Baki hangame Mama ta maimaita abin da Jamil ya fada “Ciki! Ciki fa ka ce?”
Shiru Jamil ya yi bai ce komai ba, illa wayarsa Nokia C130 da yake latsawa.
“To Allah Ya raba lafiya?”
A hankali ya ce “Amin.”
“Haba! Ni ina mamakin ciwo irin na Fatima, ta wuni ci ta kwana ci, sosai kiwo take kamar saniya. Amma wai ba ta lafiya” ta karasa maganar hannunta a kan haba alamun mamaki.
Jamil dai ba ce komai ba, wayarsa kawai yake tabawa.
A hankali maganar cikin Fatima ta zagaye dangi har zuwa kunnen Mustapha wanda ya yi farin ciki sosai, hade da fatan Allah Ya ba ta lafiya.
Satin Jamil daya ya koma India, Fatima kuma ta ci gaba da jinya, bangare daya kuma ana hidimar bikin Ummi.
Haka nan Fatima ke daurewa wajen bakin kokarinta ganin komai ya tafi daidai a bikin Ummin.
Ranar da za a kawo kayan lefe ma Ya Bashir ne ya dauke ta a mota ya kai ta gida, inda yan’uwa suka yi hidimar abinci karbar baki, Mustapha kam a lokacin bai samu zuwa ba, komai sai dai a waya ake sanar da shi.
Sai yamma aka mayar da Fatima gidan Mama, duk sauran hidimar kuwa a gidan Aunty Hauwa ake yin ta.
Ana sauran sati biki Mustapha ya iso.
Ko makaho ya lalubo ya taba fatarshi ya san cewa abubuwa sun fara gyaruwa, ruwan Abuja ya wanke shi fes, kasancewarsa dogo yanzu da ya yi yar ƙiba sai ya ƙara kyau, fatarsa ta yi haske, yayin da bakin sajensa ya kara kawata doguwar fuskarsa mai dauke da dogon hanci.
Fatima ta so dawowa gida amma Mustaphan ya hana, saboda ba ta iya yin komai, komai yi mata ake yi, hatta tsakar gida sai Mama ta kamo ta, take iya fitowa, ga rashin son hayaniya, amma bayan nan babu abin da ke damunta, kibarta take zubawa a zaune, ga jikinta ya kara murjewa ta yi kyau sosai.
Sai da aka sakko masallaci sannan Mustapha ya shigo gidan Mama, sanye yake da yadi fari Kal mai taushi, wanda har kana iya hango fara kal din vest din shi, dinki ne da ya samu kwararran tela, don sosai ya fito da Mustaphan, ga, wani kamshi mai dadi yana tashi a jikinsa.
Kafadarsa sallaya ce ya sagala, yayin da hannunshi na dama yake rike da Ziyad, wanda shi ma yake sanye cikin shadda blue da ta dau guga.
Ya yi kyau sosai ya kara girma da wayau.
Dakin Mama ya fara shiga ya gaishe ta, suka taba yar hira sannan ya wuce dakin da Fatima take.
A lokacin zaune take, sanye da doguwar rigar material mara nauyi, duk da rigar ba ta kama ta ba, amma ta cika ta dam, awara da souce din kwai take ci wacce Aunty Billy ta yo mata.
Dakin tsab yake, tun safe Ummi ta zo ta gyara mata shi. Dama haka take yi kullum, za ta zo ta kwashe duk wani kayan datti na Fatima ta je gidan Aunty Hauwa ta wanke bayan ta gyara mata daki.
Sallama ya yi hade da yaye Labulen dakin, kwayar idanunsu ta hadu, suka sakar ma juna murmushi.
Gefenta ya zauna jikinsa na gugar nata, a saitin kunnenta ya ce “Uwar biyu”
Yadda sautin na sa ya fita zuwa dodon kunnenta sai ya saukar mata da kasala, sosai ta yi kewarsa
Ganin ba ta ce komai ba, ya kara kai bakinsa daidai kunnenta, maimakon ya yi magana kamar yadda ta yi tsammani sai ya dan ciji gefen kunnen a hankali.
Dalilin da ya sanya ta dariya mai dan sauti hade da ture shi.
Shi ma dariyar yake kafin ya ce “Kina fushi ne?”
