Skip to content
Part 33 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Abu ya iske ma’iya, wai kukan aure da sallallami, kafin bakwai maganganun da Gana ta rika fada sun leka inda ba a yi tsammani ba, har ma da karin gishiri.

Abun da ya ishi ƴaƴan Aunty Adama kullum cikin kuka suke da danasanin abin da mahaifiyarsu ta aikata

Kosawa suka yi a yi bakwai saboda wasu gulma ce kawai ke kawo su da tsegumi.

Basu kadai ba, hatta Aunty kosawa ta yi a watse, saboda maganganun sun ishe ta haka, sannan yaran ma tausayi suke ba ta. Ga zafin mutuwar mahaifiyarsu ga maganganu marasa dadi da suka biyo baya.

Duk sun yi wani tsuru-tsuru babu kuzari ko ɓalli a tare da su.

*****

MARYAM

Ana gobe addu’ar bakwai muka dakko hanya ni da Baffa, dare ne ya kawo mu Yola, tun da muka taho gabana ke faduwa, yanzu kam da muka iso gate sai gabana ya tsananta faduwa.

Kamar jikakken burodi haka na rika jan jikina zuwa part din Aunty.

Ina isa kofar Aunty na bude min, Sai na fada kanta, ta rumgume ni tsam a jikinta, without making any sound muka wuce dakin Ya Azeez saboda dakina da dakinta duk akwai mutane.

“Ya hanya Maryam?”

Na dauke hawayena a hankali kafin in ce “Alhamdulillah!”

“Me ye abun kukan?” ta tambaye ni cike da kulawa tana taya ni share hawayena

“Gabana ne yake ta faduwa Aunty, na dauka ko wani abu ya same ki ne.”

“To gani babu abin da ya same ni. Amma ke ya same ki.”

Hannuna na dauke daga kan fuskata ina kallon ta cikin ido

“Abin da kike fata ne ya samu, ranar Juma’a an daura auran ki da Abdul’azeez. Na san za ki yi farin ciki da jin wannan shi ya sa na fara fada miki. Yanzu sai ki yi wanka ki sha tea ki kwanta a nan, akwai ma abinci ga shi nan duk na tanadar miki.”

Daga haka ta fice daga dakin

Ba ki na saki hade da juya maganarta cikin raina, na kasa tantance dadi maganar ta yi min ko akasin haka. Bayan haka ma sosai abun ya zo min da mamaki, ko yana ina Ya Azeez din oho.
Na mayar da idona a kan hotonshi da yake shanye da blue suit sosai ya yi kyau.

Na a wurina abun alfahari ne ace Ya Azewne mijina koda kuwa ba ma jituwa, kawai dai in kalle shi in ji cewa mijina ne, to ni hakan ya yi min.

Flask tea na fara haɗawa na sha, kafin na shiga wanka, Sai na tuna lokacin da na yi wa dakina gudun Hijra na tare a na shi. Cuta ba mutuwa ba in ji Hausawa.

Bayan na fito sallolin da ake bi na na fara ramawa, kafin na debi abinci kadan na ci.

Na kwanta a kan tattausan gadonshi da ya sha blanket masu laushi, har lokacin akwai ragowar kamshin man da take shafawa gashin shi a kan filo.

Ban jima da fara bacci ba aka kira sallahr asuba, daga lokacin hayaniya ta rika cika sassan alamun kowa ya tashi, dole ni din ma na tashi, na gabatar da sallahr asuba, sannan na kintsa dakin fes, kafin na ja kofar na haura dakin Aunty.

Duk da mutuwa ce ta tara mutane hakan bai hana wasu tsokanata da amarya ba.

Murmushi nake yi ba tare da na tanka musu ba.

Bayan an yi addu’a ne na shiga bangaren Aunty Adama don yi wa su Aunty Karima gaisuwa

Yadda na gansu sai na ji tausayinsu sosai ya kama ni, duk da su din ba kananan yara ba ne, ko wacce tana dakin mijinta da yaranta amma mutuwar iyaye komai girmanka sai ka ji ta, Sai ka ji duniya ta yi ma fadi, kamar ba kowa.

Bare su da kamar ita kadai ce danginsu, ba maganar ƴan’uwan Hammah ake yi ba, hatta ƴan’uwan Aunty Adama basu saba dasu ba. Dole yanzu su ɗimauce su fara tunanin yadda za su yi sabuwar rayuwa ba tare da Aunty Adama ba.

