Skip to content
Part 17 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Kamar yadda ake ta shirye-shiryen auran Fatima ta ko wane bangare, haka Zainab ma ake mata fafutukar wucewa Jami’ar Alkalam da ke katsina.

Microbiology ta cika, kuma cikin ikon Allah ta samu.

A bangaren Fatima kuwa duka-duka bai fi saura sati hudu bikinta ba. kasancewar an shiga sati biyu da azumi.

Mustafa tun da Allah ya sa Alhaji ya ce ya mallaka mishi Fatima, iyakar bakin kokarin shi yi yake wajen ganin ba ta yi kukan komai ba.

Yan kayan kwalliya masu kyau ya sawo ya aiko mata, yan kudin kashewa ya aiko mata.

Ko yanzun ma da bikin ya rage saura kwanaki kadan, bai daina ba. Ba kamar yanzu da ake azumi, duk bayan kwana biyu sai ya aiko mata da fruit da kayan tea.

Fatima tana jin dadin kyaututtukan na Mustafa sosai.

kwance take a tsakiyar babban falon Aunty Hauwa, iskar fanka na kadata, duk hayaniyar da yaran gidan suke yi tana jin su. Wasu har taka ta suke yi, amma uffan ba ta ce masu ba.

Zainab ta shigo dauke da yaron Aunty A’i ta zauna kusa da Fatima tana yi masa wasa.

“Ke har ma kina da ƙwarin gwiwar yi wa yaro wasa.” cewar Fatima tana kallon Zainab.

“Ni fa azumi daga 10am zuwa 12pm ne yake ba ni wahala, daga na kuma sai 6pm to shan ruwa. To ina yarawa.”

“Tabbb! Ai ni kullum azumi wuya yake ba ni.”

Zainab ta yi guntuwar dariya tana kallon agogon da ke manne a falon.

“Kuma fa uku saura.”

Fatima ta yi saurin ta shi zaune tana fadin “Allah Rahimi in ji Hauwa, Ayyo ta ce. Wai har yanzun ma uku ba ta yi ba? Ni fa kin ganni ko ma agogo bana kallo. Saboda gani nake sam lokacin baya tafiya.”

“Ni wallahi har ma kin tuna min Aunty Lami. Ita ce lokacin da na je hutun nan, abu kadan sai ta ce, Allah Rahimi in ji Hauwa, Ayyo ta ce in ji Fatima.”

Duk irin yunwar da Fatima take ji sai da ta tuntsire da dariya.

“Kai Allah ya kyauta, sai ka ce wani hadisi, wai in ji Aunty Hauwa, Ayyo ta ce in ji Fatima.” ta karasa maganar tata da wata sabuwar dariyar.

Zainab ma dariya ta yi sannan ta ce, “To ai gaskiyarta, Aunty Hauwan ce dai an yi abu sai ta ce Allah Rahimi.”

“To ita kuma Aunty Ayyo sai ta karbe, da an yi abu ita ma sai ta ce Allah Rahimi in ji Aunty Hauwa.” cewar Fatima da take kwance.

“To ke kuma abin da ya sa kika shigo, saboda ke ce mai cewa In ji Aunty Ayyo.” cewar Zainab tana dariya.

“To shi ne ita kuma sai ta ce ni ce na ce?”

“Eh mana.” Zainab ta amsa.

Cikin dariya Fatima ta ce, “To Allah ya Rahimi in ji Aunty Hauwa, Aunty Ayyo ta ce.”

A tare suka yi dariya Zainab kuma ta ce, “In ji Fatima ta ce.”

Da wannan hirar suka tashi don gabatar da sallahr la’asar.

Daga nan kuma suka kitchen don aikin abincin shan ruwa, idan dai azumi ya zo to su Aunty Hauwa hade aiki suke yi, sai azumi ya wuce sannan a koma tsarin da na kwana bibbiyu.

Haka abubuwa suka ci gaba da wakana har zuwa satin sallah. Inda Mustafa ya aikowa da Fatima kayan sallah, son kowa kin wanda bai samu ba.

