Skip to content
Part 4 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Daga lokacin da na fara zuwa school 7:30am nake fita, kuma Aunty ce kullum take kai ni, ba ta taba gajiyawa ba.

Yau ma kamar kullum na fito sanye cikin fararen riga da wando, wanda aka yi musu ado da sanda-sandar pink color din yadi akasa, dan karamin hijab Iya kafada, takalmi baƙi da farar socks, sosai kayan suke karbata musamman yadda nake goge su fes.

Tun lokacin da na fito ina jiran fitowar Aunty na hango Aunty Adama duke cikin fulawoyi, kafe ta na yi da idanuna a kokarin gano me take yi, har zuwa lokacin da ta dago ban fahimci komai ba.

Gani na da ta yi tsaye ya sa ta daure fuska, dama ko dariya take yi ta ganni dainawa take yi. Ni ban san dalili ba, duk da wani lokaci ta kan ce wai Uwata ce ta ja min, to ko me uwar tawa ta yi mata da zafi har haka oho. Ba Ta duniyar ma, amma hakan bai hana ta ci gaba da rikon abun ba.

Ban san me ya sa na kasa dauke idona a kanta ba, har ta zo saiti na

“Ina kwana?” na fada a hankali.

Ba ta amsa ba, kuma dama na san ba amsawar za ta yi ba. Harara kawai ta maka min.

Kamar daga sama kuma na ga Ya Azeez ya turo kofar gate.

Sosai na ji gabana ya fadi, har wani fitsari – fitsari na rin ga ji, hakan bai hana ni shagala da kallonsa ba. sanye yake cikin wasu kaya light brown, rigar mai dogon hannu ce round neck, wandon kuma kamar na sport, kunnensa like da earpiece.

Rabon da in gan shi tun ranar da ya biyo ni da wuka, wani lokaci dai, cikin magana na kan ji Aunty ta ce ya zo.

Hawowarshi kan entrance din ta yi daidai da bude kofar Aunty, dalilin da ya sa dukkansu suka ja burki.

Key din motar ta mika mishi, tun kafin ya yi magana tare da fadin “Kai ta school, saura daga can ka wuce ka siyar min da motar, na san za ka iya.”

Na san ta yi dabara ne, don kar ta bar shi a cikin gidan shi kadai.

Bai yi magana ba, ya dai karbi key din hade da juyawa inda motocin suke, ni ma na bi shi bayanshi.

Ku san tare muka shiga cikin motar, har ya murza key din, Sai kuma na ga ya dakata shiru kamar mai tuna wani abu.

Zuwa can ya kai hannunsa a pocket din da ke gaban motar ya bude na ga ya janyo kudi ya cusa aljihu kamar shi ne ya aje dama

A zuciyata na ce wato shigowarshi har ya ji kamshin kudin.

Haka ya rika bude-bude har sai da ya tsince duk wasu kudi da ke cikin motar nan, ko naira biyar ce sai ya dauke ta. Kuma duk inda ya kai hannu sai inga ya ciro kudi, kamar dama ya san da zaman su.

Da sauri na kawar da kaina gefe, saboda yadda na ga ya dago kanshi, ban ankara ba na ji kunnena rike a hannunshi, Sai da ya murɗa sannan ya ce “Saura ki fada ma Aunty, wlh dare zan biyo in yanke wadannan laɓɓan na ki. Munafuka, kin san akwai deal namu da har yanzu bai fada ba ko? (Bai jira amsa ta ba ya dora) to don Allah ki bude min wannan aikin, wlh! Kin ji na rantse, Sai kin yi danasanin zuwan ki duniya. “

Shiru na yi bayan na kame jikina, don kanshi ya saki kunnen nawa, ko tari bai kufce min ba, mugun tsoronshi nake ji, musamman yanzu da ya kasance daga ni sai shi.

A gaban classes dinmu ya aje ni, har na fita kuma na tuna Aunty ba ta ba ni kudin abinci ba, da kuma na dawowa.

Dalilin da ya sanya ni juyowa da dan guduna, saboda lokacin har ya fara reverse , shi ma tsayawa ya y da alama yana jiran karasowar tawa ne.

Lekawa na yi a dan tsorace na ce “Dama Aunty ta manta ba ta ba ni kudin abinci da na komawa ba”

Ido ya zuba min, kafin ya karkace ya zaro 2k ya miko min ba tare da ya yi magana ba.

