Skip to content
Part 38 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tun daga Katsina Zainab ta bayar da sakon admission din Fatima aka kawo mata, ranar kam ji tayi kamar ta tsaga kirjinta ta shigar da admission, tamkar dai result din ta na gama makaranta aka ba ta.

Ba ta damu da yawan shekarun da suka ba ta ba, fatanta dai kawar koda shekarun sun fi hudu ta gama lafiya ta kuma amshi result din lafiya.

Tana idar da sallah ko hijab din ba ta cire ba Yan tagwayenta ta kwasa sai gidan Mama.

Rabon da ta je gidan ku san sati biyar kenan.

Mama zaune tana bara gyada a kofar daki ta amsa sallamar ta.

“Yau a garin, in ji maki baƙo?”

Dan murmushi ta yi lokacin da take zama, ta kuma dora Hassan a kan cinyar Mama sannan ta ce “Ƙina ake yi kenan?”

“Ke da gidan ubanki.” Mama ta ce lokacin take kwakulo gyadar da Hassan ya ciko hannu da ita.

Da ga yadda Mama ke amsa mata magana ta fahimci jiran ta take yi, shi ya sa ta canja salon hirar ta hanyar gaishe da Mama. Bayan ta amsa gaisuwar ne kuma ta cewa “Me za a yi da gyada?”

“Dan gauda nake son Bilkisu ta yi min gobe idan Allah Ya kai mu.”

“Allah Ya kai mu”

“Amin in ji Mama.”

Fatima ta mikawa Mama admission din ba tare da ta ce komai ba.

Mama ta shiga jujjuyawa kafin ta ce “Me ye wannan din?”

“admission ne na samu”

Ba tun yanzu Mama ta san me admission ke nufi, dalilin da ya sa kennan ta mayar da hankalinta sosai kan Fatima “Na ki kuma?”

“Eh.” Fatima ta amsa ta.

Tabe baki Mama ta yi hade da fadin “Wai sai bayan ido ya mutu ne, kike son kwalli ya tashe shi?”

Shiru ba ta ce komai ba, sai wasa da bawon gyadan da take yi.

“Mustaphan ne ya samo miki?”

Kai ta girgiza alamar a’a

“To waye?” Mama ta kuma jefa mata wata tambaya hade da kafe ta da idanu.

“Ni ce na nema da kaina.”

“To wace makarantar?”

“Jami’ar Umaru Musa da ke Katsina.” Fatima ta amsa ta

“Gagaso kenan. Wai gashin mara ba ɗa. Haihuwa uku yara hudu, amma dai har yanzu a batun hankali Fatima da sauranki. To idan ba haka ba, yaushe ake kudin kasa, bayan gari ya watse? Da can ba ki yi karatun ba sai yanzu, da hidimomi suka zagaye ki. Sannan har Katsina. To tun wuri ki watsar da wannan batun, ki rungumi yaranki.”

“Zan iya Mama, in sha Allah zan yi”

“Kin ga! Ki bar wannan mafarkin, dama ce dai kin yi wasa da ita, kuma ta wuce ki.”

“Ba Ta wuce ni ba, har yanzu akwai sauran dama tun da, da raina kuma da lafiya ta.”

“To ai sai ki je ki yi ta yi, tun da dama abin da kika sanya a ranki ke shi kike yi, babu wanda ya isa bare ya hana ki. Amma wani karatu da rana tsaka haka gatsal.”

Shiru Fatima ta yi ba ta ce komai ba, har zuwa lokacin da Mama ta kuma cewa “Kuma sai ki tanadi kudin makarantar, don ba uban da za ki dorawa hidima, kowa yana fama da kansa yauwa.”

“Ba zan dorawa kowa ba sha Allah. Ni na sanya kaina, kuma in sha Allah zan yi komai da kaina.

“Ke dai kika sani kuma.”

“Ni dai kawai ki sanya min albarka” Fatima ta fada tana kallon Mama.

