

Ya mayar da hannayenshi du biyun baya ya yi dafe dasu sannan ya ce” Menene ba ki so? Menene ke kai mutum wuta? Me zai sa a faɗaɗawa mutum kabarinsa? “

Zamanta ta gyara sosai kafin ta fara amsa mishi tambayar daya bayan daya

” Abin da ba na so shi ne yadda ba ka zuwa makaranta, shekera da shekaru Azeez ka kasa karbar result dinka. Abu na biyu wasa da sallah, ban ce ba ka yi ba, amma kana wasa da ita. Abu na uku daukar abin da ba na ka ba. Azeez me ka rasa a gidan nan da har sai ka dauki abin da ba naka ba. “

Ya sauke numfashi a hankali ba tare da ya ce komai ba

Dalilin da ya sanyata dorawa” Abin da ke kai mutum wuta kuma suna da yawa, Sai dai in tsakuro maka. Akwai shirka, na fara da ita ne saboda ita ce babba. Rashin tsaida sallah. Sabawa iyaye. Ka ga wadannan suna daga cikin abubuwan da za su kai mutum wuta, idan har mutum bai yi gaggawar dainawa ba tare da neman gafarar Allah .”

Ya jinjina kai a hankali kafin ya ce” Ni ban taɓa shirka ba, ko maganin gargajiya ba na sha”

“Amma kana yin sauran abubuwan biyu”

“Zan daina”

“Allah Ya sa. (ta dora) abin da ke sanyawa a faɗaɗawa mutum kabari kuma kishiyar abin da na lissafa maka ne, duk wani aikin alkairi da ka yi ba da riya ba”

“Menene riyar?” ya yi saurin tambaya

“Ka yi abu ba don Allah don kawai ace ka yi, ko kana jiran wanda ka yi mawa ya biya ka daidai abin da ka yi mishi ko ya ninka maka”

“Ba na yin wannan.” ya amsa a hankali, har zuwa lokacin hannayenshi na dafe a bayan shi.

“Da kyau! Azeez ka ji tsoron Allah girma kake yi kullum, amma ba ka san ina ka dosa ba, ba ka kama addini da kyau ba, kai dai ka yi wanka ka sanya kaya masu kyau, ka kwanta a wuri mai kyau ka ci mai kyau. Rayuwa ba za ta yiwu ma a haka ba. Rasuwar Mamansu Huzaima kadai aya ce a wurin ka, ni ma zan iya tafiya in bar ka, watarana ma za ka iya bude ido babu Hammmah ƙasa ta rufe ido shi. Mutuwa ba ruwanta da tsufa ko yarinta. Ya kamata ka dawo cikin hankalinka. Tun ƙasa ba ta rufe idanuna ba. Addu’ata kullum shi ne in ga ka zama cikakken mutum. Ina son ka cika min wannan burin kafin ni ma in bar duniya. Musamman yanzu da nake kan siradi kila wurin haihuwa in rasu”

“Shi ya sa ai ni ban so wannan cikin ba” ya fada rai a bace

“To ya zan yi Azeez Allah Ya ba ni. Ka yi min addu’a mu rabu lafiya kawai”

Duk suka yi shiru kamar ba kowa a cikin dakin kowa da abun da yake tunani.

Hammmah ya turo kofar ya shigo hade da sallama.

Aunty ta amsa a sanyaye

“Yaronki yau duk ya yi laushi fa” ya fada hade da zama kan lokar mirror.

Ta kalle shi kafin ta kalli Hammmah ta ce “Yau ya ga kabari, shi ya sa jikin tatsaure ya yi la’asar.”

Hammmah ya ɗan murmusa kaɗan kafin ya ce “To ya za a yi, haka Allah ya hukunta mana.”

Suka yi shiru gabadayansu kafin Aunty ta ce “Ya karin hak’urinmu?”

“Hak’uri an gode Allah Aisha. Kin ga ikon Allah ko, kamar wasa Adama ta rasu, ko mutuwar iyayena ba ta kiɗima ni ba kamar ta Adama.”

“Ai duk abin da zai sa Azeez ya yi laushi haka lallai babba ne” Aunty ta amsa tana kallon Azeez din da ya zauna kamar zane

“Wai ya ci abinci kuwa?”

“Ina son tambayar shi muka shiga wata hirar. Ka ci abinci?”

Maimakon ya amsa ta sai ya ce “Aunty duk abubuwan da na daukarwa Mamansu Huzaima ta ce min ba ta yafe ba. Ya za a yi in biya ta?”

Duk suka zuba mishi ido har Hammmah da ya kasa ɓoye mamakinshi

“Ga yaranta nan, Sai ka kimanta kudin abun ka ba su.”

