Biki bidiri birede yau ake gobe sai labari, yau dai ga Fatima ta kwana a gidan Mustafa, kamar almara. Ta kwana a matsayin matarsa, shi kuma a matsayin mijinta.
Abin da ko mafarkin shi bai taba ba shi ba.
Duk lokacin da ya kalli tsaunin dukiyar da aka dankawa Fatima, sai jikin shi ya mutu, ya ji kamar ba shi da abin da zai iya ciyar da mai wannan dukiyar.
Amma yana addu'a Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da ke kansa.
Yau gidansu Mustafa kin yankewa ya yi da mutane, har aka yi magriba, kawayen Fatima da. . .