Motarmu na shigowa farfajiyar gidan Hammah na kokarin sakkowa daga entrance din Shi.
Ganinmu ne ya sanya shi tsayawa idanunshi a kanmu, har muka fita, Aunty sabe da Abdallah, ni kuma ina dangyasa kafata a hankali.
Daga inda yake tsaye ya ce “Me ya faru?”
Murya cike da ɓacin rai Aunty ta ce “Azeez ne ya yi raping dinta”
Da wani irin hanzari na ga Hammah yana sakkowa daga kan entrance din, yayin da fuskar shi take hade, tun kafin ya karaso ya fara fadin “Ban gane raping ba Aisha. Kina cikin hankalinki kuwa, wace irin banzar magana ce wannan?”
“Ba wasa nake yi ba, saboda abin da ya faru jiya, shi ne ya je ya yi abin da ya ga dama, don kawai ya ɓata min rai”
“To yanzu menene dalilin dakko ta zuwa nan? Za ki kashe auran ne? Aisha! Wai ba za ki bar yaran nan su yi zaman aure ba ne? Idan Maryam wani ne ya aure ta ba Azeez ba fa, a tunaninki zai dauki duk wannan?”
“To ai ni Hammah hankalina sai ya fi kwanciya ma, zaman Azeez da Maryam a gida daya zuciyata ta kasa aminta da shi, har yanzu ba na yi mishi kallon mai hankali”
Tsoki Hammah ya ja kafin ya ce “Wa ma ya san ina kika dosa ne Aisha? Sau nawa kina yin min korafi a kan Azeez ba shi da lafiya? Ko jiya sai da kika matsa mishi ya sha magani, yanzu kuma ya yi abin da kike so, kin zo kina korafi” cike da ɓacin rai ya yi maganar
Ita ma rai ɓacen ta ce “Amma ka san wlh don ya ɓata min ya yi hakan, har da mugunta a wannan lamarin.”
“Ni hakan da ya yi min daidai, zuwa yanzu ai kin san kalau yake ko?”
“Hammah, wannan fa ba karamin abu ba ne, ya kake daukarshi da wasa. Wannan fa tamkar fyade ne.”
Fuska Hammah ya daure tamau alamun ba wasa kafin ya ce “Aisha kar in kara jin kalmar fyade a bakinki, Maryam matar Azeez ce kuma ba fyade ya yi mata ba. And for the last time da za ki shiga harkar yaran nan, ki bar su su yi zaman auransu. Ita ma Maryam din mahaukaciya ce da tana cutuwa za ta zauna, kar ki kara zuwa gidan yaran nan kin ji na fada miki. “
Ya juyo kaina hade da nuna ni da yatsa” koma can wurin Hammawa ki samu wurin zama kafin mijinki ya zo”
Ya kai karshe maganar lokacin da yake kanga waya a kunnenshi.
Ba jimawa na ji muryar Ya Azeez ta bayyana yana fadin “Hello!”
“Ka na ina Azeez?”
“ina gida.”
“Maza zo ka dauki matarka”
“Thank you Hammah” ya amsa shi cikin yanayin da na kasa fahimta.
Ya juya kan Aunty yana fadin “Wlh Aisha kin faye rigima, a’ah! Ni na ga ikon Allah, mutum da matarshi, waye ma ya kai ki gidan ne?”
Komai ba ta ce ba ta nufi hanyar part din ta fuska babu annuri
Shi kuma ya juyo zuwa bangaren da nake yana fadin “Kin ga waccan uwar ta ki, ta faye rigima, kar ki sake ki biye mata kin ji na fada miki. Ki je ki nutsu a gidan mijinki ki yi ta hak’uri, aure hakuri ne a cikin shi.”
Horn din Ya Azeez ne ya sanya mu juyawa, muna kallon shi har ya samu wurin parking.
Yana fitowa ni kuma na nufi motar, na bar su nan tsaye da Hammah, ban san me yake fada mishi ba amma na ga ya nutsu sosai kamar yana a sahun sallah.
Ina zaune cikin motar ya shigo bai kalle ni ba har muka fice daga gidan, haka muka rika tafiya shiru har zuwa lokacin da ya yi parking a farfajiyar gidanmu.
“Za ki iya tafiya?” ya tambaye ni a lokacin da ya gama tsayawa
Kai na daga alamar eh, lokaci daya kuma Ina kokarin fita.