Lace ne dark blue da yarfin farar fulawa, dinkin riga da zane, sosai dinkin ya yi kyau.

Sai atamfa quali wax mai kyau ita ma din kin riga da zane, hijab daya da, babban mayafi, sai tarkaceen kayan kwalliya, sarka da yan hannu. Da kuma takalma kala biyu hill da kuma flat.

Sosai kowa ya ji dadin hidimar da Mustafan ya yi, duk da ba, wani samu yake yi ba, amma hakan bai hana shi yin bajinta da fitar da Fatima kunya ba.

Hatta Mama ta ji dadi ta kuma yaba, duk da ko lallen kunshi ba ta siyawa Fatin ba.

Abin da ya tsayawa Fatima uwa kashin wuya. Shi ya sa ita ma har aka gama sallahr ba ta shiga gidan ba.

Alhaji ma a barga ta je ta yi mishi barka da sallah.

Mustafa kuwa har da kajinshi biyu ya aiko mata wai naman sallah.

Sallah na yin baya aka fara shirye-shiryen bikin Fatima, yayin da Zainab ta ce ba za ta tafi makaranta ba sai an gama bikin Fatin.

Abu kamar wasa yana neman zama gaske, don kuwa yan’uwan Fatima maza da mata sun yi rawar gani, ya rage saura sati daya biki, tuni sun kammala duk wani kayan aure tun daga furnitures har kayan kitchen.

Baba kuwa keken dinki da katon Generator ya siya mata, kasancewar yaranshi sun gama komai na auran. Sannan ya zabi saniya guda daya, ya ce kyauta ce a wurin Fatima.

A bangaren Mustafa ma sha Allah. Don kuwa ya gyare bangare daya a gidansu, da yake gidan kato ne. Gini ne ya yi irin dai na cikin garin Sandamu, room and palour manya-manya da toilet a ciki. Sai doguwar baranda a waje, wacce ta hada da katon kitchen din Fatima mai store a ciki.

Akwai toilet a waje da kuma single room kato mai kama da sitting room. Bangaren nata a shafe yake da siminti lukui, akwai fulawoyi masu kyau da aka shuka a gaban barandar tata, da kuma wasu da suka zagaye katangar ginin nata.

Duk wanda ya shiga bangaren nata sai ya yi sha’awar ina ma shi ne zai rayu a wajen shi kadai cikin salama.

A bangaren su Fatima ma duk sun gayyaci kawayensu. Kasancewar Fatima ce za ta fara aure a cikinsu, dukkansu dokin abun suke yi, tare da ci mishi buri mai yawa.

Ana saura kwana uku daurin aure aka kawo lefe, akwatuna biyar shake da kaya masu kyau da tsada ba laifi. A ranar kuma yayyu Fatima mata suka hau soye-soyen biki.

Ga baki na nesa sun fara zuwa, gidan Mama ya fara cika, yayin da gidan Aunty Hauwa ma yake cike da kawayen Fatima na cikin gari.

Komai dai yana tafiya daidai.

Ana gobe daurin aure suka tafi Daura gyaran kai da kunshi da kuma dilke.

Basu dawo ba, sai bayan isha’i, a lokacin kuwa yan’uwanta mata ne ke ta chashewa da DJ a farfajiyar gidan Aunty Hauwa.

Kawaye basu huta ba, suka fada aka ci gaba da chashewa dasu, Fatima ma tun tana baya-baya har ta saki jiki ita ma ta cashe.

Basu tashi ba sai 12am shi ma sai da Alhaji ya aiko ya ce ayi hakuri haka nan.

*****

Ranar daurin aure kuwa kowa hidimar shi ta sha mishi kai, bangaren ango da na amarya, kowa kokarin fita kunyar bakin da ya gayyato yake yi.

Bangaren Fatima Zainab ce ba ta huta ba, kawayen sun tasarwa 15 baki kawai ban da na cikin gari.

Amma duk da haka sun yi kokarin fita kunyarsu ta ko wane bangare.

Misalin karfe biyu na ranar Juma’ar shekarar 2008 dubban mutane suka shaida daurin auran Fatima da Almustapha.

