Skip to content
Part 40 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ba iya dakin ne ya kasance shiru ba, hatta gidan ma tsit yake, kamar dare ya raba.

Su Hassan duk bacci suke yi, sai Abida (yarinya mai rainonsu) ita ce zaune shiru, alamun bakunta.

Mikewa Fatima ta yi zuwa kitchen ba tare da ta cire hijabin da ta yi sallahr magariba ba.

Ta Yi tsaye a kitchen din tana kallo, ku san komai na amfanin kitchen akwai, tukwane guda uku, flask babba da ƙarami, food flask set biyu, plates, cups, spoon, stove, gas da karamin electric Har kettles.

Store din ta shige, abinci ne tsaune wanda ta tabbata zai kai ta har karshen semister,

Tarugu ta dauka guda hudu ta murza a greater, sannan ta dora karamar tukunya, indomie biyu ta dafa musu.

Suna tsaka da ci, aka dauke wuta, ta fara tunanin inda Aunty Lami ta aje mata touch light din da ta sawo, da sauri ta daga filo, ta lalubo touching hade da kunnawa, a daidai lokacin ne kuma karar generator suka fara tashi a cikin gidan, wannan ya tabbatar akwai kowa, amma ko sau daya ba ta ji alamun hakan ba sai yanzu.

Karamar katifa ta nunawa Abida a kan ta kwanta ganin ta fara gyangyadi, ita kuma ta gyarawa su Hassan shimfida, sannan ta janyo time table din ta, tana duba tsarin lecture gobe Monday.

Wanshekare tun da ta tashi sallahr asuba, bata koma ba, zuwa 7:30am, ta gama kamalla duk shirinta da na yaranta.

Ta goya Hassan kasancewar ya f Hussaini jiki, Abida kuma ta goya Hussaini hade da rike lunch basket dinsu.

Har ta fice daga farfajiyar gidan babu wanda ya fito,, suka gaisa da maigadin kafin suka mike kan titi da zai sadasu da titin zuwa makarantar.

Basu jima da bulla kan titin ba, suka samu mashin.

Shigarsu makarantar ke da wuya ta rika tambayar mutane wurin da zasu yi, a hankali kuwa takarasa wajen.

Mutane birjik kowa da abin da yake, ita kadai ce me yara a wurin, ba ta jima da zuwa ba lecturer ya shigo, inda Allah Ya taimake ta har aka gama lecture din Hassan bacci yake, a can waje ma Hussaini baccin yake yi.

Sai shidda na yamma suka fita a lecture din karshe, idan ta ce ba ta gaji ba, to ta yi karya, haka idan ta ce ba ta sha wuya ba, nan ma ta yi karya, lectures daga kai sai jakar ka ma, ya ka gama da ita, bare ace yara har biyu, ta saba wancan ta aje wancan, ga rigimarsu, ga hada musu abinci, daga ita har yaran da Abida babu wanda bai gaji ba.

A haka suka karaso gate, inda suka tari mashin zuwa gida.

Yau ma tsakar gidan shiru babu ko mutum daya, abin da yake ba Fatima mamaki kenan.

Ita ma sai ta bude dakinta ta shiga, idan so samu ne ta, kwanta ta huta, amma dole ta shiga nemar abin da zasu ci, da kuma gyarawa su Hassan jikinsu, don ma sosai Abida ke taimaka mata.

Sai karfe goma na dare ta samu nutsuwa, so take yi ta duba abin da suka yi lecture a kai yau, amma bacci da gajiya sun hana ta, dole ta kwanta.

Sai 2am ta farka, shi ma Hussaini ne ya tashe ta. Daga nan kuma sai ta dakko handout din ta duba, har zuwa lokacin da aka kira sallah.

Bayan ta yi sallahr ne, ta shiga shiri don yau ma lectures din safe gare ta.

Kamar jiya, yau ma misalin karfe 7:30am ta fito, a lokacin da take rufe kofarta ne, kofar karshe a kan layin dakin da take ta bude (R-6)

Da sauri Fatima ta yi saurin juyawa, wata kyakkyawar budurwa ce shanye da doguwar riga baka, ta yane kan da mayafin rigar, kafarta ta dama sagale da jaka, fara ce tas, mai matsakaicin jiki.