Tsaye ya yi, yana kallon yadda nake lallaba tafiya har na shige ciki.
Ina zaune a bedroom dina ya shigo, gefena ya zauna a sanyaye ya ce” I’m very sorry please, I don’t mean to hurt you”
Na dauke hawayen da suka gangaro min ba tare da na ce komai ba
“I’m sorry please” ya kara fada hade da rike kunnuwanshi du biyun
“Ba komai” na fada da muryar kuka
“Thank you” kafin in ce wani abu ya dora da “Me Aunty ta ce, ta ce kin ji ciwo sosai?”
Na girgiza kai alamar a’a
“Thank God!” ya fada hade da sauke ajiyar zuciya
“Wane magani ta ce a siya?”
“Ba ta fada min ba.” na amsa a hankali.
“OK” ya fada lokacin da yake dakko wayarshi a cikin aljihu
Yatsa ya dora a kan labbanshi biyu alamun in yi shiru a lokacin da yake kan ga waya a kunnenshi.
Ba jimawa na ji muryar Aunty na fadin “Hello!”
Na waro ido cike da mamaki, lokaci daya kuma Ina ba za kunnuwana don ji me zai ce mata
“Aunty ba ki rubuto mana sunayen magungunan ba”
Yadda ya yi maganar ne, ya sanya ni rike haɓata cike da mamakinshi
Daga can Auntyn ta ce “Ƙaniyanka ne.”
Sautin dariyarshi ya fita kadan, dalilin da ya sa ni ma na ɗan murmusa kadan
Ita kuma ta ce “Azeez ka raina ni ko, ka mayar da ni kakarka”
Bai yi magana ba illa dariyar da yake yi, daga can bangaren ta ce “Zan rubuto ma”
“Thank you” ya fada hade da yanke kiran yana kallo na
Na murmusa kadan hade kawar da kaina gefe
“Kin ci abinci?”
Kai na girgiza alamun a’a
“Ni ma ban ci ba, bari in fita in samo bread”
Komai ban ce ba har ya fice, wannan ya sa na lallaba na yi wankan tsarki hade da alwala.
Sallahr isha’in jiya da asubar yau na rama, ina zaune kan sallaya bayan na idar da azkhar din safe na ji shigowar shi.
Bayan kamar minti goma ya shigo dauke da tire da ya hado mana abun kari
Bread din ne da kwai ya soya
“Ban iya abinci ba fa”
Ya yi maganar lokacin da yake aje tiren a gabana
“Na sani ai” na yi maganar hade da murmushi
“Ƙwan ma kamar na cika gishiri”
Wani murmushin na sake yi kafin na gutsiri Ƙwan kadan, Sai ko na ji gishirin nan ya fita zau.
Dariyata na kunshe tare da fadin “Idan ka sa Maggi star ba ma sai ka sanya gishiri ba ai, shi din ya, wadatar”
“Ina na san wannan”
Ya amsa lokacin da yake ba za mana carpet a gaban gadon
Dukkanmu kasa cin Ƙwan muka yi, gara ma ni, na ɗan ci kaɗan
“Ki daina fadawa Aunty komai, kin san halinta fa, musamman a kanki, ni kuma ba na son fadan ta”
Tea din da ke bakina na hadiye kafin na ce “Allah ban fada mata komai, duk abin da yake faruwa co-incidence ne.”
“Har yau ma?” ya yi maganar idanunsa ƙur a kaina
Kai daga alamar eh, sannan na dora da “Allah ganin ta kawai na yi, ko bacci ma ban tashi ba”
“Subhanah! Aunty kam mutum ya shiga hannunta ya shiga uku”
Ya yi maganar lokacin da yake mikewa tsaye “Bari in siyo miki maganin, tun kafin ta sake dawowa kuma”
Ni dai murmushi kawai na yi, shi ya kwashe kayan break din zuwa kitchen, daga can ya wuce.
Ni kuma na haye gado sai bacci
Cikin bacci na rika jin ɓurintunshi, tun ina ji sama-sama har bacci ya kuma dauke ni
Ban farka ba sai karfe daya na rana, jikina dai ga shi nan, ni ban warke ba, kuma ban ji wani sauki sosai ba.
