Skip to content
Part 37 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Misalin karfe biyu na rana sai ga shi da duk abin da na rubuta, kawai sai na ji tausayinshi ya kama ni, na fara tunanin ina ya samo kudin ya sawo, ba dai satowar ya yi ba ko, don kawai ya ga ya yi min abin da nake so.

Ba na jin ni kuma zan amince da wannan, ya fi mun in ci babu dadi ko ban ci ba ma, da ya je ya dakko abun wani ya yi min hidima.

Ina kallon shi ya gama shigar da komai cikin kitchen kafin ya wuce dakinshi.

Ajiyar zuciya na sauke lokaci daya kuma na mike zuwa dakin na shi, akwai bukatar mu yi magana da shi.

Duk da kofar a bude take ban shiga ba sai da ya yi min izni.

Ina jin shigowa ta ya sa ya mayar da dogon wandon da ya cire a kan vest din jikinsa, saboda ko belt din bai mayar ba yana gefen sa.

“Me ya faru?” ya tambaye ni ganin yadda na rabe can jikin bango.

“Dama Ina son mu yi magana ne”
Na fada a hankali

Ya gyara zaman shi hade da tattara duk hankalinshi a kaina ya ce “Ina ji”

Sosai nake mamakin canjawarshi, duk da shi dama ba miskili ba ne, bai kuma da yawan surutu, sannan yana da saukin kai sosai ba ya son hayaniya.

“Na ga ka yi siyayya ne, shi ne nake son ce ma daman idan ba ka da kudi ba sai ka damu kanka ba, zan yi amfani da abin da muke da” a ɗan tsoroce na yi maganar.

“Ba ni ne na saya ba, Hammah ne” ya amsa min a takaice

“Mun gode” na fada hade juyawa da niyyar fita daga dakin

Har na kai kofar kuma na juyo da sauri ina fadin “Ko akwai abin da kake son ci da rana”

“Duk abin da kika yi.” ya kuma amsa min, cak na yi ina kallon shi, kamar akwai abin da ke damunshi, Sai na kuma jin tausayin shi ya kara kama ni.

Lumshe idanuna na yi a hankali yayin da ruwan hawaye ya jika gashin da ya yi musu ado, a hankali na bude su a kanshi cikin raunannan murya na kira sunan shi

Bai amsa ba amma ya kalle ni

Kafafuna na kai kasa hade da dukawa cikin murya kaka na ce “Ka yi hakuri don Allah idan ni ce na ɓata ma rai, in Sha Allah ba zan kara ba.”

“Ba ke ba ce” ya kuma amsa ni a sanyaye

Hannu na kai hade da dauke hawayena ina fadin “Idan Aunty ce don Allah ka yi hakuri.”

“Ba ita ba ce” ya kuma amsawa bayan na dire maganata

Yanzu kam sai na zuba mishi ido, hawaye na saukar min, saboda na san dole akwai abin da ke damunshi

Ba haka yake ba, ya yi sanyi sosai, yadda ban dauke ido daga kallon shi ba, haka shi ma bai dauke na shi idanun a kaina ba

Abin da kuma na fahimta idanun na shi ne kawai a kaina, amma hankalinsa baya tare da shi

Na mike daga tsugunnan da nake zuwa dakina, ina zuwa na fada gado hade da sakin kukan da ni kaina ba na ce ga dalilin yin shi ba.

Ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba

Sai dai na farka na ga karfe 4:06pm, alwala na fara yi hade da yin sallah, na yi azkhar kafin na fito don zuwa kitchen

A falo muka hadu, tsaf cikin shirin ball, da alama yau ya tuna ball din ne.

A daburce na ce “Bacci ne ya dauke ni, yanzu zan yi abinci”

Baki ya taɓe ba tare da ya ce min komai ba har ya fice daga falon

Bayan na hada tea na sha, aikin abincin dare na kama gadan-gadan

Wanda ya dauke ni zuwa bayan magriba.

Ya Azeez kuma bai shigo ba sai 8:30pm zuwa lokacin har ya canja kayan jikinshi

Wannan ya tabbatar min ya je gidansu na gado ta bakin Aunty.

Yana kokarin shiga daki na ce “Na gama abincin?”

“Menene?”

“Rice and stew na yi.”

“Da daren? Waye zai ci abinci mai nauyi da dare, Sai ki ci abun ki. Just make a cup of tea for me”

Ban ji dadin yadda bai ci abinci ba, ban jima ba na kai mishi abin da ya bukata zuwa dakinshi.

