Yadda ta bar dakin haka ta same ta, ba ta bata lokaci ba ta shiga gyarawa cikin sa'a daya, ta gyare dakin tsab, kafin ta fito zuwa dakin mama da take zaune tana hada lissafi,
"Ina kwana Mama?"
"Sai yanzu ne kika ganni? To ni ma ban ga kwanan ba."
Ta marairace,
"ki yi hakuri, dazu na gan ki tare da wancan dan sa'idon ne."
"Waye dan sa'ido?" Mama ta tambaya hade da kallonta cikin daure fuska.
"Ki yi hakuri" Fatima ta kuma fada a karo na biyu.
"Ke bana jin dadin yadda kika dauki Jamilu, kodayake. . .