Skip to content
Part 22 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Wanshekare da safe haka Mustafa ya siyar da dabbobin nan, ya harhada da kudin wurin shi, suka nufi asibiti shi da su Fatima.

To jikin Inna dai ba kuka ba guda, duk jikinsu Fatima ya mutu, Ummi kuwa kuka kawai take yi, yayin da Inna ke karfin halin karfafa masu gwiwa.

Fatima ta so zuwa gidan Aunty Lami, ko don Zainab ma, amma ganin jikin Inna sai ya cire mata sha’awar komai. 

Mustafa ya biya kaso biyu bisa ukun kudin maganin da ake bukata, sannan ya barwa Inna Azumi kudin bukatu.

Da kyar Ummi ta bi su, amma ta so ta zauna tare da Inna.

Haka mutanen Sandamu musamman dangin Fatima suke zaryar duba Inna.

Aunty Lami kuwa, kullum take yin abinci Zainab ta kai masu.

Mustafa ma duk bayan kwana daya yake zuwa Katsinan, cikin sati biyu da kwanciyar Inna, duk wani tsumi da tanadi nasu sai da ya kare.

Shi ya sa malam bahaushe ya ce a nema, a aje ko don ciwo.

Lokaci kankane Mustafa ya fara fuskantar rayuwa, ga hidimar gida, ga ta asibiti, ga kuma ta makaranta, don tuni suka fara registration, amma shi bai yi ba, ba ma ta wannan yake ba.

Don ma Fatima na taimaka mishi, duk wani abu da ta samu a wajen haihuwa sai ta ba shi ya sayar a yi amfani.

Garar abinci kuwa, su ci su sayar su yi cefane, haka rayuwar ta rika gudana.

Kullum Mustafa cikin tunani, hade da kullawa da kuma kwancewa.

Kamar yadda yanzun ma yake zaune a kan kujera yar tsugunno a kofar kitchen din Fatima. Ya zuba tagumi da hannayensa biyu. 

Hana zaune a kan kekenta na koyon zama, tana ta yan kanana kukanta, wanda wuni take ta kuma kwana tana yi.

Fatima ta fito daga daki, hannunta rike da Parkern da ta kwaso shara.

Wata kujerar ta dakko hade da zama tana fuskantar shi, bayan ta zubar da sharar da ke hannunta.

Hana ta dakko hade dora ta a kan cinyarta, lokaci daya kuma tana kokarin ba ta nono.

“Ya Mustafa jikin Innan ne? Ba ka ce akwai sauki ba?”

Ya sauke ajiyar zuciya a hankali tare da cewa “Akwai sauki, jibi laraba ma za a sallame su, amma akwai magungunan da ba a so su yanke mata, kuma suna da tsada. Ga makaranta har an fara lectures, ban yi registration ba. Abun yana damuna, ina jin dole in hakura da karatun nan.”

Ido da fitar waje “Hakura kuma Ya Mustafa, bayan ka ci rabin karatun.”

“To ya zan yi Fatima, kina kallon yadda abubuwa suka damalmale fa. Damuwana yanzu wallahi shi ne karatunki. Ina son cika miki burinki.”

“Ni kuma damuwata ita ce naka karatun, gaskiya ba za ka tsaya da karatunka ba, bayan ka yi nisa.”

“To ya zan yi, kina kallon a gidan nan fa babu komai, abincin da za a ci ma, ban da Allah ya sa akwai wanda aka tara miki, kila watarana sai dai mu kwana da yunwa.”

“Duk wannan ba zai hana ka karasa karatunka ba, sha Allah Ya Mustafa.” ta yi maganar hade da mikewa ta shiga daki.

Ba jimawa ta fito, hade da mika mishi, kullin bakar ledar da ke hannunta. “

” Menene? ” ya yi tambayar hade da kallon ta.

” Ka amsa mana. “Kamar wanda ake koyawa dabarar motsa sassan jiki, haka ya mika hannu ya karbi kullin.

Lokaci daya kuma ya warware.

Murmushi ta yi, saboda yadda ta ga yana kallon ta

” Dubu ashirin ne. Baba ne ya ba ni ya ce in ja jari, kafin in sanar ma sai kuma ga Inna ba lafiya, ka je ka yi registration din.”

Ajiyar zuciya ya sauke hade da kallon kudin, ya jima shiru, kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya ce

“Mu bar maganar karatun nan nawa Fatima, je ki ajiye kudin nan, idan Inna ta dawo mun ga jikin nata da sauki, to zamu kai Hana asibiti ne ta ga babban likita. Na san yarinyar nan ba ta da lafiya, kawai dai kina boye min ne.”

