Skip to content
Part 44 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ba ta kuwa koma gidan ba sai karfe goma na dare.

Da yake akwai yanayin zafi, kwance suke a kan tabarma daya shi da Blessing, abin da ya fi ba Fatima haushi ma tabarmarta ce.

Ta dauke kai kamar ba ta gansu ba, ta shige daki tana kokarin kwantar da Hassan ne Mustaphan ya shigo.

“Sai yanzu?”

Banza ta yi da shi, ji take ina ma Mama ta bar ta ta yi tafiyarta Katsina da ba ga wannan mugun ganin ba.

Ita kam ba za ta iya wannan rayuwar ba, addinin musulunci ya yi gaskiya da ya ce a raba gida. To ai wannan kwaɓen mai zuciya kusa sai ya banka wa mutum wuta.

“are you still angry?”

“Don Allah Ya Mustapha ka fita, I’m not in the mood please.”

Yadda ta yi maganar sai abun ya ba shi mamaki, ya rasa me ya sa komai yanzu da zafi take daukar shi.

“But I’m” ya ba ta amsa yana kallon ta.

Wani takaicinshi ya kara kama ta.

“Kawai saboda kina karatu kike son ki rika kafa min sharudda? Ban da na yi wa Alhaji alkawari wlh Fatima da ba ki koma makarantar nan ba, da nuna miki ni din mijinki ne. Da sai na ba ki mamaki.

“Yo na nawa kuma? Mamaki kam ai ka ba ni shi, kana kuma kan ba ni, tun da kana tuna ma ka yi alkawarin ai da sauki. Don haka idan ka cika ka sani, idan ma ba ka cika ba ka sani.”

Kallon ta yake yi hade da nazarin kalamanta, ya rasa lokacin da ta kara yin baki, yanzu ku san fito na fito take yi da shi.

“I want you.” Ya katse shirun nasu da maganar tasa cikin bayar da umarni.

“And I’m telling you I’m not in the mood “

“And I’m telling you I’m.” shi ma ya fada a dan tsawace.

Duk suka zubawa juna ido kamar zakarun da suka gaji da fada.

Gadon ya hau, ya kwanta yana fadin “I’m waiting you”

Hawaye masu zafi suka sakko mata, da ace saki a hannunta yake yau kam da sakinshi ta yi, baya kwana a dakin.

Iko irin na namiji da yawa yake, kuma basu tashi nuna shi, sai lokacin da suka fahimci mutum baya son yin abu.

Sautin kukanta ya fara fita a hankali, har zuwa lokacin kuma a tsaye take tsakiyar dakin.

“You’re wasting time. Kar ki bari in kara yi miki magana kuma ba na son ki zo min nan da kaya.”

Tana kuka kuma tana zare kayan jikin nata.

Lokacin da ta hau gadon sai ta kuma fashewa da kuka sosai.

Abun da ya bashi dariya, a zuciyarshi kuma ya ce “Ba kin ce ba kya ji ba, zan yi maganin rashin kunyarki.”

Bai damu da kuka da kuma rashin performing dinta ba, bukatarsa kawai ya nuna mata shi din a samanta yake, kuma dole ta bi umarninsa, idan har hakan bai sabawa Allah ba.

Blessing da ta gaji da kwanciya a waje, ita kadai sai ta mike zuwa masaukinta, yau ne ta fara danasanin auran me mata, ashe haka abun yake, Lallai borin namiji ne.

Da asuba ma bai kyale ta ba, haka ta ci kukanta da kumbure-kumburenta ta yi shiru.

Sai ta wuni kumbure-kumburenta, ga shi yau ikon ya motsa, ya ce ba za ta koma gidan Mama ba, sai hakan ya kara tunzura ta. Ganin haka ya sa Blessing ta kame kanta, sai da su Hassan kawai take hidimominta.

Hakan sai ya fi yi wa Fatima dadi, sosai ba ta son Blessing na shiga harkarta.

