Skip to content
Part 40 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

A falo na hadu da Hammah, da sauri na daidaita nutsuwata muka gaisa, ya tambaye ni akwai matsala, na amsa da babu, daga nan ya haura sama, ni kuma na karasa ficewa.

Ji na yi kamar in tari Napep zuwa gida, sai dai ba ni da kudi, wannan ya sa dole na zauna cikin motar ina jiran shi.

Kamar 30mns na hango shi yana tahowa.

A zuciyata na ce “Ya Azeez kam bakinshi babu linzami.”

Bayan ya zauna sosai ne ya ce “Ke komai sai kin fadawa Aunty ko?”

“Wlh! Wlh!! Ni ban fada mata komai ba”

“Ba ki fada mata komai ba, shi ne kullum tana kan cusa min magunguna. (ya kai hannu yana goge bakinshi) yanzu ga shi ita da Hammah sai da suka matsa min na sha wani garin banza” ya rufe maganar hade da jan tsoki yana kuma goge bakin shi.

Haka nan na ji dariya ta suɓuce min, abin da ya kara tunzura shi, ya kawo min duka da bayan hannu.

Da sauri na fice a guje daga cikin motar, don dama ban rufe murfin ba.

Shi kuma ya fito a fusace, lokaci daya kuma yana zare belt din.

“Kul Abdul’aziz! Kul! ” Daga can kofa na ji Aunty ta fada, lokaci daya kuma ta sakko daga kan entrance din ranta a bace.

Tun kafin ta karaso take fadin “Ubanka bai fada ma cewa na ce koda wasa kar ka taɓa Maryam ba, idan bai faɗa ma ba, ni yanzu na fada ma. Wlh Azeez duk ranar da ka kuskure hannunka ya sauka a kan Maryam zan manta ni uwarka ce, Sai na ga gatan ka a garin nan”

“Ni ce nan na ce ka sha magani ba Maryam ba, ni za ka doka ba ita ba. Tun da kai ba ka san abun arziki ba. Na wa ka san ina kashewa a kan maganin?”

Daidai lokacin ta karaso dab da inda yake tsaye yana ta huci.

“Bari ka ji in fada ma da babbar murya, har yanzu ba a haifi namijin da zai doki Maryam ba gaskiya, ka sanya wannan a ranka, da can baya dai ka buge ta, amma ban da yanzu ni nan ba zan dauka ba. Idan kuma ka ce za ka gwada Bismillah, idan ban hada ka da kattin unguwa sun buge mun kai ba ka ce ba ni ba ce”

Yadda take fadan ne bilhakki da gaskiya ya sa na ce “Aunty, ba laifinshi ba ne na wa ne fa”

Wani kallo ta wurgo mun ta cikin hasken da ya haske tsakar gidan kafin ta ce “Ke da Allah can, sha-sha, ke kam ko kashe ki ya yi za ki magantu ne, ko laifin ki ne sai ya, warware karfinshi ya buge ki haihuwar ki ya yi. Ni ba zan dau wannan ba. Shi ya sa tun asali na ce ban son hadin nan…”

“Kuma ko yanzu kika kwace yarki, a daren nan Azeez ya ce mata goma yake son aure idan ana aure wlh na tabbata sai ya zaɓa” Hammah ya katse ta, a lokacin da yake karasasowa wajenmu

“Amma kaf goman ba za su yi Maryam daya ba ni na sani, kuma kai ma ka sani, shi kanshi Azeez din ya sani. Kyal-kyal banza din”

Dariya Hammah ya yi kafin ya ce “Aisha kina da daukar abu da zafi, ki daina shiga harkar yaran nan.”

“Ta ya ba zan shiga ba, yanzu da ban shiga ba kila ai da muna hanyar asibiti, hannun Azeez din nan kam kamar rodi ya sauka a kan Maryam. Kai ni fa wlh ji nake kamar in je in share daki a gidan can, sam ban yarda da hankalin Azeez ba.”

