Skip to content
Part 7 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Shuwakar da Hammah ya ce yana so ita na sa Hammawa ya debo min, da yake akwai bishiyar a cikin gidan.

Kujera yar tsugunno na dakko hade da zama wurin famfon gate ina wankewa.

Ban jima da fara wankewar ba Aunty Adama ta fito ita da Uncle Bandi.

Addu’a na rika yi Allah Ya kada ya yi min magana, cikin ikon Allah kuma bai yi min ba, har suka fice daga gidan.

Fitarsu babu jimawa motor Ya Azeez ta shigo.

Ya fito sanye cikin farin wando da blue din riga, farar facing cap da kambas fari mai ratsin blue.

Sosai ya yi kyau, cikin takun tafiyarshi ta mazantaka ya wuce ni tsugunne a wurin tap din komai bai ce min ba, ni ma kuma ban ce mishi din ba, Sai dai hakan bai hanani bin shi da kallo ba ganin yadda kai tsaye ya doshi kofar Aunty Adama, cikin sa a yana murza kofar sai ta bude.

Bai jima a ciki ba ya fito rungume da electric cooker din Aunty Adaman, babba ne sosai, don ya yi girman wani fridge.

Karon farko da ya dauki abu ya ban dariya, kuma ban san lokacin da dariyar ta kwace min ba.

Na yi saurin rufe bakina da tafin hannuna lokacin da ya wurgo min wata harara.

Kamar TV haka na tsaya ina kallon yadda yake ta kici-kicin tura electric din a cikin boot din motarshi.

Na juya na kalli Hammawa, wanda horn din da Ya Azeez ya yi, Ya sanya shi zabura tare da bude mishi kofa.

Muka zubawa juna ido ni da Hammawa bayan fitar Ya Azeez, kafin daga bisani na wuce ciki wajen Aunty.

A lokacin da zaune take gefen gado tana latsa wayar ta, ganina ya sanyata dakatawa hade da kallo na.

Dariyar da ban samu na yi dazu ba ce ta samu damar fitowa, na shiga tuntsira dariyar ba ƙaƙƙautawa, yayin da Aunty ke ta kallo na.

Sai da na yi mai isa ta, sannan na ce “Yau gidan nan akwai yare?”

“Me ya faru?” Aunty ta tambaya

Cikin dariya na ce “Ya Azeez ne ta daukarwa Aunty Adama electric cooker dinta” na karasa maganar cikin dariya sosai.

“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!! Yaushe?” A kidime sosai Aunty ta yi maganar.

Har zuwa lokacin na kasa tsayar da dariyata, na ce “Yanzu”

“Shi ne ba za ki kira ni ba, yana ina yanzu? ” Ta yi maganar lokaci daya kuma tana nufar kofa

“Ya tafi fa.” na yi maganar lokacin da nake bin bayanta da sauri

Ta shiga kiran lambarshi, amma ya ki dagawa, har ta gaji ta yi wurgi da wayar kan gado. Cikin kunar zuciya ta ce “Juriyata ta kusa karewa wlh, wace irin rayuwa ce wannan? To ni me na sani a dadin zaman aure kullum matsala, Allah ka saka min hannunka a wannan lamari, wlh na gaji.” kai karshen maganar tata ya yi daidai da zaman ta a gefen gado jagwab.

Wannan ya sa jikina ya yi sanyi, irin sanyi kalau din nan.

Ni kaina na san Aunty na daya daga cikin jaruman mutanen nan da suka iya jure kalubale, zai wahala ka ga weakness din ta, duk da wani lokaci ta kan manta da wannan jarumtar yanayin ta ya bayyana damuwarta.

Ni dai a nawa bangaren ina kallon Ya Azeez a matsayin babbar matsalarta, amma kuma wani lokacin sai in ga kamar tana da matsalar da ta zarta.

A zahiri kuma ba mai kallon ta ya ce tana da damuwa, tana cikin daula a ko wane lokaci, duk shekara sai ta je kasa mai tsarki. Na yi mamaki da aka ce ma tana da hawan jini, Sai daga baya ne na tafi a kan Ya Azeez ne sila.

“Aunty! Don Allah ki yi hakuri, akwai wadanda suka fi ki tarin matsala a duniya, ke matsalar ki daya ce ta Azeez, kuma In Sha Allah zai daina duk abin da yake yi.”

“To yaushe Maryam?”

Na dan yi shiru ina kallon da ta, kafin in ce “Ba da jimawa ba Sha Allah”

“Allahu Ya sha.” cike da sanyin jiki ta yi maganar.

