Skip to content
Part 39 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Muna fita daga falon Ya Azeez ya nufi motarshi tare da fadin “Ina jiran ki”

Da to na amsa kafin na nufi bangaren Aunty, Sai da na bari kowa ya shige kafin na sanya hannu cikin fulawar da ke gaban dakin Aunty na shiga lalube, har Allah Ya sa na jiyo kwalbar nan.

Da Bismillah na janyo ta kafin na koma wurin Ya Azeez na dora mishi ita a kan cinya ina fadin “Don Allah ɓoye min, ina zuwa.”

Ban jira amsar shi ba na juya zuwa part din Aunty a karo na biyu

Na lokacin da na shiga zaune take gefen gado tana ba Abdallah nono, shigowa ta ce ta dawo da ita cikin hankalinta

“Na dauka kun tafi?”

Na, girgiza kai alamun a’a

“Tafiyar za ku yi?”

Na daga kaina alamun eh

“To ki shiga wurin ƴan’uwanki ki yi musu sallama, gobe da asuba za su wuce”

“To” na amsa a karon farko

“Akwai abin da kike bukata ne?”

Na dan yi shiru alamun tunani kafin na ce “Babu komai”

“To na gode, Allah Ya yi muku albarka, ya sanya zaman lafiya a tsakaninku, ya ba ku zuriya ɗayyyiba”

A cikin zuciyata na ce “Amin”

“Maryam kin san waye Abdul’azeez, don Allah ki yi ta hak’uri da halinshi, ba sai na fada miki yadda za ki zauna da shi ba, tun da kin san halin shi kaf. Abin da kawai zan iya cewa shi ne, zaman ku a yanzu ya sha bam-bam.

Ki yi kokarin cire idanunshi a kan matan wajen nan, ki yi kokarin toshe duk wata kofa da zai ba shi damar ganin wata ta fi ki. Kin San dai irin matan da yake mu’amala dasu, wayayyu masu budadden ido. Ki zama mace ta gari, ki yi kokarin aje wani abu a kwakwalwarshi wanda ko kina kusa ko ba kya kusa zai sanya ya rika tunawa da ke. “

Kai na jinjina alamun na fahimci duk maganganunta

“Je ki yi musu sallamar kar ya yi ta jiran ki”

Tun daga kofar shiga falon nake jin hayaniyarsu

Na yi tsam ina sauraro, abin da na fahimta basu ji dadin maganar Aunty Karima ba, wai ta tonawa mahaifiyarsu asiri.

Ita kuma na ji ta ce “Tonuwar asiri na nawa kuma? Tun Mommy na shimfide a tsakar dkinta asirinta ya ke tonuwa. Ni kam abun ya ishe ni haka, ya fi min in fadawa duk wanda na san ta cutamawa gaskiya hade da roka mata gafara. Tun da ta rasu nake mafarkanta cikin yanayi mara kyau, kila fadin ya zama sauki na wani bangaren a gare ta. “

Kafin wani ya kara cewa wani abu a cikin dakin na yi knocking

Aunty Huzaima ce ta bude min,

Mu ka kara gaisawa kafin na ce” Zan tafi gida ne, Sai na ji Aunty ta ce kuma duk gobe za ku wuce”

Gabadayansu suka amsa min da “Ai kuwa.”

“Shi ne na ce bari in leko in yi muku sallama, Allah Ya tsare hanya, Ya jikan Aunty Ya gafarta mata amin.”

“Amin.” suka kuma hada baki.

Ni kuma na juya zuwa kofar fita.

Har ya yi motar key muka fice daga cikin gidan bai ce min komai ba

Bayan mun hau hanya ne ya ce “Kwalbar me ye wannan?”

“Ita ce wacce Aunty Karima ke magana.”

Da sauri ya juyo da kallon shi a kaina ya ce “A ina kika samu?”

“Tun kafin mu tafi Gembu monkey ya kawo min.”

Kwalbar ya dakko hade da jujjuyata kafin ya ce “Mutum shege ne wlh, yanzu idan ban da bala’i taya aka shigar da wannan kurmusheshiyar layar?”