Sai da ta dan harareshi kafin ta ce “Ba dole ba, tun 11am aka ce an ganka gidan Aunty Hauwa.”
Ya kamo hannunta mai rike da awarar ya kai bakinsa.
“So kike Mama ta ce ba ni da kunya, ina isowa na yo wajen ki”
Ba ta ce komai ba, sai dai ta janye hannunta da yake rike a hannunsa.
“Kin gan ki kuwa? Kamar ba a Nigeria kike rayuwa, kin yi wani fresh kamar nunan nar gwanda.”
Ya karasa maganar hade da kwantar da kansa a bayanta.
“Kai ma ka yi kyau sosai, da alama Abuja akwai dadi, lokaci daya ka canja, kamar ba kai ne Malam Mustaphan nan ba rike yar bulala yana koyarwa a islamiya.”
Dariya yake yi sosai daga kwancen da yake a bayanta kafin ya ce “I miss you a lot, and I mean it.”
Ba sai ya fada ba, daga yadda yake shige mata ta fahimci hakan, ko ba komai ma ya yi kokari almost 4month rabon shi da ita. Kuma ko yanzu ma ba za ta iya daukar shi ba, ita yanzu abu uku take iya yi, bacci, cin abinci sai sallah, ita ma a zaune take yin ta.
Wani irin ciki ne da ko a karance – karancenta ba ta karanto irin shi ba.
Sosai ya kwanta hade da dora duk rabin jikinsa a kanta.
Yayin da hannunta daya yake kan sumarsa tana shafawa a hankali. Tattaunawa suke game da bikin Ummi, kafin daga bisani Mustaphan ya fadi abin da ya tsaya mishi kamar kashin wuya.
“Fatima Blessing na san zuwa bikin nan, kamar har da kanwarta ma.”
Ya yi maganar idanuwansa kafe a kanta.
“Allah Ya kawo su lafiya. Yaushe?”
“Laraba.”
“Allah Ya kai mu.” ta fada ba tare da ta nuna wata alama ta damuwa ba.
Haka suka ci gaba da hira har bacci ya dauke Mustapha, ba kuma ta tashe shi ba, sai da ta ji an kira sallah a masallacin hakimi.
********
Satin dai ko wane bangare shirye-shiryen biki ake yi, yayin da amarya da kawayenta suke ta gabatar da abubuwan da suke son shiryawa.
Ranar Laraba kuwa gidan Fatima ya fara samun baki, haka nan ta lallaba ta koma gida.
Bangaren Inna Mustapha ya gyara domin saukar danginshi.
A ranar kuma su Blessing suka iso misalin karfe goma na dare.
Dakin Ummi na da aka gyare masu suka sauka a nan.
Mustapha ya yi musu tarba mai kyau duk da dare ne.
Da safe ne ma mutane suka san da zuwansu, masu tsegumi na yi masu zunde ma na yi. Wasu su yaba wasu kuma su ga rashin dacewar zuwan nasu.
Fatima dai ba kowa zai gane yanayinta ba, ba ta daure musu ba, kuma ba ta sake musu fuska ba, idan ba jefa ta aka yi cikin batunsu ba, ba ta shiga, amma kuma komai na kyautatawa da karramawa tana sa a yi musu.
Wani abu da ya tsayawa Blessing shi ne yadda komai ake nema sai dai a zo wurin Fatima, duk wata shawara da ita ake yi, ba a aiwatar da komai sai da cewarta.
Ita kanta amaryar kominta a wurin Fatima ne, wannan ya tabbatarwa da su Blessing ba karamar fada ce Fatima take da ita a dangin Mustapha ba.
Yadda take kamewa kamar wata Gimbiya sai ta rika yi musu kwarjini.
Sosai Blessing take son ta ga Fatima ta tsoma ta a wani lamari ko ta yi mata magana, musamman da Husaina ta shige cikin ƴanmatan amarya.
Ba za ta ce ta Fatima, Mustapha ko danginsu sun wulakantata ba, babu abin da basu yi mata ba, babu kyara babu tsangwama amma kuma dai ta rasa me ya hana ta jin dadin ziyarar.
