Skip to content
Part 10 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Lokacin da ta farka Aunty Hauwa, Aunty A’i da Aunty Ayyo ne a dakin suna hira.

Ta bisu da kallo daya bayan daya kafin su jefo mata kalmar “Sannu ya jikin?” a tare

“Da sauki” ta amsa tare da gyara zamanta tana kallon hannun, kafin ta mayar da kallon nata a kan Aunty Hauwa.

“Kai naga bala’i Aunty Hauwa, wallahi kamata ya yi in shinfida tabarma a kofar gida, in zauna a rika zuwa ana min Barka hannun nan ya warke. Amma kam naga bala’i tsirara.”

Aunty A’i ta yi dariya “Ai wallahi maganinki ma ciwon yatsan, ba ga shi ba har kin natsu.”

“To ai ke dama ba ƙaunata kike yi ba Aunty Aisha, na dade da sanin haka, don dai kawai babu yadda kika iya da ni ne.”

Aunty Ayyo ma dariyar ta yi ba tare da ta ce uffan ba.

Fatima ta dora “Wallahi Aunty Ayyo ba ta sona. Ciwon nan da na yi, na gane masoyana da makiyana, kin ga Ya Mustapha Allah dai ya saka mishi da alkairi. Sai Uwata ita ma ta nuna min kauna. Ya Jamil ma ba laifi.”

“Ai fa an taba yan baka, kura ta saci kalangu, mu kuma a wane layi muke?” cewa Aunty Hauwa.

Kafin Fatima ta ba ta amsa, Mama ta shigo hannunta dauke da kofin silba, ta mikawa Fatima.

Aunty Hauwa ce ta bude cup din, kokon gero ne fari kal, sai kamshin citta yake yi.

Dayan kwanon kuwa waina da miya ce da manshanu.

“Kai Allah ya sa dai mu yi aure gidan kudi, kuma gidan kudin inda aka san darajar cin dadi. Ba irin gidansu Zainab ba, nan ma ga kudin amma da koko ake karin safe. Wai ban da lafiya amma kalli koko aka kawo min.”

“Idan kin tashi ma a dawo miki da ɗan ƙaruna ki aura. Ba dai ki cewa ba a gidan nan aka haife ki ba.” Mama ta fada a lokacin da take zama kan tabarma.

“To yanzu dai gidan Aunty Hauwa ne ba a san darajar cin dadi ba ko?” Cewar Aunty Aisha tana dariya.

“Ni dai ba za ki hada mu da ita ba. Cewa na yi gidansu Zainab. Hala ita Aunty Hauwar a can take? Ina nan ne dai gidansu. Mama ko ba ke ce kika haife ta ba?”

“Ban sani ba.” mama ta fada bayan ta yi kicin-kicin da fuska.

Aunty Hauwa dai ba ta ce komai ba. Aunty Ayyo ma karamin kofi ta dakko ta tsiyayi kokon ta kuma debi wainar tana fadin. “Mu bari mu ci, ke kuma ki zauna zaman jiran miji mai kudin ya zo.”

Haka suka wuni gidan, a yi maganar arziki wani lokaci kuma a yi ta tsiya, har zuwa lokacin da suka tafi.

Yanzu dai ciwo ya warke sai shirye-shiryen komawa makaranta kuma.

Duk da ma bankwana take yi da makarantar, babban burinta, ta samu sakamako me kyau, ta wuce Heath Daura ko F. C. E Katsina don ci gaba da karatunta.

Tana son ta ji tana aiki, abun da ke burgeta shi ne za ta iya biyan bukutunta ba tare da ta jira an biya mata.

Lokuta da dama Babanta ya kan fada “Fatima ki mayar da hankali sosai, ni nan zan cika miki burinki har zuwa matakin da kike bukata a karatu koda kuwa kina gidan mijinki ne.”

A lokacin murmushi take ta ce, “Baba so nake na zama Malamar makaranta har zuwa matakin principal, ina son in ganni ina gabatar da assembly dalibai a gabana burjik, ina son in ganni a motata cikin kwalliya ina murza sitiyari. In ganni a office dina, a kan kujera me juyawa. A lokacin ne zan tunawa Yaya Jamil wulakancin da yake mun a kan motarshi. “

Ya kan yi murmushi” Jamil dai ya yi miki komai kina mantawa ne, kuma burin mutum baya cika idan yana da mummunar manufa a ranshi.

Ta kan yi dariya me sauti “Kuma Baba ina son zama babbar likitar mata, in ganni sanye da kayan aiki yin operation na shiga theater room.”

“Ina yi miki fatan cikar burunki ni kuma zan tsaya da kafafuna a kan ganin kin cika burinki.”

Wannan ita ce kalar hirar Fatima da Babanta duk lokacin da suka ware.

