Skip to content
Part 8 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ya Azeez ne ya shigo, hannu na sagale hade zuba mishi idanuna a tsorace.

“Je ki dafa min indomie please” ya yi maganar hade da juyawa ya fice.

Ajiyar zuciya na sauke hade da mikewa na bi bayan shi, ko loma daya ta abincin ban kara ba.

“ki je ki gama cin abincin.” ya yi maganar ganin ina bin shi a baya.

A ɗan tsorace na ce “Zan fara dorawa ne.”

Bai ce min komai ba ya wuce dakinshi.

Jajjagaggen tarugu na fara diba a fridges, na dan soya shi sama-sama da mangyada, sannan na tsayar da ruwa.

Daki na koma na dakko tuwona na dawo kitchen din na zauna, har na gama dafa mishi indomien da kwai.

Duk da kofar turo ta ya yi, hakan bai hana ni lwankwasawa ba.

“Shigo” ya fada daga can cikin dakin.

Daga bakin kofa na tsaya tare da fadin “Dama na gama ne, in kawo ma nan?”

Na karasa maganar ina satar kallon shi, kwance yake a kan gado, amma duk kafafunshi a kasa suke, Sai ear piece da ya mannawa kunnensa.

Ya mike tsaye hade da fadin “Mu je”

Kan dinning na ajiye mishi, hade da komawa dakina.

Karatu nake son yi, wannan dalilin ne ya sanya ni hawa tsakiyar gadona hade da tattaro littattafaina.

Maimakon in yi karatu kamar yadda na yi niyya, wayata na dakko hade da bude data, kai tsaye Instagram na nufa, abin da nake bukatar ganin shi na gani.

Ya Azeez ya yi sabon update, dan guntun video ne, kamar kullum sanye yake da kananun kaya, wando da riga farare tas, rigar na da hula, daga gaba rigar an rubuta CANADA. Kafarshi sanye cikin farin kambas, hannunshi rike da tsadaddar wayarshi yana shafawa. Yayin da wani dan karamin farin kare ke gefen shi yana ƴan tsalle-tsallen shi.

Ni kaina videon ya yi min kyau, comment section na shiga ina karantawa, wasu su yabawa wasu su kushe.

Turo kofar da aka yi ne ya sanyani saurin dagowa.

“Zo nan” Ya Azeez ya fada hade da juyawa.

Na mike tare da yin celebrating da duk hannayena biyun. Wani irin farin ciki da dadi nake ji, ga ni ga celen Instagram wanda yake tashe.

Da kudi wasu ke son ganin shi, ni kuma ga shi a kusa da ni kyauta, har ina yi mishi abinci yana ci.

“Wayyyo Allahna dadi!” Na fada a hankali tare da yin wani sabon celebrating, lokaci daya kuma na bi bayan shi da sauri. Saboda lokacin tuni ya bar falon.

Bin shi na rinka yi har zuwa cage din da Hammah ya yi kiwon jimina.

Tun daga nesa na hango dan karamin farin karen nan. Wani dadin ya kuma kashe ni, ga ni ga karen Cele, na rika yar rawa a hankali ta hanyar girgiza kafadu, ganin yana niyyar juyowa da sauri na daidaita nutsuwata, lokaci daya kuma na saka kaina a cikin kejin, Sai dai ina shiga ɗan karen nan ya biyo ni, na kwasa a guje ina kara, shi kuma yay ta bi na yana tsalle, haka muka rika zagaye cikin kejin, yayin da Ya Azeez ke tsaye hannunsa zube cikin aljihun wandonshi yana kallon mu.

Jin ya cafko min gefen doguwa riga ta, na buga wani tsalle hade da kwalla kara, lokacin da na fara dawowa hankalina ne na ji sautin muryar Ya Azeez cikin fada yana cewa “Dalla can ni sakanni, ga rashin kunya sai shegen tsoron tsiya.”

Na yi sakin shi daga cacumar da na yi mishi, lokaci daya kuma na nufi kofar kejin a guje.

“Where are you going to, come back” a tsawace ya yi maganar wannan ya sa na kuma dawowa baya a rude, sai kuma a lokacin ne na ga karen dan nesa damu kadan idanunshi a kaina.

“Babu abin da zai yi miki dalla” ya karasa maganar hade da jan dogon tsokin da ya zame mishi nature.

Gaban karen ya karasa hade da shafa farin bazagar din gashinshi.

“Zo mana” ya kuma fada lokacin da yake tsugune a gaban karen.

Daga da nesa dasu kadan na tsaya, har zuwa lokacin jikina rawa yake yi.

Tsaye ya mike hade da mayar da hannayensa cikin aljihunsa, har zuwa lokacin idanunshi zube a kan karen.

“Sunan shi Dog, please ki rika kular min da shi, cin abincin shi, ruwa, makwancinsa da kuma lafiyarshi. Ina son shi sosai, don Allah kar ki rika bar min shi da yunwa ko ki yi sakaci wani abu ya same shi.” yanzu kam ni yake kallo.