Yau ma kamar kullum bayan na yi sallahr asuba na shiga gyaran inda ke bukatar gyara da kuma goge-goge.

Ban saba komawa bacci bayan sallahr asuba ba.

Yanzu kam Irish kadan na soya mishi, ni kuma na dumama shinkafata na ci da tea.

10am shi ma ya fito don yin breakfast.

Ina kallon shi har ya idar, kafin ya shiga danna wayar wayar shi.

Sosai hankalinshi ya koma kan wayar, yayin da ni kuma zuciyata ke ta kwatanta min yadda zan tambaye shi zuwa gidan Aunty, tun da gobe suna, ya kamata in je yau.

Bayan na tattara duk wani kuzari nawa na ce “Ya Azeez!”

Bai amsa ba, amma ya dago hade da zuba min ido yana kallo na

Na kara tattara wani kuzarin nawa wuri daya tare da fadin “Gobe ne sunan Aunty. Shi ne nake son zuwa”

“Yaushe?” ya tambaye ni hankalinsa a kan wayarsa

“Yau.” Na amsa shi.

Ya dago idanunshi a kaina ya ce “Kin ce gobe, kin ce kuma za ki tafi yau.”

“Ai ana aiki ne yau din”

“Duk mutanen da ke gidan basu isa su yi aiki ba sai kin je. Mtswww!” ya rufe maganar tare da jan tsoki

Wannan ya sa na yi shiru, shi ma sai ya mike zuwa kofar fita. Ina jin fitar shi daga gidan.

Idan na ce raina bai ɓaci ba na yi karya, duk yadda na so in share abun sai na ga gagara, nai ta jin babu dadi.

Haka nan na kuma shiga kitchen na yi abincin rana, amma sai karfe taran dare Ya Azeez ya shigo gidan

Zuwa lokacin na cika na yi fam, ga hana ni zuwa gidan da ya yi, ga shi na ɓata lokaci na yi abinci don shi bai ci ba

Shi ya sa da ya shigo na ki fitowa falon, ina jin shi ya gama ɓuruntun shi a kitchen ya kuma ficewa daga gidan.

Tun ina tsammanin dawowarshi har bacci ya dauke ni.

Da asuba ko sallah ban yi ba, na leka dakinshi in ga ko ya dawo. Amma ba kowa

Wannan ya kara sanyawa raina ya ɓaci, don ma ni Allah bai dora min jarabar tsoro ba, da kila jiya ba zan yi bacci ba.

Bacin ran ya hanani karyawa, ga shi har goma bai shigo gidan ba, bare in samu in tafi gidan sunan. Ni kuma takaici ya hana min in kira shi.

Ina zaune ina ta kumburi ni kadai kiran Aunty ya shigo.

Bayan mun gaisa ne ta ce “Na dauka jiya za ki leko sai na ji shiru, yau ma har 11am na ji ki shiru, fatan lafiya?”

Hawayen da suka jima suna son fitowa suka fara sakko min, cikin dakusassar murya na ce “Ya sunan yaron Aunty”

“Abdallah.” Ta amsa min

Na murmusa tare da guntun hawayena ina fadin “Nice name, sunan ya yi dadi ya kuma dace da shi, Allah Ya raya”

“Amin. Ya hana ki zuwa ne?”

Na girgiza kai kamar tana kallona kafin na ce “A’a. Ya ce in jira shi, kuma har yanzu bai shigo ba.”

“Ai ko hana kin ya yi Maryam ba za ki fada ba. Azeez ko kashe ki ya yi ya kashe banza, da dai ban san ki ba” ba ta jira cewa ta ba, ta yanke kiran

Ni kuma na shiga rera kukan da ban yi ba, yar kwalliyar da na yi duk na goge ta

AZEEZ

Bayan Aunty ta yanke kiran Azeez ta kira, a, lokacin kwance yake bisa katon gadonshi na otel yana bacci.

Cikin muryar bacci ya ce “Hello”

“Oh bacci kake yi, Anya Azeez?”

“Aunty me kuma na yi?” kamar zai yi kuka ya yi maganar

“Ba ka yi komai ba Azeez. Ka zo ka kwanta a nan kana bacci, yarinya tana can tana jiranka ta taho wurin suna. Ka kyauta. Na gode Azeez.”

