Skip to content
Part 6 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Azeez & Maryam

HOSPITAL

Zaune nake a gefen gadon da aka ba ni a matsayin na kwanta in huta, yanzu kuma zaman jiran Ya Azeez nake wanda ya bi bayan likita.

Zaman da ya ba ni damar karewa dakin kallo, lokaci daya kuma Ina taba gefen bakina inda aka yi min dinki. Sosai wurin ke yi min zafi.

Ya turo kofar hannunshi rike da farar leda mai tambarin asibitin. 

“Zo mu je” ya yi maganar daga bakin kofar, lokaci daya kuma yana jeho min irin hular nan da marasa lafiya ke sanya idan za a yi musu aiki. 

Na tattare dogon bakin gashina hade da tura shi cikin hular, sannan na bi bayan shi.

Yana gabana sosai, amma hakan bai hanani ganin wurin da yake saka kafa hade da daukewa ba.

Lokacin dana iso wurin motar har ya shige, amma ya bar min kofa a bude.

Wani kamshi mai hade da sanyin AC ya ratsa kofofin hancina, hakan ya sanya ni lumshe idanuna a lokacin da nake zama.

“Sorry!” ya fada muryar shi da alamar tausayawa, Ya dauka zafin ciwo ne ya sanya ni lumshe idon.

“Thank you,” na fada a hankali, yayin da shi kuma yake kashe wutar motar, a daidai lokacin wayar shi da ke tsakiyar mu ta shiga vibration, da sauri na dora idona a kan screen din, ‘Medina’ haka na gani a rubuce.

Shi kuma ya daga wayar hade da jingina bayan shi da kujera, ban iya tsintar komai ba a wayar, saboda magana yake cike da kasaita kamar wani yarima mai jiran gado, kuma daga *Uh! Uh-uh, to, ok, yes, thanks,* wani lokaci kuma ya kan yi murmushi, after like 2mnis ya yanke kiran hade da yi wa motar key.

Ajiyar zuciya na saki mai sauti, wacce ta sanya shi saurin juyowa yana kallo na.

“Is this hot?” ya tambaya cike da kulawa.

Kai na jinjina alamar eh, saboda da gaske zafin nake ji, amma ba a wurin ciwon ba, wannan karon a zuciyata nake jin zafin.

Da wani irin salo yake tukin, wannan ya sanyani kwantar da kaina jikin kujera hade da lumshe idanuna. 

Jin ya tsaya ne ya sanya ni saurin bude idona, ina bin wurin da ya tsaya din da kallo, daga inda ya tsaya din nake hango katon farin gate din gidan mu, wanda kwayayen lantarki suka kawata. 

“Za ki iya zuwa gida?” ban kai ga amsawa ba ya dora. 

“Idan ba za ki iya ba, I will take you in my hand, inda Hammawa yake Sai ya karasa da ke ciki.” kallon shi kawai nake ba tare da na dauke idona a kan shi ba. 

Ya dan yi shiru kafin ya ce “Ba na son shiga ciki ne, Aunty za ta fara fada, kin san dai halinta, musamman abu ya shafe ki, ba ta son abin da zai taba ki, tun dazu take ta kira, kawai na ki dagawa ne.” 

Still ban ce komai ba, Sai shi ne ya kara cewa “Don haka lallabawa za ki yi ki shiga gida” ya kai karshen maganar hade da miko min ledar magunguna. 

Na karba lokaci daya kuma in bude kofar motar

“Wait please!” 

Dawowa na yi na tare zaunawa kamar yadda nake da. 

“Please! Please and please ki daina shiga harkata, idan kin ga ina abuna just watch, I don’t want anything ya kuma faruwa. Always Ina kokarin janye ki daga gare ni kina kara shige min, har sai da kika yi forcing dina na aikata ba daidai ba.” ya kai karshen maganar ta shi da alamun bacin rai. 

Ganin ban ce komai ba ya kuma cewa” To na roke ki, stop, away from me, da wani jikinki duk ƙashi. “ya kai karshen maganar tasa fuskarsa kicin-kicin, har da hadawa da tsoki. 

Kofar na kara budewa hade da zira kafafuna zuwa waje. Shi kuma ya juya kan motarshi baya.

Na shiga kwankwasawa kofar har zuwa lokacin da Hammmawa ya bude min

“Fetel! “Ya kira sunan da ake kirana da shi a kauyenmu, duk da a nan ma wasu na kirana da shi.

“Ya jikin ki? Wayyo Allahna! Walahi Hajiya ta rude, ta shiga damuwa sosai fa. “

Ni dai ban yi magana ba, taka kafata nake a hankali, yayin da yake bin bayana kamar wani bindi.

