Skip to content
Part 11 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ana kiran sallahr magriba ta shigo gidan, ganin ba kowa a tsakar gidan, kawai sai ta fada dakinta ba tare da sallama ba.

“Kai Allah ya kyauta. Mutum kullum yana zuwa islamiya amma a banza wai man kare. Sai mutum ya shigo gida kamar arne, gara ma arna ai suna fadin excuse.” cewar Mama da ta fito daga bayi, tare da zama kan dutse don gabatar da alwalar magriba.

“Na ga ba kowa a tsakar gidan, to wa zan yi ma sallamar?”

“A musulunce ko ba kowa a wuri sai ka yi sallama, halittun Allah yawa ne dasu.”

“To ai ni ban sani ba. Sai cewa kike wai ina zuwa islamiya kullum. Yanzu  don Allah Mama kullum nake zuwa islamiya? Islamiyar da sai in hada sati ma ban je ba.”

“To abun arziki ne kika yi? Na ce abun arziki ne don kin hada sati ba ki je islamiyar ba? Da har kike wani kara bude baki kina fada.”

“A’a. Wai dama don kar wani ya ji kona fada, ya dauka da gaske kullum sai na je din a toh. Ni fa islamiyar nan ma daga wannan satin na gama ban kara zuwa. Na gaji wallahi, tun da na fara wayau nake zuwa islamiya har yanzu kuma zuwa nake. Ina dalili. Wallahi na gaji ban ƙara zuwa.”

“To wa kika yi ma wa Fatima? Idan kin je kanki, idan ma ba ki je ba kanki. Ko cewa kika yi kin daina sallah iyakacinmu da ke fa addu’a.”

“Sallah kam ba zan daina ba.”

Mama dai ba ta kara cewa komai ba ta shige dakinta.

“Ba gara ma mutum ya yi auran shi ba ya huta, amma komai sai an yi ma fada. Ni da gidan ubana. Yanzu da gidana ne, waye zai tuhume ni don ban yi sallama ba? Don dai ban iya zuwa hutu ba, wallahi ni ma da hutun na tafi.”

Sallamar Aunty Bilki matar Yaya Bashir ta katse mata maganar zucin da take yi.

“Ji kuma wannan yar jarabar, ko me ya kawo ta gidan mutane ana magriba oho.”

Aunty Bilki ta daga labulen kofar tana kallon Fatima.

“Wai nan dakin ba ku amsa sallama ne?”

“Eh bamu amsawa, don Allah ki kyale ni. Wai sallamar nan, idan na amsa ko ban yi ba, ba kaina na yi mawa ba ne?”

“Allah ya ba ki hakuri, ba ni na kar zomon ba ma.”

“To je ki yi harkarki. Wacce kika zo wajen ta ga ta can tana sallah. Don jaraba, ana magriba kuna yawo.”

Aunty Bilki da ta riga ta san halin Fatima sarai, murmushi ta yi. “Yau sun motsa kenan?”

Da sauri Fatima ta mike daga zaunen da take “Su waye suka motsa din? Wallahi da ke da su Aunty A’i hukuma ce za ta rabamu. Sai kun fada min abun da suke motsawar.”

“Ke Bilkisu!” Mama da ta idar da sallah ta kwadawa Aunty Bilki kira.

“Fita harkar wannan yarinyar kin ji. Kina zaune za ta je gidanki, sai ki rama duk abin da ta yi miki.”

“To gidan nata ne? Ai na yayana ne”

“Ai Yayanki kika ce ba ubanki ba.” Mama ta amsa ta daga cikin daki.

“Yarinya ba wanda ta debewa hula, kowa ba ta bari ba. Kai Suhanallah Allah ya shirya.”

“Amin.” in ji Aunty Bilki a lokacin da take zama kan kujera hade da gaishe da Mama.

Suna tsaka da gaisawa ne Fatima ta fito, hannnunta rike da leda viva bag.

“Na tafi to, kar in tashi dawowa ace da zan tafi ban fadawa kowa ba.”

“Ashe za ki dawo ma?” in ji Aunty Bilki tana dariya.

“Ba dole ba, gidan ubana ne fa. Yana zuwa ni ma zan dawo”

Mama dai uffan ba ta ce ba, har Fatima ta fice gidan.

“Wai ina za ta je?”

“Gidan uwarta ta biyu mana”

Cikin dariya Aunty Bilki ta ce “Wai gidan Hakimi?”

“Eh ai ba ta wuce can din. Wannan yarinyar sai dai addu’a ai.”

Aunty Bilki ta kuma murmusawa, “Ni kuwa fa Mama, abubuwan Fatima basu ban haushi, dariya ma suke ba ni.”