“Allah ba zai hana mu kudin kai ta asibiti ba Ya Mustafa, don Allah ka je ka yi registration din nan gobe idan Allah ya kai mu.”

Gardama suka shiga yi, har daga karshe dai ya amince da bukatarta.

Asubar fari kuwa ya nufi kano, ya gama komai daga can ya wuce Katsina wajen Inna.

Bai dawo gidan ba sai dare.

Ita kanta ta ga walwala a kan fuskar shi, ba mamaki saboda yin registration din shi ne.

Ranar Laraba aka sallamo Inna daga asibiti, jiki kam ya yi sauki Alhamdulillahi.

Yan dubiya kuma suka shiga zuwa duba ta.

Yayin da Mustafa ke ta buge-bugen abin da zai bari a gida, da kuma wanda zai koma makaranta.

Fatima ta fahimci idan dare ya yi sam ba ya bacci, ya yi ta juye-juye kenan, daga karshe ma sai ya mike ya dauro alwala ya fara sallah.

Shi ya sa yau asabar bayan ta gama hidima da Inna, aka yi buge-bugen abin da za a yi abincin rana, sai ta barwa Ummi girkin ta nufi gida.

A lokacin ma Mama kokarin dora abincin ranar take yi ita ma, tsakiyar gidan kuwa jikokin Mama ne ke wasa, kasancewar yau asabar ba makaranta.

Cikin yaran Fatima ta tsaya na yan mintuna, tana jin korafe-korafensu. Daga bisani kuma ta aje masu Hana, sannan ta karasa cikin dakin.

Wake Mama ke gyarawa, ta amsa gaisuwar Fatima, hade da tambayarta mai jiki.

“Alhamdulillahi akwai sauki.” ta amsawa Mama a lokacin da take zama kan kujera, lokaci daya kuma tana cire hijabin jikinta.

Mama ta mayar da hankalinta inda Hana ke ‘yan korafe-korafenta, daga bisa ni kuma ta ce Al’amin din Aunty Aisha ya miko ta wurin uwar ta.

” Wannan yarinyar fa ba ta da lafiya, har yanzu ba ku kai ta asibitin ba?” ” cewar Mama lokacin da take kallon Hana wacce Al’amin ya aje a cinyar Fatima ya fice aguje.

Ta dan nisa kadan” Za a kai ta. “

” Ya kamata dai gaskiya, yarinyar nan ba iya jikinta kenan ba, ga ta kullum cikin korafi.”

Shiru Fatima ta yi, ba ta ce komai ba, magana in dai a kan Hana ne, ba ta cika tankawa ba, idan ta yi daya biyu, sai ta yi shiru.

Mama ta mayar da hankalinta sosai a kanta, ganin kamar akwai abin da ke damun ta.

” Akwai matsala ne, ko jikin Innar ne har yanzu?”

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce “Tunkiyar da kika ba ni, tana nan kuwa?”

“Ina ko za ta? Tana nan mana.”

Fatima ta dan yi shiru, har sai da Maman ta kuma cewa “Me ya faru?”

Zamanta ta gyara,, hade da sauke Hana kasa, ta ce “So nake in sayar da ita.”

Cike da mamaki Mama ke kallon ta, da alama ba ta san me za ta ce ba.

Sallama Aunty Ayyo ce ta hana Fatima kara yin magana.

Ita ma Aunty Ayyo sai da ta tsaya cikin yaran, sannan ta karaso dakin, suka gaisa da Mama, Fatima kuma ta gaishe ta.

Aunty Ayyo da tun ta shigo take nazarinsu ta ce “Lafiya dai ko? Na ga ku wani iri Mama.”

“Ummm!” kawai Mama ta ce, lokaci daya kuma tana kwace tiren waken ta da Hana ta janyo.

Fatima kam Uffan ma ba ta ce ba.

Shiru ya ratsa wurin har zuwa lokacin da Aunty Ayyo ta kuma cewa “Wai lafiya kuwa?” 

Kamar dai ba za su yi magana ba, sai kuma Mama ta ce “Yar uwar ki ce, wai a ba ta tunkiyarta za ta siyar.”

Aunty Ayyo ta kalli Fatima, wacce ta kawar da kai zuwa tsakar gida, inda yara ke wasa. Za ka rantse ba ta san me Mama ta fada ba.

“Me za ki yi da kudin?” cewa Aunty Ayyo.

“Amfani.” ta amsa kai tsaye.

Daga Aunty Ayyo har Mama babu wanda ya kara cewa komai.

“Tunkiyar fa ciki ne da ita ma.” cewar Mama, jin shirun ya yi yawa.

Fatima ta ce “Wa ke siyan tunkiya, in aika Fadila ta kira min shi.”

“Dan antai ne.” cewa Mama kanta a kasa tana gyaran wakenta.