“Ni ma sosai abun ya ban mamaki.” Na amsa shi a hankali

Hankalinshi a kan tukin da yake yi ya ce “Dole ace mata sun fi yawa a wuta, kalli fa abin da Aunty Karima ke fada”

“Allah dai ya raba mu da mu musamman kaddara”

“A haka wai in yafe, in yafe me? Wlh ba zan yafe ma wacce ta durkusar da rayuwata ba. Kalli fa set nawa wasu masters ma suke yi. Gaskiya Allah Ya isa”

Cike da jin haushi ya yi maganar, wannan ya sa ban ce komai ba

Shi kuma ya shiga bayyana min irin zafin da yake ji gami da abun da ta yi mishi.

Daga karshe ne ya ce “But in Sha Allah, after all this, zan yi making duk abin da na rasa, a bayan ranta zan zama abin da ba ta so in zama da yardar Allah.”

Yanzu kam da kwarin gwiwata na ce “Allahu Ya yarda.”

Wunin ranar kayan tafiyarshi Abuja muka tsaya haɗawa. Sai yamma lis ya fita

Karfe 8:30pm kuma ya dawo ya ce zai yi bacci da wuri saboda tafiyarshi gobe jirgin 9:am zai bi

Karfe tara ta Washegari kam ya tafi ya bar ni da kewa, ba kowa a gidan sai monkey, da tv

Shi ya sa da yamma na yi deciding shiga makota a gaisa

Gidan kusa da ni a bangaren dama na fara kwankwasawa, maigadin ya bude min, na yi mishi bayanin wacece ni a takaice.

Ya ba ni hanya na wuce cikin gidan.

Yar aiki ce ta bude min main door din na shiga

Inda na taras da wata dattijuwa mai kimanin shekaru sittin da dori, bayan mun gaisa na gabatar mata da kaina, ta yi min godiya hade da sanya albarka a zaman aurena.

Ban jima sosai ba na fito zuwa daya gidan na bangaren hagu.

Nan ma babbar mace ce wacce za ta yi sa’ar Aunty.

Na gaishe ta hade da gabatar mata da kaina, na fito zuwa gida mai facing din gidana

Nan kuma wata Cristian ce za ta ɗan girme ni da kadan, muka gaisa hade da taba yar hira kafin na fito zuwa gida.

Bayan sallahr magriba ina zaune kan sallaya kiran shi ya shigo

Bayan amsa sallamar ne ya ce “Na ga kiran ki, Kiran fa tun 11am na yi mishi shi, amma sai yanzu ya gani

Na danne fushina ina fadin “Dama na kira ne in ji yadda ka sauka.”

“OK.”, yana gama fadin haka ya yanke kiran. Na bi wayar da kallo cike da mamaki, kamar na yi mishi wani laifi.

Ni din ma yau da wuri na kwanta, shi ya sa kiran sallar farko, koda na idar sallahr ma wayata na shiga taɓawa tun da ban iya baccin bayan sallahr asuba ba

Haka na ci gaba da zamana ni kadai a gida, Sai Maman Comfort(makociyata da gidanta ke kallon nawa) da take leko ni zuwa lokaci.

Idan dai ba ta shigo yau ba, to sha Allah gobe zan gan ta.

Ni ma idan kaɗaici ya dame ni, gidanta nake shiga mu yi hirarmu.

Ya Azeez idan ba ni na kira shi ba, shi dai ba zai kira ba, idan ma ya kira din, to wata bukata ce muhimmiya yake son in yi mishi.

Duk bayan kwana biyu Hammah ke aiko min da kayan miya danyu nama da kuma kudi hannu

A kullum na kan amsa wayar shi sau biyu, safe yamma, yana tambayata ko akwai matsala.

Aunty kam WhatsApp ne wurin haduwarmu, har video call nake kira ta kanga min Abdallah wanda ke ta kara girma da wayau kullum.

A bakinta nake jin Hammah ya siyar da gonar da ya ce zai siyar, har ma an fara yi mishi ginin plaza.

