Skip to content
Part 39 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tun 8am suka bar gida, basu dawo ba sai 5pm, a lokacin kuwa hatta magana ma dakyar suke yin ta, a haka kuma basu gama ba, don ba ta bude wasu file din ba.

Yaran ma a gajiye suke, Aunty Lami na watsa musu ruwa sai bacci.

Su dai dakyar suka daure aka yi sallahr isha’i.

Washegari ma da wuri suka fita, zuwa 4pm suka dawo. Wannan karon kam wahalar akwai sauki ba kamar ta jiya ba, shi ya sa suka baje a falon Aunty Lami bayan sun watsa ruwa sun kuma ci abinci. Su Hassan ne kawai ke bacci.

Aunty Lami ta ce “Wai me ya sa ba za ki yi zamanki a nan ba, sai wani kama gida?”

“Kashh!” Fatima ta ce hade da gyara zaman zanen da ke jikinta “Ni fa ina son in yi rayuwa irin ta dalibai ne, kuma nan ai ya yi nisa ma da makarantar.”

“A shiga ruwa lahiya” Aunty Lami ta ce sannan ta dora da “Shi Mustaphan nan zai rika biyo ki kenan?”

“Oho mar!” yadda ta yi maganar ne ya sa Aunty Lami da Zainab kallon ta

“Wai har an gama soyayyar?” Zainab ta fada cike da zolaya.

Fatima ta mike zaune “To zan yi miki rashin mutunci yar rainin wayau, ki yi mata magana Aunty Lami babu ruwanta da ni.”

Aunty Lami ta fashe da dariya kafin ta ce “Ai kun hi kusa”

“Atoh” Zainab ta ce hade da dariya.

Komawa ta yi ta kwanta, tana jin duk hirar da suke ba ta sanya baki ba.

Sosai take jin wani bacin rai a kan Mustapha, ba ta taba tunanin zai yi mata haka ba, ta dauka ko dawowa ya yi gida ya samu ba ta nan, tana makaranta ba zai juya mata baya ba, duba da yadda ta yi supporting din nashi karatun. Amma tun da ya tafi ko kira, ita kuma ta dauki alkawarin koma menene ba za ta kira shi ba.

Laraba tun safe ta baro Katsina cike da farin ciki, hade da alwashi sha Allah ranar lahadi za ta dawo school, idan har maganar gidan ta daidaita, kamar yadda hakimi ya ce a jira shi, a kan maganar gida.

Misalin karfe daya ta sauka kofar gidan Mama, bayan ta biya mai mashin kudi, ta shiga gidan hade da sallama.

Mama na alwala ta amsa mata, sai da suka yi sallah, sannan ta gaishe ta hade da fiddo mata da sakon da Aunty Lami ta bayar a kawo mata.

Ta amsa hade da godiya, ta dora da “Duk suna lafiya ko?”

Fatima ta amsa da eh, sannan ta ce “Na gama komai Mama”

“To da kyau.” ” cikin hali ko in kula ta yi maganar

Ta tattara hankalinta kaf a kan Maman kafin ta ce” Don Allah wai me nake yi miki da ba kya so? “

Ga nin Mama ba ta amsa ba, sai ta kuma cewa” Don Allah Mama ki yafe min. “

Sosai maganganum suka zo mata a bazata, dalilin da ya sa kenan ta zubawa Fatima ido tana kallon ta.

” Na san na yi miki abubuwa marasa dadi, sannan kin kullace ni a kan wasu abubuwa. Shi ya sa nake neman afuwarki. Don Allah ki yafe min. “

Take jikin Mama ya yi sanyi, cikin raunannar murya ta ce “Na yafe miki. Allah Ya yafe mu ba ki daya.”

“Na gode.”

Shiru ya ratsa wurin kafin Fatima ta kuma cewa “Ban zabi karatun nan don kin bin umarninki ba Mama, kawai dai ba na son dama ta wuce ni, don Allah daga cikin zuciyarki, nake son ki sanya min albarka.”

Mama ta kuma nisawa “Har cikin ranta ta ce Allah Ya albarkaci karatunki, ya sa ki fara lafiya, ki kuma gama lafiya”

Daga can kasan zuciyarta take jin wata irin gamsuwa da addu’ar da Mama ta yi mata.

Idan har Mama ta sanyawa abun albarka, sha fushin Mustapha ba zai shafi karatun nata ba.

“Yaushe za ki tafi?” Mama ta katse mata tunani.

“Ranar lahadi”

“an samu gidan ne?”
Mama ta kuma tambaya

“Hakimi ya ce a jira shi, ni dai ko ba a samu ba, zan tafi ranar Lahadi in fara zama gidan Aunty Lami.”

“To Allah Ya kai mu. Shi Mustaphan ya amince ko?”

Fatima ta dan juya kai gefe kadan, hade da dan cije lebenta na kasa kafin ta ce “Ban sani ba dai har yanzu.”

