Skip to content
Part 21 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Lokacin da Mustafa ya koma makaranta don ci gaba da karatunshi na Zango na biyu.

Hankalinsa a kwance yake, duk da an ce mutum baya rasa matsala, shi dai a lokacin da za ace ya fadi wani abu da yake kwana da shi ya kuma tashi da shi, ba zai wuce cikin Fatima ba, bayan nan ba shi da wata matsala.

Kullum addu’ar shi da fatan shi, baya wuce na Allah ya sauke ta lafiya. Ba shi ne kadai yake wannan addu’ar ba a kullum, akwai Mama, Alhaji, Inna da kuma sauran yan’uwan Fatima.

Ita kuwa uwar gayyar ko a jikinta, cikin bai taba tayar mata da hankali ba, harkar gabanta kawai take yi. Ko maganin zaki na gargajiya sai Inna ta matsa sannan take shan shi.

Wani abu nauyin ciki duk ba ta san shi ba. Motsin cikin ma sai da ya girma sosai sannan take ganewa. Can baya ma tsoro take ji, duk da dai ba ta fadawa kowa tana jin tsoron ba.

Rayuwarsu gwanin sha’awa, cike da girmama juna, musamman tsakanin Inna da Fatima, da kuma Ummi da ke makarantar secondary aji shida a day Sandamu.

Da yawan mutane sun dauka idan Fatima za ta haihu, ba iya Sandamu ba, hatta kauyukan gefen Sandamu sai sun sani, sai ga shi cikin ikon Allah, ana kwada kiran sallahr asubar ranar juma’a Fatima ta duro diyarta mace lafiyayya zuwa cikin duniyar mu, ta sha wahala kam, amma kuma ta yi dariya sosai.

Daga ita sai Inna da kuma tsohuwar da Innar ta kira. Ba karamin mamaki kowa yake yi ba, idan aka aika mishi da sakon haihuwar Fatima. Mustafa kuwa, da kyar ya yi sallahr asuba, yana idarwa ya dakko hanyar gida. Zainab ma wacce tun ta tafi ba ta zo Sandamu ba, a ranar ta baro Katsina ta yo gida.

Zuwa karfe takwas an gyare ko ina, maijego da jaririyarta. Dakin sai kamshin turaren wuta yake. Duk yadda Fatima ke jin bacci ta samu damar yi ba, saboda sai ka rantse da Allah a ranar ake suna. Zainab kam tun da ta iso ta kasa ta tsare, Baby na hannunta, hannun karba, hannun mayarwa ake yi. Idan ta je hannun Fatima to nona aka matsawa Fatiman ta ba ta.

Duk yadda Mustafa ya iso da wuri, bai samu kebewa da Fatima sai takwas na dare.

A lokacin kuwa har ta fara bacci, shigowarsa ta sanya ta bude ido, tana kallon sa ta hasken fitilar da ke cikin dakin. Amma ba ta motsa ba. Ganin ya nufo inda take kwance, sai ta lumshe ido tamkar mai bacci. Ya tsura mata ido daga ita har Babyn, kamar mai son gano wani da ba daidai ba.

Daga bisani ya nufi goshin Fatima ya yi kissing ba iyaka, har sai da ta juya mishi baya, bayan ta sa hannu ta dan ture shi gefe. Murmushi ya yi hade da zama gefen gado, lokaci daya kuma ya dauki Baby ya yi mata addu’o’i hade da yi mata huduba da sunan Mama.

“Na sanya mata suna Hajara.”

Sai a lokacin Fatima ta juyo inda yake tana kallon shi, a hankali ta ce “Sunan Mama wai? Gaskiya sunan Inna na so a sanya.”

Murmushi ya yi hade da lalubo hannunta ya matse a cikin na shi.

“Na san hakan kike so, duk da ba ki fada ba. Ai yanzu aka fara haihuwar, nan gaba za a sanya sunan Inna ma, da kowa da kowa ma na garin Sandamu.”

Tare suka yi murmushi mai sauti, ita kanta ta san cewa burin Mustafan ne sanya sunan Mama, duk da bai fada ba, amma tana ji a jikin sunan da zai sanya kenan.

Mustafa wani irin mutum ne mai kunya, tun da ta samu ciki, bai taba yin hirar cikin da ita ba, zai dai tambayi tana lafiya, babu inda ke mata ciwo, wani lokaci kuma ya kan sanya hannu ya shafa ciki, ko ya dan dora kansa a kan musamman idan ya same ta tana bacci.

Ko kayan haihuwa da yake saye, iyaka ci ya sawo ya ajiye, ko kuma ya ba ta kudin idan tana sha’awar wani abun ta sawo. Ita ma ko pant ba ta taba saye ba, kudin da ya ba ta ma, Ummi ta ba, ta kaiwa Aunty Hauwa. Koda Aunty Hauwa ta bi ba’asin kudin, sai Fatiman ta ce Yaya Mustafa ne ya bayar wai a yi sayayya.

Aunty Hauwa ce ta bincike duk kayan da ya sawo, sai ita kuma ta siyo abin da babu da kudin.