Mama ta mika mata takardar admission din tana fadin “Allah Ya sanya alkairi.”

“Amin” cewar Fatima hade da amsar takardar.

“Yauwa!” in ji Mama alamun ta tuna wani abu.

Fatima ta yi saurin kallon ta.

“ki cire ni a cikin jerin masu yi miki raino yauwa. Don ba zan iya ba. Babu yaron da zan dauka, lokacin da na ci wahalar nawa babu wanda ya taya ni.”

Shiru Fatima ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Wani lokaci Idan Mama ta yi musu wani abu, ka rantse ba ita ce ta haifesu ba, nata ma ya fi na kowa zafi.

Shiru ta yi, hade da mikewa ta goya Hassan, sannan ta saba Husaini ta fice daga gidan.

Gidan Aunty Hauwa ta yi burki.

Aunty Hauwa zaune a tsakiyar gadonta, idan har ba ta falo ta za ka same ta bedroom a tsakiyar gadonta, ko me za ta yi a nan take yi, sallah ce ke sakko da ita.

In ji ta ta ce “A duniya dai ina son gado.”

Daga yadda ta ga Fatiman ta shigo ta san akwai matsala, shi ya sa ma ta bi ta da kallo, har zuwa lokacin da ta dire su Hassan.

Zamanta kuma ya yi daidai da sakin kukanta, irin kukan nan da ya dade yana cin mutum amma ba a samu damar yi ba

Har cikin ranta Aunty Hauwa ke jin kukan, ta sakko zuwa inda Fatima take zaune, lallashinta take yi hade da tambayarta me ya faru, sai da ta yi kukan sosai, sannan ta sassauta kukan kadan ta ce “Ina son a siyar min da saniyata, wacce
Baba ya ba ni.”

Shiru Aunty Hauwa ta yi kafin ta ce “Me ya sa za a siyar?”

“Ina son in yi registration ne.” cikin kuka ta kuma fada.

Cike da mamaki Aunty Hauwa ta ce “Wane irin registration kuma?”

Admission din ta mika mata, Aunty Hauwa ta shiga karantawa, sai ta da kai karshe sannan ta ce “Makarantar ta tashi ne?”

Kai ta daga alamar eh.

Sai da ta Aunty Hauwa ta dan nisa sannan ta ce “To me ya sa ba za ki jira ko yaye yaran nan ba?”

Hannu ta kai hade da dauke ragowar hawaye ta ce “Ba zan kara barin dama ta wuce ni ba.”

“To wai yanzu me ye ma na kukan?” cewar Aunty Hauwa tana kallon Fatima.

“Ni da Mama ne, wani lokaci sai ki ga kamar ba ita ta haife ni ba, har tsoron kawo mata kukana nake yi, saboda tsakaninmu Allah Ya kara ne, shi ya sa sai in danne damuwata.”Ta karasa maganar cikin yanayin da ya ba Aunty Hauwa tausayi.

” Sai hak’uri Mama uwa ce a gare mu, kuma koma dai menene na son tana sonmu, ba za ta so abin da zai ba ta ranmu ba. “

” Ku ko? ” Fatima ta yi saurin amshe maganar, kafin Aunty Hauwa ta ce wani abu kuma sai ta dora “Ni kam Mama tana son ta ga wani abu mara kyau da ya shafi aurena, saboda kawai ban auri zabinta ba. Ina abin da ya wuce ya wuce ai, shi Ya Jamil din ba gaya can zaune da matarshi ba.”

“Bari fadin haka ma, wlh Fatima Mama ba ta son duk wani abu mara dadi da zai taba ki. Maganar auran Mustaphan nan sosai ta ji haushinshi, wlh ba ta goyon baya.”