Har yanzu wannan shi ne burin Fatima.

Ko wane lokaci da shi take kwana ta kuma tashi da shi.
*****

A bangaren Mama kuma babban burinta shi ne Fatima ta kammala karatunta, ta hadata aure da Jamil.

Don shi ne kawai take ganin zai iya zama da Fatima saboda halayenta masu wuyar sha’ani.

Shi ma kuma Jamil din Fatiman ce daidai shi, don kuwa ta sanshi sosai ta san halayenshi.

Ba zai mata wahalar zama ba, kamar wata can da zai dakko a wani a waje.

Wannan dai shi ne burinta Mama.

Bari mu bisu don jin yadda za ta kaya.

Tun da ta dawo gida ta kasa samun natsuwa, fuskar Mustafa ya ki bace mata.

Duk yadda ta so kore damuwarta abun ya faskara

Kamar yanzu ma da take zaune tana cin tuwon shinkafa miyar ganye.

Ba za ta iya gane dadi ko rashin dadinshi ba, ci kawai take.

Sallamar Jamil ce ta dagata, ta karbi kayan hannunshi gami da gaishe shi.

“In kawo ma abinci ne yanzu?”

Ta tambayeshi bayan ya zauna.

“Tea na fi so idan akwai, ban cika son abu me nauyi ba.”

“Babu gaskiya.”

“Ba za ki samar mun ba.”

“Yaya Jamil na gaji wallahi.”
Ta fada cikin shagwaba kamar za ta yi kuka.

“Aikin me kika yi?”

“Ku san komai ni ce na yi, sai tuka tuwon ne kawai Mama ta yi.”

“To me ya hana ki tuka tuwon.” Har yanzu hankalinshi a kan wayarshi da yake yin game din maciji.

“Na je gidansu Yaya Mustafa ne na dubo shi da jiki.”

Ya dakata da game din “Har gidansu kike zuwa? Kina sonshi ne wai?”

“Ni ma ban sani ba gaskiya. Kawai dai na damu da shi.”

“Hmmmm” abin da ya fada kenan, daga nan bai sake cewa komai ba.

Ita ma da biyu ta yi maganar, ta fahimci bukatar Mama shi ne ta hadasu aure, amma kuma abin da ta fahimta shi ne, shi ba shi da ra’ayi a kanta, bai taba nuna wata alama me kama da yana sonta ba. Kullum kuma idan ta yi challenging na Mama sai Maman ta ce a’a yana sonta ita ta sani.

To ga shi yanzu ko alamar kishi bai nuna ba. Da ta yi maganar wani a gabanshi.

“Zan je in sha shayi a waje, idan Mama ta fito daga wankan ki fada mata.”

Ba ta ba shi amsa ba, shi ma bai damu da sai ta bayar ba, ya fice abun sa.

Bayan fitowar Mama ne ta kalli Fatima da ke zaune shiru, ta tasa abinci a gabanta ko rabi ba ta ci ba.

“Wai me ke damunki ne? Kin ce jikin Mustafa da sauki amma kuma kamar akwai abun da ke damunki.”

Cewar Mama a lokacin da take zama, lokaci daya kuma tana kokarin kamo gidan Radion Kano don jin shirin Iya Ruwa.

“Har lokacin jin shirin naki ya yi Mama?” Fatima ta tambaya tana kallon agogo. A kokarinta na korar tambayar Mama.

“Ya yi mana, karfe takwas har da minti biyar fa. Yauwa kin ji ma har sun fara.”

“Ke ba yar siyasa ba, ba kuma siyasar za ki yi ba amma kin iya bibiyar shirin siyasa.”

“Sai zan yi, ko ina yin siyasa ne zan bibiyi shirin siyasa? So nake kawai in ji me ke faruwa a cikin siyasar. Wai na ji kamar Muryar Jamilu?”

“Eh shi ne. Amma ya fita.”

“Ya ci abinci?” Mama ta tambaya hankalinta yanzu a kan Fatima

“Ya ce ya koshi.”

“Kodai wani abu kika mishi?”

“Wani abu kuma Mama? Ni ban yi mishi komai ba. Shi kuma ba yaro ba, bare in aje shi a kan cinyata in lallasheshi ya ci abinci. Wallahi Mama kina damun kanki akan yaya Jamil, ace ki yi ta lallabashi kamar yaro. Yanzu kalli yadda kika damu don bai ci abinci ba, kamar cikinki zai kai.” Ta karasa maganar tata cikin tabewar baki.

“To innarmu ko dukana za ki yi saboda na lallashi wani? Ke da ranki yana baci ne kawai idan aka yi maganar Jamilu.” Cewar Mama tana kallonta.