Yau Friday da misalin karfe biyar na yamma, zaune nake a kan stairs din entrance dina, monkey Kuma na ta Kai da kawowarshi, kasancewar na kwance shi.

Ina jin knocking gate zuciyata ta ba ni Maman Comfort ce.

Na saki dariya lokacin da na bude kofar na ganta tsaye sabe da comfort, hannunta daya Kuma ta rike Bible

Comfort din na amsa Ina fadin “Zuciyata sai da ta ba ni ke ce”

Mu ka kuma yin dariya a tare, lokaci daya kuma muka zauna a kan entrance din tana fadin “Daddyn Comfort bai kawo key ba”

Kai na girgiza tare da fadin “Bai kawo ba.”

“Bari in in jira shi” ta yi maganar hade da daukar kankanar da na yanka a plate Ina sha ina Kuma ba monkey

“Yaushe Oganki zai dawo?”

“Ranar dai Monday suke gama exam din, shi kam ban san ranar da zai dawo ba”

Dariya ta yi hade da fadin “Amarya, I have been telling you Ki yi amfani da damar ki, kar lokacin nan ya wuce ba ki aje komai na tarihin amarci ba”

“Ya kike son in yi Maman comfort. Shi fa ko kira ma bai faye dagawa ba”

“Ki bar kiran mana, just text him”

“In ce me?”

Wata dariyar ta kara yi tana fadin “Lallai ma matar nan, ni ce zan fada miki abin da za ki ce. To zauna nan mijinki celebrity ne, mata da yawa suna crushing din Shi. Ga shi matashi dan gayu”

“Maman Comfort, kullum ki yi ta kada min da gaba”

Ƴaƴan kankanar bakinta ta furzar cikin dariya ta ce “Amma dai kin san gaskiya na fada.”

“Shi kenan, zan gwada tura sakon yau”

“Yanzu za ki tura” ta yi maganar hade da daukar wayata da ke gefe ta ce “Cire min key din.”

Ban yi musu ba na cire mata key din

Ta shiga WhatsApp dina hade lalubo lambar Ya Azeez ta fara typing, bayan ta gama ne ta miko min tare da fadin “Duba ki gani ya yi.”

“You are the sunshine that brightens up my day and the stars that light up my night. I love you more with each passing moment. I missed you so much “

Murmushi na rika yi hade da bin rubutun da kallo, kafin na ce “Ba zan iya tura wannan ba”

“Let me see” ta fada hade da miko hannu

Na mika mata wayar, Sai ko kawai ta danna send, cikin dariya ta ce “Na tura miki ni”

Ido na fitar ina fadin “Da gaske?”

Cikin dariyar mugunta ta ce “Allah na tura”

Ta daga min screen din wayar, na kai hannu zan karbe ta boye

Na shiga magiya da rokanta ta goge kar Ya Azeez ya gani. Muna cikin hakan ne ma ta ce “Allah ɗaya ya zo online kuma har ya bude sakon.”

Ido na kwalalo waje ina fadin “Wayyo Maman comfort kin kashe ni.” Ihu da na yi ne ya ba Comfort tsoro wacce ke wasa da monkey.

Ta rarrafo da sauri zuwa wurin Mamanta tana kuka, ita kuma dariya kawai take yi

Kofar da aka buga ne ya sanyata dakatawa, daga can waje Daddyn Comfort ya ce “Your key Madame”

“Ok I’m coming” ta amsa shi hade da daukar comfort da kuma Bible dinta ta nufi kofar fita, har zuwa lokacin kuma dariya take yi sosai.

Ni kam da sauri na yi off na data, kafin na kama monkey na daure na wuce ciki

Har karfe takwas na kasa bude data, ban san wace irin amsa zan gani daga Ya Azeez ba.

Sai da na yi shirin bacci ne na bude datar sakonni Maman comfort suka rika shigowa, wanda da yawansu tsokana ce

Sakon Ya Azeez na bude zuciyata na dakan tara-tara ba ma uku-uku ba.

“Su Nasir sun shirya mana dinner, ki zama cikin shiri”

Shi ne abin da ya fada, zuciyata ta dan yi sanyi, ganin bai bi ta kan wancan sakon ba

Ni ma sai na share na ce “Yaushe kenan?”

