A hankali Fatima ta rika samun sauki, dalilin da ya sa Jamil ya ce a maido ta gida.
Mustapha kam sai da Mama ta yi da gaske sannan ya koma Enugu.
A yanzu Jamil ne ke kula da ita, kuma a hankali take samun sauki don yanzu ma an maido mata da Ziyad (Haka suke kiran Musa, wanda ya ci sunan Alhaji) da yake hannun Aunty Hauwa a da.
Sanye take doguwar rigar atamfa, hade da dan ƙaramin hijabi iya kafarda, zaune take gefen katifa tana kallon Ummi da take shirya Ziyad din bayan Mama ta yi mishi wanka, Hana kuwa zaune take tana shan tea,
Daga can bakin kofa Abdullahi ya yi sallama, ya kuma shaidawa Fatiman Jamil zai shigo ya duba ta.
Dama ta san ya kusa Shigowar, shi ya sa ma ta dauki ƙaramin hijab ta sanya. Don ka’ida ne karfe goma yake shigowa na safe, daga nan sai 2pm sai kuma takwas na dare.
Ummi ta fita, bayan ta mikawa Fatima Ziyad.
Jin alamun Shigowar Jamil din ne ya sanyata zare nonon da take bawa Ziyad, ta mayar da shi kan kafadarta, hade da bubbuga bayanshi.
Kamar kullum a kofar dakin ya tsaya yana amsa gaisuwarta, kafin ya shigo sosai.
Yana kallon yadda kanta ke a kasa, sosai ta canja, canjin da bai taba tsammani daga wajen ta ba, ta zama shiru-shiru, ga wata nutsuwa ta musamman.
A sirrince ya sauke ajiyar zuciya “Kin sha maganin ne”
“Eh.”
“To ya kafafun har yanzu suna ciwon?”
“A’a basu yi.” ta amsa a hankali, har lokacin kanta a kasa.
“To ciwon kan fa?”
“Na dan tashi da shi kadan, amma ina shan magani sai ya sauka.”
Shiru ya ratsa dakin, kawai canjin nata sai yake ganin kamar a kuntace take, irin ba ta samun kulawar da za ta ba ta damar yin walwala har ta sake ta yi abin da take so.
Amma kuma bai ga alamun hakan a jikinta ba, don jikin nata a mulmule yake fes babu alamun wata wahala, haka ma yaranta gasu nan gwanin sha’awa, musamman Hana da ta dakko jikinta har ma hasken fatar. Sai dai da alama ba za ta yi rashin jin Fatiman ba.
Duk kuwa wanda ya zauna asibitin ya ga irin kulawar da Mustapha ke ba Fatima, da kuma irin tashin hankalin da ya shiga, a lokacin da take rai hannun Allah.
Dukawa ya yi hade da kama hannun Hana mai rike da spoon din da take shan tea “In sha?”
Kai ta daga hade da murmushi har dimples din ta biyun suka lotsa.
Tea din ta debo ta kai bakinsa, ga mamakin Fatima sai ta ga ya bude bakin ya karɓa, haka ya rika karbar tea din kamar spoon biyar, sannan ya mike da niyyar tafiya, Hana ma ta mike rike da kofin shayinta.
“Na gode, Allah ya saka da alkairi”
Bai amsa ba, amma tabbas ya ji dadin godiyar, ya fice rike da hannun Hana.
Fitar shi ya ba ta damar sauke ajiyar zuciya mai nauyi, idan yana waje sam ba ta sakewa, ya canja sosai, irin canjin nan da kallo daya za’a yi mishi a fahimci hakan, ya yi haske, jikinsa ya canja irin na ƴaƴan hutun nan, ga tarin nutsuwa da gogewar aiki.
A yanzu kam ta yadda Jamil ba mijin kucakar mace ba ne, lallai sai mai sa a ce za ta same shi. Musamman yanzu da yake ta kara taka matsayi babba a rayuwarshi.
*******
Mustapha kwance a dakinshi da aka ba shi, lullube yake cikin bargo saboda ruwan saman da aka dauke ba da jimawa ba, so yake ma ya fita zuwa court din da yake service amma ya kasa fita, musamman da abokiyar aikinsa ta fada mishi ita tana can. Sai yake jin kawai yau ya huta.