Wata dariyar Hammah ya kuma yi kafin ya juya kan Ya Azeez da ya gama cika kamar zai fashe kafin ya ce” Azeez! Sakaran namiji ai shi ke dukan mace, kar ka kara gwada yin haka ka ji ko”ya karasa maganar hade da bubbuga kafadar shi

Cike da bacin rai ya ce “Ina ta kokarin controlling temper yarinyar Nan dole Sai ta kai ni karshe”

“Haka mata suke Azeez sai hak’uri, ka kara danne zuciyarka ka ji”

“Fada mishi dai, ga mari ga tsinke jaka, an dauki yarinya kyautar Allah an ba ka, sannan ka hada mata da duka. Ni fa gaskiya Hammah ban yarda ba, a zo a yi mata lefe”

Sosai Hammah ya yi dariya kafin ya kalli Ya Azeez yana fadin “Ka ji ta ko, shiga mota ku tafi abun ku.”

“Ke Maryam zo shiga ku tafi” Na baro inda nake tsaye, jiki ba kwari na shiga hade da daidaita zamana

Sosai ban ji dadin yadda abubuwa suka kasance ba, yadda muka fito cikin farin ciki na so mu koma haka.

Aunty tana da zafi sosai, sannan abu kadan Ya Azeez ke yi ya hawar da ita sama. Ni kaina ban ji dadin yadda ta dankara mishi maganganu haka ba saboda ni.

Har muka isa gida komai bai ce min ba, amma kam ko kuskuren kallon fuskarshi ba na son yi. Har wani muni na ga ya yi saboda ɓacin rai.

Bayan ya shige dakin shi tsaye na yi a falo zuciyata ba dadi, kafin daga bisani na nufi hanyar dakin na shi, ina shiga yana fitowa daga toilet, yadda na ga sashin bakinshi a jike ya tabbatar min brush ya yi.

Tun kafin ya ce wani abu na ce “Don Allah Ya Azeez ka yi haƙ…”

Ban karasa abin da na yi niyyar fada ba na ji ya fisgo ni, hade da jefa ni saman gadon, lokaci daya kuma ya shiga warware belt din jikinshi

Ban san yadda zan bayyana kalar rudewar da na yi ba, tuni na fara hangoni kwance fatata duk ta ɗaye.

Sai na ga ya hada da wandon da belt din ya zare su hade da jefar dasu, vest din jikinshi ya cire ita ya yi wurgi da ita.

Ban yi aune ba ya kuma fisgo ni hade da fisge rigar jikina da karfin bala’i wanda ya yi sanadiyar faskewar hannu bra dina

Sai ya hada da bra din ya wurgar.

Zuwa lokacin na fara tunanin ko yana da aljanu ne, shi ya sa na shiga kokarin kwatar kaina, na tattara duk karfina na dire daga gadon zuwa kofa, Sai dai kafin in karasa ya riga ni, ya kuma danna mata key ya zare.

“Ba abin da Aunty ke so kenan ba, kuma ke shi kike so, shi ne kike kai kara ta ba na yi miki ko, to yau zan yi miki.”

Yanzu kam na gane nufin shi, cike da tashin hankali na ce “Wlh ban taba kai ƙararka ba, don Allah ka yi hakuri, idan ma na kai din wlh ba zan kara kaiwa ba

“Ya fi ki tafi da shaidar lafiyata ƙalau ai. “

Ya karasa maganar hade da fisgo ni, babu wani romance babu komai Ya Azeez ya kusanci ni. Tun da na zo duniya ban taɓa jin azabar da na ji a ranar can ba, ko suma na yi na dawo oho. Bishi-bishi dai na ga Ya Azeez ya fice daga dakin ba tare da ya rufe kofar ba. Kila daga nan kara sumar na yi.

Kafin daga bisani na farka, na shiga kokarin tashi, duk yadda na gwada zan tashi sai in ji ban iyawa. Haka nai ta gwadawa har Allah Ya ba ni ikon matsawa da ƙyar daga inda nake.

