Skip to content
Part 34 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Bayan da na idar da sallah sai na rasa abun yi, na saba duk bayan sallahr asuba kitchen nake shiga.

Na kwanta bacci kuma ya ki zuwa, Sai na bude data na shiga Facebook na gama yawo na na dawo Instagram na rika kallon update din abokan Ya Azeez, ko wanne su yana wane wannan, na shiga comment section na rika ganin comment na mutane.

Na koma handle din Ya Azeez, last update na shi ya fi sati biyu, wannan ya nuna min cewa rabon shi da update tun kafin rasuwar Aunty Adama, tun da ta rasu bai kara dora komai ba.

Ina cikin karanta reply na mutane kiran Aunty ya shigo

Dadi ya kume ni, fatana Allah Ya sa ta ce ga direba nan hanya.

Bayan ta amsa gaisuwata ne ta ce “Maryam na haihu.”

Ban san lokacin da na mike zaune ba tare da fadin “Allah Aunty! Wayyo Allahna! Alhamdulillah” na fada cikin ihu, ban jira komai ba na yanke kiran.

Da wani irin tsalle na duro daga gadon na shiga tsalle ina ihun murna.

Hand bag dita na nufa, ko naira biyar babu a ciki.

Na jefar da ita na bude wardrobe na dakko doguwar rigar atamfa na sanya hade da dora hijabi, wayata kawai na dauka sai keys din gidan da Aunty Karima ta sanya min cikin lokar mirror.

Bayan na rufe ko ina, na fice daga gidan da wani irin farin ciki.

Unguwar shiru ko kare ban gani ba, bare mutum, Sai da na fita babban titi na samu Napep drop.

Lokacin da na buga kofa Hammawa ya bude hade da cin karo da ni baki saki kamar wawa yana kallo na.

“Da gaske Aunty ta haihu?” na fara jefa mishi tambayar abin da ke raina.

Sai ko ya wargaje baki tare da fadin “Walahi! An samu Baby boy.”

Wni tsallen na buga na sheka da gudu cikin gida ina fadin “Ka ba shi kudin Hammawa.”

Ina tura kai cikin falon suka dauki sallallami kamar na mutu na dawo.

“Maryam! Yau mun shige su. Aunty! Fito ki ga amaryar da muka kai jiya.” cewar wata Yadikkota.

Su Aunty Huzaima ma sai suka hau kwakwazo, dukkansu suka dunguma zuwa saman Aunty.

Sai a lokacin jikina ya yi sanyi, na yi tsaye a cikin falon, ina rarraba idanu har zuwa lokacin da na ji muryar Aunty tana fadin” La’ilahaillalhu! Ashe da gaske ne, uban wa ya kawo ki gidan nan yau?”

Ta yi maganar daidai lokacin da ta zo tsakiyar stairs

Na ja da baya ina ina kallon ta da narkarkar fuska, lokaci daya kuma Ina cin karamin yatsana

“Ba ki ji Ina magana? “

Kamar zan yi kuka na ce” Ba ka ce kika ce min kin haihu ba? “

“Shi ne kuma sai na ce ki zo? A ina kika taba ganin an yi haka. Oh ni Aishatu.”

Su Aunty Karima da ke bayanta suka hau dariya, dariya sosai suke yi.

Aunty kuma ta juya zuwa dakinta tana ci gaba da fada.

Yayin da ta bar su Adda dasu Aunty Huzaima suna ta dariya.

“Wannan ba Maryam ba?” cewar Hammah da ya shigo fuskarshi cike da madaukakin mamaki.

Aunty Nafee ce ta kawai ta amsa shi da “Ita ce”

Sauran kam duk dariya suke

“Me ta zo yi, ko ba ita ce jiya aka kai ta gidan miji ba?”

“Barka ta zo.” Yadikko ta amsa shi.

Bai ce komai ba ya haura sama, bai jima ba kuma ya sakko ya fice daga gidan.

Ni kam na ga raɓe-raɓena na haura sama, na dauka Aunty za ta kara fada, Sai ba ta ce komai ba, hidimominta kawai take yi da masu shigowa

Saboda garin na kara wayewa mutane na kara shigowa.

Yaro kam ba na jin ko Ya Azeez zai haifo mai kama da shi haka, komai iri daya tuna ya jinjiri ma. Ga shi turbakallah a koshe.

Na saki jiki sosai aka shiga hidima gida da ni, kawayen Aunty dai duk wacce ta zo sai ta ce lafiya na zo, amarya daga kai ta jiya, Aunty dariya take yi ba ta faye ba da amsa ba.