Dama ni ba hira muke ba, shi ya sa ina yi musu gaisuwa na dawo inda na fi wayau, zuwa yamma sai gidan ya zama shiru ba kowa sai su Aunty Huzaima da basu tafi ba. Sai Baffa da shi ma yake shirin tafiya gobe.

Zaune muke a falo ina matsawa Aunty Kafafunta da suka yi kumburi Hammah ya turo kofar ya shigo

Duk sai na ga ya kara baƙi ya ɗan zube kadan

Ya zauna kan kujera tare da fadin “Washh Allahna!” lokaci daya kuma yana dafe kanshi

Na yi saurin fadin “Barka da yamma Hammah, ya karin hak’uri kuma?”

“An gode Allah Maryam. Ya gajiyar hanya”

“Ba gajiya”, na fada hade da mikewa na yi hanyar dakina

“Ina za ki je? Zo mana.”

Na yi saurin dawowa hade da dukawa wurin da na tashi.

“Aisha ranar Jumma’a a fa za a raka yarinyar nan dakinta. Dazu na yi magana da su Goggoji, na ce ta turo min ko su Faɗimatu ne su yi mata rakiya, nan kuma na cewa su Karima idan ba za su iya dawowa ba, to su jira su raka kanwarsu da kanensu dakinsu.”

“Da gaggawa haka?” Cewar Aunty.

“Da an yi abu sai ki ce wai da gaggawa. Ina gaggawa a nan?”

“Ni fa ba wani abu na ce ba, na ga ko gidan zaman ba a tanada ba.”

“Ke ce dai ba ki tanadar musu ba. Amma ni tuni na zuba komai ma, kuma shi angon ai ya sani.”

“To ai ni ban sani ba” cewar Aunty tana rike haba

“To ke dama Ina ruwanki da sha’anin ango? Ke ba amarya ce ta ki ba. Ku dai yi kintse-kintsen da za ku yi kafin Friday ni ba wani taro za a yi min ba.”

“To a ina gidan mu je mu gano, mu ga abin da za mu kara”

Ya dan karkace hade da ciro key ya mika mata yana fadin “Gidan nan nawa na bajaburie na gyara masu.”

Ido Aunty ta fitar tare da fadin “Inyee! Ƴan gata haihuwar dangi, wannan tsalelen gidan aka basu? Gaskiya sun gode.”

“Kin ji abin da na ce ko?” ya juya da ganinshi kaina

Na daga kai alamar eh

“To sai ai ta hak’uri, kin san dai waye Azeez kin ma fi kowa sanin shi, na tabbata kin san yadda za ki zauna da shi. Idan kika ce za ki mishi taurin kai da Shirme, ya kwakkwaɗeki a banza”

Baki buɗe Aunty ta ce “Ban gane wannan fadan naka ba Hammah, ya za ka rika tsoratata, tun ba ta je ba an fara yi mata albishir da duka, ban gane ya kwakkwaɗeta ba, haka ya fada maka zai kwakkwaɗeta?”

Ya yi dariya kadan hade da shafa kanshi yana fadin “Me ye ba gaskiya ba a abin da na fada. Na tabbata ta ce za ta yi mishi Shirme make ta zai yi.”

Aunty ta gyara zama hade da canja fuska ta ce “Wlh blh tun wuri ma ka fada mishi, idan kuma ka fada mishi to ka kara nannaga mishi, koda wasa ya bugar min yarinya na rantse ma da Allah Hammah sai na rama mata dukanta, kuma sai ya ci prison. Ya fi ka fada mishi da wuri, idan da ya doke ta ya doki banza to ban da yanzu. Na yi hayar ƴan iskan gari su ci min kaniyarshi.”

Dariya mai karfi Hammah ya yi kafin ya ce “Lallai ke surukar zamani ce. Ki ce ke za ki kashe auran ma da wuri.” ya karasa maganar cikin dariya.

“Ai idan ma akwai maganar duka fasa wannan auran za a yi. Idan ba haka ba kuwa to za ku ga surukar zamani i, zan saba hijabina har gidan in ci ubanshi”

Dariya Hammah ya kuma fashewa da ita, ni kaina dai abun ya fara ba ni dariyar, shi ya sa na mike zuwa dakina, daga ciki nake jiyo Aunty na ta cin alwashi kala-kala idan har Ya Azeez ya ɓata min.