“Sauri kike yi? Ai idan dai Fatima ce ba a ci mata alwashi.”

Hirar tasu yau duk a kan Fatiman ne, har zuwa lokacin da Ya Bashir da Ya Jamil suka shigo.

*****

A kofar masallacin Hakimi Mustafa ne zaune, a cikin matasa suna hira.

Hango Fatima ya sanya shi mikewa ya tare ta.

Tare suka  jera zuwa  cikin gidan

“Ina za ki je?”

“Nan gidan mana. Ya kana gani kuma za ka tambaya” ta kai karshen maganar da yi mishi wani kallo, mai nuna jin haushin tambayar tashi.

Murmushi ya yi, “Yajin aka kuma yi?”

“Eh.”

“Yanzu kuma me ya faru?”

“Wai daga ban yi sallama ba, Mama ke ta fada. Ni da gidan ubana.”

Mustafa ya dan murmusa kadan “Kin yi laifi fa. Yana daya daga cikin haƙƙin musulmi a kan musulmi, idan ya hadu da shi ya yi masa sallama.”

“To ai tsakar gidan ba kowa.”

“Amma dai ai kin san gidan akwai kowa ko?”

Kai ta daga alamar eh.

“To sai ki yi sallama, a ƙa’ida ma sai kin jira an amsa kafin ki shiga.”

“Ni da gidan uban nawa?” ta yi saurin tambaya hade da kallon shi.

“Ƙwarai.”

“Hu’ummm”

“Idan wuri ma babu mutum ana yin sallama. Misali za ki zauna a wurin wata bishiya don hutawa. Sai ki ce Assalamu Alaina wa’ala ibadullahissalihin. Idan za ki zauna kuma ki ce, A’uzubikalimatullahi tammat, min sharri ma kalaqa. Sannan sai ki zauna.”

Taɓe baki ta yi tare da fadin” Umm! “

A daidai lokacin kuma suka shiga babban falon Aunty Hauwa.

Mustafa ne ya fara zama,, ita ma sai ta zauna a kujerar da ke fuskantar shi.

“Dazu Ummi ta fada min abin da ke damunka. Yanzu don Allah kan wannan ne duk ka yi wani sanyi haka?”

Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya ce “Bai isa ya sanyani hakan ba ne? Ke har yanzu yarinya ce, ba ki san menene zaman aure da wanda ba ka so ba.”

Shiru ta yi tare da juya maganar shi cikin zuciyarta.

“To ya zai kasance idan kuma kowa bai so?”

Ta jefo mishi tambayar haɗe da kallon shi.

“Abun zai kasance tamkar wani filin yaƙi, da kowa ke neman ran kowa.”

“Hu’umm! Amma yanzu misali za ka iya aurena ni?”

“Me zai hana?”

“Mama ce ke cewa wai ba namijin da zai iya zama da ni sai Ya Jamil kawai.”

Karamin murmushi ya yi “To me ya sa sai shi kawai?”

“Wai ba ni da hankali.” ta kai karshen maganar tana tabe baki.

Wannan karon ma murmushi ya yi ba tare da ya ce komai ba.

“Ya Mustafa! Babana zai zo ranar Juma’a, ka tura iyayenka su tambayar maka aurena.”

Sakin baki ya yi yana mata kallon mamaki.

“Da gaske nake yi.”

“Auranki.” ya maimaita kalmar a hankali.

“Eh” ita ma ta amsa shi.

“Saboda me to?”

“Saboda mu dukkanmu”

“Kamar ya?”

“Kai ma Inna tana son ka yi aure, kuma ta zaba mata, ka ce ba ka so. Ta ce ka kawo wata, idan ba ka kawo ba za ta aura ma wacce ba ka so. Ka ga idan ka kawo ni ai shi kenan ka samu mafita.”

Kallon ta kawai yake yi, ganin babu alamun zai ce wani abu ya sa ta ci gaba.

“Ni kuma Mama gani take yi, babu wani namiji da zai iya aurena ya yi hak’urin zama da ni sai Ya Jamil. Shi ya sa yake ganin kamar alfarma zai yi min idan ya aure ni. Mama sai cusa mishi ni take yana sharewa. Ni kuma ba zan aure shin ba. Sannan idan na yi aure, so nake in ba, kowa mamaki, suna kallo na mara hankali ko? Hmmm. “

Mustafa dai kallon ta yake ba tare da ya ce kala ba.

“Ka yi shiru. Kodai gaskiyar Maman ne, ba mai iya aurena.”

Murmushi ya yi kafin ya ce, “Wai da gaske ki ke yi ne?”

“Wallahi da gaske nake yi.” Ta amsa shi.

Shi kansa ya ga gaskiyar a cikin kwayar idonta, kawai dai ya rasa abun fada ne.