Ya katse mata tunani da fadin “Sannu Fatima, ko ba ki fada ba, na san kin sha wahala, babu wata kalma da  zan yi amfani da ita wajen nuna miki irin tausayin ki da na ji a wannan ranar. Sai dai in yi miki addu’ar Allah ya saka miki da gidan aljanna. Ta dalilinki yau ga shi ni ma na zama uba. Allah ya ba ni ikon sauke nauyinku da ke kaina.”

A can kasa ta amsa da amin.

Mikar da ita zaune ya yi, hade da kanga mata fuskar yarinyar a kan fuskarta, cike da tsokana yake fadin” Na san ba ki kalli fuskar yarinyar nan ba, wallahi kama take da ni tun yanzu.”

Kawar da kai gefe ta yi hade da ture hannunshi mai dauke da yarinya  “Haka na ji ana fada.”

“Wai da gasken ba ki kalle ta ba?”

Ba ta amsa shi ba ta kwanta.

Da gaske ne har zuwa lokacin Fatima ba ta yi wa fuskar jaririyar kallo na minti daya ba. Saboda kunya ta dan fari.

Mustafa bai kwanta ba sai da ya gabatar da nafilfili na nuna godiyarsa ga Allah subhanahu wata’ala, da ya yi masa kyautar da babu wanda ya isa ya mishi ita.

*****

Haka zaman bakwai ya ci gaba da gudana, ko wane lokaci gidan a cike, Mustafa bai sha wahalar komai ba, saboda ya tanadi komai, Fatima kam gata take gani tsagwaron shi, ta ko wane bangare.

Ba ta san yawan yan’uwa na da dadi ba, sai wannan lokacin da ta haihu. Tun saura kwana uku suna suka cika mata gadonta da dinkuna masu tsada, babu wanda ya yi mata kala daya, daga kala biyu ne abin da ya yi sama.

Mama kam da yake ba ta yi komai a bikin ba, katuwar tunkiya ta bawa Fatima kyauta.

Bayan dinkuna da kayan kitchen sabbi fil, har da sabon fridge.

Mustafa ma dinkuna kala biyar ya yi mata, kaya dai kamar an hada mata sabon lefe.

Baby kuwa Ghana must go biyu aka cika mata, na dangi da abokan arziki, don ko Uwarta ta biyu Zainab set biyar masu tsada ta siya mata. Alhaji ma tsabar kudi 20k ya ba Fatima ya ce ace ta ja jari.

An yi shagalin suna kam, kamar kada ya kare. Wanshekare aka tafi da mai jego gida, don wankan jego, yayin da Mustafa ya koma makaranta. Sosai Fatima ke samun kulawa a wajen Mama. Ba Fatima kawai ba, hatta Baby da suke kira da Hana, ba karamin so Mama ke gwada mata ba, kamar a kanta aka fara haifa mata jikoki.

Kullum tana goye a bayan ta. Hatta fitinar jarirai irin ta daren nan, Mama ce ke fama, Fatima kam baccin ta take yi. Dalilin da ya ta kara cika, ta yi haske gami da kiba, duk sati biyu, Mustafa na hanyar ganinsu, yayin da Inna ke zuwa duk bayan kwana biyu.

Ummi kuwa kullum ne sai ta zo.

*****

Yau da misalin karfe  tara na safe Aunty ta shigo gidan, Mama na jijjigar Hana da ke ta kuka.

Fatima kuma zaune tana cin danwake, bayan sun gaisa, Aunty Hauwa ta dauki Hana tana fadin “Yarinyar nan anya ba za a kaita asibiti ba Mama, ya kamata ace ta yi sauki da rikicin nan?”

“Tunanin da nake yi kenan ni ma a zuciyata wallahi. Kukan ya yi yawa, wata biyu fa kenan.” Cewar Mama a lokacin da take zama.

Aunty Hauwa ta sanya yatsunta biyu tana bubbuga cikin Hana “Kuma ba kumburin ciki ba ne?”

“Ba shi ba ne. Tun da cikin satin nan zasu koma, kuma Baban ya gama jarabawa zai dawo sai ya kai su asibitin.”

Fatima dai cin danwakenta take yi tamkar abun bai shafe ta. “Karbarta ki gwada ba ta nono ko za ta yi shiru.”

Shiru Fatiman ba ta motsa ba, har sai da Mama ta kuma, maimaita mata. Aunty Hauwa ta yi dariya “Wai su Fatima an san kunyar dan fari, Allah Rahimi!”

Fatima dai ba ta tanka ba, har Aunty Hauwa ta dora mata yarinyar akan cinyarta.

A lokacin ne ta fitar da nonon ta sanyawa Hana a baki. Tun tana kuka har bacci ya dauketa.

“Wai Mustafan har ya cinye wannan semister?”

Kai Fatima ta daga alamar Eh.

Aunty Hauwa ta dora da “To ke sai yaushe ne naki karatun?”

“Yo wane karatu kuma yanzu? Da wannan yarinyar mai ka gyare za ta tafi makarantar?”

Cewar Mama bayan ta tabe baki.