Falo na fito hade da yaye labulen windows ta yadda zan hango farfajiyar gidan
Mamaki ya kama ni, ganin yadda Ya Azeez ya yi wanki, tun da nake ni ban taɓa ganin ya yi wanki ba, ko inner wears na Shi ban taɓa gani a shanye ba.
Na yi mamakin yadda ya wanke wannan jibgegen zanen gadon, duk da akwai washing machine.
Dakinshi na koma, nan din ma a gyare tsab sai kamshi yake
Na fito zuwa dakina, alwala na fara yi hade da brush, na yi sallahr azhur
Bayan na idar na dauki wayata, miscalled din Aunty da na Maman comfort ne da kuma Hammah, duk sai na kira su, Hammah dai tambayata ya yi ko akwai matsala na ce ba komai, Aunty ma dai abin da ta tambaye ni kenan, Sai ta kara da “idan ina jin zafi wajen yin fitsari, idan na ji fitsarin in fara tsarki da ruwan dumi kafin in yi fitsarin”
Sosai ko na ji dadin wannan shawarar, saboda tashin hankalina shi ne in ji fitsari, da kuka nake gama shi.
Maman Comfort kam bayan ta yi min sannu da jiki, Sai kuma ta shiga tsokanata, dole na kashe wayar ina dariya
Yanzu kam yunwa nake ji sosai, shi ya sa na fito don nemawa kaina abinci, saboda na san tun da Ya Azeez ya fita gidan nan ya dawo da wuri shi ne 8:30pm
Kitchen din na fara gyarawa, saboda yadda ya yi girkin haka ya bar shi, bawon kwai kawai ya saka a dustbin, amma komai yana a wurin da ya yi aikin.
Ina tsaka da gyaran ne na ji shigowarshi.
Ya shigo kitchen din hannunshi rike da ledar take away guda biyu
“Ka siyo abinci, maimakon ka bari a yi?”na fada idanuna a kanshi
” Na san ba za ki iya yi ba, ni kuma ban iya ba”
Murmushi na yi kafin na ci gaba da abin da nake yi, shi, kuma yana tsaye a kitchen watching my all steps
“Ban so kana dorawa kanka hidima, ko wurin Aunty ka je za ta ba ka abinci ai”
Na katse shirun da ya ratsa tsakaninmu.
“Me ya sa?”
“Na san ba ka da kudi” na amsa shi
Ya ɗan taɓe baki tare fadin “Hammah fa ya rabar tas abin da ya ce zai rabar din nan.”
“Haka Aunty ta fada min” Ni ma na amsa shi
Tsayuwarshi ya gyara hade da cewa “Ya siyar da gonar nan har ma ya fara ginin plaza”
“Ma Sha Allah,” na amsa
Shi kuma ya ce “Na san mutane da yawa fa, da kudinsu ba ta hanyar da ya dace suka tara su ba, wasu kuma sun fara tarawa ta halastacciyar hanya, daga baya suka cakuda da haramun.”
Ina goge hannuna da tsumma na ce “ai mutane, burinsu kawai su yi kudi”
“I see. Kuma idan suna da, kudin burinsu kawai yay ta ƙaruwa, wannan ke sanya ai ta fadawa ga halaka”
Na jinjina kai alamun gamsuwa da maganarshi, daidai lokacin da muke fita daga kitchen din na ce “Shi ya sa wasu ga taron dukiyar amma babu kwanciyar hankali, kullum cikin nema da fafutuka suke, kar dai ta kare, ta haka sai ka ga har an sabawa Allahn kamar yadda ka ce. Wasu bacci wannan gagararsu yake yi”
“Har ma kin tuna min da wani labari” ya yi maganar daidai muna zama a kan dinning
Kunnuwana na sauraronshi, lokaci daya kuma Ina fitar da take away din a cikin leda.