Ya mike zaune sosai yana fadin “Oh my God! Komai na yi Aunty laifi ne, ni na hana ta zo ne, ta yi tafiyar ta mana”

“Za ta rika tafiya ko ina ba tare da izninka ba ne, kana son koya mata hakan ne?”

“Shi kenan.” ya fada hade da yanke kiran

Lokaci daya kuma ya ja tsoki, a bayyane yake fadin “Wai haka auran ne, haba, ni ne a takure ba ita ba. Zan ci kaniyar yarinyar nan kam, wannan takurar ta ishe ni. Na kwanta kaɗan. Haba this and that each and every minute. What’s all this?”

Magana yake lokaci daya kuma yana tura wayar shi aljihu.

Dama bai yi tsammanin ganin ko daya daga cikin abokan na shi ba, saboda ya tabbatar ko wannensu yanzu yana wurin neman kudin shi.

Ina zaune a falo zuciyata a cunkushe na ji karar shigowar motarshi.

Ba jimawa kuma na ji karar shigar key a kofar falo.

Wannan ya tabbatar min da shigowa zai yi, sai na kara hade fuskata sosai

Yana shigowa kwayoyin idanunmu suka hadu, ni ce na fara dauke tawa zuwa wani gefen.

Shi kuma ya tunkari kofar shi.

Daidai zai shiga ya juyo tare da fadin “Wlh idan na shirya ba ki shirya ba, Sai dai ki tafi da kafafunki ko ki samu keke.”

“Ni na shirya ai” na fada cikin zumbura baki.

Ya juyo sosai yana kallo na

“Haka ne kin shirya? Ku da kun tashi fita sai ku kwaso wasu jibga-jibgan kaya ku sanya. Kalle ki, ki dakko wani jibgegen abu kin sanya. Dalla malama ki je ki canja kaya idan dai ni za ki bi” a tsawace ya yi maganar

Da hanzari na mike tsaye ina fadin “To wanne zan sanya?”

Ya kara dallare ni da harara kafin ya ce “Ki sanya doguwar riga” karshen maganar ta shi ta yi daidai da shigewarsa cikin daki.

Bayan na shiga daki tsaye na yi gaban mirror ina kallon yadda lace din ya yi min kyau sosai, don ma na goge kwalliyar fuskar, amma shi bai yi mishi ba, kodayake shi dama baya son manyan kaya, a jikinshi ko a jikin wani.

Doguwar riga onion color na dakko, bayan na sanya na yi rolling veil nata

Kafin na dauki siriririn eyes glass fari na sanya, takalmi flat silver da aka silver na sanya.

Duk da ban kara gyara fuskar ba sosai na yi kyau.

Kuma sai na ga kamar kwalliyar ma ta fi kyau a yanzu.

Zaune na yi a falo ina jiran fitowarshi, ban jima da zama ba ya fito sanye da baƙin wando mai santsi sai farar shirt ita ma mai santsi ya yi stoking da bakin belt. Takalminsa baƙi cover wanda ya sha mai.

Yarinta da kuriciyarsa suka fita sosai a cikin kayan. Kallo daya za ka yi mishi kasan bai san wata abu wahala ba, jikinshi ya gama nuna hakan.

Bai yi min magana ba ya nufi kofar fita, wannan ya sa na bi bayan, har ya rike handle din kofar sai kuma ya juyo yana fadin

“Me kika fadawa Aunty?”

Da sauri na shiga girgiza kai ina fadin ” ban fada mata komai ba”

Ya kara hade fuska sosai kafin ya ce “Ke ma so kike ki zama munafuka, da dai ba haka kike ba, kodayake tun can kin iya shiga abun da babu ruwan ki. Wa ye ya fada mata na hana ki zuwa wurin suna?”

Na daga hannayena du biyun tare da fadin “Wlh ban fada mata ka hana ni zuwa ba. Ce mata na yi ina jiranka ne, shi ya sa ban tafi ba”

“You know how much I hate irin fadan can na Aunty. Ki ci gaba da fada mata komai. Dama a nan dina kike?” ya kai karshen maganar hade da nuna makogwaranshi

Kafin in ce wani abu ya dora da “Wlh ban da I’m try to change myself from duk wani abu mara kyau. Da na tabbatar miki kina zaune da wanda ba kya so. Har za ki iya bude baki ki ce ba kya sona.”

Ya fisgi kofar da karfi ya fice

Na yi tsaye ina mamakin yadda wannan magana ta ƙi wucewa, da alama ta yi mishi zafi.