“Good morning!” ta fada a hankali daidai lokacin da ta zo saitin Fatima.

“Morning!” Fatima ta mayar mata, lokacin da ta dauki Jakarta, tana kokarin zaro wayarta da ke kara

Mama ce ta kira, bayan sun gaisa, sai ta kira Ummi wacce ta kira ta tun asuba, da yake tana tsaka da shiri sai ba ta daga ba.

Tare suka jera da budurwar har zuwa inda suka samu mashin.

Yau ma kamar jiya, lectures suka yi sosai, basu fito lecture karshe ba sai 5pm, zuwa lokacin wani irin ciwo kanta ke yi, ga, Hussain ma da alamun zazzabi a jikinsa, saboda rigimarsa ta yau din ta fi jiya.

Shi ya sa har lecture din da shi take shiga.

Haka suka dawo gida a gajiye, ta rasa wane abu za ta fara, ga maganar abinci, na ta da na su Hassan don yanzu suna cin abinci musamman indomie, ga ciwon kai, ga kuma na Hussaini da duk ya hanata sakewa.

Lokaci na farko da ta ji idan har haka za a tafi anya ba ta yi kuskure ba kuwa?

Gaskiya akwai kalubale a gabanta, za ta sha wahala ba karama ba.

Ita ta yi wa su Hassan wanka, bayan ta dora indomie, ita ce abincinsu yanzu ku san ko wane lokaci. lokacin da ta gama shiryasu indomien ta dahu.

Ta zubawa Abida tata, sannan ta sanya ma su Hassan a wani wuri daban ta ce ta basu, ita kuma ta shiga wanka, sai da ta yi sallahr magariba ta ci tata indomie sama-sama.

Hussaini take son kaiwa chemist, amma ba ta ga chemist ma fi kusa a unguwar ba, dole sai ta tambaya amma wa za ta, tambaya to, kowa baya son shiga harkar kowa.

Haka nan ta fito dakin ba tare da sanin ina za ta je ba, ya barwa Abida Hassan a kan ta kula da shi.

Tsakar gidan fayau ba kowa sai hasken kwai da ya haske ko ina, tana ta tsaye a wajen ta ji an turo kofar gate. Da sauri ta mayar da kallon ta wajen.

Ta zubawa matar ido wacce za ta iya kaiwa shekaru arba’in a duniya. Hannunta janye da akwati sai kuma karamar jakar da ta sagala.

Maigadi na biye da ita da wasu manyan ledoji, a cikin hirar da suke yi, Fatima ta ji matar na fada mishi wai motorta ce ta samu matsala.

Suna zuwa saitin inda Fatiman take tsaye sai ta karbi akwatin da ke hannunta tare da faɗin “sannu zuwa”

Da fuskar rashin sani ta amsa mata bayan ta mika mata akwatin, har kofarta suka kai mata kayan, inda ta rika bin su da godiya.

Da wannan damar Fatima ta yi amfani wajen tambayarta chemist.

Cike da kulawa matar ta kwatanta mata, hade da addu’ar Allah Ya ba yaron lafiya.

Duk a tsorace Fatima ke tafiya, kasancewar layin shiru kamar a tsakiyar dare, don ma ko ina a fayau yake da haske.

Ba ta jima ba ta isa chemist, cikin sa’a kuwa babu kowa sai mai shagon.

Sai da ta gaishe shi, sannan ta yi mishi bayanin abiin da ya kawo ta.

Magunguna masu kyau ya hada mata, lokacin da ta zo gidan tuni Hassan ya yi bacci, ita ma sai suka shiga shirin baccin bayan taba Hussain maganin shi.

Cikin dare Hassan ma ya farka ba lafiya, dama ta san hakan zai iya faruwa, don ka’ida ne, idan har daya ba shi da lafiya shi ma dayan sai ya kamu.

Kwana uku dai sai da ta gane Isa ba ɗan Allah ba ne bawansa ji take yi kamar ta sawake ma kanta karatun don dawainiyar tana da yawa.