Da daren ma yau din ma bai daga mata kafa ba, duk kuwa da ta fara ba shi tausayi, amma so yake ya dafa ta da ruwan sanyi, kuma da gasken ta dahu, sosai ta yi la’asar har da magariba.

Shi ya sa safiyar Sunday ta fara hada kayanta.

A cikin bacci ya rika jin buruntunta, ya bude ido yana kallon yadda take ta shirya kaya cikin karamar jaka, don wannan karon yar karama za ta dauka, ba za ta koma dasu Hassan ba, yaye su za ta yi.

Sai da ya yo brush, sannan ya koma gefen gadon ya zauna yana kallon ta, can kuma ya duba wayarsa, takwas saura na safe.

“Ina za ki je?”

Take zuciyarta ta karye, ba ta son ya ce mata ba za ta tafi ba.

Shi ya sa ta fara sharce hawaye ba tare da ta yi magana ba.

“Ko ba ki ji?”

Sautin kukan ta ya fito sosai ta yadda ko wanda yake falo zai iya jiyowa “Makaranta zan koma.” cikin kuka ta yi maganar tare da aje kanta cikin kafafunta tana kara Sautin kukan nata.

Duk yadda ya so rike dariyarsa sai da ya murmusa “Zo nan.” ya fada muryarsa da alamun dariya.

Kallonsa take da jikakkun idanunta, yayin da tsoronsa ya bayyana a cikin idon nata.

Sai hakan ya kara ba shi dariya.

“Ki zo na ce.” ya kuma yin maganar bayan ya kafe ta da idanu.

Har lokacin ba ta yi alamun zuwa ba.

“Ko ni in zo?”

Da sauri ta mike, ta kuma fashewa da kuka.

Daga inda yake ya sa hannu ya fisgo ta, sai ko ta fada kan jikinsa, ya yi mamakin yadda ya ga tsoro karara ya bayyana a tare da ita, hakuri take ba shi kamar za ta yi mishi sujjada.

A zuciyarsa ya ce” Wannan ta gane da gari ake tuwo”

“Just relax! Me ye wannan? ” ya yi maganar bayan ta tashe ta zaune

Lokaci daya kuwa ta nutsu.

“Yau za ki koma school din?”

Kai ta daga alamar eh

“Why today?”

Cikin muryar kuka ta ce “Ina da lectures da yawa gobe.”

Dariyar da yake boyewa ta bayyana “Zuwa yanzu kin gane punishment ba sai da duka ba ko?”

Shiru ta yi ba ta ce komai ba.

“Ko ba ki gane ba?”

“Na gane.” ta yi saurin fada hade daga hannayenta sama kadan.

“Nawa zan biya kudin punishment din?”

Shiru ta yi ba ta ce komai ba, a daidai lokacin da wayarta da ke kan mirror ta yi kara.

“Go check it”

Da sauri ta mike zuwa inda wayar take, credit alert ne daga Shi na 20k.

“Na gode” ta fada a hankali.

“Fatima kina son ba ni ciwon kai ne, in tare ki nan, ki bulla can, me ya sa kike haka?”

Shiru ta yi ba ta amsa ba.

“Shi kenan.” ya yi maganar hade da daga kafadunshi sama, kamar ba zai kara magana ba, sai kuma ya ce “Yaushe za ki tafi?”

A hankali ta furta “Yanzu”

“Look at you. Yanzu ba ko kunya, na tambaye ki, kin yi shiru, amma na yi maganar tafiya, zaraf kin ce yanzu.”

Hannu ta kai Saman kanta tana sosawa a hankali.

Sai kawai ya yi kwanaciyarsa, wannan ya ba ta damar ci gaba da hada ragowar kayanta.

Sai da ta gama shirinta tsaf cikin atamfar cote divoire mai kalar coffee, ta, dora farin hijab, tana son farin hajabi sosai, dama tuni ta aika da su Hussain gidan Mama.