Aunty Ayyo dai ba ta tanka ba, sai ma wasa da take wa Hana.

Fatima kuwa fita ta yi, ta aika Fadila kiran Dan’antai. 

Ba jimawa ta dawo tare da shi. 

Bayan kamar mintuna talatin ana ciniki, daga karshe dai aka yi wa tunkiya kudi 12,500. (kar ku manta muna maganar shekarau 15 ne baya.) Aunty Ayyo da ke tsaye da goyen Hana ta ce “Ni zan bayar da kudin, na sayi tunkiyar.”

Wani irin sanyi Mama da ke zaune cikin daki ta ji, don ji take kamar cikin yayanta ne aka kama daya za a sayar.

Shi ya sa ma ko fitowa wajen ta ki yi.

Su Dan’antai ta yi wa ihsani, sannan ta cewa Fatima ta je, gida za ta aika mata da kudin.

Ko Hana Fatima ba ta saurara ba, da ke bayan Aunty Ayyo tana bacci, ta yi tafiyarta gida.

Wani irin abu take ji, da ta kasa fassarawa, bacin rai ko farin ciki oho.

 Ita kanta tana son tunkiyar, duk lokacin da ta shigo gidan ta ganta daure a matsayin tata, ta kan ji wani irin farin ciki, yanzu kuma sai ta shigo ta kalle ta ba a matsayin tata ba. Haka ta ci gaba da wannan tunanin har ta isa gida. 

Lokacin da ta isa Ummi har ta kusa gama abinci, don haka ta kama mata suka karasa.

Misalin karfe daya Fadila, ta kawo Hana gida hade da kudin tunkiya.

Kasan filo ta sanya kudin, ta yi sallah, bayan ta ba Hana nono.

Misalin karfe biyu Mustafa ya shigo gidan, don cin abincin rana.

Yadda ka san mara lafiya haka yake tafiya, duk ya kara tsawo, ya yi baki, alamun rashin kwanciyar hankali duk sun tabbata a tare da shi.

Sai da ya fara shiga dakin Inna ya duba ta, duk da babu wani abu da ke damun ta a lokacin.

Amma ka’ida ne idan ya shigo gidan, muddin Inna na gida, to sai ya fara leka dakinta sannan. 

Da Hana ya fara cin karo, wacce ta jawo jiki har bakin kofa tana wasa.

Ganinsa ya sanya ta daga hannuwa alamun ya dauketa, ya fadada fuskar shi da fara’a.

Ko wane irin bacin rai da damuwa yake ciki, muddin zai yi arba da Hana, sai ya ji kaso hamsin din damuwar ta gudu. Musamman idan ya ganta tana farin ciki, sabanin lokutan da take koke-kokenta, alamun dai akwai abin da ke damunta

Ya dagata sama yana mata wasa, ita kuma tana kyalkyala dariya sosai.

Fatima da ke kwance kan kujera tana kallon su, duk da irin ciwon kan da take ji, hakan bai hana ta yin murmushi ba.

Ya janye kafafunta kadan, ya zauna har zuwa lokacin Hana na hannunshi.

Fatima kuwa mikewa ta yi, hade ta kawo mishi abincinshi.

Ya sauka kasa, bayan ya yi Bismillah ya fara cin jalof din shinkafa da wake da manja.

Hana kuwa na ta rashin jin ta.

Fatima kam komawa ta yi ta kwanta, tana kallon sa.

“Har yanzu kan na ciwo ne?”

Kai ta daga alamar eh, bayan ta lumshe idon ta.

Ya dakata da cin abincin, lokaci daya kuma ya sanya hannunsa ya kama mata kan, ya gama tofa addu’ar yana fadin “Sannu. Dole idan aka yi salary ki je asibiti”

Ita dai ba ta ce mishi komai ba.

Salaryn duka 25k ne, kasancewar Mustafa teaching yake a primary.

25k kuwa a wannan matsalolin da suka taso su gaba, babu abin da zasu yi masu. Ga magungunan Inna, da suke kwashe ku san rabin kudin.

Ta yi saurin bude idonta, jin yadda Hana ta kyakyace da kuka, haka take yi, tana cikin wasa sai ta kwala kuka, kamar wacce aka tsirawa allura.

Mustafa ne ya yi saurin daukar ta, hade da tofe ta da addu’a, kamar mintuna biyu kukan nata ya yi sauki.

“Matsalar yarinyar nan na damuna gaskiya, ya kamata in yi wani abu.”

“Allah ya kyauta.” Fatima ta ce tare da mikewa tsaye ta shiga bedroom.

Ba jimawa ta fito, a lokacin kuwa Hana ta yi shiru, sai ajiyar zuciya.