Wannan ya sa na nufi kofar fita.

Ni na shiga duk wasu ayyukan gida, na yi miyar Shuwakar da Hammah ke so, sannan na yi mana tuwo iyakar na rana kawai, muka ci da vegetable soup, Shuwakar Kuma na bari sai dare mu ci da ita.

Misalin karfe biyar na yamma zaune nake a falo, yayin da na bude datar wayata, kai tsaye Instagram na dosa.

Wasu tarin DM na gani, mamaki ya mamaye ni, ba a taba min DM ba sai yau, ga wasu tarin followers da na samu.

DM din na shiga budewa, ashe Wai duk masu son sanin relation dina da Azeez ne, du maganganun basu wuce *”Don Allah kin san shi? A Ina yake? Me ye tsakaninku? Saurayinki ne? Brothernki ne? Kina da Lambar shi? Don Allah ki taimaka min da lambarshi.”*

99% na DM din abin da yake cewa kenan. A, zuciyata na ce Ya Azeez kamar nama, kowa so yake yi, ko, yaushe mata suka zama haka oho.

Knocking din da aka yi ne ya sanya ni tashi zuwa wajen kofar.

Aunty Adama na gani tsaye bayan na bude kofar.

“Aishar na nan?”

Ta tambaye ni ba tare da ta amsa min gaisuwar da na yi mata ba.

Takun sakkowar Auntyn ne ya hana ni ba ta amsa, Sai dai na ba ta hanya ta shigo cikin falon sosai.

“Aisha! Na gaji da satar da yaronki yake min gaskiya. Wlh za a rika biyana duk abin da ya daukar min. Ki ja mishi kunne ya raba kanshi da sashena. Haka kawai yarana basu dora min hawan jini ba, na wata ya dora min” cewar Aunty Adama cikin fada.

“Ki yi hakuri don Allah Mamansu Huzaima, wlh ban san ma ya shigo gidan ba.”

“Ni dai na fada miki, ki fada mishi da budaddiyar murya, don wlh nan gaba ya kara daukar min ko cokali ne station zan kai shi. Haka kawai kai da dakinka, ba ka isa ka aje komai ba, dan’iskan yaro ɓarawo.”

Ta kai karshen maganar hade da ficewa daga falon,.

Na bi Aunty da kallo, wacce ta yi tsaye cike da bacin rai. Sai kuma ta juyawa zuwa saman.

Da sauri na bi bayanta, Sai dai kafin in isa, har ta juyo hannunta rike da key din motarta.

“Je ki dakko hijab naki ki raka Ni”
Ta fada min lokacin da take gyara zaman nata hijabin.

Farin dogon hijab dina na sanya, lokacin da na fito har ta fara warming din motar, shi ya sa ina shiga ta fice daga gidan.

Tafiya muke shiru babu mai cewa komai, har zuwa lokacin da ta yi horn a kofar wani katon gini, wanda daga sama a ka rubuta

King & Kings Hotel

Ba jimawa maigadin ya bude, muka silala cikin harabar hotel din, muna shiga na fahimci Ya Azeez na da alaƙa da wajen, saboda akwai wuraren da na ga yana yin hotuna.

A nutse ta parker lokaci daya kuma ta shiga kiran Ya Azeez, amma bai daga ba, hakan ya sa ta tura mishi sako, ban san me ta rubuta ba, amma na ga ta kife wayar hade da zubawa kofar fitowa ido.

Kamar 10mns da tura sakon, Ya turo kofar ya fito.

Duk muka zuba mishi ido har ya karaso wajenmu,

“Fito Maryam” cewar Aunty a lokacin da take bude kofarta ta fita.

“Mu je dakin naka?” ta umarci Ya Azeez, bai musa ba ya shige gaba muna bin shi a baya.

Dakin a gyare yake tsab, babu wani datti sai kamshin freshener da ya hadu da sanyin A.C.

Ni dai rabewa na yi jikin kofa, yayin da Aunty ke tsaye a tsakiyar dakin tana karewa ko ina kallo kamar mai neman kuskuren da aka yi wajen gina shi.

Lungu da sakon dakin ta shiga bincikewa, kamar mai neman kayan laifi, amma ban ga wani abu da ya yi kama da rashin dacewa ba, da alama ita ma ba ta ga komai din ba. Dalilin da ya sa ta koma gefen gado ta zauna tare kallon Ya Azeez wanda ke tsaye a tsakiyar dakin.