Ni taka zuwa kofar na fita jiki a sanyaye

” Ya Azee! “na kira sunan shi daidai lokacin da na isa kan entrance

Ya fasa shiga motar da ya yi niyya ya juyo hade da kallo na.

Na taka a hankali zuwa inda yake.

Na tsayar da idanuna a kanshi a sanyaye na ce

“Abin da zan fada yanzu, ko ka yarda, ko kar ka yarda shi ne gaskiya, kuma shi ne a cikin zuciyata har karshen numfashina. Ni ban taɓa ƙin ka ba. Idan ka dauke Hammah da Aunty ba na jin ko kai kanka kana yi wa kanka son da nake yi ma. Wannan shi ne gaskiya. “

“Mtswww! (ya ja dogon tsoki kafin ya dora) ki kwance min zane a kasuwa ki dawo gida a daki ki ce za ki daura min saboda rainin hankali. Ki gama fadawa mutane ba kya sona, yanzu daga ni sai ke ki dawo ki ce kina sona”ya kai karshen maganar hade da shigewa cikin motar.

Ni ma zagayawa na yi dayan bangaren na zauna kusa da shi.

Zuciyata tana min ba dadi, ba zan kuma iya cewa Aunty ba gaskiya ta fada mishi ba. Kuma Ina son ya yarda ya kuma tabbatarwa da kansa ina son shi.

“Ba a gaban kowa na fada ba fa” a hankali na yi maganar, daidai lokacin da yake murza key.

“Shi ne har Aunty ta ji?” ya tambaye ni lokacin da yake ribas

Ajiyar zuciya na sauke hade da lumshe idanuna a hankali na kuma bude su lokacin da muka fita daga farfajiyar gidan.

Shi ne ya fito ya rufr gate kafin ya koma mazauninshi

Sai da na bari ya fara tafiya ne na kuma cewa “Aunty ba ta fahimta ba ne, ni na ce ne ba na son auran wanda ba ya sona.”

Ya yi saurin juyowa yana kallona. Wannan ya sa na dora da

“Tun farko Ya Azeez ba ka shiryawa aure ba, bayan haka ma ba ni ce a zuciyarka ba. Dole in ce ba na so a lokacin da na ga ana kokarin cusa maka ni ba ka shirya ba.”

Komai bai ce ba, amma na fahimci kamar maganata ta yi tasiri. Shi ya sa ma ban kara cewa komai ba. Har zuwa lokacin da ya yi parking a kofar babban shopping mall din nan na SAN HUSSAIN.

“Ki zabi kayan jarirai masu kyau na maza kala goma, sai ki hada da sauran tarkacen kayan baby”

Kai na jinjina alamar to.

Face mask ya sanya hade da dora facing cap, na san ya yi hakan ne don kaucewa idanun mutane.

Kai tsaye bangaren kayan jariran muka nufa, na rika zabar latest masu kyau, shi kuma yana kallo na, bayan na gama zaɓar kayan na dauki roll din pampers da set na nycil, socks da takalman jarirai masu kyau.

Muka tura zuwa wurin biyan kudi, muna wurin a tsaye ne na hango Ya Nasir yana shigowa hannunshi rike da na wata mace.

Na fahimci Ya Azeez ma ya gan shi amma sai ya dauke kai.

Sai da suka zo gab damu sannan ya ganmu, da sauri ya zare hannunshi ya karaso in da muke.

Yadda yake ta kame-kame sai abun ya ban dariya, saboda na san yana yi ne saboda ni, bai san ni na wuce wannan babin ba kuma.

Tsabar ya rude bai kawo ma kanshi ko ni ce matar Ya Azeez ba, me za mu yi da kayan jarirai, hankalinshi duk bai kai nan wajen ba, kokarin wanke kanshi kawai yake, yayin da bangare daya kuma yake ɗar-ɗar da kallon da Abigail take watso mishi

Bayan gajeruwar gaisuwa Ya Azeez ya dauki ledar da aka zuba mana kaya, ni kuma na bi bayan shi.

Bayan mun zauna a cikin motar ne ya ce “kin baro saurayinki”

Baki na tura ba tare da na ce komai ba.

“Ai shi kina son shi ko? Tun da yana son ki.”

Komai ban ce ba, na yi shiru, ban san yana da mita ba sai yanzu.

Shi ma bai kara cewa komai ba, muka dauki hanyar Dougirie.

<< Da Magana 36Da Magana 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×