“Ni fa gaskiya kawai na fada, Jamilun nan ba yaro ba, amma ki yi ta lallabashi kamar yaro. Yanzu ki kalli yadda kike ta son cusa mishi ni, kuma ba sona yake ba. Ni fa in fada miki gaskiya ba zan aureshi ba, muddin ba shi ne ya bude baki ya ce yana sona ba, kuma ya kula da ni kamar yadda masoya ke kula masoyansu. Amma haka kawai ki hadani da mutumin da kanshi na gabas nawa na yamma.”

Baki Mama ta rufe hade da sauke hannunta da rike habarta da shi alamun mamakin maganar Fatima.

“Lokacin dana auri tsohonki mun yi soyayya ne? Ku nawa na haifa a tare da shi? Ni fa idan na hadaki aure da Jamilu ma gatanci na yi miki. Za ki zauna kina fada mun magana. Aure nawa aka yi ba so, bayan auran kuma son ya zo? Idan ba rashin kunyar yaran zamani ba, har yaushe za ki zauna kina mun maganar so.”

“Ya za ki hada lokacinmu da naku? Babana ai mutumin kirki ne.”

“Shi kuma Jamilun na banza ne?” Mama ta tambaya fuska a hade.

Shiru Fatima ba ta yi magana ba, illa turo baki da ta yi.

“To Jamilun dai da kika raina shi ne mijin naki Fatima ko kina so ko ba kya so. Ta shi ki ba ni guri, kin hanani jin shirina ma.”

“Idan ya ce yana sona ba.”

“Za ki fita ko sai na make bakinki da ko wace magana yana da amsarta. Ya ki ya ce yana son naki yar gold, sai ki fada mun mutane nawa ne suka ce suna sonki din? Ana yi miki gata kina shirmen banza. Na ga kafarki gurin wani ki ga yadda zan sanya sanda in makesu.”

Baki zumbure Fatima ta fice daga dakin.

2007 ita ce shekarar da Fatima ba za ta taba mantawa ba, don kuwa ita ce mabudin nasarori da kuma kaddarorinta.

A shekarar ne ta kammala karatunta secondary wanda a lokacin take da shekaru sha takwas a duniya.

Girman jikinta kamar ya fi shekarunta, tana da tsawo da ma kuma jiki, ko ina jikinta a ciki ne, dumui- dumui da ita.

Kallo daya za ka yi mata ka fahimci ba ta san matsololin rayuwa ba, kuma ba ta da damuwa kota sisin kobo.

Ita kan ta ma ta san ba za ta iya cewa yanzu wannan shi ne matsalarta ko damuwarta ba.

Koda ace wani abu na damunta bai wuce fatan samun sakamako me kyau ba, wanda shi ne tsanin da za ta taka zuwa makarantar gaba secondary. Daga nan ta aza harsashin ginin kyakkyawar rayuwar da take hasashen samu.

Karfe biyar na yamma ta fito sanye da doguwar bakar rigar jallabiya, sai guntun hijabi me ruwan madara wanda ya tsaya iya kafadunta.

Fuskarta fayau idan ka dauke farar hodar Tony mantana da ta sha sai ban lebe me kyalli. Kamshin turaren laylatussahara na fita a jikinta.

Mama da ke tsakiyar gida zaune tana kara duba shinkafar tuwon da Fatima ta gama gyarawa dago kai ta yi tana kallonta, hade tambayarta ina za ta je.

“Zan kara zuwa gidansu Yaya Mustafa ne in dubo shi, har satin nan ya kare bai je Islamiya ba, tun da muka dubo shi tare da ‘yan Islamiyar ban sake komawa ba.”

Cewar Fatima tana goge bakin takalminta flat.

“Amma jikin na shi da sauki dai shekaranjiya da na je, idan kin je din ki gaishe shi. Kin ga ban da Zainab ta tafi hutu Katsina ai da ta raka ki.”

“Wallah ni ma sai dana tuna ta, na yi kewarta sosai. Sai na dawo, zan fada mishi kin gaishe shi.”

Ta fada lokacin da take kokarin fita daga gidan.
******

Sallama ta yi, amma ba kowa tsakar gidan, har sai da ta kara wata sallamar a lokacin da take shiga cikin gidan sosai.

Sannan ne Ummi karamar kanwar Mustafa me kimanin shekaru sha biyar ta leko hade da amsa sallamar cikin sakin fuska.

Dakin Inna ta fara shiga, Innar a kwance take kan gadonta me rumfa.

A hankali take amsa gaisuwar Fatima.

“Lafiya Inna take kuwa?” ta yi tambayar tana kallon Ummi

“Da sauki dai, ciwon kirjinta ne ke son tashi. Amma ta sha magani.”

“Subhanallah! Allah ya ba ta lafiya.”

“Amin” Ummi ta amsa.