Kasancewar kwan ɗakin a kunne yake wannan ya ba ni damar karewa jikina da inda nake kwance kallo

Jini-jinin da na gani ba karamin tayar min da hankali ya yi ba, ban san lokacin da na aro karfi na sauka bisa gadon da rarrafe ba.

Towel din da na gani a kasa na dauka hade da rumgume shi a kan kirjina, har zuwa lokacin idanuna na a kan jinin da ke saman gadon can.

Duk yadda na so in tashi in yi tafiya kasawa na yi.

Dalilin da yasa na rika rarrafe kenan, idan na yi kadan sai in huta, har zuwa lokacin towel din na hannuna, kuma jikina ko kyalle babu.

Da kyar na samu na karaso falo inda na yasar da wayata da kuma mayafin da na yafa

Karfe goma da rabi na dare agogon ya nuna, Maman comfort na kira, na yi mamakin yadda na ji muryarta raɗau babu alamun bacci

“Amarya, kun dawo ne?”

“Eh, tun dazu ma, kina gida ne?” na fada a hankali

“Eh. Akwai wani abu ne?”

“Don Allah ki zo yanzu.” cike da karfin hali nake maganar.

Ko minti daya ban yi da yanke kiran ba na ji tana knocking kofa.

Ba zan iya zuwa in bude mata ba, shi ya sa na kara kiran ta “Kina ji na Maman comfort, Idan Daddyn Comfort na gida, don Allah ya hauro katangar nan ya bude miki gate ni ba zan iya ba.”

“Jesus!” Ta ambata da sauri
Kafin ta ce “Ba ki da lafiya ne?”

Kamar tana kusa da ni na gyada kai kafin na ce “Don Allah ya yi sauri Maman Comfort.”

Ina jin yadda ta ji na karasa maganar ne ya sanyata azamar kiran mijin nata saboda tsakanin yanke wayar da jin durowar Daddyn Comfort da kuma bude kofar gate din bai fi minti biyu ba

Sai a lokacin ne na rika kokarin daura towel din nan, Don da na san ma Daddyn Comfort ba zai shigo ba ba zan daura ba, ni kadai na san azabar da nake ciki.

Kasancewar Ya Azeez a bude ya bar kofar ba ta sha wahalar shigowa ba, a rude ta karaso inda nike durkushe tare da fadin “Amarya what’s wrong with you, What is happening? Oh my God.”

Cike da karfin hali na ce “Daga ni ki kai ni toilet don Allah”

Rufe bakina ya yi daidai da cicciɓoni da ta yi a kokarin ta na mikar da ni kamar yadda na ce

Wata irin azaba na ji wacce ta fi ta baya, da sauri na kwalla ƙara ina fadin “Aje ni Maman Comfort, wayyyo Allahna ajiye ni don Allah”

A hankali ta ajiye ni, towel din dana daura ya fadi, ko ta kanshi ban bi ba, ita ce ta dakko ta kuma ɗaura min

Bayan na huta a karo na biyu na kuma ce mata “Daga ni yanzu”

Tana kara cicciɓata na ji irin zafin dazu, na kuma kwalla ƙara tare da fadin “Ajiye ni Maman Comfort, ajiye ni zan mutu”

Ta kuma sauke ni a hankali, na rika mayar da numfashin azaba

“Amarya wai me ya same ki?” cike da kulawa ta yi min maganar.

Maimakon in amsata sai na shiga rarrafawa zuwa hanyar dakina kamar dazu.

Ita kuma tana bi na a baya, idan na tsaya ina hutawa ita ma sai ta tsaya.

Da haka har muka shiga daki, daga duken da nake na ce” Hada min ruwa mai zafi in shiga. “

Ba ta ɓata lokaci ba ta hada min, ita ce ta kama ni zuwa kwamin wankan, ina shiga ban san lokacin dana rarrafo da sauri na yo waje ba, hade da kwalla ihu, ranar kam ba ta ɓoye jiki nake ba, na ma manta akwai wata abu kunya a duniya, ni ba ma ta ganin tsiraicin nake yi ba. Da alama ma ita kanta Maman Comfort din ta manta da wannan shafin, kokarinta kawai in dawo cikin hayyacina

Haka ta rika danne ni a cikin ruwan nan ina ihu ina komai tun da ta fahimci abin da ya faru

A ruwa nake amma saboda azaba zufa nake yi, wajen sau goma tana danne ni a ruwan zafin nan, kafin ta je ta kawo min diclopain da paracetamol.

