Skip to content
Part 13 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Wanshekare da safe, haka kowa ya wayi gari babu walwala. Mama kam ko gaisuwar Fatima ba ta karɓa ba. Zuwa karfe ɗaya gidan ya cika da ƴaƴan Alhaji Musa mata su biyar, ko wacce da abin da ta kawo mishi. Aunty Lami ce kawai babu, kasancewar ita a Katsina take aure.

A lokacin ne kuma Mama ta basu labarin abin da ya faru jiya da dare. Ta dora da “A wannan lokacin zan ba Fatima mamaki, za ta san cewa jin dadin zaman duniyar nan, ya hada har da rashin fushin iyaye. Idan aljanun ne a kanta, zan sauke mata su daya bayan daya, kai ko kukar mulukiya ce a kanta sai na sare ta.”

Kasan bishiyar dalbejiyar inda suke zaune, ya yi shiru kamar ba kowa. Dukkansu abun ya zo masu da mamaki, rashin walwalar Fatima yau, sun dauka dai halin nata ne ya motsa, take ta kunci. Basu dauka wani abu ne mai girma ya faru haka ba.

” Uhhhh! Hu’ummm!! Ai Mama hakuri kawai za ki yi, kin san wacece Fatima, tun da ta ce Mustafa idan za a tara Katsina gaba daya da makotanta, ba za ta taba canjawa ba.” cewar Aunty Hauwa tana kallon Mama.

Kafin Mama ta ce wani abu Aunty Ayyo (Maryam) ta amshe” Wannan gaskiya ne Aunty, Fatima tana da tauri kamar ganda, idan dai ta  ce yes, to a yes din nan za ka same ta komai kunci. Sai dai idan yes dinta ya ci karo da addini.”

“To wai yaushe ma suka fara soyayyar ne ita da Ya Mustafa din?” Aunty Aisha ta tambaya hannunta a kan habarta. Alamun mamaki.

Wannan karon Mama ce ta amshe “Babu wata soyayya wallahi, kawai ta shirya ne don ta bata min rai. Tun da ai ta san burina dai a yanzu baya wuce ta auri Jamilu.”

“To wai karatun fa?” cewar Aunty Sadiya da take kwance a kan tabarma tana shayar da yarinyarta.

“Ai ba ta karatun take yi ba. Burinta dai kawai ta ga ta baƙanta min ta kaucewa zabina.” cike da kunar zuciya Mama ta dire Maganar.

“Kayya Mama! Ki daina cewa Fatima don ta bata miki ta yi haka. Ku har yau kun kasa fahimtarta. Ita fa yar ra’ayi ce. Jamilu bai taba furta kalmar so wa Fatima ba. Hasalima bassa shan inuwa daya. Amma Mama kin dage ke sai ta aure shi. Yana da ra’ayinta ba shi da ra’ayinta ke dai kawai ya aure ta. Shi zai iya auran nata a hakan. Amma wallahi ni dama na san Fatima zai wahala ta aure shi, a dai yadda kike nuna mata dole ne sai ta aure shin. Dama dai lallashinta kika rika yi, maimakon nuna mata dole sai shi din, saboda shi ne kawai zai iya hakurin zama da ita. So ita kuma gani take yi, kamar bai sonta kawai zai aureta ne saboda ke. Sannan da gaske ya aureta ne don babu wanda zai iya auran ta.” Cewar Aunty a lokacin da take tashi zaune.

“To lauyarta. Ai daman na san duk bakinku daya. Idan ma an ce hada baki kuka yi ai ba zan yi gardama ba. Tun da ai a gidanki suke haduwa. Fatiman uwata ce da zan lallabata don ina bukatar abu a wurin ta. Idan ta auri Jamilu ai gata na yi mata.”

“Kin san yaran zamani ai Mama sai da lallashi.” Aunty Aisha ta fada cikin raha.

“To ni ba zan lallashetan ba, Mustafa kuma ta je tai ta auran shi. Idan dai aure bai kawo ta ba, saki ai ya kawo ta.”

