Skip to content
Part 30 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ba kowa a tsakar gidan sai Fatima da ke goye da Ziyad, tana shanya kayan da ta wanke na Ziyad da Hana a kan igiya.

Wayarta da take kan turmi, tana wakar sai WATARANA ta Nazifi Asnanic.

Bin wakar take yi, tamkar ita ce ta rerata, alamun dai tana cikin nishadi.

Ya dade a tsaye jikin bishiyar yana kallon ta, tsawon wata guda da yake zaune a gidan, wani abu yake ji game da ita sabo, shi ya sa ma yake son tafiya a gobe, ba zai iya zama har a yi arba’in din Alhajin ba, kamar yadda ya so a farko.

Kwanaki goman kallon su yake kamar wata goma, tun kafin kowa ya fahimci halin da yake ciki, gara ya kama gabanshi. Hakan ne kawai mafitarsa.

Amma a kullum idan yana kallon ta a cikin gidan tana harkokinta, musamman ya gan ta goye da Ziyad ko tana rungume da shi, sai ya ji ina ma ace ita din mallakinsa ce, kawai sun zo ganin gida ne.

Sometimes ya kan bata lokaci wajen tunanin hanyar da zai bi ya mallake ta, wanda ya san wasikar jaki kawai yake tsarawa, baya jin akwai wani dalili da Mustapha zai rabu da Fatima sai dai idan ko mutuwa.

Amma tabbas a yanzu da zai samu irin waccan damar da ya rasa, to da zai tabbatar Mustapha bai yi nasara a kansa ba.

Ya kai hannu hade da dakatar da wakar, daidai inda ake cewa “Ashe sabo yana da dadi, amma in zai ai rabo da zafi, ga shi za mu yo rabo da juna, dama na sani ni ban da rai ma…”

Ta yi saurin juyowa lokaci daya kuma ta dakata daga bin baitin da take yi.

Ganin wayar a hannun Jamil, sai ta mayar da hankalinta a kan shanya ragowar kayan.

Shi ma wucewa ya yi da wayar zuwa dakinshi.

Ya rika juya wayar, yayin da zuciyarsa ke azalzalarsa shiga bangaren sakoninta, bayan ya fito daga call history dinta, gabadaya kiran Mustapha ne ya cika wurin.

Ya kasa bijirewa zuciyarsa, sai kawai ya bude inbox din, sakonnin Mustapha ne da yake fada mata yadda ya yi kewarta, da kuma irin alkawuran da yake daukar mata muddin abubuwa suka daidaita yadda yake so.

Jefar da wayar yi, bayan ya karanta sako daya da Fatiman ta turawa Mustapha, sako ne da ke jaddada mishi tana tare da shi duk wahala.

Ya jima a kwance a kokarinsa na daidaita kansa, sannan ya mike zuwa dakinta.

A lokacin zaune take tana sosawa Ziyad kunne, shigowarsa ya sanya ta dago kai, hade da mika hannu ta karbi wayar da yake mika mata.

Maganganu ne da yawa a bakinsa, amma bai san ta ina zai fara ba, hasslima kiwar bude baki yake yi, da kyar ya iya cewa “Gobe zan tafi in Allah ya yarda, please idan kina bukatar wani abu koma menene akwai lambata just flash me, I mean koma menene please”

Kai ta daga alamar gamsuwa.

Ba iya maganar da yake son fada kenan ba, amma ba zai iya fadin sauran ba, don haka ya juya ya fita daga dakin.

Ta bi bayansa da kallo, cike da mamakin canjawarshi, ya koma mai saukin kai sosai, duk da halinsa na rashin magana a kan ko wane abu yana nan, amma tana mamakin yadda ba ya gajiya da surutu da Hana.

A zahiri ba za ta iya kwatanta irin tsantsar son da yake nunawa Hana ba, wannan na daya daga cikin abin ya sa a yanzu take ganin wani irin girmansa, sannan ko me ya yi baya ba ta haushi.

Enugu

Lahadi

Da misalin karfe tara Mustapha ne tsaye a kofar dakin Blessing yana jiran a bude mishi bayan ya kwankwasa.

Husaina ce ta bude, sanye take da doguwar riga ash color, ba sai an fada ma tsadar rigar ba, musamman yadda ta yi wa Husainar kyau. Kamshin da tun zuwansu ya mamaye dakin Blessing ya daki hancinsa, kamshi ne mai sanyi, hade da sanyaya zuciyar mai shakarsa.

Cike da girmamawa ya gaishe da Momy, ta amsa mishi cike da kulawa, yayin da Husaina kuma ta gaishe shi, bai gama amsawa ba Blessing ta turo kofar ta shigo.