Ranar Alhamis amarya da kawayenta suka shirya dinner gidan Hakimi, Fatima ba ta je ba, amma ta sanya an taka Blessing, kuma zuwa wurin ya yi mata dadi, daga nan ne ma ta shiga gidan Mama, sai ta ji gidan ya fi mata dadin zama.
Tun daga lokacin Kuwa ta tare a gidan Maman sai dai aka aiko mata da kayanta.
Ranar Juma’a aka daura aure, sosai Mustapha ya yi kokari wajen fitar da kanwarsa kunya, Fatima ma da take matsayin uwa ta yi kokari, don san ta daya ta sayar ta yi wa Ummi kayan kitchen masu kyau.
Ko me ta yi wa Ummi ba ta fadi ba, don Ummi tamkar kanwa take a wurin ta, ta yi mata komai, tun ba yanzu da take fama da rashin lafiya ba, ku san kominta Ummi ce ke yi.
Blessing ma kuloli da turarukan wuta da na kamshi ta kawo ma Ummi.
Bayan gudunmuwar kudin da ta ba Mustapha har dubu 50 daga iyayenta.
Misalin karfe hudu aka fitar da kidin ƙwarya a tsakar gida, wanda ya sa Fatima barin gidan dole, don Sam ba ta son hayaniya karfin hali kawai take yi.
Dole ta taho gidan Mama yayin da ƴanmatan amarya da abokanni arziki suke ta rakashewa a gidan.
Misalin karfe takwas tana zaune gefen gadon Mama mutane suka shigo rike da Ummi wacce ke lulllube cikin mayafi, daga lokacin da aka shirya ta zuwa gidan miji kawo yanzu kuka take yi. Haka ta kafe a kan lallai ba za ta tafi ba, sai an kawo ta wurin Fatima. Dalilin da ya sa kenan motar ta ci burki a kofar gidan Mama.
Karasowarsu dakin ke da wuya Ummi ta fada kan Fatima hade da sakin kuka mai karya zuciya, lokaci daya Fatima ta tuna da lokacin nata auran, lokacin da aka lullubota daga gidan Aunty Hauwa zuwa wurin Mama.
Take ta ji zuciyarta ta karye, idanunta suka cika da hawaye.
Sai ta shiga bubbuga bayan Ummin hawaye na ci gaba da zarya a kan kuncin ta
Hakan duk sai ya kashe zuciyar mutane, wasu suka kasa rike kwallansu sai da ya zubo. Wasu suka shiga jimami.
Sosai Ummi ta kankame Fatima, cikin kuka take fadin “Aunty Fati ki yafe min don Allah”
Ita cikin muryar kuka ta ce “Na yafe miki Ummi, babu abin da kika min, na rayu da ke babu raini sai girmamawa, ina yi miki fatan alkairi da zama lafiya Ummi, ki yi hakuri, shi ne jigon ko wane irin zama…” ta yi shiru lokaci daya kuma tana dauke hawayen da ke bin kumatunta.
A hankali ta daga Ummin daga jikinta, cike da karfin hali ta nufi kofa da ita, a lokacin ne ta ci karo da Blessing da kanwarta Husaina.
Yadda Blessing ta ga Ummi da Fatima sai, zuciyar ta ta kuma karyewa. Ba san me ya sa ba, duk lokacin da za ta ga Fatima sai gabanta ya yi wata irin faduwa ko sunanta aka ambata gabanta faduwa yake yi.
A, bangaren Fatima kuwa haka nan dai ta kasa sakin jiki da Blessing, ba ta kin ta kuma ba za ta ce tana sonta ba.
Sai da ta saka Ummi a mota sannan ta dawo gida, kuka take yi sosai, kukan da ita kanta ba ta ce ga dalilinshi ba, ya fi kama da dama jiran abun kukan take yi.
Kan gadon Mama ta kwanta ta ci kukanta mai isar ta, sannan ta yi shiru.
“Idan kin gama kukan ki fita ga mijinki can ya zo za ku tafi gida.” cewar Mama da ta shigo dakin rike da hannun Ziyad.
