Skip to content
Part 16 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Safiyar litinin Fatima ta shi ta yi jikin da sauki sosai, idan ka dauke rashin kwarin jiki.

Tun safe Mustafa ya zo duba ta, daga nan ya wuce makarantar da yake koyarwa.

Mama kuwa bacci kauracewa idonta ya yi. Ga tunanin Jamil ga rashin lafiyar Fatima, abun ya tsaya mata, ga ba Aunty Hauwa, ta yi tsammanin bayan sun dawo asibitin nan gidan zasu biyo Fatiman ta zauna, amma shiru kamar an aiki loma zagayar wuya.

Koda gari ma ya waye, hankalinta duk yana gidan Aunty Hauwar.

Ganin har 10am babu Mustafa babu Fatima, sai ta kasa hakura ta dauki hijabinta zuwa gidan.

A lokacin kuwa Fatima zaune take tana kallon film, kasancewar an tayar da inji.

Sama-sama ta rika jin maganar Mama, tare da Aunty A’i daga bisani kuma ta ji shiru, mikewa ta yi  zuwa tsakar gidan, babu Mama sai Aunty A’i da ke hadawa mai wanki kaya.

“Na ji kamar maganar Mama?”

“Eh ita ce, ta fita ma, dama ta zo neman Bilal ne, wai ya ce ba zai je makaranta ba, ta yi tunanin ko nan ya zo.” Cewar Aunty A’i tana ci gaba da yin abin da take yi.

Komawa Fatima ta yi ta zauna a kan kujera, ta yi shiru cike da tunani.

Da can idan ba ta da lafiya, to Mama ba ta taba samun natsuwa, idan ma ba a dakinta ta kwana ba, to kwana take yi zarya dakin Fatima game da taba jikinta.

Idan kuwa a dakin Mama ta kwana, motsi daya sai Mama ta tambaya, “Fatima jikin ne?” idan kuma shiru ba ta motsa din ba, nan ma sai Mama ta taba ta tare da tambayar, “Fati ko jikin ne?”

Amma a yau Mama ta ji labarin ba ta da lafiya har zasu je asibiti, amma ta zo har inda take ba tare da ta tambayi ina take ko ya ta kwana ba. Lallai borin namiji ne.

Hawayenta ta share, tare da kwanciya a kan kujerar, za ta ba Mama hakuri amma ba yanzun ba, har sai an yi auransu da Mustafa.

A duniya kaf ba ta da kamar Mama, yanzu haka ba ta jin dadin yin komai, saboda fushin da Maman ke yi.

Abin da ba ta sani ba shi ne, Mama ta ki leka inda take ne, saboda tun da ta shigo gidan, ta leka falon Aunty Hauwa ta window, kuma a nan ta ga Fatima zaune tana kallo, wannan ya tabbatar mata akwai sauki.

Sannan kuma yadda Aunty A’i ta yi shiru ba ta yi zancen ciwon Fatiman ba, ya kara tabbatar mata akwai sauki.

Tana fushi da Fatima saboda kafiyarta, amma kuma tana sonta, tana jiran ranar da za ta zo ne ta ba ta hakuri.

*****

Misalin karfe hudu na yamma su Aunty Hauwa suka iso, inda suka yada burki a gidan Mama.

Zainab ce kawai ta runtumo inda Fatima take.

Tana shigowa suka rungume juna cike da kewar juna.

Kafin daga bisani suka koma kan gadon Aunty Hauwa suka zauna a tare.

“Wai kawai na ji an ce za ki auri Ya Mustafa, ni ko na ce yaushe kuka fara soyayyar?”

Fatima ta yi dariya tana kallon Zainab “Yo sai an yi soyayya ake aure.”

“Heeee!” Zainab ta fada hade da fadawa kan gadon tana fadin “Don Allah ta ya za ki fara hada ido da Ya Mustafa a matsayin miji?”

Tare suka yi dariya, kafin Fatima ta ce wani abu Zainab ta kuma cewa “Wallahi na dauka Kawu Jamil za ki aura Goggo Fati.”

“Ban san Goggo nan fa ke ma kin sani, kamar wata tsohuwa.”

Suka yi dariya a tare kafin Fatima ta ce “Don Allah Ya Jamil fa, da zai tafi ya ya yi?”