“Shi kenan, zan jira in samu kudi da gumina sai in biya su, ba na son in biya da kudin kowa. Kin yafe min abubuwan da na daukar miki ko ke ma in biya ki?”

Hawaye suka cika idon Aunty, jikinta ya yi sanyi, ta rika jin ko shi ma dai mutuwar zai yi ne, ko ita ce za ta mutu

Hawaye na bin fuskarta ta ce” Matso Azeez “ta yi maganar hade da ya fito shi da hannu.

Ya matso sosai kusa da ita, sai ta karasa janyo shi jikinta ta rungume shi sosai. Cikin muryar kuka ta ce” Duk wani laifi da ka yi min, da wanda na sani da wanda ban sani ba, da wanda ka san ka yi min da wanda ba ka sani ba, na yafe ma har abada. Allah Ya yi ma albarka ya shirya min kai”

Ta kai karshen maganar hade da zare jikinta da na shi, tare da fadin ka fi saɓawa mahaifinka a kaina. Shi ma ka roki gafararshi kamar yadda ka roki tawa.

A hankali ya isa wurin Hammmah ya duka kan kafafunshi. Kafin ya yi magana Hammmahn ya dafa kanshi tare da fadin “Na yafe ma Azeez, Allah Ya yafe mu ba ki daya. Allah Ya yi ma albarka ya shirya ka”

“Amin.” suka hada baki su ukun wurin fada.

Daga haka ya fice daga dakin, zuciyar shi wani iri, ita ba ɓacin rai ba, ba kuma farin ciki ba.

Hammah ya kalli Aunty wacce har a lokacin hawaye take ya ce “Allah Ya sa hakan shi ne sanadin shiryuwar yaron nan”

“Amin” ta amsa cikin kuka

“Mun aikata abubuwa marasa kyau, ko sau daya Allah bai taɓa tona mana asiri ba, fatanmu da rokonmu ya sa yadda muka tuba, kar mu yi tuban muzuru. Ko da zan tafi tsirara in Sha Allah ba zan kara saɓawa Allah ba. Wannan alkawari ne na yi.”

“Allah Ya amince.”

“Amin” ya amsa da alamun mutuwar jiki.

Idan akwai wani abu ki samarwa yaron can, kin san ba zai taba cin abincin gidan nan ba yanzu “

Ba tare da ta ce komai ba ta mike zuwa dakinshi da niyyar duba shi sannan ta tambayi me yake so.

Ba ta iske shi a dakin ba wannan ya tabbatar mata da ya bar gidan. Ya tafi inda ya fi wayau (hotel)

Haka gidan ya kasance kullum cikin baƙi, yayin da maganganu marasa dadi suke fitowa daga bakin Gana wacce take yin abu kamar ta haukace

Kullum sai Aunty ta ji sabon labari daga bakin su Adda Halima, saboda a can suke wuni, Sai dare su dawo bangarenta su kwanta.

Ranar Juma’a aka yi addu’ar uku, ana idar da addu’ar aka daura auran Azeez da Maryam, daurin auran da ya zo ma kowa a bazata, ciki har da Angon.

Shi ya sa rai ɓace ya fito daga masallacin, bai damu da tarin matan da ke fsrfajir gidan nasu ba, ya rika tsallake su a zafafe.

Falon Aunty ma a cike yake, nan ma ya rika ratsa su yana wucewa, har zuwa lokacin da ya tura kofar dakin Aunty.

Nan din ma cike yake, ma fi akasarinsu kuma kawayenta ne

Yadda ya shigo ne ya sanya ta tattara duk hankalinta a kanshi

Tsaye ya yi yana mazurai, bai yi tsammanin ganin dakin a cike ba.

Dalilin da ya sanya shi juyawa baya da sauri.

Aunty da ke fama da nauyin ciki ta yunkura dakyar ta bi bayan shi, lokacin tuni ya gama sauka a kan stairs din

“Azeez!” ta kwala mishi kira ganin yana niyyar fita

Juyowa ya yi ba tare da ya amsa ba.

Ta karasa sakkowa stairs din dakyar tana fadin “Zo mana, me ye ya faru?” ta kai karshen maganar hade da riko hannun shi ta yi hanyar dakinshi.

Bayan sun shiga dakin ne ta ce “Me ya faru? Na ganka rai ɓace”

Ya furzar da iska mai zafi kafin ya ce “Me ya za a yi min aure? Ni na ce ina son aure ne?”

Cike da mamaki Aunty ta ce “Wane irin aure kuma?”