“Fatan Alkairi dai Mama.” Cewar Aunty Ayyo.

“Fatima!” Aunty Hauwa ta kwala mata kira.

Ba ta amsa ba, illa ta fito fuskar nan kamar yaƙi ya riga ta ƙofar gida.  Duk suka bi ta da kallo idan ka dauke Mama da ta ƙara haɗe fuska ita ma.

Wuri ta samu akan tabarmar ta zauna.

“Fatima da gaske auran kike so?” cewar Aunty Hauwa cikin taushin murya.

Kai ta daga alamar eh.

“To karatun fa?” Aunty ta tambaya ita ma.

“Zan yi.” Ta amsa ta.

“Shi Mustafan ya amince da hakan?”

Kai ta dagawa Aunty Sadiya alamar Eh.

“To amma Jamilun fa?”

“Wai Aunty Hauwa a kan me zan auri Ya Jamil ne? Mutumin da bai taba furta min kalmar so ko alamun so ba. Tallata fa ake kai mishi.”

“Uban waye ke kai mishi  tallar kin?” Mama ta café.

“Amma Mama dai ai kin san cusa mishi ni kike yi. A gida daya fa muke kwana, ki bari mana da kanshi ya fada min yana sona. Amma ba ki yi ta cusa mishi ni yana kaucewa ba.”

“Ke ba ki da hankali, amma wallahi ni na san Jamilu yana sonki, kuma da kin aure shi da kin tabbatar da hakan.” Cewar Mama tana kallon Fatiman.

“Ni gaskiya baya sona, idan kana son abu ba ka iya boyewa.”

“To ki je ki auri Mustafan, ba baki na yi miki ba, amma za ki yi dana sani.”

“A’a Mama don Allah ki daina cewa haka.” Aunty Sadiya ta kuma fada a ladabce.

“Na ce din. Ba ta yi min daidai ba ta ya za ta ga daidai.”

“Fisabilillahi Mama me na yi? Kawai fa na ki auran Ya Jamil ne da bai taba nuna yana sona ba.”

“Ke rufe min baki kafin in yi miki shegen duka. Ubanki da na aura cewa ya yi yana sona?”

“Zamaninku da namu ba daya ba Mama, namiji ma ya ce yana sonka ya kuka kare, bare ace cusa mishi kai aka yi. Yana kallon auranka da ya yi alfarma ya yi ma. Maganar gaskiya ba zan auri Ya Jamil ba, ya rika kallon alfarma ya yi min da ya aure ni.”

“To don ubanki kada ki aure shi din. Ki ga ko zai mutu bai yi aure ba.” Mama ta fada a zafafe lokaci daya kuma ta yi kan Fatima da zummar dukan ta.

Cikin hanzari Fatima ta mike haɗe da yin hanyar kofar gida. Mama ta dora “Ni za ki fadawa zamani? Lallai Fatima wuyanki ya isa yanka. To ki je ki auri Mustafa, idan ma har da yan gidansu za ki aura bismillah. Amma wallahi…”

“Wallahi me? Hajara sau nawa zan fada miki kada ki yiwa yarinyata baki? Ranki zai fi na yanzu baci Hajara.” cewar Alhaji da ya shigo gidan.

Duk ya bi yaran da kallo, kafin ya ce ku zo nan ina son ganinku, har da Fatiman.”

Jiki a mace suka bi bayan shi.

Basu jima da zama ba Jamil ya shigo.

Shi ma gefe ya koma ya zauna hade da sadda kansa kasa.

Bayan sallamar da Alhaji Musa ya yi masu, suka amsa sai ya dora da fadin” Abin da ya sa na ce ku zo shi ne. Jiya na yanke hukunci ba tare da na tuntubeku ba. Ni kuma abin da ya sa na yi hakan, gani na yi shi wanda ake magana a kan shi, shi ma dan gida ne.”