“Wani mai kudi sosai, kullum da dare baya bacci saboda lissafi da neman yadda wasu hanyoyin samu zasu kara samuwa”
Na jinjina kai alamun ina ji, lokaci daya kuma na tura mishi abincinshi a gaban shi
Ya ɗora da “Duk lokacin da ya kasa bacci sai ya fito kofa ya tsaya, abun mamaki sai ya hango maigadinshi kwance a saman benci yana ta bacci”
Kai daga gyada hade da murmushi
“Wannan abu ba karamin mamaki yake ba wannan mai kudi ba, shi da ya aje makudan kudede ya kasa bacci , Sai maigadi da yake aiki a karkashinshi. Haka kullum yake tunanin me ya sa ba ya bacci amma maigadinshi yake bacci”
“Ya kamata ya sani kam” na fada a hankali ina cin abincina
“Shi ne fa ranar Alhaji ya dawowa daga hidimominshi, maigadi ya bude mishi kofa. Sai Alhaji ya ciro kudin miliyan daya ya ba maigadi ya ce zakka ce. Maigadi yay ta godiya, Alhaji kuma ya haye sama. Can dare kamar ko wane lokaci Alhaji ya fito, Sai ya ga maigadi yana ta zagaye, ya shiga daki ya fita, ya zauna ya tashi ya kasa bacci “
Ban san lokacin dana, kyalkyale da dariya ba, shi kuma yana ta cin abincin shi, shi haka yake dama, ya yi abun dariya sai ya bar ka da dariyar.
Cikin dariya na ce” Wato Maigadi ya samu kudi ya kasa bacci, ashe kudin ma na hana bacci. “
” Sosai na. “ya amsa min
A zuciyata na ce” Na yarda kam, Hammah na dare ai shi ne safiyarshi a lokacin da yake na shi neman kudin “
“Za ki iya zuwa dinnern nan ranar Asabar? “Ya, katse min tunanina
Shiru na yi kafin in ce” In Sha Allah “
“OK be ready “
Kai na jinjina, shi kuma ya mike zuwa dakinshi yana fadin” I want to sleep. “
Haka nan sai nake ji na cikin Nishadi, Ya Azeez yana da sauki kai kamar Hammah, amma idan ka kalli fuskarkarsu sai ka ce ba zasu tankwasu ba.
Haka Hammah da Aunty, duk irin rikicinta zai wahala ka ji yana fada sai abu ya kai karshe, kafin zai yi fada.
Ga Ya Azeez ma jini baya karya, zam Hammah a wasu halayen.
Ina samun sauki ana ci gaba da shirin dinner, sosai Ya Azeez ke shirin dinnern nan komai latest yake saye.
Ranar Juma’a kam ban wuni gida ba, Dougirie na tafi Aunty ta kira mai lalle dama Maman Comfort ta gyara min Kai.
Zuwa yamma sai na fito fes, gaskiya kwalliya ita ce mace.
A gidan ne Ya Nasir ya kawo gown wajen kala goma azaɓa.
Ni dukkansu sun yi min kyau, Aunty ce dai mai kushewa, ta ce wannan kirji a bude, wannan ta sauka ya yi yawa, wannan ta matse, wannan hannaye duk a waje.
Dakyar dai ta zabi wata, ni kaina ta yi min kyau, babu fitar da tsiraici sosai
Sai 9pm muka koma gida, koma ya mayar da ni, saboda shi kam kara fita ya yi, sai can dare na ji dawowarshi.
Misalin karfe uku da rabi bayan na yi sallahr la’asar mai make up da Maman Comfort suka shigo, kamar yadda ya sha nanata min kar a yi min kwalliyar nan kamar ta bakin aljanun kauye haka na fadawa mai kwalliyar. Shi ya ya ta yi min light make up.
Zuwa 4:30pm daga ni har Maman Comfort din mun gama shiryawa, na yi kyau kam, Amarya a rana ta musamman a wurinta ba sai an fadi kyawunta ba. Musamman ni da ban san ko dubu dari nawa ya kashe a hidimar ba. Shi ya ka san zuciyata cike da tambayoyin ina yake samun kudi ne.
Muna isa gate din even center din sai na ji gabana ya tsananta faduwa, ba jimawa abokan ango suka fito tararmu cikin shigar nevy blue suit.
Ya Azeez kam white suit ya sanya
Lokacin da suka yi arba da fuskata hannuna a cikin na Maman Comfort ba karamin mamaki ne ya bayyana a a fuskarkarsu ba, suka hau ihu, irin na abun mamaki ya faru.
Haka muka shiga hall din suna ta hayaniya hade da tsokanar Ya Azeez, a maimakon shiga a jeren da suka shirya za su yi.
Duk rashin son dariyarshi bakinshi kam ya ki rufuwa saboda tsokanar abokan na shi. Ni kaina dai da Maman Comfort ta ya shi dariyar muke yi.