Zainab ta mike zaune “Bawan Allah! Wallai ni dai har kuka na yi, shi ma ina jin ya yi kukan, kin ga ma sako ya ce in kawo miki.” ta karashe maganar lokacin da ta mike zuwa inda ta yada jakarta. Budewa ta yi hade da zaro envelope, wanda aka ci bakinsa da kalar blue and red, ta mika mata.

Filo kawai Fatima ta daga tare da tura envelope din.

“Ban san munafurci, ba za ki bude ba in gani.”

“To ai ke ce mai son munafurcin ba ni ba. Ina ruwan kallo da gajiya.” Cewar Fatima tana kara danne filon.

“Wai aka ce barayi sun shiga gidansu Aunty Lami?”

Zainab ta mike tsaye gabadaya bayan ta zaro ido hade da rike habarta

“Keee! Cire wai, wallahi mutuwa na gani tsirara in fada miki gaskiya. Na ce ina ma ke ce a gidan ba ni ba.”

Fatima ta kwashe dariya ta ce “Wallahi da ba zan san lokacin da zasu fita ba, saboda  suna shigowa zan suma. Zauna ki ba ni labari.”

“Wai ba ki ji labarin ba ke?” Zainab ta yi tambayar daidai tana zama.

“To wurin wa zan ji, uwata ce za ta fada min kuma fushi take yi da ni.”

“Ai in fada miki, misalin karfe biyu na dare, suka ta so maigadi da bindiga aradu har dakin Aunty, Allah ya taimake ni ina kwance a falo, daga ni sai wata doguwar riga, gai kaina gashi ya, mimmike  kin san ba abun. Aiko na ce masu ni yar aiki ce.”

Tare suka kwashe da dariya, kafin Fatima ta ce, ” Wallahi ni dama tsoron fyade nake yi.”

“Wallahi ni ma shi nai ta jin tsoro, suka kwashi kudin Aunty da sarkokinta da kudin maigidan suka tafi. Wai kin san abun dariya kuwa?” Cewar Zainab tana kuma kyakyacewa da dariya.

“Wai kawai Aunty ta bi bayansu, wai su taimaka mata da kudin da za ta hau mashin zuwa wajen aiki gobe.”

Fatima ido ta zaro alamun tsorata. Zainab kuwa, dariya take yi sosai, kafin ta ce “Suka wullo mata dari biyu, wai shegiya mayyar kudi, wani ya ce mata.”

Tare suka kara kwashewa da dariya Fatima na fadin “Kamar kuwa ya san ita din mayyar kudin ce fa.”

“Sai fa da ta sha ruwa, leda biyar a asibiti. Dalilin da ya sa kenan ba ta zo rakiya Kawu Jamil ba.” Cewar Zainab.

“Ita da Aunty Ayyo kam ban san wa ya fi son kudi ba.”

Zainab ta yi zaram ta ce, “Wallahi Aunty Ayyo. Aunty Ayyo na rakata gidan suna aka sace mata dari biyar, kafin mu iso gida zazzabi ya rufe ta.”

Suka kuma kwashewa da dariya, sannan Zainab ta ce,

“Mama za ta huce fa, kawai ba ta lokaci, amma ai ba za ta iya yin fushi mai tsawo da ke ba.”

Zama Fatima ta gyara tana fadin “Dazu fa har gidan nan ta zo, na rantse miki da Allah ko ta tambayi ya jikina, kuma ta san ba ni da lafiya fa.”

“Allah ita din ma ta damu, amma ki bar ni da ita, zan bugar miki ruwan cikinta.”

Shigowar su Aunty Hauwa ne ta sanya su mayar da hankalinsu akansu.

“Wallahi tun da na tafi hankalina yana akan gadona, ina can ina tausayin shi, saboda na san Fatima wuni za ta yi tumurmusar shi, idonta idon gado. To sai Allah jakka cikin dakin.” Cewar Aunty Hauwa a lokacin da take cire hijabinta.

“Kuma ita bari ki gani nata bayya hawuwa. Ido ga wani kuda kan ci naka.

” Yo aike dama Aunty Aisha ba kya taba min zaton alkairi, ba kya kuma taba fadin alkairi a kaina, ba tun yau ba na san zaman da nake yi da ke.” Cewar Fatima tana gyara kwanciyarta a kan gadon.

“Amma dai ai gaskiya na fada.”

“Dama bakin wasu shi ke ja masu dauri, ko gaskiyar ce ina ruwan ki, ki yi shiru mana. Idan na zama alkali idan ba Aunty A’i zan fara daurewa ba ku ce ba uwata ce ta haife ni ba.”