Hammah kuma na ta dariya, da alama abun Nishadi yake ba shi.

Abu kamar wasa sai ga shi karamar magana na son zama gaske, saboda har Aunty ta dauki kawayen zuwa Bajabourie federal housing sun gano gidana, sun kuma kara abin da suke son karawa.

Su Aunty Huzaima ma basu tafi ba, saboda dama 3dz ne tsakanin addu’ar bakwai da tarewar tawa.

Ni irin abu da ake ba amaryar nan, ban ga Aunty ta ba ni komai ba,

Magana kadan ta ce “Azeez kam mutum ne da za a yi rawar kai a kanshi.”

Ni ce kawai nake hada madara da zuma a sace ina sha ba tare da ta sani ba.

Na san kuma duk ranar da ta kama ni, to sunana sorry.

Ita ta fi mayar da hankali wajen kamshi, humrah kam da airfreshner gasu nan kala-kala, saboda Ya Azeez baya son abu mai hayaƙi.

Ranar Juma’a da misalin karfe tara ƴan Minchika suka iso, har da dangin Mamana.

Sai na rika jin wani dadi da farin ciki

Zuwa karfe biyu gida ya cika, babu wani kide-kide amma an yi abinci da drinks masu an ci an sha, an, kuma yi zumunci.

Zuwa karfe biyar aka shirya ni cikin lafaya white mai kwalliyar golden yellow.

Sai na fito fes, duk da ba wata kwalliya aka yi min ba, amma na yi kyau aka yi hotuna sannan Hammah ya bayar da motoci aka tasa keyata zuwa Bajabourie.

Ina jin a tarihi ni ce amarya ta farko da ba a yi wa fada ba lokacin da za a kai ta gidan miji.

Ina jin ƴan rakiyar amaryar sun manta ana kai amarya wajen iyaye su yi mata fada, haka su ma iyayen basu nemi a kai ni ba.

A zuciyata na ce ina ruwan “Salaha”

Shi ya sa ni ma ban yi kuka ba, zuciyata dai ta yi wani dundurus kamar dutse, komai ba dadi.

Lokacin da muka isa unguwa Bajabourie ana kiran magriba, shi ya sa kowa yana isa ya fara alwala. Ni ma alwalar na yi don yin sallah.

Bayan kowa ya idar aka dasa hira, a yi ta dariya a yi ta ban haushi ni dai duk ina sauraronsu.

Ta dariya in yi dariya a hankali. Ta takaicin kuma in yi Allah Ya kyauta.

Sai da aka kira sallahr isha’i kowa ya tashi don yin sallah

Bayan kowa ya idar aka kuma dasa wata hirar, wannan ya sa na manta da maganar ni amarya ce na ji ba na jin wata kewa ko fargaba aka yi ta Nishadi, hatta su Aunty Karima sun saki jiki an yi dasu. Sai karfe tara na dare Hammah ya turo daukarsu.

Sannan ne na ji kamar ba ni lafiya, ga kuka ya ki zuwa, Sai dai kamar fuskata kamar an kawo ni kabarina.

Ina cikin daki gefen gado na ji tashin motocinsu.
Tsoro sai ya kama ni, duk da gidan ba kato ba ne, amma shirun da unguwar ta yi ya isa ya ba wanda bai saba da unguwar ba tsoro.

Na rasa dalilin Hammah na matsawa a kawo ni bayan Ya Azeez din ma baya nan.

Haka na yi zaune har wajen 10pm da kiran Aunty ya shigo wayata

“Ba ki yi bacci ba?” Abin da ta fara tambaya kenan

Kamar zan yi kuka na ce “Tsoro nake ji”

“Ai dole tun da ba ki saba ba, na cewa Hammah a bari Abdul’azeez din ya dawo amma ya ƙi”

Mai nema a duhu bare an haska mishi, kukan da nake ta son yi dazu ne ya taho gabadaya,.

“Ba na fa son kuka ke ma kin sani. Ki yi addu’a ki kwanta, gobe zan sanya a maido ki gida”

Wani dadi ya baibaye ni, cike da doki na ce “Don Allah Aunty a zo da wuri”

“in Sha Allah, ki yi addu’a ki kwanta”
Maganganun Aunty sai suka kara min kwarin gwiwa, na shiga toilet na dauro alwala kafin na kwanta hade da yin addu’a ina fatan gari ya waye da wuri.

<< Da Magana 32Da Magana 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×