Ta zauna kusa da shi, hade da mika mishi kudin da ke hannunta.

Bai karba ba, kuma bai daina kallon ta ba.

“Tunkiyar da Mama ta ba ni, ita ce na siyar, ga kudin nan, ka yi amfani dasu zuwa makarantar.” ta yi maganar a tausashe. 

“Ni na ce ki sayar? Me ya sa za ki siyar? Abubuwa nawa za ki sayar ne saboda ne Fatima?” 

” Kawai na yi abin da nake ganin ya dace ne Ya Mustafa, makarantar nan saura shekara daya, ba zamu bari komai ya lalace ba. Kuma na tabbata idan abin da ya same ka, ni ce ya sama za ka yi, fiye da abin da nake yi a yanzu.”

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali “Fatima ki daina sayar da kayanki kina ba ni kudin don Allah. Kin san halin mutane fa. Sannan ina jin wani iri, kamar dai ba ni da wani amfani.”

“Mu ma’aurata ne Ya Mustafa, dole mu rufawa junan mu asiri, ba ruwan ka da maganar mutane.”

Ya dan nisa kadan “Kullum ina godiya ga Allah da ya ba ni ke a matsayin mata Fatima. Wasu matan sukan guji mazajensu ne, a lokacin da suka shiga matsalolin rayuwa misalin kamar nawa. Ke kuma a lokacin ne kike nuna min kina tare da ni. Allah ya saka miki da mafificin alkairi. Amma kudin nan ku yi amfani dasu, ku je asibiti ke da Hana. Kin ga kuma ba lafiya ne da ku ba.”

” Wannan dai na makarantar ne, sai ka tafi gobe, ni da Hana kuma ranar Monday sha Allah zamu je asibiti. “

” Ina za ki samu kudin? “

“Allah zai kawo, kai dai ka tafi makarantar gobe idan Allah ya kai mu.”

Rungumota ya yi, zuwa jikinsa, ya kwantar da fuskarsa a kanta

“Na gode Fatima, Allah ya ba ni abin da zan fita kunyarki. Ina fatan Allah ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

“Kar ka damu Ya Mustafa, zan iya yi ma fiye da wannan ma. Allah dai ya yaye mana matsalolinmu, ya ba Inna lafiya.”

“Amin” ya fada a hankali.

Ranar Sunday kuwa misalin karfe hudu Mustafa ya daga zuwa Kano.

Fatima kuwa wasu daga cikin zannuwan da ta samu a suna, ta kwashi guda biyar ta sayar ranar Monday suka tafi asibiti.

Sai dai ba karamin tashin hankali ta baro asibitin da shi ba, tun a hanya take kuka, maimakon ta wuce gidanta sai ta yi gidan Aunty Hauwa.

Kuka rurus ta sakawa Aunty Hauwa, ga Aunty Hauwa ba ta iya rudewa ba, lokaci daya tafirgi ce.

” Innar ce ta rasu?”

Kai Fatima ta girgiza.

“Wani abu ya samu Mustafan ne?”

Nan ma kan ta ki girgiza mata.

“Daga ina kike?”

Da kyar cikin kuka ta bude baki ta ce “Asibiti.”

“Me ya faru a can din?”

Wani kukan Fatima ta kuma saki, sai da ta yi mai isar ta sannan ta ce “Cewa aka yi ciki ne da ni”

Aunty Hauwa ta ja dogon tsokin takaici “Shi ne za ki zo ki tayar min da hankali haka, kamar kin yi cikin shege. Wane irin rashin hankali ne wannan? Mtswww!” ta kulle maganar tata da wani dogon tsakin.

“Ai cewa aka yi ita ma Hana ba ta da lafiya, cibiyarta ce ke nade yan hanjinta, idan ba a yi mata aiki cikin gaggawa ba, komai zai iya faruwa.”

“Hana din?”Aunty Hauwa ta yi gaggawar tambaya.

Kai ta daga alamar eh, lokaci daya kuma tana share hawayenta.

” Subhanallah! ” cewa Aunty Hauwa.

Lokaci daya kuma shiru ya ziyarci dakin.

” Ki yi shiru, ki yi hak’uri, in sha Allah komai zai wuce, kuma za a yi aikin cikin nasara. Sai ki kira Baban ki shaida mishi.”

Kai ta daga alamar gamsuwa.

Aunty Hauwa ce tai ta kwantar mata da hankali, har zuwa lokacin da natsuwarta ta dawo jikinta, ta rika jin kamar ba ta wata matsala mai girma.

Sai da ta ci abincin rana sannan ta bar gidan Auntyn, kuma ba ta shi ga gida wurin Mama ba.

Gidanta kawai ta wuce.

<< Daga Karshe 21Daga Karshe 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×