Aunty Ayyo da tun dazu ba ta ce komai ba ta ce, “Mai mugun nufi dai Allah ba ya cika mishi burin shi.”

“To ke ina ruwanki, na sanya da ke ne? To ku shaida Aunty Ayyo ce ta biyun daurewa.”

Wannan karon kam kowa dariya ya yi, kafin Aunty Hauwa ta ce “Wato zuwan Zainab kin yi baki kenan.”

“Ni dama can da bakina wallahi, kun kuma sani, kawai dai iya taku ne.”

“To Allah shi bi mamu mutuwar jikin da kika sanya mu ka yi.”

“Aunty Hauwa ke ce babba, don Allah kin ga lokacin da Mama take ba Aunty A’i nono?” cewar Fatima tana kallon inda Aunty Hauwan take

“Idan ban gani ba me ye?”

“Sai in ce rikonta ake yi, saboda abin da take min.”

“Ke me ye ba ki yi min ba Fatima, ko don doki mai baki ya fi gudu. Har gidana kika je, kika yi min fatan kishiya.”

“Amma kuma ai kin yi min bugun mutuwa ko? Wallahi ko uwata ba ta yi min dukan da baiwar Allahn nan ta yi min ba.”

Fita Aunty Aisha ta yi tana dariya.

Yayin da Fatima ta dora da “Wallahi kahirin bugu ta yi min.”

Aunty Ayyo ma ta mike tana fadin “Zainu za a koma Katsinan ne?”

Aunty Hauwa ta kece da dariya, Zainab kuma ta ce

“Ai Aunty Ayyo an yi kenan auran wata da wani, ba yaji ba ganin gida. Ni Katsina ko a mafarki.”

Aunty Ayyo ma dariya take yi kafin ta ce “Ranar dai na so ace ina nan, ka ji tsantsar Katsinanci wurin Aunty Lami.”

Cikin dariya Aunty Hauwa ta ce, “Ki ji tana cewa billahillazi kadan ya hana in yi zawo, kudina hwa kaf suka tsince min, kai na rantse da Allah na ga tashin hankali.”

Aunty Ayyo dariya take yi a lokacin da ta fita, su Fatima ma dariyar suke yi.

“Wash Allahna! Wallai na gaji” cewar Aunty Hauwa a lokacin da take mikewa tsaye.

“Yo Aunty tururuwa ma ta yi jeran banza, bare ranar garar yarta. Haka nan ma fada kike yi kin gaji bare kin je kano.” Cewar Fatima a lokacin da ta gyara kwanciyarta.

“Ke tashi ku koma can dakinku, ni ma ko na yi tusa mai karfi a dakina, haba ina dalili an zo an dame ni.”

Kora su Fatima ta yi zuwa waje, ta tura kofar ta.

*****

Dawowar Zainab sai Fatima ta koma normal, duk wannan yawan damuwar babu.

Har islamiya sai da Zainab din ta rika jan ta, sosai Mustafa ke ba ta mamaki, saboda yadda yake nuna kamar ba komai a tsakaninsu.

Dalilin da yasa kenan ita ma ta rika kamewa, abu daya ne ta rage yawan tsokanar dalibai da su kansu malaman.

Gidan Mama kuwa ba ta zuwa sai ranar da Alhaji ya zo, abun da yake matukar batawa Mama rai, shi ya sa idan ta shigo sai ta yi banza da ita.

Kamar yau ma da ya kasance juma’ar karshen wata. juma’ar da ta kasance daga ita sai ta azumi.

Iyalan Alhaji duk suna gidan, har da Aunty Lami, sun kawo mishi kayan daukar azumi.

Fatima ba ta shigo gidan ba sai da aka sakko masallaci, tana sane ta ki yin sallama, sai dai kawai suka ganta a kansu.

Aunty Lami ce ta fara cewa, “Ke hala ba ki iya sallama ba. Ko kurma ce? Sai kawai ki hwadowa mutane uwa gini.”

“Na yi fa.”

“A gidan ubanwa kika yi ta, ina nan dai kwance, idan kin yi ni ce zan hwara ji ai.” Cewar Aunty Lami a lokacin da ta tashi zaune.

“To ji kike yi sosai Aunty Lami.”

“Ban ji sai ke hala, wannan kunnuwan nawa na banza ne? “

Fatima dai ba ta tanka ta ba, ta wuce bangaren Alhaji.