Gefen gadon ta zauna tana taba shi a hankali, ya bude idanun nasa wadanda suke da bacci sannan ya lumshe hada janyo ta jikinsa “I’m going to miss you” ƴa yi maganar hade da tura kai yana shakar sansanyar kamshinta.

Lamo ta yi a jikinsa, sai yanzu ita ma take jin za ta yi kewarsa, kwana biyun wasa-wasa ya aje mata wani record mai wahalar mantawa

“Do you?” ya yi tambayar murya can kasa.

Kai ta jinjina alamar eh.

“Please say it out, Ina son ji.” ya yi maganar lokacin da yake kara janyo jikinsa sosai.

Nema yake ya sanyata canja wanka, don haka cikin dabara ta janye jikinta.

“In raka ki ne?”

Da sauri ta girgiza kai, ina, za ta yadda ya bi ta, ya jika mata aiki, so take ta bar su Hussain dazarar ya bi ta kuwa, to ba zai amince ba.

Haka ta fice janye da akwatin, sai da ta bacewa ganinsa, sannan ya juya don komawa baccin sa.

Kamar ta wuce, sai kuma ta nufi dakin Blessing.

Ita ma baccin take yi, amma ta ji lokacin da Fatima ta turo kofa ta shigo.

Ganin za ta fita ne ya sa ta ce “Excuse me Momy Momy Ziyad, kina son wani abu ne”

“Dama zan wuce makaranta ne, shi ya sa na ce bari in fada miki”

“Oh my God, are you going today?”

Kai Fatima ta jinjina alamar eh.

“Please just 2mns Ina son yi miki rakiya” ta yi maganar ne daidai tana sakkowa daga gadon.

Fatima ta bi ta da kallo, sanye take cikin rigar bacci golden mara nauyi mai siririn hannu. Blessing mace ce duka dauka, ta kusan hada komai, matsakaiciya, mai cikakken jiki, ga gashi, tsabta, ilmi ga iya kwalliya.

Don dakin Innar kamshi ne kawai mai dadi ke tashi sakamakon zaman da Blessing ke yi a dakin.

Ba jimawa kuwa ta zira doguwa riga, hade da yafa dankwalin rigar, ita ta rikewa Fatima jaka suka jera, yau da yake hirar tasu a kan makaranta ta tafi, sai Fatima ta bayar da attention hade sakin jiki, musamman yadda Blessing din ke kara mata haske a wasu bangarorin.

Wani lokaci kuma Fatima kan fashe da dariya sosai idan Blessing ta ba ta wani labarin na makaranta.

Sai Blessing ta fahimci idan tana son hirarsu ta yi tsawo da Fatima dole ta rika sako labarin karatu, ta samu weak point nata guda daya.

A hankali sai shiga rayuwarta sha Allah.

Lokacin da suka isa gidan Mama dama jiranta ake yi, don motar Hakimi za ta bi, za a mayar da wasu ƴan biki.

Taso ganin Jamil, amma har motarsu ta taso basu hadu ba.

Sai Blessing ta, tabbatar ta samu lambar Fatima sannan suka rabu.

Kuma koda ta koma gida, ba ta fadawa Mustapha Fatima ba ta tafi da ƴan biyu ta ja bakinta ta yi shiru.

Yana daya daga cikin iya takun zama da kishiya, kar ki yarda miji ya rika jin munanan labarin abokiyar zamanki daga bakinki, da kuma yawan kai mishi korafi, wannan yana rage kimar mace a zaman aure.

*****

Tun a mota Fatima ta fahimci ta yi kewar yaranta, ji take yi kamar ta ce a tsaya ta koma ta dakko su, tun da take yaye ba ta taba yaye yaro ta damu irin wannan lokacin ba.

Har kofar gate dinsu drivern ya aje ta, sannan ya wuce da sauran mutane zuwa unguwanninsu.