“To ai shi kenan. Bari in je masallaci, kin ji har an kabbara sallah.”

Ya yi maganar tare da mikewa tsaye.

Ba ta ce mishi komai ba, har ya fice, ita ma sai ta mike zuwa ƙaramin falon Aunty Hauwa.

Ba ta a falon, dalilin da ya sanyata shiga cikin bedroom kenan.

Ganin tana sallah sai ta fada kan gadonta, da yake gyare lukui ta kwanta.

Mustafa take tunani, yanayin fuskarsa ya nuna mata kamar wasa ya dauki maganarta.

Ita kuma gaskiyarta ta fada. Idan har zai je neman auranta tabbas za ta aure shi. Da ta auri Jamil dai da yake mata kallon auranta alfarma ne, gara ta auri Mustafa ko don nunawa Jamil auranta ba alfarma ba ne.

“Ina Mustafan?” Aunty Hauwa ta katse mata tunani, a lokacin da take shafa addu’a.

“Ya tafi masallaci.” ta ba ta amsa ba tare da ta motsa daga yadda take ba.

“Me ya faru a gidan?”

“Mama da Aunty Bilki suka haɗe min kai. Ni da gidan ubana. Idan ya dawo sai in koma.”

“Ummm! Allah dai ya shirye ki.” cewar Aunty Hauwa a lokacin da take cire hijabin da ta yi sallah.

“Ke ma hala kallon mahaukaciyar kike min. Don fa kawai ina zuwa gidan ki, sannan ina jin kunyarki Aunty Hauwa. Amma da har da ke hukuma ce za ta raba mu.”

“Uwar hukuma ma ta raba mu Fatima, gidana daga yau kar ki kara zuwa. Ai ba kiran ki nake yi ba.”

“Kar ki yi min gorin gida Aunty Hauwa, ni ma fa auran nan zan yi.”

“Amma dai kafin ki yi ai ni na yi. Don haka gaba na yi kika biyo bayana.”

Kamar ba za ta tanka ba, sai kuma ta ce, “Don Allah san min kudi in sawo pad.”

“Ban da su.” Cewar Aunty Hauwa a lokacin da take fita.

Fatima da take kwance ta tuntsire da dariya. A zuciyarta kuma tana fadin, “Kya ma nemo su.”

A karamin falon ta cin mata.

“Haba Aunty Hauwa’u. Ke fa kamar uwa kike a wurinmu.”

“Yanzu kika san haka. Kodayake uwar ma ba ki raga mata a rashin kunyarki ba bare ni.”

Ta kai karshen zance haɗe da jefa mata gudar dari biyu.

“Ki maido min canjina wallahi.”

“Canjin fa duka naira 30 ne.”

“Ko naira biyar ce.”

Dariya Fatima ta yi kafin ta ce, “Ke dai ki yi addu’a yadda kuka yi hakuri da ni, Allah ya sa in yi da yaranku.”

Aunty Hauwa ba ta tanka ba, har Fatiman ta fice tana dariya.

*****

Ku san tare suka shigo gidan da Jamil, dalilin da ya sanya kenan ya tsaya a second gate din gidan har ta shigo.

Duk da gabanta ya fadi ta dalilin ganin sa, fuskarta ba ta nuna hakan ba.

“Ina kayan naki?” tambayar da ya fara jefo mata kenan.

Tura baki ta yi ba tare da ta amsa ba.

“Minti daya kawai, ki dakko su ki same ni anan.”

Wannan karon ma ba ta amsa ba, illa ta wuce cikin gidan. A can ma ba ta yi wa kowa magana ba, ta dakko ledar kayanta ta fito.

Aunty Hauwa da ke zaune tana cin tuwo ta ce “Kaza kanki da motsi.”

Fatima dai ba tanka ta ba.

Ita ce a gaba, yana bin bayanta. Har suka isa gidan babu wanda ya yi magana.

Mama kwance a tsakar gida tana sauraron radio, Fatima ta shigo wannan karon dai ta yi sallamar.

Mama kuwa ta amsa mata a sake.

“Ina Aunty Badiyyar kuma?”

“Ta tafi.” cewar Mama daga kwancen da take.

“Mama wai fushi kike yi ne? Ke fa kin san halina. To yanzu dai yi hakuri don Allah. Na san illar fushin iyaye.” ta kai karshen maganar dab tana zama kusa da Maman.

“Ke kam idan na ce zan rika ɓata raina a kanki Fatima, ai ba zan dade a duniya ba.”

Murmushi ta dan yi kafin ta ce “Ki rika min addu’a.”

“Ina yi ai.”