Ina aje sakon ya bude, ya kuma yi reply da “Saturday”

“Allah Ya kai mu, kai yaushe za ka dawo”

“This coming Wednesday” ya kuma amsa min

“OK Allah Ya kai mu”

“Waye ya rubuta wancan sakon?”

Emojin mai alamar hawaye na aje ba tare da na ce komai ba

“Ke ce kika fadawa Aunty tun da kika zo ban taba kwana dakinki ba?”

Emojin zare idanu na ajiye kafin na kara da “Wlh ban fada mata haka ba”

“Da ke aka yi maganar ba ni da lafiya?”

“Ba da ni ba ne.”

“To me ya sa Aunty kullum take ba ni magunguna wai in sha?”

“Ban sani ba ni ma” na yi mishi reply

Bayan ya bude sakon bai kara cewa komai ba.

Ni ma sai na tafi yi wa Maman Comfort gulmar maganar dinnernmu.

Ta aje min emojin rawa kafin ta ce “Ki ce akwai casu, zan kai ki wurin mai gyaran jiki daga gobe, ki tanadi kudi.”

Dariya kawai na yi. Na yi off na data, hade da yin addu’ar bacci

Da safe sai ga Aunty na yi min maganar dinnern, wai Ya Azeez ya fada mata. Me da me nake bukata

Na fada mata gyaran jiki kawai, Maman Comfort ta ce za ta raka ni inda ake yi

Sai ga 100k Aunty ta turo min, wai mu fara zuwa yau.

Daga ranar kam muka fara zuwa, within 3dz jikina ba karamin canjawa ya yi ba, na yi wani irin kyau mai taushi.

Ranar Larabar da Ya Azeez zai dawo tun safe na gyara gidana tsab, na turareshi da wuri, kafin na shiga kitchen.

Masa da miyar egusi na yi mishi, na san yana sonta sosai

Sai nono da dakkere da Aunty ta aiko min da shi, saboda ta san yana son shi sosai.

Tun da na yi sallahr la’asar nake tunanin wane kalar kaya zan sanya, shi dai ba ya son manyan kaya.

Ni kuma ba ni da kanana, Sai dogayen riguna.

Haka na birkice kayan kaf, ban samu na sanyawa ba

Jakata na nufa na duba ina da almost 30k

Hijab kawai na zira hade da rufe gidan na nufi kasuwa a gaggauce

Ban fi 30mins ba na dawo gida.

A gurguje na shirya cikin kayan, bayan na sanya ne na isa gaban mirror, ba karya kam kayan sun karbe ni. Dama mai shagon ya fada min cewa idan har na sanya ba su yi min kyau ba, in mayar mishi ya ba ni kudina

Budadden jan wando ne dogo wanda aka fitar mishi da hips

Sai rigarshi long sleeve Kamar ta maza Sai dai ita tana da sharp din mata, an jera mata jajayen maɓallai a gaba. Na rika juyawa cikin kayan sai na ga kamar ba ni ba.

Kananun kaya kam ba karamin fitar da mace suke yi ba. Na zama wata yar shafal-shafal abu na.

Da white ribbon na kama gashina Wanda Maman comfort ta wanke min ya sha maya-mayai.

Yau kam na yi kwalliya sosai a fuskata, saboda har da red lips na sanya, wanda ya kara fito min da kyawun kwalliyar tawa

Ina tsaka da mayar da kayan da na jibge a kan gado, na ji horn din motarshi alamun har ya bude gate din ya shigo.

Na bar abin da nake yi zuwa falon, labulen window na kwashe, tsaye na yi ina kallon shigar da ya yi, kamar mun hada baki

Jan wando da farar riga ne a jikinsa hade farin cambas, sosai ya yi kyau duk da baya ya juya.

Labulen na sake, zuciyata na fada min in je in taro shi, kodai in yi zamana

Ban san na dade cikin tunanin ba, Sai da na ji shigar keynshi a kofar falo, kafin in yi wani abu kuma har ya shigo

Da hanzari na nufe shi tare da mika hannu na zare jakar da ke makale a kan kafadarshi

“What a surprise? Mun yi anko ne?”