Wannan ya sa na shiga gyada kaina da sauri, kafin in ce” To me yake ci? “

Idon shi ya mayar a kan Dog din, kamar yana jiran ya amsa min tambayata, kafin ya ce” Komai. Yana cin komai. Amma ki tabbatar a kullum ya ci nama da madara, zan siyo madara sannan idan babu nama ki sanar min, ko idan Aunty ta hana ki ba shi.”

Kai na kuma jinjinawa alamun fahimta.

“Karfe goma na dare, ki fito ki ba shi abincin daren shi, ki tabbatar ya koshi, har ya yi rogowar wanda zai ci idan ya ji yunwa kafin gari ya waye”

“To.” na fada tare da jinjina kaina.”Karfe bakwai na safe ki ba shi abincin kari, shi ne za ki ba shi madara mai dumi.”

Na kuma jinjina kai tare da fadin “To.”

“Zan fita ni.” ya yi maganar lokaci daya kuma yana dukawa kusa da Dog yana shafa gashinshi.

“Nan za ka kwana ne?” Ni kadai na san irin jarumtar da na yi wajen yi mishi wannan tambayar.

Juyowa ya yi fuska a daure “Za ki fara ko?”

Na marairaice kamar zan yi kuka na ce “Don Allah Ya Azeez ko iya yau kawai, ka kwana a gidan nan saboda Aunty.”

Komai bai ce min ba, Sai ma mikewa da ya yi hade da nufar fita, Dog kuma ya bi bayan shi yana tsalle, Sai da ya kai bakin kofar ne ya juyo hade da fadin “Go back inside Dog, za dawo yanzu.”

Ga mamakina karen ya tsaya hade da kallon shi, irin dai kamar bai so hakan ba.

Dalilin da ya sanya shi dawowa baya, Ya kuma dukawa wajen shi yana shafa jikinshi, cikin sigar lallashi yake cewa “Sorry! Zan dawo ba da jimawa ba, idan kana son abu ne wannan za ta ba ka” ya yi maganar hade da nuna ni da yatsa.

Sai ko Dog din ya dago yana kallo na.

Kamar wawiya haka na warware fuskata zuwa fara’a ina kallon Dog na ce “Yes! I will give you. Duk abin da kake so zan ba ka.”

Da alama Ya Azeez ya ji dadin yadda na yi, don sai da ya dunkule yatsunshi hudu tare da dga babban yatsanshi alamun jinjina.

Tare muka fita zuwa farfajiyar gidan, yayin da Dog ke tsugunno a cikin keji yana kallonmu, Sai na ji kamar in koma mu kwana tare, sosai ya ba ni tausayi.

“Ya Azeez!” na kira shi da dan karfi ganin ya nufi motarshi

Dakatawa ya yi tare da zuba min ido a cikin hasken da ya gauraye farfajiyar gidan.

Yadda ya daure fuska tamau ya sanyani saka yatsana karami a baki ina taunawa kadan. “Ina jin ki fa” a fusace ya yi maganar.

“Don Allah Ya Azeez ka dawo gida ka kwana, don Allah!”

“Mtswww!” ya ja dogon tsoki kafin ya ce “Na ji.”

Na sauke ajiyar zuciyar jin dadi, cike da murna na ce “Thank you”

Bai ce komai ba, har zuwa lokacin da ya daidaita zaman shi a cikin motar, sannan ya ce “Zan kira ki bude min kofa.”

“To!” na amsa shi, lokaci daya kuma Ina kallon yadda yake ficewa daga gidan.

Da wani irin farin ciki na shiga dakina, lokaci daya kuma na fada kan gado ina celebrating jin dadi, wani irin dadi nake ji, from no where.

Ina karatu ina duba time, karfe, na nufi kitchen, madara na fara kwbawa da ruwan zafi a cikin karamar roba, sannan na dauki plate na kwashi tafasasshen naman da ke cikin fridge yawa.

Kofar cage din na tsaya Ina kallon Dog da ke kwance, da alama bacci yake yi.

“Dog!” na kira sunan na shi, ga mamakina sai na ga ya dago kai.

“Ni ce wacce Ya Azeez ya ce in zo in ba ka abinci, ba za ka cije ni ba in shigo?”

Kallo na kawai yake yi.

“Dog! Come now.” na Kuma fada hade da ya fito shi da hannuna. Bai motsa ba, Sai dai idanunshi zube a kaina bai ko kyaftawa.

“Please come, abinci na kawo ma” na yi maganar hade da nuna mishi abincin

Kallo na dai kawai yake yi. Haka nai ta surutu da kuma lallabashi, har daga karshe ya dan tako kadan zuwa kofar kejin Kofar na buda hade da tura mishi abincin, ina kara fada mishi ya ci abincin, dakyar! Na samu ya fara lasar madarar, yana yi yana dago kanshi yana kallo na har ya shanye tsab ya lashe robar.

Ganin zai juya na kuma cewa “Dog ba ka ci naman ba.”