“Shigo” ya fada daga cikin bargon, don ya san Blessing ce, dalilinta ne ma ya sa bai sanyawa kofarsa key, ya tsani yana jin dadin kwanciyar ko zama ta tashe shi da buga kofarta.
Tun yana fadan shigo mishi daki da take yi har ma ya hakura ya kyale ta, yanzu haka ma akwai key din dakinsa a hannunta.
“Hey! Sleep – sleep. Are you still sleeping? Enjoy now.”
Ta yi maganar fuskar ta dauke da murmushin da ya bayyana siririyar wushiryarta.
Hannunta kuwa madaidaicin tire ne, ta aje tiren a kusa da shi, lokaci daya kuma ta koma kan plastic chair ta zauna.
” Kana duba agogo kuwa? ” ta yi maganar cikin yanayin hausarta mai dadin sauraro.
Ture bargon ya yi, ya mike zaune, lokaci daya kuma kamshin abincin da ta ajiye ya daki hancinsa.
Indai girki ne, to Blessing ta san hannunta, tun yana kin ci, yanzu kam ya saki jiki ci yake yi, musamman da ya kafa mata sharuddan cire dogayen farcenta, masu kama da na tsohuwar mayya.
Bai tanka ta ba, ya shiga toilet, brush ya yi sannan ya fito, yana kokarin zama ta kuma cewa
“Ba za ka fita aiki ba?”
Kai ya daga a hankali alamar eh, sannan ya ce “Good morning”
“Morning Malam Musty, how was your night?”
“It’s cool” “
” I see” ta fada hade da siririyar dariya.
Chips ne da pepesoup din kayan ciki, sai tea mai kauri yana fitar da kamshin ovaltine.
“Thanks” ya fada wannan karon yana kallon ta
“You deserve more than that”
“Thanks again”
“Please stop thanking me”
“Why now?” ya yi tambayar a lokacin da yake kurbar tea din
“No need” ta fada hade da mikewa tsaye “Ina da class, sannan zan shiga kasuwa kana da sako ne?”
“Ke wai kullum sai kin shiga kasuwa?”
“Not kullum malam, almost 3days ban je ba”
Bai ce komai ba, illa abincin da yake ce a nutse.
Daya daga cikin dabi’un Mustapha wanda yake burge Blessing tun daga ranar da suka hadu.
“You can go now.”
“Ok.” ta fada, hade da gyara zaman Jakarta.
Ya bi bayan ta da kallo har ta fice.
Blessing ita ce mace ta farko da ta fara nuna mishi, a cikin abu mara kyau akwai mai kyau, kamar yadda ake samun mara kyau a cikin mai kyau.
Suna da bambancin addini, amma kuma duk wasu nagartattun halaye tana dasu, wata baiwa da Allah ya yi mata kuma ita ce shiga rai, tana da shiga rai sosai.
Don duk yadda ya so janye ta daga jikinsa ya kasa, ba wai yana son ta ba ne, amma kuma yana shiga lamarinta sosai kamar yadda take shiga nashi.
Zai iya cewa ma a kaf gidan nasu da shi kawai Blessing ke magana, a cikin maza, a mata ma gaisuwa ce kawai tsakaninsu.
A bangaren Blessing ma Mustapha shi ne musulmi dan arewa na farko da ta fara gasgatawa, saboda nagartattun halayensa, abin da ta tashi da shi, aka dasa mata a zuciyarta shi ne, duk wani musulmi musamman dan’arewa to tamkar dan’ta’adda, ba shi da amana, sannan da yawansu jahilai ne, basu dauki mutane da daraja ba, basu ganin girman kowa.
Amma haduwarta da Mustapha sai ya goge mata duk waccan karatun.
Lokacin da ta iso camp din misalin karfe shidda ne na yamma, amma haka tai ta zama a kofa ita da kayanta kasancewar ba a bata daki ba, duk wanda ya zo sai ya kalle ta ya wuce, ciki kuwa har da wadanda suke addini na daya.
Tun tana yin shiru har dai ta fara neman taimakon wadanda suke a lodge din, amma kowa da complaint din da yake kawo mata, abin da ta fahimta dai basu son a rabesu.