Har dare ban ji wanda ya ce in tafi gida ba, ai sai na yi kwanciyata a dakina na sha baccina

Da safe aka shiga hidimar aikin jego da ni da karbar yan barka, Aunty ba ta ce komai ba, Hammah bai ce min komai ba

Su Aunty Karima ne dai da mun hada sai su kama dariya.

Har kwana uku babu wanda ya ce in tafi gida, zuwa lokacin tuni na daina noƙe-noƙe na saki jiki sosai kamar dai ba a yi min aure ba.

Yanzu ma zaune muke a falo da su Aunty Huzaima, saboda basu koma ba, suka ce za su jira ayi suna, tun dukkansu a nesa suke, ba sai sun dawo ba.

Hira muke yi sosai, ban san suna da hira ba sai a kwanaki ukun, sun saki jiki sosai, dama Aunty ita ba ruwanta. Duk yadda ka zo mata za ta karbe ka.

Ƴan kayana da na bari a gidan su nake ta sanyawa.

Yanzu tummy black siket ne a jikina da farar shirt mai taushi, kaina kuma sanye da bakar hula ina gyara busasshen kifi

Ba kowa ne ya mayar da hankalinshi a kofar da aka turo ba ciki har da ni

Sai da na ji ihun Aunty Huzaima ta na “Ga ango! Ga ango!! Ga ango”

Na yi saurin dago kaina gabana na wata irin faduwa, zuwa lokacin tuni sun rungume shi, Aunty Huzaima kuma na video, shi ya sa ban tantance ya yake ba.

Na yi saurin daukar farantin kifin na shige kitchen. Na yi tsaye har wani fitsari – fitsari nake ji.

Yadda suke ihu ina kuma jiyo sautin dariyarsa ne ya sanya ni matsawa wurin window ina kallon yadda suke ta tsokanarshi, duk da rashin samun n fara’arsa yau kam ya kasa rufe bakinsa, haka suka tasa shi zuwa upstairs wurin Aunty.

Bayyanannar ajiyar zuciya na sauke bayan sun bacewa gani na

Na rufe idanuna gam, ina jin yadda ko wane bangare na jikina yake komawa muhallinshi bayan rikewar da suka yi na dan wani lokaci.

Daga bisani na zame a wurin na zauna tare da hada bayana da kitchen cabinet.

Daga wurin da nake zaune nake jiyo karaɗinsu, a zuciyata na ce lallai na san Aunty Adama ta rasu, dama kenan ita ke hana su shiga sabgarmu. Yanzu gidan ma ya fi dadi, saɓanin baya da kowa ke harkar shi.

Ina zaune a wurin suka kuma sakkowa, shi ya fice su kuma suka zauna a falon suna kara mayar da labari

Aunty Farida ta ce “Ina Maryam?”

Rufe bakinta ya yi daidai da shigowar Aunty Huzama ta jawo ni zuwa wajen falon. Suka shiga tsokanata

Dakyar na samu na yi dakin Aunty, time da na je yaro take shayarwa.

“Lafiya?” ta tambaye ni saboda yadda ta ga na shigo

Na karasa tattara nutsuwa na duka ina taba kumatun yaron na ce “Waye ya fadawa Ya Azeez kin aihu?”

“Babanshi.” ta ba ni amsa

Ba tare da na dago ba na ce “Me ya ce da ya zo?”

“Daukar shi ya yi ya rungume har yana cewa Hammah ya yi gaskiya, dama ya ce yaron kama yake da shi. “

Duk mu ka yi dariya a tare
“Na so in fada mishi, ina jin tsoro kuma” na fada lokacin da nake dagowa.

“Kuma da ya zo sai da ya tuhuma, wai babu wanda ya fada mishi. Na ce to kai da kake jin haushi.”

Muka kuma yin dariya a tare.

Jin falo shiru ya sa na sakko saboda na san su Aunty Huzama sun fice dora abincin ranar su. Don har lokacin su ke yin abincinsu.

Ban kammala abinci ba sai 2:30pm

Bayan na yi sallah abincin na zubo hade da dakko wayata

TikTok na fara shiga, karon farko da posting din Aunty Huzaima na fara karo bai fi 2hrs ba, amma ta samu like da comment sun fi dubu ashirin. Abin da ba ta taba samu ba duk da kasancewarta mai koyar da abincin zamani da na gargajiya.

Da yawan comment din tambayarta ake yi ta san Ya Azeez, da gaske ya yi aure, yaushe ya yi auran har abun ya rika ban mamaki, ashe haka mutane ke damuwa da abin da bai shafe su ba.

Zuwa yamma videon ya zagaye media, ya kuma zama topic din tattaunawa har da gidajen jaridar online.