Sanye take da wani tsadadden lace dinkin riga da siket din da ya fito da surarta duk da bai matse ta gam ba, daurin dankwalin ya yi mata kyau sosai, kila ko don ba ta saba daura dankwali ba ne, wuyanta da kunnenta siririyar sarka ce golden color mai kyau Sai walkiya take, hannunta rungume da Bible da wanda ke nuna alamar ta dawo daga church ne.

A zuciyar Mustapha mamakin irin rayuwar da suke yi yake yi. Hankali uwa kwance yarta ta tafi church, hankali ƴa kwance Mamanta tana sallah ita tana kwance.
“Ikon Allah” ya fada a zuciyarsa, ni kuma na karasa masa da”Ikon Allah mai tsaida wando ba zariya.”

“Malam Musty how are you?” cewar Blessing bayan ta aje Bible din ta a ma’ajiyarsa.
Sai ya tsinci kansa da kasa yi mata reply, illa kansa da ya dukar.

Ta yi dariya mai dan sauti tana kallon Momy “You see! Haka fa yake anything kunya, hey the northerners”

Momy ma sai ta yi murmushi tare da fadin “Alhaya’u minal Iman! Kunya ado ce, not only in women wa kowa ma”

Husaina dai kanta a kasa tana ta kankarar yatsan kafarta ba tare da ta ce komai ba.

Ganin ya mike alamar tafiya Blessing ta ce ” But wait, Have you take your breakfast?”

Kai ya daga alamar eh. Ta kuma yin dariya tana fadin “Oh my God, har Yanzu kunyar ce?”

Bai tankata ba ya fice yana murmushi.

Bai jima a cikin dakin ba, Blessing ta shigo.

Harara ya fara aika mata.

“What?” ta yi tambayar lokacin da take zama a kan plastic chair.

“Idan kina ba ni kunya ko… Tam”

Ta dan murmusa “I see nothing like kunya a abin da na yi fa”

“Ya jikin ki?”

“I feeling much better”

“I see” ya ba ta amsa.

“Momy ta ce ka zo mu tafi kasuwa”

Ya waro ido alamun mamaki “Kasuwa kuma? Kai haba.”

“I’m not kidding”

“Akwai inda zan je yanzu, kawai ku je please, ki yi kokarin barking dina, I’m not feeling comfortable…”

“Idan kuna tare da Momy.” ta yi saurin katse shi.

“Exactly” Ya bata amsa kai tsaye.

Duk yadda ta yi kokarin ganin ta shawo kansa don su je kasuwar ya ki amincewa.

Dole ta hakura suka tafi.

Ganin sun tafi sai ya janyo littattafanshi ya shiga dubawa, a haka har bacci ya dauke shi.

Basu dawo gidan ba sai la’asar. Yana sallahr la’asar ya ji Blessing ta shigo hade da aje wasu abubuwa ta fita.

Sai da ya sallame sallah ne, ya waiga don ganin me ta ajiye.

Katon din indomie ne, kwai, kayan tea, Irish, doya, sai juice da kuma tarkacen kayan girki dangin su mai da Maggi.

Sai da ya yi azkhar dinsa, sannan ya kira wayar Blessing.

Ba ta daga kiran ba, kai tsaye dakin nasa ta taho.

Duk yadda ya so ta kwashe kayan zuwa dakin ta ba ta yi hakan ba, dole ya hakura ya bisu da godiya.

Wanshekare tare da shi aka yiwa Momy rakiya zuwa airport. Shi ma kuma sai ya fara na shi shirin tafiyar.

Tun da satin tafiyar ya kama bai zauna ba, sosai Blessing ke tsokanarshi da ango-ango. Shi ko sai yay ta washe mata baki, da gaske jin shi yake kamar angon, karon farko da yake dokin zuwa gida fiye da ko wane lokaci.

Blessing kayayyaki masu kyau latest ta siyawa Hana da Ziyad, takalma masu kyau da kayan kitso wa Hana.

Ta so ma bin sa, amma ya ki, ta ya zai yadda ta bi shi, ko za ta je ba yanzu ba.

********

Duk yadda Fatima taso yakice kewar Jamil bayan ya tafi ta kasa, ku san ko wane lokaci tunininsa na makale a zuciyarta, ko wane dare akwai ka son mafarkinshi, ta yadda tabbas kulawa na kore kiyayya, hassada ce kawai ba ta korewa.

A wasikarsa lokacin da zai tafi India, ya shaida mata Mustapha bai kai shi sonta ba, wannan karon ta fahimci hakan a kwayar idonsa, kamar don ita ya zo, daga ita sai yaranta yake hidimtamawa. Shi ya sa ba za ta daina yi mishi fatan alkairi ba.