A karshe ta hakura ta koma inda kayanta suke ta zauna, tana jiran tsammanin wa Rabbuka.
Ganin dare na yi, ta kuma bin su, da rokon alfarma su aje mata kayanta, za ta shiga gari ta samu wurin kwana kafin gobe.
Nan ma dai haka suka rika yi mata hanya-hanya, haka ta fito lodge din rai bace, kamar ta fasa ihu don takaici.
A daidai lokacin kuma suka ci karo da Mustapha wanda ya dawo daga cikin gari, don tun da ya tafi sallahr juma’a bai dawo ba, sai da aka yi isha’i.
A ranar juma’a ne kawai take samun damar yin sallah cikin jam’i saboda a inda yake ko kiran sallah ba ya ji. Shi ya duk ranar Friday yake shiga bangaren Hausawa sai dare ya dawo.
“Excuse me please” Blessing ta dakatar da shi ganin yana niyyar shigewa Kamar bai ganta ba.
Tsayawa ya yi hade da juyowa yana kallon ta.
Jiki a mace ta fara labarta mishi matsalarta, har zuwa kan taimakon da take so ya yi mata.
Ya yi shiru yana nazarin maganar hade da kare mata kallo.
Doguwar riga ce a jikinta iya gwiwa sai wando irin pencil din, kanta dauke da kitson attach.
“Dakko kayan” ya fada a takaice, wani sanyin dadi ta ji, ba ta taba tsammanin shi din zai taimaketa ba, ba sai an fada mata ba, ta san musulmi ne kuma bahaushe a kayan jikinsa ta fahimci hakan.
Shi ya kama mata kayan har zuwa kofar dakinshi.
Key ya zaro hade da bude kofar, ya shigar mata da kayan kaf. Tana tsaye tana kallon sa, har ya gama jerasu, sannan ya juyo yana kallon ta
“Thank you so much” ta fada har da dan dukawarta.
“Ina za ki je ki kwana?”
” I don’t know” ta amsa a sanyaye.
Duk sai suka yi shiru, kafin ya ce “Ina zuwa.”
Dakin Idris ya shiga, ba jimawa kuma ya dawo, har lokacin Blessing na tsaye a inda ya bar ta.
Key din dakin ya mika mata “Ki kwanta a nan kafin safiya, ni zan kwana a wurin abokina”
Da hannu biyu ta karbi key din hade da godiya.
Har ya tafi sai kuma ya dawo, dalilin da ya hana ta rufe kofar.
“Idan kina bukatar abinci akwai indomie sai ki dafa.”
“Na gode sosai” ta fada cike da girmamawa.
Bayan fitar shi ne ta karewa dakin kallo, komai an aje inda ya dace, ga kamshi turaren maza irin su After shaved roll on yana tashi.
Sai misalin 9:00am Mustapha ya kwankwasa mata kofa, ta bude hade da komawa gefe alamun ya shiga.
Maimakon ta shigan sai lissafa mata abin da yake so ta dakko mishi, da kuma inda suke.
Yana kallon yadda take taba komai a nutse har ta tattaro mishi abin da duk ya fada.
Sai da ta durkusa sannan ta mika mishi.
Tun daga wannan lokacin kuwa ba ta kara ganinshi ba sai karfe takwas na dare, a lokacin har an ba ta daki, ta yi Park ta kuma gyare mishi na shi dakin tsab.
Godiya sosai ta yi masa, a lokacin da ta mika masa key din dakinsa da plate din abincinsa na dare.
Tun daga wannan lokacin Blessing ke girmama Mustapha, ba ta da wata kawa ko aboki sai Mustapha.
Idan dai yana gida to shi ne abokin hirarta, idan ba ta dakinta to tana dakinsa, abinci kam kullum akwai kwanonshi a wurin ta.
Wannan shi ne silar haduwarsu, yayin dangantakarsu ke kara karfi, sai kyawawan dabi’unsu suka rika bayyana a hankali.
Zuwa yanzu dai a lodge din kowa ya san cewa tsakanin Mustapha da Blessing akwai alaka mai karfi, hade da girmama kowa.
Wannan kenan, bari mu koma Sandamu.