Kamar ko wace ranar Juma'a idan Alhaji ya zo gidan yake kasancewa a cike, da yaya da kuma jikoki, wannan lokacin ma hakan yake a cike.
Shigowar Fatima yasa gidan ya barke da hayaniyar ganinta, ita kam wangale baki kawai take yi, yayin da Mustafa tuni ya shige wajen Alhaji.
Su Aunty Aisha sai tsokanarta suke, ita kanta Mama bakinta ya kasa rufuwa, sai murmushi take yi, cike da jin dadin ganin yadda Fatiman ta canja a cikin sati hudu kacal.
Ta murje ta yi haske, jikinta ya kara mulmulewa gwanin sha'awa. Lokacin da ta shiga bangaren Alhajin. . .