Ya dan nisa kadan sannan ya ci gaba” Jiya iyayen Mustafa sun zo wajena da maganar Mustafan yana son auran Fatima. Na tambayi Fatima ta amsa min cewa tana son shi. A iya sanin ban san Mustafa da wani mugun hali ba. Dalilin da ya sa kenan na amince tare da ba shi auran Fatima. Tun daga jiyan mahaifiyarku ke ta bacin rai, ta hana kowa sakat. Abin da nake son sani shin Mustafa yana da wani hali ne mara kyau, da bai cancanci a ba shi aure ba?”

Uffan babu wanda ya ce har sai da Alhaji ya kuma cewa, “Ina sauraronku.”

“To iya sanina da shi dai, ban san wani hali na shi mara kyau ba gaskiya.”

Cewar Aunty Hauwa a labdace.

“Ni ma dai haka.”  Aunty Ayyo ta fada a hankali. Dukkansu suka rika furta ni ma haka. Idan ka dauke Jamil da bai ce komai ba.

“Kai fa Jamilu, kai ne ke yawo, shin yana da matsala?”

Kai Jamil ya girgiza alamun a’a.

“To Alhamdulillahi ma sha Allah. Haka ake so. Bari in dawo kanka Jamilu.” Cewar Alhaji bayan ya tattara hankalinsa a kan Jamilun.

“Na san ba ka san lokaci da ka dawo gidan nan da zama ba. Tun daga kuma wannan lokacin har zuwa yanzu, wallahi Jamilu ko a zuciyata ban taba bambantaka da yaran da na haifa ba. Ba gori nake yi ma ba, maganar da zan yi ce ta kama da sai na yi hakan. Jamilu tun daga ranar da ka fara hankali zuwa yanzu da muke a nan, ka fada min, ka taba zuwa da bukata ban yi ma ba? “

Kai Jamil ya girgiza alamar a’a

“Bude baki za ka yi, ka yi min magana.”

“Ba ka taba ba Alhaji, ka yi min duk abin da uba ke yi wa yaransa. Ta dalilinka ban yi kukan maraici ba kamar yadda ban san dacinsa ba. Babu komai a tsakaninmu sai addu’a.”

“Ka taba yi min maganar kana son Fatima da aure?”

Nan ma kan ya girgiza alamar a’a.

“Bude baki za ka yi fa.”

“Ban taɓa ba gaskiya.”

“To ku dai kun ji ko?” Alhaji ya yi tambayar tare da kallon yaran na shi mata.

Bai jira amsarsu ba ya dora “Jamilu bai taba zuwar min da maganar yana son auran Fatima ba. Da Jamilu ya furta hakan, bana tursasawa yarana auran wanda basu da ra’ayi, amma tabbas da na yi hakan a kan Fatima. Don Jamilu ba zai nemi abu wurina ya rasa ba.”

Ya kuma nisawa ” Daga Jamilu har Fatima ba zan tursasu auran wanda basu da ra’ayi ba. Ba yau Jamilu da Fatima suke zaune a gidan nan ba. Idan suna son junansu zuwa yanzu kowa zai iya sani. To saboda wata bukata ko manufa ba zan daure kugun su zauna a bishiyar ma’aurata ba, bayan basu da bukatar hakan.”

“Ke Hauwa’u!” Alhaji ya kira sunanta.

Kai ta dago tare da kallon sa cikin girmamawa.

“Ki dauki yar’uwarki zuwa gidanki. Na danƙa miki ita amana, har zuwa ranar da za a lullubeta zuwa gidan mijinta.”

Kai ta shiga jijjigawa alamar gamsuwa da bayanin shi.

“Shi kenan. Idan kuma akwai mai magana to ya yi.”

Shiru kamar kowa ba zai ce komai ba, sai kuma Aunty Ayyo ta ce “To Alhaji karatunta fa?”

“Wannan kuma ita da Mustafan zasu yanke shawararsu.”

Alhaji ya amsa ta tare da kallon ta.

Shiru ya kuma ziyartar wajen.