Na yi dariyar jin dadin ina fadin “Kawai coincidence ne”

“Let’s have a picture”

Sai ko na gyara tsayuwata muka rika yin hotuna kala-kala, abu ga babbar waya sosai suka yi kyau

Wanka ya fara yi, ni kuma na koma daki domin in karasa mayar da kayan da na fitar

Bayan na gama ne na dawo falo, ban jima da zama ba shi ma ya fito zuwa dining

Abinci na zuba mishi, yana ci yana mun hirar yadda suka yi exams, da kuma target din da yake hari idan har ya samu sa’ar cin jarabawar.

Duk da shi din ba miskili ba ne amma na yi mamakin yadda ya saki jiki muke hirar sosai musamman yadda a waya ko chat ba ma magana doguwa

Abin da na lura da shi kawai shi ne bai faye dariya ba, lokuta da dama ya kan yi abun dariyar amma ni kadai ce zan dara.

Wani lokaci kuma zan yi abun da ya kamata ace ya yi dariya, amma ba ya yi, ba karamin abu ne zai sanya shi murmushi ba

Bakinshi ya goge bayan ya gama cin abincin, lokaci daya kuma ya mike tsaye, kasancewar hankalina yana kan wayata ban san lokacin da ya kara so wurina ba.

Sai dai saukar kiss din shi na ji a goshina tare da fadin “kin yi kyau. Ina son irin wannan dressing din”

Basarwa na yi kamar ban yi mamakin kiss din ko na ji kunya ba, “Thanks” na fada hade da ci gaba da abin da nake yi

“An ji ma zamu je wurin Aunty, I want to see her”

“Allah Ya kai mu.”

Na fada hade da mikewa na shiga gyara wurin da ya ci abinci.

Bayan sallahr magriba muka tafi Dougirie, sosai na ga farin ciki da annashuwa a fuskar Aunty, sakamakon ganinmu da ta yi.

Ni hankalina duk yana kan Abdallah ne, wanda ya yi ɓul-ɓul jawur kamar nunanar gwanda

“Aunty har da madara kike ba shi ne na ga ya yi Kato?”

Murmushi ta yi kafin ta ce “Nonon dai”

Ya Azeez da ke tsaye ya mika mata ledar da ke hannunshi

Ba ita kadai ta yi mamakin abin da ke cikin ledar ba, har da ni, saboda na dauka tsaraba ce ya kawo mata.

“A’uzubillahi!” ta fada da sauri hade da janye hannunta daga kan kwalbar tana fadin “Me ye wannan?”

Yadda ta yi din sai ya ban dariya, na shiga darawa a hankali.

“Menene?”

Ta kuma tambaya idanunta a kaina.

Na dakata da dariyar da nake yi ina fadin “Ina kwalbar da Aunty Karima ta ce an binne, amma an tono ta…”

“Eh na fahimta.”
Aunty ta katse ni

“To ita ce fa”

“A ina ku ka samu?”

“Tun kafin mu tafi Gembu Monkey ya tona ta wajen rashin jin shi, shi ne na jefata cikin fulawa.”

Ta shiga jujjuya kwalbar tare da fadin “Kai mutum sai a bar shi, yanzu don Allah ya aka wannan kurmusheshiyar layar ta shiga kwalbar nan ta zauna das da duwawunta?”

Duk mu ka yi shiru muna kallon kwalbar

“Na dauka tsaraba ce ma”. Cewar Aunty lokacin da take aje kwalbar kasa

“Tsaraba kuma Aunty, ni kin san ai ba na tsaraba”

Lokacin da ya kai karshen maganar har ya fice daga dakin

“Da gaske haka ya shigo miki hannu na dukan cinya?”