Amma wata zuciyar na karfafa mata gwiwa a kan ta jajirce, in sha Allah komai zai wuce.

Sam ba ta da ta lokacin kanta, lokutanta a kididdige suke, duk abin da ba ta yi ba a lokacin da ta ware mishi to kodai ta hakura ko kuma ta yi shi ba yadda ta so ya kasance ba.

Cikin wata guda da zuwanta sai ta rame, duk yadda jikinta baya nuna rama wannan karon kam kallo daya za ka yi mata ka shaida ramarta

Da Zainab ta kawo mata ziyara ma haka ta ce ta rame, ita ma da ta shiga garin wajen Aunty Lami haka Aunty Lamin tai ta fadin ramar Fatima ta lokaci daya.

Zaman gidan nasu kuwa ba kuka ba guda, zama ne irin na yan gayu, kowa harkarsa yake yi, kamar ba students ba.

Abin da Fatima ta fahimta shi ne, da yawan masu zama cikin gidan rainon quarters, kowa jin kansa yake yi.

Mutane biyu ne kawai take gaisawa dasu sama-sama.

Momy (matar da ta dakkowa akwati, haka kowa a gidan yake kiranta) suna gurmamata sosai.

Sai Yusrar farar budurwa da suke yawan fita ko dawowa lecture a tare.

Duk lokacin da ta ga Fatiman za ta je ko tana dawowa, sai ta, rage mata hanya a motarta, da Fatima ta ga an kawo mata ita daga baya.

Tun da haka suka zabi rayuwar haka nan Fatiman ke yinta, ba don tana yi mata dadi ba, idan dai haka yan gayu ke rayuwa to ba ta ga kyan makanta ba Sam, da ta runtse idonta.

      ******

Lokacin da suka fara tests ne aka fara hidimar bikin Mustapha.

Tun ya rage saura sati daya Mustapha ya ce ta dawo gida, amma fir ta ce ba za ta dawo ba, sai hakan ya kara tunzura shi, ya kai kararta wurin Aunty Hauwa, koda Aunty Hauwar ma ta tuntube, kai tsaye ta ce ita fa a kyale ta ba za ta zo ba.

Ita ma Aunty Hauwar sai ta kaiwa Mama kara, tabe baki Mama ta yi kafin ta ce tun da ta ce ba za ta zo ba, a kyale ta mana ko dole?

Maganar da ta ba Aunty Hauwa dariya gami da mamaki, saboda yadda kai tsaye Mama ta goyi bayan Fatima ko irin yar alkunyar nan.

Fatima abubuwa da yawa ne suka hade mata, ga shirin exam, ga kuma presentation da and zasu yi a kan muhimmancin radio ga al’umma. Ga kuma wani irin kishi da take ji a kirjinta, duk yadda za ta kwatanta zafin abun ji take za ta rage wani abun, macen da aka yi wa kishiya ce kawai za ta fahimci halin da take ciki.

Shi ya sa tun ranar Alhamis da ta kama gobe daurin auran Mustapha ta kashe wayarta.

Amma duk da haka sai da ta ware lokaci ta yi kuka mai yawa, kukan da ya sanyata safiyar juma’a ta tashi da wani irin ciwon kai mai zafi, ko sallahr asuba sai dai ta yi ta kai a dafe.

Yau kam ku san Abida ce ta yi komai da safe, hatta shirya su Hassan, Fatima kwance take dafe da kai.

Sai misalin karfe goma na safe ta shirya da kyar zuwa wajen presentation din.

Sosai ta yi kokarin bayar da abin da ake so, abin da ta fahimta shi ne, yan ajin basu san a hada su yin wani abu da ita, kila suna yi mata kallon ba za ta iya tabuka komai ba sai dai a yi mata, kasancewar tana da yara har biyu.

Amma yau kam sai ta shayar dasu mamaki, kuma tun daga lokacin kimarta ta karu a, idanunsu.

Karfe biyu na rana ta dawo gida dakyar, ciwon kai kam ko idonta ba ta son budewa.

Abida ta barwa duk hidimar su Hassan dai ta wannan ranar hatta abinci ita ta kwaba musu.