“Yaya Mustafa fa?”

“Yana cikin dakinshi, yanzu ma ya tashi a nan.” Ummi ta kuma amsawa

“To ya jikin nashi kuma? Na ga bana ganinshi a ko ina ma.”

Sai da Ummi ta kalli Inna sannan ta juyo kan Fatima hade da tabe baki “Da sauki. Ki shiga yana ciki.”

Mikewa Fatima ta yi bayan ta kara yiwa Inna sannu ta wuce zuwa dakin Mustafa

Matsakaicin daki ne, me dauke da teburin da ya jera littattafai na addini dana zamani, sai katifa madaidaiciya da kuma akwatin kayanshi da ya dora a kan wani teburin, kasan teburin kuma takalmanshi ne a jere.

Idan ka dauke wadannan kayan babu wani tarkace, kuma komai an aje shi inda ya dace.

Kwance yake ringigine da alama ya yi zurfin cikin tunani. Don ta dade a tsaye tana kallonshi, kafin ta yi sallama.

Ya amsa sallamar hade da dago kai, ganinta ne ya sanya shi tashi zaune, fuskarshi dauke da murmushin da bai boye damuwarshi ba.

Kujerar gaban teburin litattafanshi ta dakko hade da zama tana kallonshi.

“Ka rame da yawa, wai me ke damunka ne haka?”

Ya sauke numfashi, hade da shafa fuskarshi “Zazzabi kawai.”

“Bayan shi akwai wani abu Yaya Mustafa.”

“Ba komai.”

“Ba dai ka son in sani. Me ya sa to ba ka dan fita kana mike kafa, sai kullum kana gida.”

“Bana son hayaniya ne.”

Shiru ya ratsa dakin, yayin da Fatima ke bin bangwayen dakin da kallo.

“Shi kenan, zo ki tafi gida.”

Ta yi saurin kallonshi “Korata kake yi kuma? Ko ni ma har na dame ka da hayaniyar?”

“Ba ki dame ni ba.” ya fada hade komawa ya kwanta.

Zuba mishi ido ta yi tana kallon tsantsar damuwar da ke kan fuskarshi.

Ba ta da zabin da ya wuce ta tafi kamar yadda yake bukata.

Mikewa ta yi, har yanzu idonta a kan fuskar shi “Na tafi.”

“Na gode” ya fada, ba tare da ya kalleta ba.

Jiki a mace ta shiga dakin Inna ta yi mata sallama sannan ta fito don zuwa gida.

Amma abun mamaki Mustafa bai leko don yi mata rakiya ba.

Sai Ummi ce ta sanyi hijab suka jera zuwa kofar gida don yi mata rakiya.

A hanya ne Fatima ta ce “Ummi me ke damun Ya mustapha ne?”

Tabe baki Ummi ta yi kafin ta ce “Ya mustapha yana son ci gaba da karatun shi ne…”

“To me ye matsalar hakan?” Fatima ta yi saurin katse Ummi da tambayarta.

“Inna so take ya yi aure.”

Tare suka dakata daga tafiyar da suke yi, lokaci daya suna kallon juna. Ummi ta ci gaba

“Wata fa yar kauye ce mai talla Inna take son ya aura. Shi kuma baya so. Ko ni ma bana so. Wai idan ya yi aure sai ya ci gaba da karatun. Da ya nuna baya so shi ne ta ce sai ya kawo wacce yake so, idan ba haka ba wancan yarinyar zai aura.”

“Ikon Allah! Shi Ya Mustaphan kamar dai mace.” Fatima ta yi maganar tare da dariya.

“Ni ma fa haka Mama ke matsa min lallai sai Ya Jamil zan aura, ni kuma ba na son shi. Ban san me ye damuwar iyayenmu ba, ta son yi mana auran cushe.”

Ummi ta yi saurin cewa “Haba ke kuwa, ai Ya Jamil ba shi da wani aibu. Ko wacce mace ma za ta so auran shi.”

Fatima ta taɓe baki “Ba za ki fahimci komai ba. Amma don wannan ne Ya Mustapha ya damu. Ni fa ban san wani abu damuwa ba. Bare har ta hanani bacci.”

Tare suka tuntsire da dariya, kafin Ummi ta ja ta tsaya.

“Komawa zan yi Fatima. Amma kin ban dariya sosai, wai ba ki san damuwa ba.”

“Su Aunty Lami ma cewa suke wai ban da hankali, kuma fa da hankalina.”

Su kuma yin dariya a tare, sannan Ummi ta juya zuwa gida. Fatima ma ta nufo gida, zuciyata cike da sake-saken da take ganin shi ne mafita.

<< Daga Karshe 9Daga Karshe 11 >>

1 thought on “Daga Karshe 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×