“Na gode” na fada a hankali hade da juyawa zuwa class. Wannan yana daya daga cikin abin da yake burgeni da shi, idan har zan nuna ina son abu, to fa koda kudin sata ne sai ya siya min. Shi ya sa idan ya ba ni abu, sai Aunty ta ce shi ɓarawon tsaye ni ta zaune.

Azeez

Lokacin da ya dawo harabar gidan ba kowa, bayan ya yi parking kai tsaye bangaren Aunty Adama ya nufa.

Cikin sa a kofar a bude, shi ya sa kai tsaye ya shige.

Ba kowa a falon sai TV da ke aiki, tsaye ya yi tsakiyar falon, kafin daga bisani ya nufi kan stairs din da zai sada shi da bedroom dinta.

A hankali ya murza, handle, jin karar saukar ruwa a toilet, kasan filonta ya yi wa tsinke hade dagawa, wayoyinta guda biyu babba da karama ya kwaso, cike da kwarewa ya zare mata sim din ya watsa mata a tsakiyar gadon ya fice abun sa.

Lokacin da ya shiga part din Aunty karyawa take yi, key din kawai ya aje mata ya juya ba tare da ya ce komai ba, ita ma ba ta tsinka mishi ba.

Shi yana cikin sahun miskilai, kuma ba miskilai ba.

Har ya je tsakiyar farfajiyar gidan, Sai kuma ya koma baya zuwa bangaren Hammah, kofar ya fara tabawa ya ji a rufe, baya ya zagaya, da ya rasa abun dauka, ACn da ke manne da ginin ya kwance ya fice da ita.

Aunty Adama

Lokacin da ta fito wanka kai tsaye kan dressing mirror ta nufa, tana tsaka da lafta maya-mayan bleaching din ta ne, ta tuna suna magana da costumernta da ke Kano zai turo mata wasu kaya ta WhatsApp ta gani.

Tuna wannan ya sanyata mikewa zuwa inda pillown yake, hannu ta sanya hade da lalubawa ba ta ji komai ba, da sauri ta daddage dukkan pillows din, still babu komai.

Ta dago da niyyar zuwa falo ko can ta bar wayar, ta yi arba da Sim din ta guda uku a tsakiyar gado

Baki bude ta ce “Kan’ubannan! Ba dai wannan aljanin satar ya samu sa a ta ya shigo min daki ba”

Kai karshen maganarta ya yi daidai da ficewarta daga dakin tana kwalawa Zubaina yar aikinta kira.

“Abdul’azeez ya shigo dakin nan?” ta tare Zubaina da tambaya.

A tsorace Zubaina ta ce “Bai shigo ba Hajiya”

“Ke dalla can matsa! Kina can kina sokancinki kin bar min kofa a bude ya shigo ya min barna, wawuya kawai.”

Kai karshen maganar tata ya yi daidai da komawarta sama.

Hijab ta saka a kan towel din da ke jikinta, gudu-gudu, sauri-sauri haka take tafiya.

Ta san idan har Azeez ya shigo gidan babu tantama shi ya kwashe mata wayoyi, fatan ta Allah Ya sa bai bar gidan ba

“Hammawa!” ta rika kwada mishi kira tun kafin ta iso.

“Abdul’azeez ya shigo gidan nan yau?”

“Eh Hajiya”

“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!” abin da ta fada kenan, sannan ta dora “Ya fita ne?”

“Eh zai kai 20mns haka da fita.”

“Shi kenan?” ta kuma fada cike tashin hankali, sannan ta dora
da” ba ni wayarka.”

Ba musu ya mika mata, ta shiga shigar da lambar Hammah

“Hammah ka ga Abdul’azeez ya shigo har bedroom dina ya kwashe min wayoyi ko?” ta yi maganar kamar karamar yarinya. Lokacin da ya daga kiran

Daga can bangaren Hammah ya ce “Yaushe kenan?”

“Yanzu fa da safen nan”

“Ya bar gidan ne?” Hammah ya kuma tambaya.

“Eh. Hammawa ya ce ya fita” Ta amsa shi.