Sosai nake ganin tausayina a idanunta, sannan ta yi min abin ko ƴar’uwata abin da za ta yi min kenan.

Cikin musulmai ko Cristians dole akwai na kwarai, kawai abin da ake bukata shi ne kyautata mu’amala.

Ba ta bar gidana ba sai karfe daya saura.

Ba ta jima da fita ba, barcin wuya ya dauke ni.

Ban san lokacin da aka kira sallahr asuba ba har aka yi ta, ni dai cikin bacci na ji kamar ana knocking kofata.

Da kyar na samu na sakko daga gado, towel din nan dai shi na daura, da dabara na rika daddafa bango har zuwa kofar falo.

Ganin Aunty tsaye tare da Maman Comfort ba karamin kayar min da gaba ya yi ba. Agogon falon na kalla karfe 7:30am daidai

Ta rika bi na da kallon sama da kasa, ni kuma na shiga kame-kame.

Duk yadda na so in yi tafiya normal kasawa na yi, dole sai da na rika dafa bango. Yayin da na rika kyaftawa Maman comfort ido a kan kar ta ce ban lafiya, Sai dai ba ta fahimce ni, don cewa ta yi “Amarya ya jiki?”

“Da sauki” na amsa ina ta ƴan kame-kame.

Aunty dai bi na da kallo kawai take yi, har zuwa lokacin da Maman Comfort ta fice, wai Daddyn Comfort Zai fita aiki za ta dawo.

“Dukan naki ya yi?” Aunty tambaya idanunta a kaina

A zuciyata na ce “Yo ba gara dukan ba.”

A zahiri kuma na ce “Ki zauna mana Aunty”

“Zan zauna din ai, ina Azeez din, dukan naki ya yi?”

Kai na girgiza a hankali ina fadin “A’a”

“To me ya sa me ki, ko tafiya ba ki iyawa?” Rai a matukar ɓace ta yi maganar.

Na narke fuska kamar zan yi kuka ina fadin “Wlh Aunty bai dake ni ba”.

“Wallahi Maryam zan yi miki ɗan’iskan duka a gidan nan, da Azeez ya rika dukan ki, ya fi min kullum in zo in doke ki in koma gida, saboda kar ki fada min ya doke kin, shi ne tun jiya kika ƙi daga wayata ko?”

Yadda take maganar a harzuƙe ne, ya sanya ni fashewa da kuka, na rika ja baya karamin yatsana a bakina.

“Za ki fada min abin da ya faru, ko sai na sauke goyon nan na daka ki? “

Sai na kara fashewa da kuka, abin ya ƙara tunzurata take ganin kamar dai ya doke nin ne kawai ban son fada ne.

Sai ko ta kwance goyon Abdallah a fusace ta ajiye bisa kujera.

Da sauri na shiga dafa kujeruna a kokarina na gudu, Sai dai ban je ko ina ba na fadi kasa, wannan ya sa na zauna dirshan a kasa ina kuka.

Ita kuma kitchen ta nufa hade da dakko muciya tana fadin “Gara in yi miki shegen duka Maryam zuciyata ta rage radadin da take yi min. Ke kin zama kyandir ko, kone kan ki, ki raya wani”.

Allah Ya taimake ni, kafin ta kwala min muciyar Maman Comfort ta shigo hade da shiga tsakaninmu tare da fadin “Ya haka kuma, me ya faru?”

Cikin kuka na ce “Wlh Aunty ba dukana ya yi ba”.