Da alama ya ji me na fada, saboda dawowa ya yi tare da shinshina naman, Ya dan ci tsoka biyu sannan ya koma inda yake kwance da. Wannan ya tabbatar min koshi ya yi.

“Sai da safe to.” na fada daga wajen da nake a tsaye tare da dago mishi hannu.

Da ido yay ta bi na, har na juya da zummar komawa daki.

Lokacin da na fito kwanar da za ta sadani da part din Aunty ne, na ga Aunty Adama tsugunne a gaban entrance namu, tana jera wasu abubuwa.

Da sauri na koma baya, amma ina satar lekenta har zuwa lokacin da ta mike zuwa kofarta.

Sai da na tabbatar ta shige, sannan na fito. Wurin da na ga ta duka na tunkara.

Na yi tsaye ina kallon wasu bakaken duwatsu guda bakwai da ta jera, kamar in taba, Sai kuma na fasa na shige cikin namu part din, Sai dai zuciyata cike da tambayoyi da kuma son sanin ma’anar jera duwatsun da kuma dalilin da ya sa ta jera su.

Da wannan tunanin na zauna har zuwa lokacin da kiran Ya Azeez ya shigo wayata. 

Ban daga ba, amma na nufi kofar dakin, tare da duba agogon wayar da ya ce 11:45pm.

Ledar da ke hannunshi ya miko min, tare da nufar kofar shi. Yana fadin “Na ki ne, and ba ki ba Dog ruwa ba.” 

Sai a lokacin na tuna da maganar ba shi ruwan, shi ya sa kai tsaye na nufi kitchen, na samu wata roba mai fadi na zuba ruwan. 

Har lokacin duwatsun da Aunty Adama ta jera suna wurin, wata zuciyar ta rika fada min in kwashe, wata kuma ta rika fada min in bar su. 

Lokacin da na dawo daga wurin Dog ma sai da zuciyata ta kara fada min in kwashe su. Wata kuma ta hana ni. 

Tsakiyar gadona na zauna tare da bude ledar da Ya Azeez ya ce tawa ce, kaza ce ciki da souce, ba karamin dadin kyautar na ji ba, sosai na ci, sannan na kai ragowar fridge. 

Ban kwanta ba sai daya saura na dare.

Karfe hudun asuba kuma na farka kamar wacce aka tayar.

Ji na yi ina son ganin Dog, ba tare da wani tsoro ba, na fito zuwa wajen kejin.

Takuna da ya ji ne ya sanya shi dago kai, ba tare da tsoro ba, na shiga cikin kejin, ruwa da naman da na ajiye mishi na duba, naman saura yanka uku, ruwan kuma akwai da yawa.

Kai na dago ina kallon yadda yake kallo na, kafin na fice zuwa daki.

Lokacin da zan fita kwanar still Aunty Adama na gani duke a gaban entrance namu, da sauri na koma baya, Sai da na tabbatar ta shige part din ta sannan na fito.

Abun mamaki babu wadannan duwatsun da ta shirya, da alama kwashe abun ta ta yi.

Wannan ya kara sanya zuciyata zargin lallai duwatsun babu alkairi a tare dasu.

Gefen gado na zauna cike da tunanin abin da na gani, har zuwa lokacin da Aunty ta buga min kofa, alamun lokacin sallah ya yi.

Bayan na yi sallah kitchen na wuce, saboda akwai makaranta, ina ciki Aunty ta same ni, mu ka gaisa, sannan mu ka shiga aikin tare, kasancewar ita ke da miji.

Misalin bakwai muka hada sassaukan breakfast, daga nan toilet na fada, na shiga shirin tafiya makaranta.

7:15 na gama shiri, Dog na hadawa na shi break fast din na Kai mishi, a tsaitsaye na karya, Aunty ta ba ni kudin keke na wuce school.

Sai da na shiga makaranta na tuna ban taho da wayata ba, kuma ga Ya Azeez yana gida, Sai dai in bi ta da addu’ar Allah Ya kare ta.

Azeez

Misalin karfe tara ya tashi, kuma sai a lokacin ne ya sallahr asuba, bayan ya idar ne ya yi wanka hade da shiryawa cikin bakin wando da bakar riga, farin kambas ya daura, sosai kwalliyar ta yi mishi kyau.

Ba tare da ya saurari gargadin da Aunty ta yi mishi kafin ta fita ba, na kada ya sake ya daukar mata wani abu, Ya nufi saman, fatanshi ya samu kofar a bude.

“Mtswww!” ya ja tsoki lokaci daya kuma yana rike da handle din kofar, wayar da ke cikin aljihunshi ya jawo, Nasir ne ke fada mishi shi suke jira.

Wannan ya sa ya rika sauka kan stairs din da sauri, har zuwa lokacin da ya shiga dakin Maryam, ki filo ya daga, cikin sa a ya yi arba da wayarta, take ya sanya pin ya cire mata layikanta tare da watsa su saman gadon ya fice.

Sai da ya fara leka Dog ya shafa shi, sannan ya fice daga gidan ba ki daya.

<< Da Magana 7Da Magana 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×