Auran da ya zo ma kowa da mamaki, musamman Fatima da Mustafa, kamar da wasa suka fara maganar ga shi ta tabbata.

Misalin karfe hudu, mai amada (kidin kwarya) ta warware tata tabarmar a tsakar gidan Mama ita da bataliyarta.

Haka duk kawayen amarya suka kwashe zuwa gidan Mama, aka bar Fatima ita kadai a gidan Aunty Hauwa.

Lokaci zuwa lokaci dai sukan leko su ba ta labarin abin da yake faruwa su koma.

Sai misalin karfe biyar na yamma, Aunty Lami da Aunty A’ita zo ta shiryata cikin wani fari kal din lace, farar jaka da farin takalmi, hatta dambareriyar sarkar wuyanta fara ce, agogo fari, komai na jikinta fari ne.

Ta yafa mata ashobe fari da farin gwaggwaro, sannan ta kamo hannunta zuwa gidan Mama.

Ai take gidan ya kara kacemawa da sowa hade gude-gude, mai kida ma ta canja salon kida da wakarta, yayin da kudi suka rika shawagi a tsakiyar filin.

Fatima wani irin dadi da kaunar yan’uwanta take ji. Ji take ina ma kar lokacin ya wuce, tana son ta ga ana nishadi. Musamman mawakiyar da take ta wasata cikin wakarta, cewa take

“Bikin yar gata mu ka zo mu kwashi taushe.”

Amshi “Mandula”

“Bikin mara gata sai dai asha kubewa.”

“Mandula.”

“Sai da ta lalubo ta lalubo kuma sai da ta lalubo dankirki.”

“sai da ya lalubo ya lalubo kuma sai da ya lalubo yar dangi.”

“Bikin yar gata naira ake rabawa.”

“Mandula.”

“Hajiya Hauwa kin ba ni kin dada min.”

“Mandula”

“Uwar amarya Zuwaira Allah bar ki lafiya lau…”

Haka aka ci gaba da cashewa, har bayan isha’i, lokacin da dangin ango suka taho da tasu tawagar rokon amarya. Wata al’ada ce da ake yi a kasar Hausa, musamman yankin Katsina.

Ranar daurin aure da dare dangin ango zasu zo gidansu amarya suna waka, to da sun shigo dangin amarya sun san cewa rokon amarya suka zo. Ma’ana sun zo daukar amarya ne. Saboda haka ko me ake yi dole a lalubo amarya a shiryata a mika masu.

Idan ma basu zo ba, to amarya ba ta zuwa ko ina, sai ace yan rokon amarya basu zo ba.

Kamar yadda al’adar ta tanadar, cikin gida suka shigo daga kofa suna waka kamar haka…

“Rabo yay rabo Allah ya yi sai a bamu

” Rabo yay rabo Allah mai rabawa.”

” Ku bamu saniya zamu hada da san garinmu.”

“Da ke uwar diya tashi ki wanke ki bamu.”

“Da ke masokiya allurarki ta ji kunya.”

“Da ke masokiya ruburbudin wutar kiyama.”

“Da dare mu ka zo kar mu koma da rana”

“A da takuce yanzun baaa taku ce ba.”

“Da yar gidanku ce,
yanzun ba yar gidanku ce ba. “

“Da yar gidanku ce, yanzun sai dai ta zo da yawo.”

“Farin kallabi maza ka wale ka walwalesu.”

“Farin kallabi kyau da amarya kyau da ango.”

Jin wannan waka tasa aka janye Fatima, domin shiryata tare da mikawa dangin mijinta ita. Kamar yadda al’adar ta tanadar.

Ba jimawa aka shiryata cikin atamfa mai kyau, tare da fesa mata turarurruka masu kamshi, aka lulluba mata zanen atamfar.

Sannan aka shiga da ita wajen Alhaji, fada ya yi mata sosai hade da nasihohi masu ratsa jiki.

Dama su Aunty Hauwa tun suna shiryata suke ta yi.