“Kamar ya?” Mama ta yi saurin tambaya

Cikin muryar da ke nuna damuwa ta ce “Ya ce duk abin da ya shafi karatuna ba da shi zan tattauna ba”

Mama ta kafe ta da ido kafin ta ce “Me yasa ya fadi haka”

Sai da ta lashi labbanta sannan ta ce “Wai ban sanar mishi ba tun farko.

Gyara zama Mama ta yi hade da fadin” Kin yi kuskure kam, koda ba zai ba ki goyon baya ba, ya kamata ki fada mishi shi din mijinki. “

Hanyar kofar gida take kallo kamar mai jiran shigowar wani, jimawa kadan ta mayar da hankalinta a kan Mama.” Abin da na yi shi ne ya dace, Ya Mustapha hankalinshi ba a kan karatuna yake ba, a kan auransa ne. Yaushe zan zauna ina jiran gawon shanu?”

“Gaba dai kar ki kara wannan kuskure ne.”

“Ba zan kara ba sha Allah.”

Duk suka wai ga suna kallon Aunty Hauwa da ta shigo tana waya.

“Anya akwai ranar da Aunty Hauwa ba ta shigowa gidan nan Mama? Ita fa kamar ba aure ma ta yi ba.”

Duk da wayar da Aunty Hauwan ke yi hakan bai hana ta wurgawa Fatima harara ba.

Mama dai ba ta ce komai ba. Fatima ta dora da “A rana ta zo sau uku shi ne ta zo kadan, haka nan ma sai ta shigo ta sha ruwa ta koma. Kai jama’a, har bayi sai ta baro gidanta ta zo nan ta shiga, aure kusa da gida bai yi ba.”

A daidai lokacin Aunty Hauwa ta kare wayar, ta juya kan Fatima tana fadin “Ina ruwan ki idan na shigo sau goma ma, ba gidanmu ba ne, ko cewa na yi zan dawo da kwana ina ruwanki?”

“Allah Ya ba ki hakuri”

Yadda ta yi maganar sai ya kara harzuka Aunty Hauwa ta ce “Billahillazi zan cire hijabi, mu daku cikin gidan nan idan ganin ci kike min.”

Daga Fatima har Mama dariya suka saki, cikin dariya Fatima ta ce “Yo Aunty Hauwa fada da ke dambe ai sai dai mai kararren kwana. Kishiyarki ma bin ki take sau da kafa.”

Harara dai ta kuma aikawa Fatima sannan ta ce “An samu gidan”

Sai Fatima ta mike zuwa inda Aunty Hauwa take hade da rungumeta tana fadin “Wayyo Allah masoyiyata na gode, Allah Ya saka miki da alkairi dama na san daga uwata a yanzu dai sai ke wadanda suka fi sona. Ashe abun alkairi kika zo fada.”

Ture ta Aunty Hauwa ta yi tare da fadin “Aike raininki ya yi yawa.”

Kakkabe wurin zama Fatima ta shiga yi tana fadin “Zo ki zauna ranki ya dade gimbiya Aunty Hauwa, ke da gidanku, wa ya isa ya yi miki iyaka, zo ki zauna ranki ya dade.”

Zama ta yi hade da fadin “Allah dai Ya, shirye ki”

“Amin Auntyna masoyiyata.”

Gabadayansu suka yi dariya, kafin suka shiga hira, har suka gangaro maganar auran Mustapha.

A nan ne Fatima ke jin cewa a Abuja za a yi komai ba a Sandamu ba.

Sosai abun ya taba ta, amma sai ta share, abin da ta sani dai shi ne babu inda za ta je, har a yi a gama ma tana makaranta.

Ba ta koma gida ba sai 8am.

Tun daga lokacin kuma ta fara shirye-shiryen tafiya, Ummi ce ke taya, Mustapha kam ko sau daya bai kira ta ba, ita ma kuma ba ta kira ba.

Ranar asabar Ummi tun safe tana gidan Fatima, sai da suka shirya duk wasu kaya da za ta tafi dasu, da wanda kuma za ta bari, gidan bai koma daidai ba, sai wajen karfe shidda na yamma. Wanka suka yi, sannan suka ci jallof din taliya, Fatima ta yi wa Ummi rakiya.

Misalin karfe goma ta turawa Mustapha sako kamar haka “Zan wuce Katsina gobe.”

A lokacin zaune yake yana nazarin wani littafi sakon ya shigo.

Ya zubawa sakon ido, kamar ba zai yi reply ba kuma sai ya tura da “Allah Ya tsare hanya”

Wayarta da ke kasan pillow ta yi kara, ta zubawa rubutun na shi ido, sai kuma kawai ta yi murmushi hade da mayar da wayar inda take.