“To Aunty me zai kawo min shi da ya je jarabawa”

Taɓe baki ta yi tare da fadin “Ai fa, dama ke ba laifinshi kike so ba, amma lokaci na zuwa da hakan zai rika ba ki haushi. Shi dai namiji kamar jariri ne, yadda kika raine shi haka zai ta shi. Macen farko ita ke gyara miji”

Komai ban ce ba, hankalinta kuma mayarwa kan kwalbar kafin ta ce “Mutane babu Allah a gabansu. Ni ban san ina Allah Ya jefo ni da zaman aure ba. Miji da abokiyar zama ko wanne sai a hankali. Shi ya sa idan kika ga mutum da kudin kawai ki kalle shi, shi kadai ya san hanyar da ya bi wajen tara dukiyarsu. Mutanen wannan zamanin sai addu’a, amma ace ka ci haram, ka yi aure da haram, ka tufatar da matarka da haram, yaranka haram. Maryam wannan abu na tayar min da hankali duk lokacin da na tuna, Hammah ya aure da kudin haramun, ya ciyar da ni, ya shayar da ni, ya tufatar da ni, ya ba ni ilmi duk da haram, gabadaya jikina haram ce ke yawo. Kai Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un. Allah ka gafarta mana “

” Amin”na amsa a sanyaye.

“Ranar lahira kam akwai rikici Maryam, Allah dai ya jikan mu”

“Amin” na kuma amsawa

Zamanta ta gyara sosai kafin ta ce “Kina ganin Azeez na shan wani magani?”

Kai na girgiza hade da fadin “A’a”

“Azeez! Hmm! Shi bai san yadda ake fadi tashi a kanshi ba. Sai Shirme yake yi. Yana kwana dakinki?”

Nan ma kan na girgiza

Mikewa ta yi hade da dakko wani kullin magani tana fadin “Kin ga wannan maganin da muruci aka hada shi. Kin san muruci ai?”

Na daga kai alamar eh

“To a tsakiyar shi ba akwai wani tsinke mikakke ba?”

Na kuma gyada kai alamar eh

“To da shi aka hada wannan maganin, Maryam don Allah ki tabbatar Azeez ya sha. Adda Faɗi ta fada min cewa ta ji Gana kawar Mamansu Huzaima ta ce Azeez ba zai taba yin mu’amalar aure da ko wace mace ba.

Tun daga wancan lokacin nake ta faman neman magani amma Azeez ba ya sha, Sai ya ce min kalau yake shi. Yana lafiya shi ne zai kwana da mace a gida daya ba tare da komai ya faru ba. Gaskiya ban yarda ba.

Idan kuwa har Adama ta taba min lafiyar yaro gaskiya ba zan yafe mata wannan ba. Allah Ya sani”

Ni shiru na yi, saboda ban san me zan ce ba.

Kullin maganin ta miko min “ki hada mishi da nonon nan ya sha”

“Ai ba zai sha ba Aunty” na yi saurin fada

“Ke wawuyar ina ce, Sai ka ce ba mace ba, ba ki san yadda za ki lallabashi ya sha ba”

Kamar zan yi kuka na ce “Allah Aunty ni na san ba zai sha ba, gara ma ke idan kika tsare shi sai ya sha.”

Dire maganar tawa ta yi daidai da shigowarshi, duk sai muka zuba mishi ido muna kallon shi

Cike da bacin rai Aunty ta ce “Wato Abdul’azeez duk maganin da na ba ka, ba ka sha ba ko?”

Kallon da yake min ne ya sa na ce “Ba ruwana”

“Ya aka yi ta san ban sha ba to?”

“Ni da kaina na gane” Aunty ta yi saurin amsa shi

“Je kitchen cikin fridge akwai nono Maryam ki dakko min shi”

Mikewa na yi da zummar zuwa kitchen din, Sai ya tare kofar, a shagwabe ya ce “Aunty ni kin san ba na son Irin magungunan nan don Allah”

“Ka san nawa na kashe aka ba ni?”

“Amma ai lafiyata ƙalau”

“Karya kake yi” “Allah da gaske nake, and I’m going to prove it soon”

Idanuna na ware sosai a tsakaninsu, na rasa me nake ciki, tsakanin kunya da mamaki.

Ban san yadda aka yi ba, ni dai kawai na ji na kutsa a tsakanin hannayenshi da ya tare kofar na fice.

<< Da Magana 38Da Magana 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×