Wani irin kallo yake wa Nasir mai cike da bacin rai, yayin da zuciyarsa ke wani irin zafi, kokarin controling din kansa yake yi, kar ya aikatawa Nasir ba daidai ba. Yau ce rana ta farko da aka yi wa dan’uwanshi abu ya yi mishi zafi, musamman yadda Nasir ya kwatanta Maryam.
Cikin sauri Nasir ya yi kneeling a tsakiyar gadon, lokaci daya kuma ya damke hannayen Azeez du biyun tare da fadin “Don Allah ka yi hakuri idan ranka ya baci, don Allah, wlh kawai na kwatanta ne.”
Ya fitar da wata iska mai zafi, ba tare da ya ce komai ba, hakan ya sa su Mubarak ma sanya bakin su a ba shi hak’urin, har zuwa lokacin da suke ganin ya dan yi cooling down.
Sun san halin Azeez, zasu iya cewa a kaf cikinsu ya fi su hak’uri hade da iya danne abu, saboda ko sa’in’sa ba a faye yi da shi ba, idan abu bai yi mishi ba, shiru kawai yake yi, wannan yake basu tabbacinn baya so, Sai duk su shiga hankalinsu, idan kuma aka kai shi karshe ana ganin danyen aiki.
Akwai wani lokaci da suka je wetland fada ya hada su da wani click din matasa, a ranar suka san Azeez bai tara ƙwanjin banza ba, a kuma ranar ne suka kara tabbatar da karin maganar nan ta Hausawa da suke cewa mai hak’uri bai iya fushi ba, saboda duk wanda Allah Ya ba Azeez damar kai mai naushi, to sai ya zubar da jini, daga shi sai Anwar ne suka ceci group din nasu, don ta Nasir da Mubarak kaca-kaca za a yi musu.
Duk wanda zai kai Azeez maƙura, to baya kwashewa lafiya, shi ya sa suke tsoron bacin ran shi.
Nasir da Mubarak ne suka fice, Anwar ne kawai ya rage a dakin yana kara rarrashin Azeez kamar karamin yaro, har Sai da Azeez din ya ce “Ka je kawai sai da safe” da wata irin dakusassar murya ya yi maganar alamun dai ranshi a bace yake.
Aunty & Maryam
Tun lokacin da na dawo makaranta na fahimci kamar ran Aunty ba dadi, saboda ta cika shiru, hade da yin alamun nisa cikin tunani.
Shi ya da na idar da sallahr isha’i na haura zuwa saman.
Zaune take kan sallaya tana lazumi, shigowata ce ta sanya ta saurin waigowa.
Gefen gado na zauna, wanda ya ba ni damar fuskantarta
“Me ya faru?” ta tambaye ni cike da kulawa.
Sai da na marairaice sannan na ce “Aunty Ya Azeez ya yi wani abu ko?”
“Me ya sa kika tambaya?” ta tambaye ni alamun mamaki shimfide a kan fuskarta.
Na dan murmusa kadan sannan na ce “Na ga alamar hakan ne a yanayinki”
“Dole Azeez ya ce kina sanya mishi ido, ko me yake kina kallonshi, ni ma ga shi kin sanya min idon” ta yi maganar hade da dariya mai sauti.
Ni ma dariyar na yi ba tare da na ce komai ba.
“Ban san ya zan yi da Azeez ba a duniyar nan tamu, wlh har ba na so ya shigo gidan nan. Shigowar shi dazu sai da ya daukar wa Mamansu Huzaima waya.”
Na fitar da ido alamun tsoro ina fadin “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Aunty ki gwada kiran shi mana ko bai siyar ba. Na ji su Aunty Luba ranar can suna cewa53000, 00 ta saye ta.”
Auntyn ma zaro ido ta yi alamun tsaro ta ce “Allah!”
“Wallahi!” Na amsata jiki a mace.
“To wallahi na kira Azeez Maryam ya ki dagawa, ya ma kashe wayar gabadaya, ki gwada kiranshi ke, tun da wani lokaci kuna ɗan ɗasawa.”
Jiki ba kwari na mike hade da fadin “Bari in gwada to, ko zai dauka.”
Azeez
Bayan fitar Anwar, toilet ya shiga hade da dauro alwala, jallabiyar sallahrshi ya zira, ya shiga jero sallolin da bai yi ba.
Bayan ya idar tebur din kayan tea din shi ya nufa, coffee ya shiga hadawa kanshi, har zuwa lokacin zuciyarshi wani daci da zafi take yi mishi, na maganar Nasir.