Da kyar wuri ya lafa, aka fara gudanar da shirye-shirye, wanda ya sanya ni cikin nishadi ba ni kadai ba, ku san duk mutanen da ke wurin ma
Duk da babu mata sosai, hakan bai hana dinnern ta kayatar ba.
Abokan ango suka shiga mika min gifts, kyautar da ta fi ban mamaki ita ce ta click dinsu Ya Azeez, key din mota kirar Mercedes Benz S-class Suka ba ni, take hall ya dau ihu, ni kaina ina jin kamar dai ba gaskiya ba. Wai yau ni ma ina da mota.
Ana kiran sallahr magriba taro ya tashi, kowa fuskarshi cike da annashuwa.
Ban samu kaina ba sai 9pm lokacin na samu sukunin lekawa online, babu abin da ake magana sai dinnernmu, hotunana da na Ya Azeez ne ke ta yawo ko ina a social media.
Wasu su fadi alkairi wasu sharri, wasu su yaba wasu su kushe.
Comment din da ya fi yawa dai shi ne masu tambayar amma ni da shi ƴan’uwa ne ko? Wasu kuma kai tsaye suke yanke hukunci su ce ni da shi ƴan’uwa ne. Wasu kuma bayan sun ce mu ƴan’uwa ne saboda kamarmu, har sai sun lissafo inda muka yi kamar.
Abu na biyu da ya fi kar daukar hankali shi ne har aka gama dinnern babu inda Ya Azeez ya rike min ko yatsa.
Wannan abu ba karamin girgiza tebur ya yi ba, aka shiga mocking din masu bayar da kansu a waje, da masu rungume-rungumen matansu suna dorawa a social media. Satin nan dai kaf a kan batun auranmu ya kare, har malamai sai da suka yi sharhi a kan abun. Sai a lokacin na ji dadi dana sanya rigar da ta suturta min jikina.
A satin ne kuma aka saki result din su Ya Azeez. Yana daya daga cikin wadanda result dinsu ya yi kyau. Shi ya sa aka neme su Abuja.
Tun kafin ya tafi dama Aunty ke fadin kar ya sake ya karbi upper zuwa wata kasa, ita dai ba za ta yarda ba, wai ya je ya karasa lalacewa ya yi ta dukana ba uwa ba uba.
Haka na ci gaba da zama ni kadai, ga yawan ciwon kan da yake damuna, ban dai rasa komai ba, Aunty da Hammah duk suna kokari, matsalata wannan ciwon kan da ba ya sauka, Ya, Azeez kam yau ne gobe ne sai da ya yi wata daya a Abuja, seminar aka yi musu, sannan ya dawo da upper aiki a hukumar tsara birane ta jihar Adamawa Asupda
Ni dai na fi kowa farin ciki da wannan upper, ko ba komai zai samu hanyar shigowar kudi sabanin baya da Sai ƴan buge-buge, kuma shi ba ya son a ga ya gaza, har tausayi yake ba ni, idan ya ga ya kamata ace ya kawo abu, bai kawo ba, to hankalinshi baya kwanciya sai ya kawo.
Tun da ya iso yake tambayata dalilin ramata, na yi haske kam, amma sosai na zube.
Yanzu ma da yake tsaye a gabana yana kallon yadda nake naɗa veil din doguwar rigar da na sanya, tambayar da ya kara yi min kenan “Wai me ya same ki ne? Wannan ramar ta yi yawa?”
Na sauke hannayena cike da gajiyar naɗa veil din kafin na ce “Ciwon kan ne dai kawai.”
“Ya kamata mu biya asibiti kafin mu karasa wajen Auntyn.”
“To. Na amsa lokaci daya kuma Ina daukar hand bag dita, Sai da na shiga wurin Maman Comfort na fada mata zan raka Ya Azeez gida ya gaishe da Aunty, kafin nan muka wuce.
Peace hospital muka fara biyawa, ni da shi ban san wanda ya fi mamakin sakamakon da aka bamu ba, wai ina da ciki
Duk mu ka yi ta kallon juna cike da mamaki, bayan mun fito daga asibitin ne na ce ni kam ba zan je Dougirie ba, saboda ina zuwa Aunty za ta gane ina da ciki.
Shi ma sai ya goya min baya ya tare min keke na dawo gida.