“Abdul’azeez ina electric din Mamansu Huzaima?” ta yi maganar idanunta kafe a kanshi.

Bai amsa ba sai dai ya juyo yana kallona fuska a hade.

A tsoroce na ce “Ba ni ce na fada mata ba wlh, Aunty Adaman ce da kanta ta zo ta fada mata.”

“Ina ka kai shi?” Aunty ta kuma tambaya ba tare da ta damu da abin da ke faruwa tsakaninmu ba.

“Na sayar da shi.” Ya amsa ta rai bace

“Ka kyauta da kenan?”

Bai amsa ba, illa ya kara juyowa yana kallo na. Yayin da narke fuska kamar zan yi kuka.

“Tattaro kayanka kaf zuwa gida, daga yau Abdul’azeez, Idan har ni ce na haife ka, na hana ka kwana ko ina sai a gida.”

Komai bai ce ba, kamar yadda bai yi niyyar tattare kayan ba.

Ita ce ta mike tare da nufar closet din, tsadaddun kayan shi ta shiga tattarewa hade da mika min ta ce in kai mota, a tsorace na karbi kayan idanuna kur a kan shi, ganin bai yi alamun zai yi min wani abu ba, sai na fice da kayan.

Haka Aunty ta rika shirya min kayanshi ina, ficewa dasu, har sai da ta tattare su dukka, sannan ta mika mishi key din motorshi tare da fadin “Let’s go”

A fusace ya fice daga cikin dakin, muka dafa mishi baya, lokacin da muka isa farfajiyar hotel din har motorshi ta fice daga harabar hotel din.

Mu dai kai tsaye gida muka wuce, yayin da shi kuma ya yi wata hanyar daban.

Lokacin da muka isa gida tuni an yi magriba, shi ya sa Aunty ta ce in fara yin sallar in ci abinci sannan in gyara mishi dakinshi.

Aunty Adama

Zaune take cikin kayataccen falonta, har zuwa lokacin tana jin zafin yadda Azeez ya dauke mata electric, yau dai ta kwashe mishi albarkatu ba ta san ko sau nawa ba, kwanakin nan yana yi mata sata mai zafi.

Kofarta a ka shiga knocking wannan dalilin ya sanya ta yunkura zuwa wurin kofar.

Ganin Aunty tsaye bakin kofar, sai ta kara fitowa amin sosai kan kofar ta tsaya, da farko ta dauka Bandi ne, har ta tanadi kalaman da za ta yi mishi warning da shi, a kan ya fitar da ita, a kan maganarshi da Maryam.

“Ina wuni Mamansu Huzaima” cewar Aunty cikin lallausar murya.

A kausace Aunty Adama ta ce “Lafiya ƙalau.”

Ganin dai Aunty Adama ba ta da niyyar ba ta kofa su shiga cikin falon ya sa ta ce “Dama na zo kara ba ki hak’uri ne a kan abin da Azeez ya yi miki, don Allah ki yi hakuri.”

Fuska ta kara hadewa, alamun dai an tabo mata inda ke yi mata zafi.

Ajiyar zuciya Aunty ta sauke, cikin ikon tattausar murya ta kuma cewa “Don Allah ki yi hakuri, na san kuma ban isa in biya barnar da Abdul’azeez yake yi miki ba, Sai dai ga dan wani abu ki rage asara don Allah” ta kai karshen maganar tata hade da mika mata kudi da ya tasar ma 500k.

Kudin ta kalla shekeke hade da yin wani murmushi wanda ita kadai ta san ma’anarshi sannan ta ce

“Aisha ki saka idonki a cikin nawa da kyau, ke kin san har yanzu Allah bai yi miki arzikin da za ki biyani ɓarnar da yaronki ke yi min ba” ta kai karshen maganar idanunta zube a kan Aunty.

“Na sani. Shi ya sa na ce ba zan iya biyanki ba, ki dai rage asara.”

“Na ji ki sosai fa, na rage asarar ma, wlh ba ki dasu, ni har yanzu ina yi miki kallon yar tallar nono, darajarki ba ta wuce haka a wajena ba har gobe.”

Wannan karon murmushi Aunty ta yi, hade da juyawa zuwa part din ta, komai ba ta cewa Aunty Adama ba.

Daidai lokacin motar Hammah ta shigo gidan, da ido Aunty ta bi motar har ya parker.

Kai tsaye kuma ya fito zuwa inda take tsaye tana kallon shi.

“Me ya faru?”

Ya yi tambayar idanunshi a kanta.