“Hmmm!” Fatima ta ce kafin daga bisani ta ce

“Idan ta ji haushi me ya sa ba ta taimaka min wajen daga tawa darajar ba, na zo mata da batun karatu, wai dole sai in bari ba zan iya ba, na ce zan iya ta ce wai to in nemi kudin registration dina, haka kar in lissafata cikin masu yi min reno” wannan karon sai da guntun hawaye ya gangaro mata

Murmushi Aunty Hauwa ta yi sannan ta ce “Amma ai da gaskiyarta. Ni ba zan hanaki karatu ba, har yanzu kina d dama, amma da ki bari sai kin yaye. Makaranta akwai struggling sosai, yin sa da yara biyu kuma ba karamin aiki ba ne”

Shiru Fatima ta yi alamar nazari “Ki yi min addu’a kawai” Ta ce cike da kwarin gwiwa.

“To na ga Yar’aduwa University, ya abun zai kasance, ko gidan Lami za ki zauna?”

Kai ta girgiza alamar a’a

“Hostel?”

Nan ma kan ta girgiza alamar a’a sannan ta ce “Gida zan kama, idan na tafi sai semester ta kare.”

Aunty Hauwa ta saki dariyar da ba ta yi niyya ba ta hada da fadin “Lallai abun azeemun ne. To auran fa?”

Zumbura baki ta yi “To ni ina, ruwana da shi, ba ya yi aurashi ba”

Wani Murmushin Aunty Hauwa ta yi “Kenan kin bar amaryar ke kuma kin tafi jami’a?”

Ta kara turo bakinta sosai sannan ta jinjiga kai.

“Lallai yarinya da sauranki, ba a yi wa namiji haka, idan ba haka ba kuwa wlh to tsugunne ba ta kare miki ba, kamar kin siyar da kare kin siyo biri.”

“Don Allah kar ki kara caza min kai” cewar Fatima cikin sauri.

“To yaran fa?” Aunty Hauwa ta kuma tambaya.

“Zan bar ƴar Ummi (Haka take kiran Hana wani lokaci) wurin Auntynta. Ziyad kuma dama ai dan gidanki ne.” ta karasa maganar tana kallon Aunty Hauwa.

“Uhhh! Lallai,, ke kin gama tsara komai ma. To shi Mustapha bai da kudin registration din ya nemar miki admission?”

“Bai san ma da maganar ba, sai ya zo cikin satin zan yi mishi.”

“Uhhhh! Umm!” Aunty Hauwa ta kuma fada tana jujjuya admission din.

Duk suka yi shiru. Aunty Hauwa ta katse shirun da fadin “Maganar registration Fatima ai ba sai an sayar da saniya ba”

“Ni dai a sayar min, ban son in tambayi kowa” yadda ta yi maganar sai ya ba Aunty dariya, Fatima kallon hidimar makarantar high institution take Kamar ta secondary.

“Dama saniyar ba an ce ba ta da lafiya ba?”

Fatima ta tambaya hade kallon Aunty Hauwa.

“Eh kam. Zan dai je wurin Ja’en duk yadda muka yi zan zo gidan in same ki.”

Hira suka shiga yi, a kan bikin Zainab da bai wuce wata uku ba, na Mustapha ne saura wata biyu, sai da aka yi magariba sannan Fatima ta tafi gida, bayan ta ci abinci.

Tun da Fatima ta bar gidan, Aunty Hauwa ta kira Jamil ta labarta mishi, sosai ya ji dadin yunkurin Fatiman, kuma shi decision din ma ya burge shi, ko shi zai iya biya mata haya, har ta kare shekarun da suka ba ta.

Yanzu ma ya ce da Aunty Hauwa zai biya kudin registration din amma kar ta fadawa Fatiman.

Ranar Laraba da misalin karfe 11am Aunty Hauwa ta isa gidan Fatima.

A lokacin Hussain take yankewa farce yana bacci.

Suka gaisa sannan Aunty ta mika mata kudi 120k ta ce na saniyar da aka sayar ne.

Ta kuma mika mata wasu 100k, ta ce sune suka hada mata a matsayin gudunmuwarsu, don sai da Aunty Hauwa ta kira duk sauran ƴan’awan ta ce kowa ya hado na shi.