“Ai tun da ya riga ya fita Adama sai dai ki yi hak’uri kuma”

“500k+ fa na sayi wayar.” ta fada cike da bacin rai

“Ko million ne Adama, Azeez kam bakonki ne, you know him well, Idan Har zai fita da abu shi kenan kawai.”

“Hammah ko fa wata wayar ba ta yi da saye ba, don Allah ni dai ka kira shi” kamar za ta fashe da kuka ta karasa maganar.

“Do you think he’ll pick the call, (ya dan yi wani murmushi) not this Abdul’azeez, kawai ki yi hakuri Idan kuma you have any other ways to find your phone try it.” ya kai karshen maganar hade da yanke kiran.

Wani malolo na bacin rai ya tsaya mata a wuya, ba yau Azeez ya fara mata sata ba, amma ta yau ta fi kona mata rai fiye da sauran” Shegen yaro kawai barowa”ta fada a bayyane cike da kunar zuciya lokacin da take mika ma Hammawa wayar shi.

Aunty da take sakkowa daga kan entrance din ta ta ce “Ina kwana?”

“lafiya lau!” ta amsa ba yabo ba fallasa hade da tura kofarta ta shige.

Sambatu kawai take “Dan’iskan yaro ɓarawon banza, duka-duka yaushe na sayi wayar, shi ne ban ci ba, ban sha ba za ka jaza min asarar dubu dari biyar, wlh ba zan yarda ba.”
Haka ta rika fada a fusace lokacin da take hayewa sama.

Megadi Aunty ta nufa, Sai da suka gaisa sannan ta ce” Me ya faru ne na ga Momynsu Huzaima kamar ranta bace? “

Cike da sanyi ya ce” Wai tambayata take yi Yallaboi Abdul’azeez ya fita. “

Gaban Aunty ya fadi, cike da fargaba ta ce” Me ya sa take tambayar shi? “

Ya shiga inda-inda, dalilin da ya sa ta ce” Ya daukar mata wani abu ko? “

Cikin Hausarsa ta Minchikawa ya ce” Eh…to… Walahi Hajiya…. To haka dai ta ce… Wai ko ya daukar mata… Uhhh… Wai ko ya daukar mata waya. Walahi Hajiya kuma ni ban ga ya fita da komai ba. Sai Ac. “ya karasa zancen hade da watsa hannayenshi du biyun alamun dai nothing serious.

Kwalo ido Aunty ta yi tare da fadin” A.C kuma Hammawa? “

A rude Kuma a daburce ya ce” Aaa! Ba fa sabuwa ba ce, ina jin ma da ita ya shigo ai. “

Aunty dai tsaye ta yi kamar ta kada suruka, kafin daga bisani ta taka zuwa inda motarta take jiki a mace. Lokaci daya kuma tana kiran Azeez wanda ya ki daga kiran.

Azeez

Bayan fitar sa gidan, kai tsaye wajen customers na shi ya wuce, 300k ya siyar da wayar Aunty Adama, ACn kuma ya 50k, karamar wayar kuma ya bayar kyauta.

Bai dawo hotel din ba sai 5pm daidai.

Kai tsaye dakinsa ya wuce, yana kokarin cire kayan jikinsa ya shiga wanka ne, ya ji an turo kofar.

Madina ce ta shigo cikin shiga ta alfarma, kamshi mai dadi yana take mata baya.

Ya fasa abin da ya yi niyya lokaci daya kuma ya zauna kan dan ƙaramin teburin da ke gaban gadon.

“Azeez!” ta kira sunan a yangace.

Bai amsa ba, amma ya dago kai yana kallon ta.

“Tun dazu nake nan ina jiranka, kuma Ina ta kiran wayarka a kashe, hope everything is well?”

Sai a lokacin ya tuna ya kashe wayar saboda kiran da ya ga Aunty ta yi mishi, kuma ya san a kan maganar wayar Aunty Adama ne.

“Na kashe wayar ne?” ya ba ta amsa kamar ba ya so.

Wannan ya sa ta zare face mask din da ke fuskarta, hade da janyo karamar kujerar da ke gaban teburin da ke dauke da kayan shayi.

Zaunawa ta yi suna fuskantar juna, a marairai ce ta ce “Abdul’azeez ina son ka wlh, a shirye nake na yi maka duk abin da kake so, I promise you, zan biya kudi ka yi karatu a kasar waje, zan siya ma duk kalar motar da kake so, na yi ma alkawarin rayuwar duk da kake son yi ta hutu, don Allah ka karbi soyayyata”

Yadda ya nutsu kamar tuwo a kula shi ya fi yi mata dadi, karon farko da ya mayar da hankalinsa a kanta lokacin da take mishi magana.