Lokaci zuwa lokaci ya kan ja dogon tsoki, a kokarin shi na rage ɓacin ran da yake ji.
Yana cikin juya coffeen ne wayarshi ta shiga vibration alamun kira, mug din ya dauka ya nufi inda wayar take lokaci daya kuma yana juya coffeen da spoon a hankali.
Maryam Aunty shi ne sunan da ya gani a kan screen din wayar yana yawo.
Har kiran ya yanke bai daga ba, yana niyyar komawa inda yake dazu wani kiran ya kara shigowa.
Karamin tsoki ya ja, lokaci daya kuma ya zauna gefen gadon, hade da daga kiran
“Menene? ” shi ne abin da ya fara tambaya.
Jin sautin muryarshi cike da kauri ya sa gabana faduwa, lokaci daya kuma na mike zaune daga kwanciyar da na yi. A ladabce na ce “Ya Azeez barka da dare.”
“Yauwa” ya amsa lokaci daya kuma yana sipping din coffee din Hannun shi.
“Ya Azeez dama Aunty ce ta ce ta kira ba ka daga ba.”
Jin shiru bai ce komai ba ya sa na marairaice kamar zan yi kuka na ce “Ya Azeez don Allah idan ba ka siyar da wayar Aunty Adama ba ka kawo ma Aunty ta ba ta. Wlh Aunty ta shiga damuwa ko abinci ta kasa ci.”
Cikin kakkausar murya ya ce “Ke! Ni sa’anki ne? Wlh zan ci kaniyarki, don Allah ki kara kirana.” daga haka ya yanke kiran, ci gaba ya yi da sipping din coffee din shi a hankali lokaci daya kuma yana taba wayar shi.
Duk jarabar Aunty Adama haka ta hakura da maganar wayar ta, saboda Hammah kai tsaye ya ce shi ba zai biya ba, ita ma Azeez din a danta ne. Sai dai daga lokacin ba ta kara sakacin barin kofarta a bude ba, abin da ba ta sani ba shi ne, Azeez din ma bai kara zuwa gidan ba.
5:00pm
Maryam
Zaune nake a kitchen yayin da wayata ke gefe ina jin waka, na kai hannu hade da rage volume din jin kamar ana knocking kofa.
A nutse na nufi kofar hade da budewa, Ya Azeez ne tsaye, kamar ko wane lokaci sanye cikin kananun kaya, riga ash color da wandon jeans blue latest, rigar mai guntun hannu wacce ta fito da lafiyayyen jikinsa mai dauke da alamun jin dadi.
Kafarsa farin kambas ne, wanda na tabbatar bada karamin kudi ya saye shi ba, haka ma hannunsa daure da wani latest agogo ash color, Idan dai Iya dressing ne Ya Azeez Allah Ya yi mishi wannan baiwar.
Earpiece din kunnensa guda ya zare lokacin da yake shiga cikin falon sosai, kai tsaye dakinsa ya nufa, dadi ya kume ni, saboda ban jima da gama gyare mishi dakin ba.
Kullum sai na gyare mishi dakinshi fes, saboda shi kamar kurma ne, baya sallama sai dai a ganshi. Shi ya sa daidai da rana daya ban taba tsallakewa ban gyara ba, tun da na lura duk ranar da ban gyara dakin ba, ranar yake zuwa.
Ganin ya shige dakinshi, ni ma komawa kitchen na yi, na ci gaba da aikina.
Na fito da niyyar zubar da datti ne, na ganshi yana sakkawo daga stairs hannunshi rungume da laptop.
Wannan ya tuna min kofar Aunty a bude take, laptop din da ke hannunshi a dakin Auntyn ya dakkota, kuma ba tata ba ce, wata kawarta a wurin aiki ne za ta saya, shi ne aka ba Auntyn ta kai mata.
Tsaye na yi da dustbin a hannuna, lokaci daya kuma ina tuna me ya kamata in yi, ko na kira Aunty kafin ta zo ya bar gidan, idan kuwa har ya bar gidan laptop din ta zama ba tamu ba.
A tsakiyar falon na aje dustbin din hade da bin bayan shi da sauri saboda har ya fita daga falon.
“Ya Azeez!” na kwala mishi kira lokacin da nake sauka daga kan entrance.
Bai amsa ba, amma ya tsaya hade da juyawa yana kallon yadda nake gudu zuwa wajensa
Daga dan nesa da shi na tsaya cike da tsoro na ce “Ya Azeez, laptop din ba ta Aunty ba ce wlh, ta wata abokiyar aikin su ce, gobe za ta kai mata.” Na dago kai hade da satar kallon shi, kasancewar tun da na fara maganar kaina a kasa yake.
