JumanaTun da aka ɗauko amarya take kuka na zuci da na zahiri har za a tafi da ita wani matashi ya zo gaban motar yace "ku tsaya dan Allah zanyi magana da Amarya" Jumana na jin muryar shi ta fito da sauri tazo inda yake bata jira wata wata ba ta faɗa jikin shi ya rungume ta suna ta kuka a tsakanin su kowa ya tsaya yana mamakin Ganin shi a wanan lokacin da zuwan shi kenan ko gida be shiga ba ko mahaifiyar shi be nema ba sai ita, mahaifiyar shi kuwa da ta kasance uwa ga Amarya mutuwar. . .