“Yauwa to na gode”

Jamil da ke tsaye, ya jingina bayansa da bishiyar dalbejiya, duk yana jin su amma bai ce komai ba.

*****

Yammacin laraba, da misalin karfe shidda na yamma, Fatima ta shigo gidan bakinta dauke da sallama.

Mama da ke kofar kitchen zaune ta amsa sallamar tare fadin, “Wai don Allah kaya suna tsunkulinki ne. Ace kamar jira kike yi ki shigo gida. Sai ki fara kwaɓe komai. Kai Alhamdulillahi!”

Fatima da take zare wandon uniform din islamiyarta ta ce, “To ba dai na shigo gidan ba.”

“Amma shi ne tun daga kofa?”

“Gidan ubana ne fa Mama.”

“To mai gidan uba. Kai da bamu da gidan uba dai da mun yi kuka. Ke da ko wace magana kina da amsarta.”

Wannan karon ba ta ce komai ba, kayan da ta cire take sagalewa a igiyar shanyar tsakar gidan.

Jin alamun za a shigo, sai ta kwasa da gudu ta fada dakin Mama.

Mama da ke zaune ta yi siririn tsaki.” Karamar mara kunya, da dai ki tsaya daga ke sai rigar. Ai gidan ubanki ne.”

Mustafa ya duka jikin bishiyar tare da gaishe da Mama, ta amsa, sannan suka shiga taba hirar duniya.

Fatima duk tana daki tana jin su, kwance saman gado daga ita sai rigar, ba ta nemi zane ta daura ba.

Haka nan ta ji tana jin nauyin hada ido da Mustafan, kila ko don wasikar da ta jefa mishi ne yau da suka je islamiya.

Sosai take son ta ji matsayarsu, ita da gaske take yi ba da wasa ba. So take ta ba kowa mamaki da kwatsam din da take shiryawa.

“Ina Fatima ne, kar dai da aka tashi islamiya ba gida tayo ba?”

Ta jiyo Mustafan yana tambayar Mama.

“Tana cikin daki, tana jin ka. Ka san halin ta dai ai.” 

Murmushi ya yi, sannan ya tunkari kofar, abin da ya sanya Fatima saurin fitowa falo sanye da zumbulelen hijabin Mama.

Karamar takarda kawai ya jefa mata, ba tare da ya yi magana ba ya juyo. Buta ya dauka saboda an fara kiran sallahr magriba.

“Mu hadu gidan Ya Bashir gobe da yamma idan Allah ya kaimu.”

Abin da ya rubuta kenan a karamar wasikar.

Ta zubawa rubutun nasa ido tana kallo, tamkar ba ta fahimci abin da ya rubuta ba.

Wani irin yanayi take ji wanda ta kasa fassarawa.

Da sauri ta cukuikuye takardar ta boye saboda jin shigowar Mama.

*****

Alhamis misalin 5:00pm daidai, ta shirya cikin riga da sicket na shadda kamfa, mai kalar purple da ratsin fari.

Farin hijab ta sanya, hade da farin takalmi mai dan tudu.

Kamshin turarenta na balila ya cika tsakar gidan.

“Ina kuma zuwa?” cewar Mama lokacin da take fitowa daga daki.

“Gidan Ya Bashir.”

“Ki gaishe su.”

“Zasu ji sha Allah.”

Tsaye ta yi a kofar gida, tana karewa majilisar matasan da ke zama a kofar gidan hakimi kallo.

Kafin daga bisani ta dauki hanyar da zai sadata da gidan Ya Bashir.

Aunty Bilki zaune a falo tana ninke kayan Bilal, juyowa ta yi haɗe da amsa sallamar da Fatima ta yi, kafin ta ce,

“Me kuma ya kawo ki gidana?”

“Gidanki fa. Kodai gidan Bashir.”

“Koma dai menene. Na aika miki da wasika ki zo ne?”

“Ni da ke dai Aunty Bilki ni dake fa kalwa ta san Inna ne, Inna ta san kalwa a toh.”

Shiru Aunty Bilki ta yi ba tare da ta ce komai ba, har sai da ta ga Fatima ta yi hanyar bedroom din ta ta ce,

“Ina za ki je nan?”

“Yau na shiga uku. Wai yau har iyaka ne da ni a gidan nan?”

“Ke ai kin iya yi wa mutum rashin mutunci, ki nuna kamar ba ki yi ba, yar rainin hankali. Yanzu ranar can dubi abin da kika yi min.”

“Yo me ne miki? Aunty Bilki yanzu har halina yana bata miki rai ashe?”

Sallamar Mustafa ta hana Aunty Bilki ba ta amsa.

<< Daga Karshe 10Daga Karshe 12 >>

2 thoughts on “Daga Karshe 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×