A can bangaren Mustapha ma bayan ya tura sakon, zuba ma wayar ido ya yi, idan ya ce bai yi kewar Fatima ba ya yi karya, tana da babban matsayi a zuciyar sa, ita din ta kwashi kaso mai tsoka a zuciyarsa.

Ya aure ta, ba tare da wani so ba, ƙauna da shakuwa suka wanzu. Uwar yaransa, ta kula da mahaifiyarsa, ta kula da kanwarsa, uwa uba ta tsaya mishi a lokacin da kafafunsa ke neman durkushewa.

Anya ta cancanci ya yi mata haka kuwa?

Ya lumshe idon shi da karfi, a zahiri ya rika furta “Yes she deserved, she deserved more than that, Ina son ta gane ta yi kuskure, ni mijinta ne, ko ita ce sarauniyar Katsina idan za ta yi abu da ya, shafe ta kai tsaye ya kamata in sani”

Ya rufe maganar da bude idanuwansa da suka yi ja, lokaci daya kuma ya mike daga zaunen da yake, ya shige toilet.

Safiyar Sunday ma misalin 8am ta gama kintsa kanta da yarannta, ta kira Aunty Hauwa ta turo mata yara, suka daukar mata kaya zuwa gidan Mama.

A can kuma suka hadu da Ummi da ta ce za ta yi rakiya.

Hakimi ne ya bayar da mota aka loda kayan Fatima a ciki, Aunty Hauwa, Ummi, Ziyad, Hana da kuma Aunty Ayyo sune suka yi mata rakiya.

Sosai zuciyar Fatima ta yi rauni, sai take jin kamar dai ta bar garin kenan, dakyar ta iya rike hawayenta, Ummi, Ziyad, Hana sune a gaba, Aunty Ayyo Aunty Hauwa da ita Fatiman sune a baya.

Surutunsu kawai suke yi Fatima na jinsu, kamar an kulle mata baki, abu daya take iya yi, gyara zaman Hussaini da yake Hassan na hannun Aunty Hauwa.

Don ma kar su fara yi mata ihun ta yi laushi sai ta kwantar da kanta hade da lumshe idanunta kamar mai bacci.

Gidan Aunty Lami suka sauka, sai da suka ci abinci sannan suka dunguma zuwa gidan da Hakimi ya ce ya kama mata.

Dole suka tafi da direban mijin Aunty Lami, saboda sun kara yawa, Zainab Aunty Lami, da kuma yarinyar da Aunty Lamin ta nemawa Fatima don taimaka mata da rainon su Hassan.

Daga titin makarantar ake yankewa a shiga estate din, basu yi tafiya mai nisa ba, suka isa wurin wani katon gida mai dauke da katon farin gate kamar yadda fentinshi ma yake fari tas.

Mai gadin ya bude kofar, motocin biyu suka silala cikin gidan, mai dauke da doguwar farfajiya.

Tsaye Fatima ta yi tana karewa gidan kallo, bangare biyu, dama da hagu, ko wane bangare yana dauke da dakuna shida, kenan gidan dakuna shabiyu ne.

A ko wace daga gaban dakunan fulawoyi ne masu kyau da suka kara kawata interlock din da ke shimfide a farfajiyar gidan, akwai manyan tankunan ruwa guda biyu.

Shiru gidan kamar ba kowa, kuma har suka kwashe kayansu suka shigar zuwa dakin da aka ce shi ne na Fatima babu wanda ya fito.

Ko wane daki yana da maidaidaicin entrance wanda ya zama kamar baranda. Sannan a ko wace kofar daki akwai no.

A bangaren dama Fatima ce Room no 4 (R-4)

Madaidaicin daki ne mai dauke da toilet da kuma kitchen, a cikin kitchen din akwai store dankarami. A tsakar dakin katifa ce inchi takwas mai fadin gado 6-7. Da pillow guda biyu.

Kamar an kai amarya haka su Aunty Lami da su Zainab suka rika bude ko wace kofa suna yabawa. Musamman yadda kwayaye masu haske suka haske ko ina, ga iska mai dadi da fanka ke bayarwa.

Basu wani bata lokaci ba, suka juya kasuwa, sayayya suka yo wa Fatima ba karamar sayayya ba, ita kanta ta san wannan sayayyar ta fi karfin kudinta. Don har da karamar katifa suka karo mata.

Bayan sun dawo suka shiga shirya komai inda ya dace, cikin kankanin lokaci suka gama kimtsawa, amma duk da haka a nan suka yi sallahr magariba.

Sosai suka yi wa Fatima fada wajen mayar da hankali a kan abin da ya kawo ta, kare mutumcinta da mutumci auranta tare da taka-tsan-tsan da abokon zamanta.

Fatima har da kuka ji take yi kamar wani sabon auran ta yi.

Haka suka tafi suka bar ta da kewar duk wani abu da ya shafe su.

<< Daga Karshe 38Daga Karshe 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.