Sau daya kacal na yi knocking kofar, kafin in yi na biyu, Aunty har ta bude kofar, wannan ya tabbatar min zaune take a falon.

Da wani irin tashin hankali ta tare, yayin da take ta watso min tambayoyi “Me ya yi miki? Ina ya kai ki? Me kika yi mishi? Yana ina? Tun dazu ina kuke?”

Murmushi na yi hade da rabata na wuce, yayin da take bi na a baya har zuwa lokacin ba ta fasa yi min tambayoyin ba.

Bisa gado na dora ledar maganin da ke hannuna lokacin da na shiga dakina

“Aunty! Ba gani ba, asibiti muka je, kuma bai yi min komai ba” Na amsa mata tambayoyinta ina fuskantar ta

“Kamar ya bai yi miki komai ba, bayan Hammawa ya ce min a sume ya bar gidan nan da ke.”

Ido na zaro alamun mamaki, kafin in ce “In ji Hammawan? Gaskiya ni da kafafuna na tafi asibiti”

Ta bi ni da wani irin kallo, wannan ya sa na kirkiro murmushi, wanda ya sa dole na dafe wurin da aka yi min dinki saboda zafi. 

“Me ya samu bakin ya kumbura to?”

Gefen gadon na zauna tare da cewa “Dinki aka yi min”

Wani irin zabura ta yi “Dinki. Wai Ina Azeez din, me ya yi miki?”

“faduwa na yi fa.” Na yi maganar kamar zan yi kuka.

“Ohh! Kina boye min, ai Hammawa ya fada min, marinki ya yi har kika suma, but still you’re backing him. Ya yi miki kyau” ta karasa maganar rai a matukar bace, lokaci daya kuma ta nufi kofar fita.

Da sauri na mike hade da riko hannunta, cikin muryar kuka na ce “Aunty! Don Allah ki yi hakuri, ba na son ki yi mishi fada ne.”

Wani irin kallo take bi na da shi, shi ya sa na kuma sassauta muryata na ce “Don Allah Aunty ki rika hak’uri da halin Ya Azeez, ke kanki kin san da ba haka yake ba, ki rika janyo shi jikinshi, ki rika rage yawan fadan nan da kike mishi, yana daya daga cikin abin da ya sa baya son zuwa gidan nan.”

“Oh ni Aisha! Maryam! Wato ma yanzu laifina kike gani, ba na Azeez ba. Ikon Allah! To ni ma bari in fada miki, daga yau idan Azeez ya zo gidan nan ya dauki abu, just call me, Kar ki kara yi mishi magana koda kuwa zai nade gidan nan ne. Yanzu ba ga shi an yi ba Wan-ba wan ba, wai karatun ɗankama.”

Hannunta na saki lokaci daya kuma Ina dauke hawayen da ni kaina ban san dalilin yin su ba, wani dai zafi nake ji a can kasan zuciyata.

Haka na dora jinya ko makaranta ban iya zuwa ba 2dz,abinci ma tea Kawai nake iya sha shi ma mara zafi sosai, sai fruit.

Ku san kullum sai Aunty ta yi mita, wai ga shi nan ina ta kare Ya Azeez ko duba ni ya kasa zuwa ya yi. Shiru kawai nake mata, duk da ni ma ina son ya zo din, amma ya ki zuwa, Sai dai in ganshi a Instagram yana posting din hotunan shi, hotunan da ke matukar yamutsa hazo. Saboda yadda yake daukar wanka, ga shi danye sharaf, kuma jike da kudi, wannan ke kara sanyawa ƴanmata na crushing dinshi. Wani lokaci haka zan ga hotunanshi na yawo a group din mata na Facebook wai suna son shi, ko yana burgesu, ko su ce a taimaka musu da lambar shi. Haka zan ta bin comments din mutane ina karantawa kowa da abin da yake fada a kan shi. Wani abun ya ban dariya, wani kuma ya ban haushi. Wani lokaci kuma in ce su Ya Azeez an zama Cele.

Yau Lahadi da misalin karfe goma na safe, zaune muke a entrance, Aunty na min kitso, da yake ta iya kitso sosai, ita ke min ba na fita ko ina.

Daidai lokacin Hammah ya fito sanye cikin shadda Gezna fara tas dinkin babbar riga, bakar dara da bakin takalmi ya sanya, wadanda suka kara fito da kyawun kwalliyar tashi.

A ladabce na gaishe shi, Ya amsa lokaci daya kuma yana fadin “Aisha kin ga yaronki ya kwashe mana batiran sola ko, kai! Allah ya shiryi Abdu’aziz.”

Baki bude alamun mamaki Aunty ta ce “Yaushe?”