Aunty Sadiya ta tuntsire da dariya, tana kallon Aunty Lami da ke ta masifa ita kadai.

A can kuwa Mama ce tsaye suna magana da Alhaji, da alama fita za ta yi daga falon.

Ta amsa sallamar Fatima ba tare da ta kalle ta ba.

“Ina wuni Mama.”

“Da ban wuni ba kin ganni.”

Alhaji ya dan murmusa, “wai har yanzu fushin ne?”

“Yarinyar nan fa idan ka ganta a gidan nan, to kai ne ka zo. Amma ni dai ban isa ta zo ta gaishe ni ba.”

“Wai haka Fati?”

“Ko na zo fa ba ta yi min magana.”

“To kin ji.”

Shiru Mama ta yi ba ta tankasu ba, yayin da Fatima ta shiga gaishe da Alhaji.

Bayan sun gama gaisawa ne, ya mika mata wasu takardu, yana fadin “Result naku ne ke da Zainab, yau na biya na karbo maku.”

Farin ciki ya bayyana a fuskar Fatima, cikin murna ta karbi results din tana dubawa, ganin yadda ya yi kyau, sai ta kwasa da gudu zuwa inda yan’uwanta suke.

Lokaci daya gidan ya rude da hayaniya, musamman da Zainab ta shigo.

Da ihu ta amshe takardun ta yi gida aguje, don nunawa Aunty Hauwa, kasancewar ba ta a gidan.

“Su wance an yi abun kai fitsari da kumfa.” cewar Aunty Aisha tana zunden Fatima da ta juya baya suna magana da Aunty Lami.

Aunty Ayyo da Aunty Sadiya suka tuntsire da dariya.

Sai a lokacin Fatima ta juyo tana kallon su “Me Aunty Aisha ta ce don Allah. Ke dai Aunty Sadiya na san ba a munafurci da ke.”

Aunty Lami ta yi caraf ta ce “ai ni zan hidi ba a munahicci da Sadiya, ni da ta tonawa asiri a gaban kishiya. Kai Subhanallah wannan yarinya ranar ta ba ni haushi aradu.”

Duk suka yi dariya yayin da Fatima ta ce” Allah Aunty Aisha ma haka take.”

“Yarinyar nan fa ganinta take yi daidai da ni wallahi.”

Ficewa Fatima ta yi ba ta amsata ba, yayin da Aisha ta kuma cewa “Nan da sati shidda dai masu zuwa mun kai ki gidan Mustafa.”

Fatima dai tuni ta riga ta fita.

Cin karo suka yi da Mustafa a zaure na biyu, da alama wajen Alhaji ya zo.

Gefe ta koma, lokaci daya kuma tana gaishe shi.

“Bakin ki da magana.” ya yi maganar bayan ya amsa gaisuwarta

Sai ko ta kara wangale bakin hade da sanya tafukan hannunta ta rufe fuskarta.

“Ba ni labari”

Siririyar dariya ta yi kafin ta ce, “Alhaji ya karbo min result dina, sosai ya yi kyau.”

“Eh lallai dole ki yi farin ciki, ni kaina na taya ki murna. Menene burinki?”

Tsayuwarta ta gyara sannan ta ce “In zama likita ko principal.”

Ya dan murmusa kadan”Buri mai kyau, in sha Allah zan yi kokarin wurin ganin kin cika burin nan Fatima. Ina son in yi miki wani abu da zan ji ni ma na yi miki abin da ya dace. Ko wane lokaci ina mamaki sosai wai za ki zama matata. Ni dai har yanzu ban yarda ba.”

“Saboda me? ” ta tambaye shi ba tare da ta kalle shi ba.

“Gani nake yi ban isa ba, kin fi karfina.”

“Hmmm!”

Abin da ta ta ce kenan.

“Idan kuma ya kasance, zan yi kokarin ganin ba ki rasa komai ba, sannan ba ki nemi komai ba.”

“Allah ya ba ka iko.”

“Amin” ya amsa a hankali, da alama tunanin wani abu yake yi.

“Shi kenan, ki je an jima zan zo in ga result din?”

“Allah ya kawo ka.”

“Amin” ya kuma fada, a lokacin da yake shigewa cikin gidan.

Ita ma gidan Aunty Hauwa ta nufa zuciyarta fes, kamar farar takarda.

<< Daga Karshe 15Daga Karshe 17 >>

2 thoughts on “Daga Karshe 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×