Sai shidda na yamma ta tashi daga baccin wahalar da ta yi, zuwa lokacin ta san an daurawa Mustapha aure, ya zama mallakinsu su biyu, yana can yana farin ciki, ya manta da ita da Sanin ko wane hali take.

Yanzu da aka daura mishi aure to wane irin zama kuma za ta yi da shi, tarairarayarshi, ko kuma ta watsar da lamarinsa, in ya so can gaba idan ta ga sosai hankalinsa ya kara nisa da ita, ta nemi ya yanke igiyar da ta hada tsakaninsu, ta koma gida ta yi zaman jin Allah Ya kara dama mun fada miki?

Turo kofar ne ya janye mata hankali, Abida ce ta taso su Hassan zuwa daki, wannan ke nuna mata magariba ta yi, kuma ko azhar ma ba ta yi ba.

“Sannu Aunty” Abida ta fada da alamun tausayi a kan fuskarta

“Yauwa. Sannu ke ma Abida.”

“Zan yi miki wani abu ne?”
Cike da ladabi Abida ta yi tambayar.

“a’a.” cewar Fatima a lokacin da ta yunkura da kyar ta tashi dafe da goshinta.

Toilet ta fada hade watsa ruwa, sannan ta dauro alwala.

A zaune ta yi rabin sallolin.

A dan tsorace Abida ta ce “Aunty na ga ba ki ci komai ba.”

Shiru Fatima ta yi kamar ba za ta amsa ta ba, sai kuma ta ce “Zan ci. Na gode, ku kwanta kawai.”

Tun tana jin motse-motsensu da korafe-korafensu har bacci mai nauyi ya dauke su.

Duk yadda ta so ta ci abincin abun ya gagara, ba ta taba tunanin za ta damu haka a kan auran Mustapha ba.

Haka nan ta rika sipping din shayin ba don tana jin dadinsa ba, sai don jin yadda cikinta ke naman tona mata asiri.

Ba ta samu bacci ba sai gab asubah, shi ya sa ta makara a sallahr asuba.

Yau din ma ba ta iya yin komai, wani irin jiri take ji dazarar ta mike, dalilin da ya sa kenan yau ma Abida ce ta yi komai a dakin, hadawa su Hassan cerelac, gyara daki, yi musu wanka da kuma dafa musu indomie.

Fatima kam sharkaf take a kwance, ko mikewa sai ta dafa bango.

      ********

Bangaren Mustapha kuwa tun ranar Alhamis yake neman layinta ganin da gaske ba za ta zo wajen bikin amma bai samu ba.

Ya dauka abun na dan lokaci ne, amma haka ya wuni kiran layin ranar Juma’a nan ma shiru.

Idan ya ce hankalinsa yana jikinsa ya yi karya, yake kawai yake yi, amma ji yake kamar ya taho Katsina a ranar.

Duk wani shagalin biki da aka rika, shi dai ba ya masa dadi, karshe ma ba a tashi wurin dinner ba ya gudu.

Da safe ma bai hakura ba, ya dora daga inda ya tsaya wajen kiran layin Fatima. Amma har azhar layin bai shiga ba, sai duniyar ta kara mishi ba dadi, ya ji kamar ya ce kowa ya tafi gida ya sallame shi.

Koda Blessing ta yi mishi magana a kan Shuwa day din da zasu yi da karfe hudu kai tsaye ya ce ba zai iya zuwa ba, baya jin dadi.

Ba tun yanzu ta fahimci baya cikin nutsuwarshi ba, hankalinsa baya kanta ba, ta yi shiru ne amma tabbas tana zafi da kishin yadda Mustapha kan rasa nutsuwarshi muddin Fatima ta yi mishi bore. Baya iya boye damuwarsa a kan Fatima.

Rai bace ta ce ita ma ba za ta je wurin Shuwa Day din ba, ba amfanin zuwan ta idan har shi ma ba zai je ba.

Sosai ya so ya lallasheta sannan kuma ya je wurin taron, amma ya kasa yin hakan, yana kallon Blessing din ta fice daga dakin rai bace.

Matar J✍🏻

<< Daga Karshe 39Daga Karshe 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×