“Allah kadai ya sani, jiya da dare ne hankalina ya kai wurin, ina dubawa kuwa sai na ga babu su”

“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un! Oh Allahna! Allah Ya shirya.”

“Amin Ya Rabbb” cewar Hammah lokacin da yake daga kiran da ya shigo wayar shi

Horn din da mu ka ji ne ya sanya mu waigawa, dukkanmu mun dauka Azeez ne.

Uncle Bandi ne kanen Aunty Adama, mutumin da na tsana ba dalili, kuma daidai gwargwado yana da halaye masu kyau, zan iya cewa ma ya fi Aunty Adama kyawawan halaye.

Ya iso wurin baki bude, yayin da ni kuma na hade fuska, ya shiga gaishe dasu Aunty cike da girmamawa.

“Aunty zan biya kudin kitson.”, Ya fada da alamun zolaya.

Dariya Aunty ta yi kafin ta ce “Akwai tsada fa.”

Shi ma cikin dariya ya ce “Ko nawa ne zan biya.”

“Zan fita Aisha, a yi min tuwon semo da miyar shuwaka please” Hammah ya katse su.

Kafin Aunty ta amsa Uncle Bandi ya ce “Hammah zan zo gaisuwa da, rokon iri wajenka.”

Cikin rashin muhimmantar da zancen Hammah ya ce “Sai ka zo Bandi, Idan yammatanka sun bari.”

“Ahhh! Hammah ya kake son jika min aiki kuma.”

Daga can Hammah ya yi dariya tare da fadin “Karya na yi?”

“Amma Hammah wannan kam ba ya wuce ba.”

Daga Hammahn har Aunty dariya suka yi.

Ni dai hankalina na kan wayata inda wata ta dora hoton Azeez a wani group na Facebook, tana neman wacce ta san shi ko take da lambarshi, har da kyautar kudi ta sanya ga wacce duk ta biya mata bukatarta.

A nan ne na ga wata ta yi comment kamar haka “Abdul’azeez A Yola kenan, ko Azeez, ko kuma Done AZ a Instagram, ɗan yola ne, amma ban san gidansu ba, tare muke karatu da shi a MAUTECH, ko a zahiri dan gayu ne, kuma iyayenshi na da kudi sosai, ya jiku da Naira, Amma na tabbata ba zai kula ki ba wlh, yana da girman kai sosai, saboda ban taba ganin yana magana da wani ba, jarabawa ce ma kawai ke kawo shi makarantar. Yana gamawa yake fita, gara ki samawa kanki lafiya. “

Wannan comment ya yamutsa hazo, saboda akwai comment sama da dari biyar a kasan shi.

Ni mamaki nake yi, yaushe Ya Azeez ya yi suna haka, da fara Instagram dinshin nan bai fi wata uku ba, amma hankalin mata duk ya koma kanshi.

Karanta comments ya dauke min hankali, shi ya sa ban san abin da Aunty da Uncle Bandi ke fada ba, Sai da ya aje kudi 5k kusa da ni yana fadin “Maryam ga kudin kitso nan ki biya Aunty.”

Na yi saurin dago kaina tare da fadin “Wayyyo! Uncle Bandi na gode, amma ba zan karba ba.”

“Ba a mayar da hannun kyauta baya ai” haka ya fada lokacin da yake tafiya bangaren Aunty Adama.

Na hade fuskata daga guntun murmushin da nake yi “Aunty me ya sa kika bari ya aje min?” na yi maganar hade da daga kaina ina kallon ta kamar zan yi kuka

Ta dakata da kitson tare da fadin “Ni na ce ya ba ki, yau na ga ikon Allah.”

Baki na tura lokaci daya kuma Ina juyawa, ita kuma ta ci gaba da kitson.

Instagram na shiga, in ga ko Ya Azeez ya yi sabon update, amma babu, hotunan da ya dora na baya na rika bi ina karanta comments nasu, ina cikin karatun ne na ga ya yi update din sabon hoto.

Sanye yake da coffee colour din wando iya gwiwa, sai farar Tshirt mai guntun hannun, kansa sanye da facing cap fara da farin cambass, sosai ya yi kyau.

Karon farko da na ji, ina son yin comment a hoton shi.

Emoji din hannun da yake nuna alamar kyau na ajiye.

Saukar comment din ke da wuya ya yi like, sannan ya yi reply da emoji na AMIN.

Abin da ban taba ganin ya yi ma kowa ba, tun masu following din shi suna korafi har sun gaji sun bari. 

Wani dadi ya kume ni, ni ma sai na yi like a reply din da ya yi min. 

Sannan na rufe data, saboda Aunty ta gama min kitson. 

<< Da Magana 5Da Magana 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.