Jin bai ce komai ba na ce “Don Allah ka yi hakuri ka ba ta, Idan ma kudi kake so, idan ta dawo zan sanya baki a ba ka.”
Kai karshen maganar tawa ya yi daidai da takowarshi wajena lokaci daya kuma yana mika min laptop din.
Hannu biyu na sanya da zummar amsa, Sai dai maimakon in ji laptop a hannuna, sai na ji saukar wani abu a gefen fuskata gumm! kamar katako ko an maka min faskare.
Wani dummmm! Na ji daga nan kuma na ji duk kunnuwana sun toshe, idanuna basu ganin komai sai duhu. Na ji kamar ana yawo da ni a sama daga nan kuma sai na ji ma ban jin komai, duniyar ta yi shiru.
Azeez
Bayan ya dauke ta da marin, da hanzari kuma ya tallafeta zuwa jikinsa ganin yadda ta tafi za ta fadi. Kasa Ya kwantarda ita da zummar ya tafi ya bar ta a wurin, Sai dai kuma ya kasa yin hakan, musamman yadda ya ga jini na fitowa daga bakinta. mintuna biyu ya bata yana kallon ta, kafin daga bisani ya wuce inda motarshi take.
Wannan ya ba Hammawa damar karasowa inda take kwance a tsorace, da gudu ya nufi Azeez wanda yake kokarin fita, da wata irin firgita a muryarshi yake fadin “yallaboi kodai za a kai ta asibiti ne, ba ta numfashi fa walahi”
Shiru Azeez ya yi kafin daga bisani ya fito zuwa inda take kwance, dukawa ya yi kanta a kokarinshi na tantance maganar Hammawa.
Da wani irin hanzari ya cuccubota zuwa jikinsa, aguje kamar bai dau komai ba ya nufi inda motarshi take, da hannu daya ya yi amfani ya bude motar hade da kwantar da ita a kan kujera.
Zuwa lokacin tuni Hammawa ya bude mishi gate ya fice da wani irin gudu, daidai lokacin da Aunty ke kokarin sawo kai.
Kai tsaye peace hospital ya wuce da ita, saboda shi ne ma fi kusa da shi.
Tun da ya shiga asibitin bai zauna ba, Sai da ya tabbatar Maryam ta samu kulawa, duk kiran da Aunty take mishi kuma bai daga ba.
Aunty
Bayan ta yi parking motarta a parking space, wurin Hammawa ta nufa, wanda yake tsaye jiki a mace, alamun dai yana cikin yanayi mara dadi.
“Hala Azeez ya yi wani abu ne, shi ya sa ya fita aguje haka?” cewar Aunty tana kallon Hammawa.
Cike da jimami Hammawa ya ce “Ah-ah! Shi da wannan yarinyar ne Maryam.”
Cike da tsoro Aunty ta ce “Me ya yi mata?”
Har zuwa lokacin jikin Hammawa a mace yake, wannan ya kara firgita Aunty ta san lallai koma menene Azeez ya yi wa Maryam to babba ne.
“Me ya yi mata Hammawa?”Cike da tsoro ta yi maganar.
Hammawa ya shiga tafa hannayenshi alamun jimami sannan ya ce” To! Walahi Hajiya ni ban sani ba, kawai dai na ga ta biyo bayan shi, daga nan kuma sai naga ya mare ta, to yanzu dai sun tafi asibiti, amma abun kam babu dadi.”
Aunty da ta kwakkwalo ido hannayenta a saman kai ta ce “Na shiga uku! Ka ce kawai ya kashe ta. Hannun Azeez da yake kamar rodi shi ne ya mare ta da shi. Na shiga uku ni Aisha. “Ta kai karshen maganar tata hade da juyawa wurin motar ta a kidime.
Da wani irin gudu ta fita, Sai da ta fita titin unguwarsu ne ta fara tunanin ina kuma za ta je, dalilin da ya sa ta rika kiran Azeez ba ƙaƙƙautawa amma bai daga ba.
FMC ta fara zuwa ta bincika, kafin ta wuce specialist asibitin da take aiki, nan ma babu Azeez, ga shi ya kashe wayar ma gabadaya, hakan kuma ba karamin kara firgitata ya yi ba.
Ga lambar Hammah ba ta tafiya, wannan ya tabbatar mata da har zuwa lokacin yana kauyen da ya ce za su je.
Jiki a mace ta juyo da kan motarta zuwa gida, zuwa lokacin kuma karfe takwas na dare.