Abin da ba ta sani ba shi ne, his mind is somewhere else, Shi kawai yana mamakin So din ne, hade da tambayar kansa me ye so, ya kuma yake? Idan mutum yana son abu ya yake ji.

“Azeez” ta kira sunan shi.

Firgigit! Ya dawo cikin hankalinsa, dalilin da ya sa ta ce “Are you alright”

“I’m. I’m just tired”

Hannayensa ta kama du biyun hade da narkewa cike da kissa. Ya zuba ma hannayen nata ido for some minutes, a hankali kuma ya janye na shi hannayen hade da mikewa tsaye.

Ita ma mikewar ta yi, cikin kasalallar murya ta ce “Azeez ina son ka, son da ban taba yi ma wani jinsi irin naka ba. Na yi bincike ko akwai wacce ke janye hankalinka a kaina ne, an tabbatar min babu. Ba zan gaji ba na san watarana burina zai cika.

Kai karshen maganar tata ya yi daidai da bude jakar hannunta, bandir din kudi ta dire mishi a gefen gadon, kafin ya ankara kuma ya ji saukar kiss din ta a gefen wuyan sa.

Ido bude ya bi bayanta da kallo lokacin da take fita daga dakin, daga bisani kuma ya kai hannu hade da shafa inda ta yi kissing din nashi.

“Mtswwww!” ya ja dogon tsaki tare da fadin “Yar wahala. Waye zai wani aure ki, ke aure ya dama, ni baya gabana.”

Toilet ya wuce, yana cikin toilet din ne ya ji, shigowarsu Anwar, ya san gulma ta kawo su.

Ya fito wankan daure da towel, hannunsa kuma rike da wani towel din, yana tsane ruwan jikinsa.

Anwar ne ya fara cewa” Angon yar majalisa”

“Yar wahala dai” Azeez ya yi saurin ba shi amsa.

Nasir ya gyara zama tare da bubbuga kudin da Madina ta ajiye bisa gadon yana fadin “Wai me ye problem naka ne? Matar nan akwai kaya a, wajenta, yanzu haka ta shaida min idan ka aure ta, za ta dauki nauyin karatun ka a ko wace jami’a a duniya ba ma Nigeria ba.”

Azeez da ke shafa mai ya ce “Ta dauka a gidanmu babu wadannan kudin ne? Ko ina nake son yin karatu a duniya zan yi ba tare da ta sanya min hannu ba.”

“So why kake karbar kudinta, tun da ka san a gidanku akwai” cewar Mubarak cikin tabe baki.

“Saboda ita ce ta ba ni, ban tambaye ta ba.”

“Ka ga! Kawai a kawo karshen wannan game din, ka fada mata gaskiya kawai”
Cewar Anwar.

“Ya fada mata gaskiya shi ba cikakken namiji ba, ba shi da feelings” Nasir ya yi maganar ya na latsa wayar sa.

Azeez ya juyo yana kallon sa, da alama bai san me zai ce mishi ba, yayin da Anwar da Mubarak ke dariya sosai.

Nasir ya mike zaune daga kishingidar da ya yi tare da fadin “Keep joke aside, Azeez wlh Ina son Maryam, abun mamaki dazu kawai na ganta a nursing school Lokacin da na mayar da Abigail. Kai mutumina! Ban taba ganin wacce kayan nursing suka karba ba irin yarinyar nan (ya yi maganar hade da bubbuga kafadar Azeez) Waiyaushe ta fara nursing school ne ban sani ba? “

“Kana can kana neman matanka?”
Azeez ya amsa shi hade da janye hannunshi daga kafadar shi

“Ka san Allah wadannan matan da kake gani duk fake ne, original dinsu Maryam ce, ko kwanciya da ka ga ina yi dasu, Sai na kawo Maryam a zuciyata nake gamsuwa.”

Dukkansu ukun suka zubawa Nasir ido, kafin daga bisani suka mayar kan Azeez, wanda ke yi wa Nasir wani kallo mai cike da bacin rai.

<< Da Magana 3Da Magana 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×