Shi kansa da za a tambaye shi a tafiyar wa ya fi kewa, zai ce Hana, wani irin so yake yi mata, tamkar dai shi ne ya haife ta, kila son da yakewa Fatima a yanzu ne ya tattare shi a kan Hana, saboda ita kawai ce yake da damar nuna mata kauna ba ma soyayya ba, ba tare da an tuhume shi ba.

Ranar da Mustapha ya dira Kano, a ranar aka mayar da Fatima gidan ta, bayan Aunty Bilki ta hada ta da magunguna masu kyau da inganci,, ita kanta Fatiman ta ji canji a jikinta.

Dakin Fatima cike da yan’uwanta suna ta raha, abin da ya sanya ta cikin nishadi, lallai ƴan’uwa rahama ne, komai lalacewarsu akwai lokacin da zasu yi ma rana. Duk yadda suke ta fadin basu yi mata komai sai ga shi sun yi mata komai din, da gara sosai suka rakota har da buhun shinkafa, ban da zannuwa dinkakku da wanda ba a dinka ba, ga kudi da suka hada mata wai ta yi sana’a.

Sai take jin wata irin kaunarsu, basu gajiya da yi mata hidima ita da yaranta, don Hana kusan ko wane sati sai ta samu dinki, dankunne, takalma, hijabai na yara da huluna, kamar ita kawai ce jika a gidan.

Kowa ya yi ragowar dinki ko ya ga abin sha’awa sai ya tuna da ita. Wannan kadai ya isa ta yi alfahari dasu.

Ranar da Mustapha zai diro gyara na musamman hade da abinci na musamman suka yi a gidan.

Fatima ta shirya cikin Swiss lace Coffee colour riga da siket, sosai ta yi kyau, musamman yadda kayan suka haska fatar ta, simple dauri ta yi wanda ya kara fito mata da kyawan fuskarta.

Wuyanta sanye da sarka wacce ta kwanta lif a cikakken kirjinta, hannaye ta da kafafunta dauke da kunshi zane na ja da bakin lalle, sai ta fito tamkar amarya.

Ziyad ma ta shirya shi cikin riga yan kanti sky blue masu taushi, Hana Ummi ce ta shirya ta cikin doguwar riga yar kanti fara kal mai siririn hannu, ta raba kanta gida uku ta kama shi da ribon masu kyau da suka kara fito da kyawan kwalliyar tata.

Fatima na sallahr la’asar ta ji ihun Ummi, alamun Mustapha ya iso.

Duk sai ta rasa abin da take karantawa ma, sai sautin dariyar Mustapha wacce take fita cike da annashuwa.

Ya shigo bedroom din dauke da Ziyad wanda ya ci karo da shi a falo kwance kan kujera.

Ganin ta manta abin da take yi, kawai sai ta zare hijab din lokaci daya kuma ta kai hannayenta du biyun ta rufe fuskarta.

Abin da ya yi matukar daukar hankalin Mustapha, ya aje Ziyad tare da janyo ta jikinsa ya rungume yana shakar kamshinta da ya yi kewa. Sai da ya gamsu, sannan ya janye ta a jikinsa yana fadin “I really miss you, ban fahimci haka ba sai yanzu”

Murmushi kadan ta yi hade da zama gefen gado tana daukar Ziyad da ya fara kuka “Mun yi kewarka fiye da yadda baki zai ambata.”

“Really?” ya tambaya daidai yana zama kusa da ita.

“Ba ka fahimci hakan ba?”

“Na fahimta. Ni ma kuma a can ko wane lokaci kuna raina ban taba mantawa daku ba, ki yarda da hakan.”

“Dama ban taba jin cewa ka manta ko za ka manta damu ba.”

Sun Dade suna fadawa junansu yadda suka yi kewar juna, sannan ya riko hannunta zuwa falo, ta yi saurin ja baya ganin kayan da ke jibge a tsakiyar falon.

“Ya dai?” ya yi saurin tambaya ganin yadda ta ci burki kamar ta ga abun tsoro.

“Wadannan kayan fa?”

“A kansu nake son yin magana madam”

Ya dan juya kamar mai neman wani abu “Wai ina Hana da Ummi?”

“Na san sun wuce islamiya” ta ba shi amsa daidai tana zama.

Ya kai hannunsa a kan kwalin generator yana fadin “Na san kallo bai dame ki ba, amma akwai lokacin da za ki ji kina sha’awa sannan ga yara, shi ya sa na sawo mana ƙaramin in ji, tun da ba ko wane lokaci ake samun wuta ba.