“Wallahi ni ban so aka yi auran nan ba tare da Fatima ta gama karatun ta ba. Saboda idan har mace ta fara haihuwa, ba lallai ta iya karatun ba kuma. Mu kan mu da mu ka yi, mun yi shi ne tun kafin mu fara haihuwa. Amma yanzu kam ta ina za ta fara.”

“Uhmmm! Sai ta jira sai ta yaye idan Allah bai kawo wani ba.” Cewar Mama cikin halin ko in kula.

Fatima dai uffan ba ta ce ba. Idan ma ba ta yi karatu ba, ba ta da wata matsala. Mustafanta ya dauke mata komai, ya kuma hana ta kukan komai, to me zai sa ta matsawa kanta yin wani karatu.

Ba mai tayar mata da hankali a kan wani karatu, abin da take fada kenan a ranta.

Tana jin su suka sakk hirar suka dakko ta Jamil. Wanda dama ita a yanzu labarin na shi kawai take ji, ko lambar shi ba ta ita. Duk ta ka samu sakon gaisuwarshi, a wurin Mustafa, Aunty Hauwa ko Zainab.

Don Mama tun da Jamil ya tafi basu taba yin hirar shi ba.

*****

Ranar Laraba aka mayar da Fatima gidanta, hade da gara mai yawa. Ranar Juma’a kuma Mustafa ya dira gida, bayan kammala jarabawar shi da 1st semister 200 level.

Sai dai maimakon farin ciki, kwana suka yi basu bacci ba saboda rashin lafiyar da Inna ta kwana da ita. Asubar fari, aka kira kanwar Inna suka nufi babban asibitin Daura. Sosai su Fatima suka shiga tashin hankali, musamman yadda Mustafa bai dawo gidan ba sai wajen tara na dare. A nan yake shaida masu an sanyawa Innar robar fitsari ne, ranar Monday ma zasu wuce Katsina, don ganin babban likita.

A kwana biyun dai Mustafa ya kare su ne, cike da tashin hankali, gami da buge-bugen kudin zuwa ganin likita. Daga Ummi har Fatima sun so bin Mustafa, amma ya ce su jira tukun. A babban asibitin Katsina a ka ba Inna gado, inda aka tabbatar tana da ciwon ƙoda.

Hankalin Mustafa ba karamin tashi ya yi ba, musamman da aka fada masa irin kudin allurai magungunan da za a rika siyawa  Inna.

Jiki a mace ya dawo gida, tun daga yadda Fatima ta ga jikinsa a lokacin da ya dawo, ta san akwai matsala. Abinci ma kadan ya taba, ya ce ya koshi. Yanayin da ta gan shi a ciki ne, ya hana mata sanar mishi da rashin lafiyar Hana.

Saboda yau kuka ta wuni yi, ko nono sai yanzu ta sha, bayan an ba ta paracetamol.

Tsaye take a tsakar dakin goye da Hana tana jijjigata. Ta yi magana a hankali

“Tun da ka dawo na fahimci akwai matsala, amma ka ki cewa komai.”Ya mike zaune daga kwancen da yake a kan 3sitter. Cikin karfi hali ya ce “Hana ba ta kwanciya ne, kike ta wahala da ita a baya tun dazu?”

“Idan tana jin rikici haka take yi, ko na kwantar da ita, ba za ta kwanta ba.”

Ya dan nisa kadan “Lafiyarta kalau dai?”

Kamar ta fada mishi  cewa akwai bukatar a kaita asibiti, sai kuma ta fasa, kada a hada mishi zafi biyu.

“Lafiyarta kalau. Rigima ce kawai.”

“Miko min ita.” ya yi maganar hade da mika mata hannayemshi biyu.

A hankali ta kwantota hade da mika mishi kamar yadda ya bukata.

Ya tsura mata ido sannan ya  ce “Kamar fa ta dan rame.”

Ita kanta ta san Hana ta saki, amma cike da kwarin gwiwa ta ce “Babu wata ramar da ta yi.”

Ya kuma kafe Hana da ido, a kokarinshi na san tabbatarwa. Daga karshe dai ya ce

“Ciwon koda ne ke damun Inna”

Fatima ta yi saurin zabura hade da sallallami.

“Da gaske?”

Kai ya jinjina alamar eh.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un. In sha Allah za ta ji sauki.”

“Ina fatan hakan ni ma. Sai dai za a kashe kudi sosai”

“In sha Allah! Allah zai rufa asiri.”

“Allah ya sa.” ya fada hade da janyota zuwa barin jikinsa.

Duk suka yi shiru na wani lokaci kafin ya  ce “Ina jin gobe zan kira Iro mahauci ya yi wa Akuyar can kudi, da wancan Ragon, mu ga nawa za a hada. Don yanzu haka lissafin da aka yi min a asibiti zai cinye sama da dubu talatin.”

Kai ta jinjina cike da mutuwar jiki ta ce “Allah ya ba ta lafiya dai, kashe kudin ba shi ne damuwar ba, fatanmu ta samu lafiya, koda za mu yi wayi gari bamu da komai.”

Ya kuma rungume ta a jikinsa, cike da kaunarta, hade da fatan Allah ya karbi addu’arta.

<< Daga Karshe 20Daga Karshe 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×