Duk da Mama ba ta so hakan ba, so take a bar Fatima ta ji jiki, kila ta kara hankali.

Har kukan murna ta yi, no matter how dan’uwa ba ƙashin yadawa ba ne, musamman ace irin nata, da suke kokarin rufa mata asiri a duk lokacin da yake son tonuwa

Fatanta Allah Ya ba ta abin da za ta yi musu ita ma.

Duk bayan sati biyu Mustapha yake zuwa gida, wannan Juma’ar haka ya iso gidan ana sakkowa masallaci.

Kamar kullum gidan tsaf, Matar gidan ma tsaf, duk da ga duk wanda ya santa, idan ya tsananta kallon ta zai fahimci akwai abin da ke damunta, sai dai ita din macece mai boye rauninta.

Ita kadaice zaune a falo, don yara sun dauki su Hassan zuwa yawo, sai ta yi shi kyau sosai, kuriciyarta ta kuma bayyana sosai a cikin riga da siket din ba.

Ba shi kawai ya ga kyan Fatimar ba, ita kanta ko wane lokaci idan ya zo canjawa yake, wayewa gayu da kyawonsa kara karuwa suke, sai ta ganshi kamar ba mijinta ba.

Ba yabo fa fallasa ta tare shi, ba ta nuna mishi admission din ba sai da dare, sannan ta mika mishi, hade da kafe shi da ido tana jiran respond din shi.

Ya gama jujjuya admission din sannan ya ce “Me kenan?”

Sosai ranta ya baci da tambayar da kuma yadda ya yi tambayar.

“Makaranta zan koma” kai tsaye ta yi maganar

“Makaranta?”

“Eh.” ta kuma amsawa.

“Kin san abin da kika yi kuwa?” ya yi tambayar hade da mikewa zaune daga kwancan da yake a kan tabarma.

“Me na yi” ita ma ta tambaya cikin halin ko in kula.

“Amma dai kin san ba zaman kanki kike yi ba ko?”

“To ai shi ya sa na nuna ma. Idan ina zaman kaina ne, ai sai dai kawai ka ga bana nan.”

Ta cikin duhun yake kallon ta, yadda take maganar ya tabbatar mishi kadan take jira.

Sai ya mika mata admission din ya ce “To aiko yanzu ba amfanin ba ni, wanda ya isa, kuka yi shawarar neman admission din, aka samu admission din shi ya kamata ki ci gaba da shawarar yadda karatun zai kasance, amma ni ki bar ni a yadda kika aje ni”

Sosai haushinshi take ji, musamman yanzu, wai shi ne har da zuwa wurin Aunty Hauwa yana fada mata lefen da za a yi wa Blessing a samu atamfofi masu kyau yadda ba za a raina su ba, shi ta hidimar auranshi kawai yake, me ye laifi don kowa ya yi abin da yake gabansh.

“Zan je registration ranar Monday, idan na kammala komai zan tafi next Sunday”

“Duk yadda kika yi, ai ke ce da kanki, ni kuma yanzu ina ruwana, in ya so ma, ki tafi yanzu. Duk wani abu kuma da ya shafi karatunki ki daina yi da ni, ki je can ki yi da wanda kuka fara.”

Tsawon shekara hudu wannan ne karon farko da suka samu babban sabani, sabanin da kowa yake ji dole sai dan’uwansa ya ba shi hak’uri sannan zai sakko.

Saboda kowa gani yake shi aka yi wa laifi.

Kwana biyun haka ya yi su ba dadi, shi ya sa asubar fari ranar Sunday ya bar garin.

Zuciyarta ba dadi, amma haka ta shiga shirin tafiya registration din ta, maimakon ma ta tafi Monday din sai kawai ta tafi Sunday da yamma.

Gidan Aunty Lami ta sauka, inda Zainab za ta yi mata rakiya.

<< Daga Karshe 37Daga Karshe 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×