“Wai yau Fatima ce ke ma wani fada, ko yaushe aka gama ma mata nata har take ma wani oho”
Murmushi kawai ta yi, a lokacin da take gyara zaman hijabinta, kamar dai mai koyon tafiya haka ta fita tsakar gidan, a lokacin tsaye yake da Husaina, koda ta isa ba ta katse masu maganarsu ba. Husainar tana fada mishi kan Blessing na ciwo ne, shi ne ya ce Husainar ta biyo su ta karbi magani ta kai mata.
Ko a hanya Husaina da Mustapha ne ke hira jefi-jefi, amma Fatima ko sau daya ba ta jefa tata ba.
Sai da aka sayi maganin ne ta ce “Ki yi mata sannu, Allah Ya sawake”
Husainar ta amsa da amin.
Bayan sun dauki hanyar gida ne ya ce “Ina Ziyad din?”
“Ya na wurin Mama.”
“Can zai kwana?” ya kuma tambaya.
“Eh.” ta amsa shi.
Ya dan yi shiru kafin ya ce “Wai me ya sa kamar hankalinki bai kwanta dasu Blessing ba?”
Shiru ta dan yi kafin ta ce “Ban sani ba ni ma, amma dai ina jin haka nan, saboda dai tana daya daga cikin mutanen da tarihina ba zai cika ba sai da ita.”
“She is very simple”
” I know and I see” ta kuma ba shi amsa.
Sai ya yada maganar Blessing din ya dakko maganar yadda bikin ya kasance.
“Abin da na fahimta shi ne Ummi ta fi kewarki fiye da kowa”
Murmushi ya bayyana a fuskar Fatima hade da fadin “ko a cikin yan’uwana ban taba jin na shaku da wata ko ina sonta ba kamar Ummi.”
Ya san gaskiya ta fada, hatta shi da kanshi, zai iya cewa ba ta son shi kamar yadda take son Ummin.
Ita kamar ba ta san so ba, kawai dai jin shi take yi.
Kalaman nata sun yi mishi dadi, don yanzu dai a duniya bayan yaranshi, ba shi da wata ko wani mafi kusanci da shi kamar Ummin. Yana son ta sosai, baya son abin da zai bata mata rai, sosai take son ya ji ya yi mata wani abu da za ta ji dadinshi.
A wajen auran nan bakin rai bakin fama ya yi, ku san duk wani tsumi da tanadinshi sai da ya kare a kanta. Abin farin ciki kuma shi ne yadda mutane suka rika shi mishi albarka a kan ya fitar da ƴar’uwarshi kunya.
Ya janyo ta jikinsa hade da shafa faffadan bayanta, sosai yake jin sonta da kaunarta a zuciyarsa, wannan ya faru ne saboda yadda ƴan’uwansa ke ta yaba bajintar da ta yi a wurin bikin, tun daga kan gudummawa, saboda duk abin uwa ke yi, babu abin da Fatima ba ta yi ba. Har kawo kan abinci da hidima da mutane, a kananun shekarunta babu wanda ya yi tunanin ita kadai za ta iya handling din auran da ƴa. Sai ga shi ta ba kowa mamaki don ma ba ta da cikakkar lafiya.
Cikin murya mai taushi ya ce “Ko wane lokaci idan zan gode miki, sai in ji kalmomin duk sun yi kadan wajen yin hakan. Fatana kawai Allah Ya ba ni abin da zan yi miki, kada ki yi kukan komai, kamar yadda kika hana ni da kuma ƴar’uwarta kukan maraici. Na gode Fatima, duk namijin da ya same ki a matsayin mata tabbas ya yi dace, tsawon shekarunmu na aure, ba na ce ga laifinki ba, idan har ni ne zan daga kafa ki shiga aljanna Fatima, Allah ka shaida ni dai na daga wa matata Ya Allah don ni kada ka hukunta da laifin komai na yafe mata.”
Sai Fatima ta tsinci kanta da zubar da hawayen da ta rasa dalilinsu, abu ma fi tsada a wurinta, ba komai ne ke sanyata kuka ba, amma a wannan lokacin sai ta ji zuciyarta ta yi rauni, tana jin kamar mutuwa za ta yi.
Shi ma ji ya yi zuciyarsa ta laushi, ya ka sa furta komai a matsayin lallashi, illa shafa ta da ya shiga yi cikin sigar lallashi.
I like this book,Allah ya kara basira.
Amin Ya Rabbb
Ina godiya Hajara