Kamar ko wane lokaci gidan tsit kamar ba kowa, sai sautin kide-kide da yake fita a hankali a wasu dakunan, kan katifa ta fada bayan ta bude dakin ta shiga, kewa ce cike da zuciyarta, kewar ƴan’uwanta wadanda ko daya ba ta gani ba lokacin da za ta taho sai Aunty Hauwa, kewar Mustapha da uwa uba yaranta, ji take yi kamar ta koma.

Haka ta kwanta tsawon lokaci kafin ta lalubo wayarta, kunnawarta ke da wuya sakon Mustapha ya shigo “Wayarki a kashe, hope kin isa lafiya?”

Tana kokarin ba shi amsa kiran Blessing ya shigo, ta daga suka gaisa sannan Blessing ta ci gaba da tsokanarta tana fadin “Students – students” Fatima kam na washe baki. Yanzu ma hirar tasu duk a kan karatun ne, Blessing ta yi mata fatan nasara sannan suka yi sallama.

Mikewa ta yi ta shiga gyaran dakin, sai da ta gyara ko ina sannan ta nemi abinci.

Zuwa magariba kam zazzabin yaye ya rufe ta.

Duk yadda ta so fita lecture da safe, hakan bai samu ba, dole ta hakura don zazzabi ne sosai a jikinta, ga shi ko riga ba ta iya sanyawa.

Mama ta fada mata su Hassan basu yi rigima Sosai ba, sai ta dan rage damuwa.

Ba ta samu fita ba sai ranar Laraba, misalin karfe biyar ta fito lecture din karshe, wayarta ta dakko don cire ta daga silent tare da duba wadanda suka kira ta.

Kiran Mama ta fara bi, sai dai ba a daga ba, shi ya sa ta kira Mustapha.

Yanke kiran ya yi sannan ya kira ta baya.

“Me ya sa kike yin abu kai tsaye?” ita ce maganar farko da ya fara yi.

Daga yanayin muryar ta san ran shi a ɓace yake.

“Me na yi?”

Kamar jira yake ya ce “Ban sani ba. Me ya sa za ki cire yaran nan a nono ba tare da masaniyata ba?”

Shiru ta yi, ba tare da ta ce komai ba.

“Saboda karatunki?”

Nan ma ba ta ba shi amsa ba.

“I’m warning you Fatima for the last time.”

Daga haka ya yanke kiran.

Ta sauke ajiyar zuciya, ta san ya yi fushi sosai, amma Allah Ya sani ba ta yi hakan don ɓata mishi rai ba, ita kadai ta san wahalar da take sha dawainiya da yaran nan, ga kuma lectures.

Haka ta koma gida jiki a mace, tsakar gidansun dai ba kowa, shi ya sa ta shige daki, ta ci gaba da hidimominta.

Yanzu kam sai lecture ya yi mata sauki, saboda babu dawainiyar yara, abu daya ne yake damunta, yadda lokacin period nata ya wuce da kusan sati biyu ba ta yi ba.

Tsoron zuwa asibiti take yi kuma, kar ace mata ciki ne.

Mustapha kam rabon da ya kira ta, an shiga sati na uku. Ta san fushi yake yi, kuma ta tura mishi text na ban hakuri, amma bai kira ba, kuma bai yi reply ba.
Yana da mugun son yara, shi abu idan har ya shafi yaranshi bai daukar shi da sauki.
Shi ya sa ita ma ta fita batunshi.

Yau dai da ta fito lecture, sai ta biya chemist ta sayi pt strip, don kore shakkun da ke damunta.

Yau kam ta samu Momy a tsakar gidan, ita ba ta faye zama ba, za ta iya yin sati ma ba ta a gidan , a mutumce suka gaisa sannan ta shige dakinta.

Wunin yau addu’arta Allah Ya sa kada test din nan ya nuna ciki ne, sosai ba ta son ciki a yanzu, musamman yadda take jin dadin zama single din yanzu.

Da fitsarinta na farko ta yi amfani wajen test din.

Ta kurawa strip din ido, har zuwa lokacin da ya nuna positive. Alamun akwai ciki kenan.

Matar J✍🏻

<< Daga Karshe 43Daga Karshe 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×