Azeez

Bayan fitar shi kai tsaye dakinsa na hotel ya nafa wani irin farin ciki yake ji, shi kadai ya san yadda yake ji idan ya tuna Aunty na da ciki, damuwarshi kar ta rasu wajen haihuwa, Sai ga shi ta haihu lafiya, wannan shi ya fi sanya shi farin cikin fiye da babyn. Shi bai san wani dadin yaro ba.

Bayan ya watsa ruwa ya sanya aka kawo mishi abinci yana tsaka da ci Anwar ya turo kofar hannunshi rike da waya, lokacin da ya iso wurin Azeez din sai ya mika mishi wayar yana fadin “What is? Da gaske wai?”

Ya dakata da cin abincin haɗe da karbar wayar yana kallon videon mai tsawon minti daya da rabi

Bayan ya kare ne ya mikawa Anwar wayar ya ci gaba da cin abincin shi.

“Wai da gaske don Allah?”

“Da gaske.” ya amsa a hankali ba tare da ya daina cin abincin ba

Cike da madaukakin mamaki Anwar ya kuma cewa “Don Allah da gaske”

Siririn tsoki ya ja tare da fadin “Me zai sa kuma in yi ma karya? Mtswww!” ya kuma kullewa da tsokin

Anwar ya saki baki sosai yana kallon shi har zuwa lokacin da Nasir da Mubarak suka shigo su ma da irin zancen da Nasir ya shigo da shi.

Kafin Azeez ya yi magana Anwar ya ce “That’s what I was asking right now.”

Yadda suka zuba mishi ido ne ya sa ya ce “amma kai ba na fada maka ba da gaske ne.”

“Amma wlh har yanzu ban yarda ba Azeez, ta ya za ka yi aure haka, aure babu invitation, mu ko sau daya ma bamu taɓa ji ba sai kawai mu ci karo da abu a online. Mu ka yi mana adalci kenan? Ka kyautawa alakarmu?” Rai ɓace Anwar ya yi maganar.

“Kai!! Subhnallah!” cewar Azeez a hankali, alamun ya gaji, ko sun takura mishi.

“Gaskiya ya fada, wannan abun gori ne ka janyo mana wajen abokan adawarmu ai. A yadda muke da kai ace ba mu san komai ba sai dai mu ga ni a online. Haba Abdul’azeez” cewar Nasir cike da ɓacin rai

Mubarak ya ce “Kune kuke ganin muna daya, amma tun yaushe gayen nan yake bambanta kanshi da mu. Yanzu ai sai mu kara sanin matsayinmu a wurin shi.”

Jibgegiyar harara Azeez ya aika mishi haɗe da jan dogon tsoki, dama basu cika zama Inuwa daya ba.

Ya mike tsaye yana fadin “You guys allow me to rest mana a’ah.”

“Wa ya jawo? Laifi ka yi mana, kuma dole ka bamu hak’uri ka kuma amsa laifinka” cewar Nasir shi ma yana mikewa hade da zagayawa saitin Azeez suna fuskantar juna

“To zo ka doke ni ne Nasir?”
Ya yi tambayar tare da haɗe fuskarshi sosai

“Ka fi karfin dukan ne Azeez? Idan ban da ka raina tarayyarmu, ba ka dauke mu a bakin komai ba, ace a social media muke ganin aure. ” A fusace sosai Nasir ya yi maganar.

“To dokanni, na yi aure ban fada ma ba, nawa kake ba ni?” Ya yi maganar hade da balle rigar shi ya jefar saman gadon.

“Ko ban ba ka ba, ai na taɓa kawo ma mai ba ka.” Nasir ya amsa shi ma yana kokarin balle tashi rigar.

“Ka fadi ko nawa ne zan biya, kai ne kake talaucin kudi ba ni ba.”

“Kai din banza, kana da abun da za ka biya ne? Nawa ka tara?”

Anwar ya yi saurin ta shi hade da shiga tsakiyarsu yana fadin “Please guys you calm down please, what’s all this. Ku Kullum Kuna fada kamar ka ji, ba za ku girma ba ne?”

Ya Kai karshen maganar haɗe da zaunar da Azeez kan gadon, kafin ya janye Nasir zuwa inda ya tashi.

“Shi kenan ya isa don Allah. Ku tashi mu je. Kamar yadda Mubarak ya fada, yanzun kam mun san matsayinmu a wurin shi. Ba tun yanzu yake son raba kanshi damu ba.”

Mubarak ne ya fara durowa daga gadon, Nasir ma ya mike suka dafawa Anwar baya

zuwa hanyar fita daga dakin.

<< Da Magana 33Da Magana 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×