Cikin jin zafi ya ce “Ba ga shi can a masallaci ba, Hammah yana cewa wai a daura aurena da Maryam”

Aunty ta kuma yin kamar ba ta san batun ba ta ce “Wace Maryam ɗaya?”

“Yarinyar nan ta wajen ki mana” har zuwa lokacin huci yake

Ido ta fitar waje kafin ta ce”, To me ye matsalar a nan, so that in san yadda za a magance, auran ne ba ka so ko yarinyar”

“Duka ni ba na so” ya yi saurin ba ta amsa

“Shi kenan ta zo gidan sauki, saboda ita ma Maryam din ba ta so, kuma na dauka Hammah ya bar maganar, tun a Gembu ya yi mata magana kuma ta ce ba ta sonka. Ban san dalilinshi na daura auran ba, bayan yarinya ta ce ba ta so.”

Sosai Azeez ya saki baki yana kallon Aunty, irin kallon mamakin nan, ya dade a haka kafin ya ce” Ta ce ba ta sona? “
Cike da mamaki ya yi tambayar

” Kwarai ma kuwa. “

” To me ya sa da ta ce tana son nawa? “
Yadda jikinshi ya saki ne yake son sanya Aunty dariya, amma sai ta danne ta ce

” Haka shi ma Hammahn ya ce, ta ce wai saboda ba ta son auran Bandi ne”

Har zuwa lokacin idanun Azeez a kan Aunty suke, Sai kuma ya janye su a hankali zuwa kasa.

Aunty kuma ta nufi kofa tare da fadin “ka sha kuruminka, Hammahn na shigowa zan sanya a warware auran tun da duk ba kwa so.”

Komai bai ce mata ba har ta fice, a sannan ne ta samu damar darawa kadan tana fadin “ɗan kundun uba, ashe ba dadi, kai tsaye ka ce ba ka son mutum”

Azeez kam tana fita sassan jikinsa ya rika bi da kallo, daga bisani karasawa ya yi gaban mirror yana karewa kan sa kallo.

“Ba ta sona!” ya jinjina maganar a hankali

“Why? Me ya sa?” ya tambayi kansa cike da kunar zuciya

Lallai yarinyar ta raina mishi wayau, yanmata nawa ne ke rububinshi amma ita ta ce wai ba ta son shi.

“Anya ba shirin Aunty ba?” ya tambayi kansa

Hannu ya sanya cikin aljihunshi ya shiga kiran wayar Maryam, Sai dai a kashe.

“Zan ci kaniyanta kuwa, ita har ta isa ta ce ba ta sona, wacece ita?” ya fada a fusace hade da komawa kan gadonsa ya zauna ransa a matukar ɓace.

Aunty kam tana shiga dakin ta iske Gana da Karima, da alama tafiya za ta yi, saboda har da karamar jakarta a hannun Karima.

A mutumce suka gaisa, ta kara yi mata gaisuwa

Gana kuma ta ce “Zan tafi, na ce bari in sallame ki”

Aunty ta fadada murmushinta tare da fadin “Na gode, Allah kuma saka da alkairi.”

“Amin” cewar Gana, tana kallon Azeez da ya shigo bayan shi goye da jaka

“Ina za ka je kuma?” Aunty ta tambaya idanunta a kanshi

“Abuja” ya amsata fuskar nan a hade.

“Allah Ya kiyaye hanya. Ka dai fadawa Babanka.”

“Zan fada mishi” ya amsa hade da juyawa ya fice

“Wannan shi ne yaron naki da aka daura aure yau?”

Aunty ta daga kai alamar eh

“Allah sarki, yaron da mu ka so kashewa tun a ciki Allah bai yi ba. Shi ya sa mu ka hada shi da shashatau baya iya aikata komai sai sata. Ko baya sata?” ta kai karshen maganar tana kallon Aunty, wacce ita kuma ta sake baki kamar wawiya tana kallon ta, ta dauka fade-faden da aka ce ta na yi bai kai haka ba

Mutanen dakin ma tsit suka yi, Karima dai kamar ta nutse sai aikawa Gana harara take, amma ko a jikinta.

“Allah sarki, ita kuma Maryam din da har Adama ta ce a kashe ta, Sai kuma ta fasa ta ce a kashe maigadi, Allah bai nufa ba.”

Da karfin tsiya Karima ta janye ta zuwa kofar fita, wannan na daya daga cikin dalilan da suke so ta tafi gida ba tare da an yi bakwai. Bankadar da take musu ta isa.

Abu ya iske mata, ai take dakin Aunty ya kaure da surutu, kowa da abin da yake fada.

<< Da Magana 31Da Magana 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×