Take jikinta ya mutu, ta yi likis kamar fulawar yin burodi.

Daga dakin Alhaji aka ratso da ita tsakar gidan, inda ake ta cashewa da kidan kwarya, su kansu dangin ango sun shige fili suna ta rawa ana gude-gude, masu barin baki na yi. Kun san dai taron mata.

Suna shiga dakin Mama, Fatima ji ta yi da kyar take cira kafarta, wata irin kewa ta rabuwa da mahaifa ta kara kamata, tana son gida, shi ya sa ko huta ba ta iya zuwa. Daga gida sai gidan Aunty Hauwa, gidan Aunty Hauwar ma saboda ko ihu mai kwari ta yi za a ji ta a gida.

Mama da ta juya baya suna magana da wata yar’uwarta, sai ta ji kawai an fado mata, lokaci daya kuma an fashe da kuka. Irin kukan nan da ke nuna mutum yana cikin wani irin shauki na rabuwa da abin da yake so.

Take jikin Mama ya yi sanyi, lokaci daya ta juyo hade da rungume Fatima tsam a kirjinta. Hawaye masu dumi suka shiga sakko mata.

Tun tana yi a boye har ya fara fitawo, Fatima ma kuka take yi kamar an fada mata tana tafiya Maman za ta mutu.

“Mama don Allah ki yafe min, ki sanya min albarka, ban zabi Mustafa don in bakanta miki ba. Don Allah ki daina fushi da ni.” cikin kuka Fatima ke magana

Mama ma cikin muryar kuka ta ce “Fatima na yafe miki, Allah ya yi miki albarka, ya albarkaci auranki da zuriyar da za ki samu. Allah ya baku zaman lafiya ke da mijinki. Ki yi ta hakuri kin ji, gidan miji ba gidan Babanki ba ne Fatima. Ki koyi adana sirrinki da na mijinki, yan’uwanki sune abokan shawararki kin ji. Uwar mijinki ki rike ta kamar ni don Allah.” Ta karasa maganar tata cikin wani sabon kukan.

Sautin kukan Fatima ya karu a lokacin da dakin ya rude, nasihar da mutane suke mata, kowa da abun da yake fada, su Aunty Hauwa kuwa tuni an fara matsar hawaye.

Zainab ma kuka take yi kamar an ce mata Fatima ta mutu.

Da kyar aka yage ta daga jikin Mama zuwa waje, inda aka dankata a hannun yayar Innarsu Mustafa. Sai a lokacin yan rakiyar amarya suka bi bayansu.

Kamar yadda Alhaji ya umurta haka din ne ya faru, da kafa Fatima ta taka har dakin mijinta. Yayin da zugar mata yan rakiya, yan mata gami da kananun yara suka dafa mata baya.

Bakinta dauke da addu’a har aka dorata a bakin gadonta, da ya sha lutsetsiyar katifa.

Aunty Lami ta zauna kusa da ita tana fadin “To Fatima, ga dai katifwa nan an samu, sai ai ta hawa ana tsalle, ba mai miki hwada, yadda kika so haka, za ki yi.”

Wadanda suka ji me Aunty Lamin ta fada suka kwashe da dariya hade da yin guda.

Ita dai Fatima kukanta kawai take yi, ji take kamar ta ce ta fasa.

Misalin karfe goma na dare gidan ya zama shiru tamkar ba kowa.

Duk gayyar mutanen da suka rako Fatima ba kowa, hatta kawaye sun koma gidan Mama.

Saboda Alhaji cewa ya yi bai so a baro kowa. Ana kai amarya kowa ya dawo gida.

Fatima zaune shiru, mamakin take yi, wai ta yi aure da Mustafa nan ma dakinsu ne.

“Ikon Allah mai tsaida wando ba zariya.” ta ce a hankali hade da rike haba alamun mamaki.

Ni kuma cewa na yi

“Allah Rahimi in ji Aunty Hauwa, Aunty Ayyo ta ce in ji Fatima.”

Ni ma na dan dana.

<< Daga Karshe 16Daga Karshe 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
1
Free daily stories remaining!
×