Kafin ta yi magana Maman Comfort ta ce “A’ah Aunty! Ba dukanta ya yi ba. They are having sex, I think kuma ya dan zo mata da karfi, so Sai ya ji mata ciwa.”

Da muciyar hannunta da bakinta ta saki gabadaya, after some seconds ta ce “Azeez din?”

Ni dai kukana nake yi

Maman comfort Kuma ba ta amsa ba

Kai tsaye ta nufi hanyar dakinshi, kamar mintuna biyu, ta fito idanunta kafe a kan tiles din da ke shimfide tun daga corridorn kofar shi har zuwa babban falo.

Bayan ta iso inda muke ne cike da tashin hankali ta ce “Ki ce min dai fyaɗe ya yi mata. Wai Allahna Ni Aisha, Azeez zai kashe ni wlh” Da sauri ta juya wajen da hand back dinta take, ba sai na na tambaya ba na san Ya Azeez take kira.

AZEEZ

Kwance yake saman gadon ya yi ɗai-ɗai, kallo ɗaya za ka yi mishi ka san yana jin dadin baccin, sanyi AC hade da kamshin air freshener na daya daga cikin abin da ya karawa baccin na shi dadi.

A cikin baccin ya ji vibration din wayar Shi, hannu ya cusa kasan filon tare da janyo ta, ganin sunan Aunty sai ya bude idon sosai, cikin muryar bacci ya ce “Hello!”

“Duk inda kake, ka zo gidanka yanzun nan ina jiranka” daga haka ta yanke kiran.

Ido ya zuba ma wayar karfe takwas da minti biyar. “gidana kuma?”

Ya maimaita abin da ta fada hade da mikewa zaune da sauri.

Tunanin da ya yi ne ya sanya shi sauri durowa daga kan gadon, duk da irin ciwon da jikinshi ke yi.

Sport wear ya sanya farare na kungiyar, a gaggauce yake yin komai, shi ya sa bai dauki lokaci ba ya fice daga hotel din

MARYAM

Mu biyu ne a falon, kasancewar Maman comfort ta koma gida, wai za ta je prayer

“Kun je asibiti ne? “

Aunty tambaye ni idanunta a kaina

Kai na girgiza alamun a’a. Hannuna ta kama sannu a hankali tare da fadin.

“Mu je dakin in duba ki.”

Ba karamin dadin furucinta na ji ba, saboda ni a duniyata yanzu babu abin da nake so irin a duba wurin nan, tsoro na kar in kamu da yoyon fitsari.

Ko yanzu idan zan yi fitsari sai na ci bakar azaba sannan.

Sannu a hankali na hau saman gadon na kwanta, ban ji komai ba na tsaya Aunty ta duba ni.

Ta dago kanta hade da jan dogon tsoki, abin da ya kara jefa ni cikin fargaba cike da tsoro na ce “Aunty sai an yi min dinki?”

Kai ta girgiza alamun a’a.

Wani sanyin dadi ya ziyarce ni, abu biyu nake tsoro dama, yoyon fitsari da dinki.

Ina gyara zaman towel din ne Ya Azeez ya shigo, gabana ya rika dukan tara-tara ba ma uku-uku ba.

Ni tsoron abin da zai faru tsakaninsu da Aunty da kuma yadda zai dauki abun kawai yake damuna.

Tun da ya shigo take aika mishi da wani kallo, shi kuma a ka san ran shi ganin Maryam zaune, ya rika jin koma menene zai biyo baya mai sauki ne.

“Sannu Azeez, na gode sosai Allah Ya saka maka da alkairi. Ka dai rantse sai ka ɓata min rai ko? To ya yi kyau. Yanzu Maryam za ka yi wa fyaɗe Abdul’azeez, to sannu da kokari, zan dauke ta, ba sai ka kara ganin ta ba ma. Kuma gidan nan kai ne za ka gyara shi wlh. “

Shi dai bai yi magana ba, tsaye kawai ya yi yana jin ta.

Da kanta ta lalubo min kayan da na sanya, har muka fice daga dakin bai fito ba.

<< Da Magana 39Da Magana 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×