“Ba komai. Kawai dai na dawo da Azeez gida ne.”

Wata yar dariya ya yi kafin ya ce “Kina son jawo ma kanki bacin rai Aisha, yau ne kika fara dawo da Azeez gida yana komawa ne?”

Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Wannan ya sanya shi juyawa zuwa bangaren shi yana fadin “Ya kamata zuwa yanzu ki saba da halin yaronki, ki godewa Allah tun da baya dakko miki magana a waje, baya bin mata kuma baya shaye-shaye.”

Bin bayan Hammahn ta yi da ido har ya shige bangarenshi, ajiyar zuciya ta sauke a hankali.

Gaskiyar Hammah ne, zuwa wannan lokacin ya kamata ta saba da halin Abdul’azeez, amma irin halin Abdul’azeez ba shi ne irin halin da ake sabawa da shi ba.

Zuwanta gidan Hammah a matsayin matar aure, ta saba da abubuwa da yawa, ciki kuwa har da gorin Mamansu Huzaima, wanda ita ma zuwa yanzu Mamansu Huzaiman ta gaji da yin shi, Sai abu ya hado su da kuwa a rana ta yi kadan shi ne ta yi mata kamar goma.

Da wannan tunanin ta kwankwasa kofa, na yi saurin kammala daure duwon da na saka a leda, sannan na nufi kofar.

Dama na san Aunty ce, yadda na ga fuskarta babu walwala sai na ji jikina ya yi sanyi, rashin walwalar tata, ya tafi da duk wani ragowar kuzari nawa.

“Idan kin gama tuwon, Hammah ya dawo, ki, hada mishi komai ki kai sashen shi.”

Kai na jinjina alamar na fahimta, sannan na bi bayan ta da kallo lokacin da take hawa stairs din da zai sada ta da dakinta.

Sai da ta kai tsakiyar stairs din sannan ta juyo, hade da dago hannunta na dama ta bude yatsunta a kan saitin fuskata (irin kaniyarkin nan)

Wannan ya sa na saki handle din kofar hade da rufe fuskata da tafukan hannuna ina dariya.

“Kin cika sa ido Maryam.” ta yi maganar cikin murmushi.

Ba ta jira cewa ta ba, ta ci gaba da haura stairs din.

Na dauke tafukan hannuna daga kan fuskata har zuwa lokacin fuskata akwai ragowar murmushi.

Ko wane lokaci na kalli Aunty a zuciyata sai in ce, wai me Aunty ta gani a jikin Hammah ta aure shi?

Ana cewa dan’adam tara yake bai cika goma ba, ni har yanzu ban san ina ne ya rage Aunty ba ta cika nata goman ba.

Fara ce tass! Allah Ya cika halittarta daidai gwargwado, fuska madaidaiciya mai dauke da dogon hanci, madaidaicin baki mai dauke da siraran labba, siririn gashin gira, dogon bakin gashi, ga wata ƙiba mai kyau wacce ta karawa tsawon ta kyau.

Akwai riko da addini, kyautatawa, hak’uri da kuma jurewa kalubale.

Sabanin Hammah da yake baki, baƙi sosai, ga shi dogo sangameme, komai na jikin Hammah babba ne, amma fa akwai tarin dukiya, wanda ina jin shi kanshi bai san yawan arzikin da Allah Ya yi mishi ba, kullum arzikinshi ka karuwa yake kamar saukar ruwan sama lokacin marka-marka.

Hammah ba dansiyasa ba, kuma baya aikin gwamnati, sannan ban san shagonshi a kasuwa ba, amma kullum ina mamakin habakar arzikin shi, kodayake kullum baya zama a gida, wani lokaci ma sai ya yi fiye da sati daya a waje.

Da wannan tunanin na koma kitchen na hada wa Hammah abinci kamar yadda Aunty ta bukata, a kan babban tire na hada komai sannan na nufi sashen.

Bayan na dawo dakin Ya Azeez na shiga, na ci gaba da gyarawa.

Gyara na musamman na yi wa dakin, na feshe shi da room freshener kala-kala, sannan na dakko wasu daga cikin turaren kamshin Aunty, wanda ajiye su kawai ake yi a daki a dan bude su kadan kamshin ya rika fita a hankali.

Daga nan dakina na wuce na yi sallahr isha’i sannan na zauna cin abinci.

Ina tsaka da cin abincin ne na ji an murza handle din kofata alamun za a shigo.

Da yake key din kofar ya bata sai aka yi hooking din jam lock din

<< Da Magana 6Da Magana 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.