“Idan ba komai, za ku iya tafiya.”

Kamar umarninshi suke jira kuwa, suka rika mikewa a hankali suna ficewa daga falon a sanyaye.

Daga nan ma sai ko wacce ta kama hanyar gidanta, saboda yadda zaman gidan ya zama ba dadi.

Fatima kuwa kaf kayan amfaninta  ta kwashe, zuwa gidan Aunty Hauwa.

*****

Tun lokacin da Fatima ta bi Aunty Hauwa, ko kofar gida ba ta kara lekowa ba, bare ta shiga asalin gidansu.

Ko wane lokaci tana  cikin gida, yanzu kam duk ta zama shiru-shiru, abin da kowa bai taba tsammani daga gare ta ba.

Safiyar laraba da misalin 10 am, kwance a karamin falon Aunty Hauwa kan 3 sitter, sama-sama bacci ke daukarta, kamar daga sama ta ji sallmar Mustafa.

A hankali ta bude idonta masu cike da bacci haɗe da dorasu a kansa.

Mikewa zaune ta yi. “Ina kwana?”

“Lafiya ƙalau. Fatan kina lafiya.”

“Alhamdulillahi” ta fada tare da jingina bayanta a jikin kujerar.

Kare mata kallo yake kamar yana son gano wani abu da ba daidai ba a jikinta.

“Fatima!”

“Na’am.” ta amsa shi a hankali.

Ya ja numfashi haɗe da fadin ” Yau kusan kwana biyar kenan, nake ta kokarin zuwa mu yi magana, amma na ƙasa.”

“Saboda me?” ta yi tambayar tare da kallon shi.

“Kunya nake ji. Yanzu ma sai da na hangi Aunty na tafiya aiki sannan na zo.”

Karamin murmushi suka yi a tare, lokaci daya kuma yana gyara zaman shi.

“Fatima anya ba zamu janye maganar nan ba kuwa?”

“Me ya sa?” ta yi saurin tambaya.

“Abubuwa da yawa. Saboda maganar nan kin ga yanzu ba kya gida, ban san me ya faru ba, amma Alhaji ya fada komai zan ji in dode kunnena, wannan ya tabbatar min da akwai matsala.”

Ganin ba ta da niyyar magana ya sa ya ci gaba

“Ba na son damuwa  Fatima, ba haka kike rayuwarki ba, amma saboda maganar duk kin yi laushi, ba zan iya, jure ganinki haka ba.”

Murmushi ta yi mai kama da yaƙe “Ban taba tunanin za ka sare da wuri ba haka. Kar ka wani damu da ni, ina lafiya. Me Alhaji ya ce ma.”

Nisawa ya yi lokaci daya kuma yana mamakin yadda take kokarin shanye damuwarta.

“Ya ce in zabi lokacin da nake so a daura mana aure. Sai kuma batun karatunki.”

“Me ka ce kai kuma?” ta kuma tambaya idanunta a, kansa.

“Ce mishi na yi auran bayan sallah, kin ga nan da wata uku kenan.”

Kai ta jinjina alamar gamsuwa.

“Maganar karatu kuma na ce mishi ba zan hana ki cika burinki ba, zan zama tamkar tsani da za ki taka zuwa cika burinki.”

“Na gode.” ta fada a hankali.

Ya bi ta da kallon mamakin  canjawar da ta yi lokaci kankane. Ta yi sanyi da yawa, duk wannan rashin jin da rawar kan babu.

Sai ya ji sam bai ji dadin hakan ba, ta fi mishi kyau da halayenta na baya.

“Yaushe za ki koma gida?”

“Ban sani ba tukun.” ta amsa a hankali.

“Fatima!” ya kuma kiran sunanta cike da kulawa.

“Ba zan jure ganinki a wannan yanayin ba, zan sanarwa da Alhaji a bar maganar nan kawai.”

Bai jira cewarta ba ya mike hade da ficewa daga gidan.

<< Daga Karshe 12Daga Karshe 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×