Kallon sa kawai take ba tare da ta, ce komai ba, ya janyo katuwar Ghana must go, ya fara ciro kayan ciki, yana ware na kowa, har ya gama, sannan ya ce “Wannan naki ne, wannan Ummi, wannan kuma na Hana, wadannan kuma na Ziyad ne. Kin san ban yi komai ba lokacin da kika haihu. Rago ma yana nan tafe sha Allah. Fatima ni kam na yi sa a samun ki a matsayin mata, tsawon lokacin nan ba ki taba ko canja min fuska ba, saboda ban yi miki komai a haihuwarki ba. “

Ta sauke hannayen da ta zuba tagumi hade da sauke ajiyar zuciya” To duk ina ka samu kudin yin wannan hidimar? “

” Loan na karba”

“Loan kuma?” ta yi saurin tambaya.

Ya jijjiga kai alamar eh.

Shiru ya biyo baya, kafin ta nisa cikin kwantar da murya ta ce “Abban Hanan wannan abun da ka yi shi ake kira da ba cinya ba kafar baya ko ace arziki ya ci Uban na da, an sayar da gida an sawo yashi. . Me ya sa za ka ci loan? kafin duk wadannan kayan muna rayuwarmu cikin farin ciki, wannan ya nuna kenan ko basu za mu yi farin ciki. Ba wai ina kushe ko kashe ma jiki ba ne a kan abin da ka yi, na san ka yi ne don kawai ka faranta min, amma Abban Hana ba bukatar sai ka karbi loan, in Sha Allah inda kake son mu je, za mu je a hankali komai yana da lokaci.”

Ya mike zuwa inda take zaune, hade da zama dab da ita
“Dalilin da ya sa tun farko ban fada miki ba, saboda na san za ki hana ni, kuma ina bukatar in yi wannan, ko wane lokaci ke ce kike sadaukarwa gare ni, ya kamata ni ma ko sau daya in yi hakan. Please ki yi farin ciki don Allah, hakan zai faranta min rai” ya maganar hade da lalubo kwayar idanunta. Duk sai suka yi murmushi, yayin da langabar da kai gefe yana sauraronta.

“Wato shi auran miji mai ilimi, riba biyu ne, ka ji dadin zama da shi a duniya, ya kuma ja ka zuwa aljanna”

Duk suka yi dariya a tare, kafin ya ce “Abu da ma kin ki karatun, da an fara sai ki watsar?”

“To ai kai din ma ba ka zauna ba.”

“Soon zan dawo in zauna, har sai na ji kina jin larabci kamar bakuwar Balarabiya”

“A wannan bakin?” ta yi saurin tambaya hade da nuna bakinta.

Ya juya gefe kadan sannan ya ce “Au! Na manta fa, ke kin ce ba za ki bata lokaci a duniya wajen koyon larabci ba, tun da a lahira kowa da shi zai yi magana ko?”

Cike da wasa ta ture shi “Haba wannan fa har da kuruciya.”

Suka kuma yin dariya a tare, musamman da tuna lokacin da ta fadi hakan. Mikewa ta yi zuwa inda kayan suke, ta shiga dagawa tana yaba ko wanne daga ciki. Ta dire a kan jakar da bai bude ba. “Wannan kuma fa?”

Ya dan yi jim, Sam baya son abin da zai kawo masu damuwa, bai san ya za ta dauki abun ba, shi ya sa kan dole ya karbi kyautar Blessing din.

“Wata da muke lodge daya, sunanta Blessing, ita ce ta bayar a kawo ma Hana da Ziyad”

Ga mamakinsa, sai ya ga ba ta nuna komai ba, hasalima cika fuskarta ta yi da fara’a tana daga kayan hade da yaba kyawunsu. Ta rufe da kwararowa ko wane addu’a a cikinsu.

Dalilin da ya karfafa masa gwiwar isar da sakon Blessing na tana son hotunan yaran.

Nan ma Fatima ba ta musa ba, ta ce sha Allah za a yi masu ya kai mata.

Wanshekare yan’uwanta Fatima suka cika gidan suna kallon kayan da Mustapha ya siya da kuma suyar ragon da aka yanka.

Ranar dai sai Fatima ta ji ta da kwarin gwiwarta, ko ba komai yan’uwanta na ta yabon Mustapha da fatan Allah ya sa hakan ya dore. Ba ta kwauron baki wajen cewa amin.
Karon farko ya nuna masu shi din dan halaka ne, ba a banza take sadaukarwa a kansa ba, ya cancanci hakan.

Addu’ar arba’in din Alhaji a masallaci aka yi ta, Fatima ji ta yi kamar a ranar aka yi mutuwar ta yi kuka ba kadan ba.

Mustapha ne ya yi ta lallashi, har ta dan saki jiki, a hankali kuma sai ta koma yin walwalarta.

<< Daga Karshe 29Daga Karshe 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×