Tafiyar ta da kwana daya Mustapha ya zo Katsinan, sai dai Aunty Lami ta shaida mishi ai ta wuce Sandamu tun jiya, duk da ranshi ya baci sai ya yi kokarin dannewa, yana matukar ɓata mishi rai yadda Fatima ke abu kai tsaye, shi ya sa koda ya sayi fili Mama da Aunty Hauwa kawai ya fadawa, ya san ta ji amma har yanzu ba ta taba ce mishi ashe ya sayi fili ba, wato tana jira sai ya ce mata ya saya sannan za ta tanka.
Akwai abubuwa da yawa da yake mata, wanda yake jiran cewarta, amma ba ta magantuwa, bugu da kari nunawa ma take yi ba ta san an yi ba, kuma ba ta ji haushi ba.
Allah Ya yi mata baiwar iya shariya, ta share abu ko a jikinta wai an mintsini kakkausa.
Ba shi da zabi da ya wuce zuwa Sandamun, don shi ne kwanciyar hankalinsa, idan bai je ba, Mama za ta kuma ƙara tarfa shi, har ga Allah maganganun da ta fada mishi wancan sun taba shi sosai.
Haka ya je ya tari mota, ya ma gaji da shiga motar hayar nan, shi ya sa ya fara shirin sayen tashi. Ko zai samu sauki, hidimomin ne ke yawa daga wannan sai wannan .
Lokacin da ya isa Sandamun karfe 5pm daidai, kai tsaye gida ya nufa.
A lokacin kuwa Fatima shirye take tsab cikin atamfa coffee color riga da siket, ta yi kyau sosai, ita ba ramamma ba, kuma ba mai ƙiba ba, ta kara haske kadan, gidan ma tsab sai kamshi mai dadi ke tashi, ba ta jima da shirya su Hassan zuwa islamiya ba, haka nan suke tafiya duk da bakin bai bude sosai ba.
Yanzu kuma zaune take a kan 2sitter tana yankewa Beauty(Haka suka fi kiranta yanzu, saboda yadda Umaima ta dage a kan sunan) farce da nail cutter
A ba za ta ta ji sallamarshi, cikin rashin tsammani ta ji gabanta ya fadi, dalilin da ya sanyata amsa sallamar a sanyaye.
Ya zuba mata idanunsa daga inda yake tsaye a bakin kofar dakin, wadanda suke cakude da abubuwa da yawa, ita ma shi take kallo a kokarinta na gano yanayinsa.
Sanya yake cikin farar shirt mai dogon hannu, sai coffee brown din wando mai santsi kamar na suit, yayin da kafadarsa ta dama take makale da bakar jaka ta matafiya.
Ta kawar da kai gefe, cikin mamakin canjin da kullum take gani a jikin Mustapha, kallo daya za ka yi wa duguwar surarshi ka fahimci yana jin dadi, komai na jikinsa ya canja.
“Come in now! You’re welcome!”
Bai amsa ba, amma ya tako cike da gajiya, ya wuce bedroom dinta kai tsaye.
Dalilin da ya sa ta bi bayan shi.
A lokacin botiran rigar yake cirewa, ya saba da yanayin ko wacce a cikinsu, idan Blessing ce za ta taimake shi wajen cire botiran, amma ya san Fatima abu ne mawuyaci, yadda ya za ta din haka ne ya faru, jikin kofar ta tsaya tana kallon sa, har sai da ya miko mata rigar, ta amsa, lokaci daya kuma ya zauna gefen gadon yana zare coffee color din safar da ke kafarsa.
“Sannu da zuwa” ta kuma fada a lokacin da take amsar socks din daga hannunsa.
Ya lumshe ido hade da bude su a kanta, har zuwa lokacin bai yi magana ba, dalilin da ya sanyata murmusawa a hankali. Ta nufi hanga tana sagale kayan, daidai tana dawowa ne ya sanya mata kafa, sai kuwa ta fado gefen shi, kallon sa take kamar ba shi ne ya yi sanadiyyar faduwarta ba.
Yunkurawa ta yi da niyyar tashi, ya mayar da ita, lokaci daya kuma ya yi amfani da dayan hannunsa ya janye zip din rigar da ke jikinta.
Ba ta yi kokarin hana shi duk abin da ya yi niyya ba, don wannan karon ta dauki matakin kariya.
Kuma ko ba komai ta yi kewarsa, almost 4 months rabon ta da shi.
Ita kan ta taga alamun ya yi kewar tata, sosai ya sarrafa ta yadda yake so ita ma sai ta ba shi hadin kai fiye da tsammanin sa.
Bai bata lokaci ba wajen shiga wanka ganin lokacin sallah ya yi, bai dawo gidan ba kuma sai da aka yi isha’i.
Sannan Fatima kuma zaune take tana cin tuwo.
Karon farko tun zuwan shi da ya yi magana “Tuwo kika yi?”
Kai ta girgiza alamun a’a, sannan ta ce “Daga gidan Mama aka kawo min”
“To ni me zan ci?” ya tambaye ta idonsa a kanta lokaci daya kuma yana zama kan kujera.
“Hakuri” ta amsa shi kai tsaye.
Sai ya mayar da kan ya kwantar kan kujera ba tare da ya kara cewa komai ba.
Ita kuma ta mike zuwa kitchen, abinci ta hado mishi shinkafa ce da miya, sai hadin coslow wanda sai da ya zo ne ma hada shi.
Ya zamo daga kan kujerar ya zauna sosai hade da lankwashe kafafunsa.
Lomarsa biyu a abincin ya ce “Ina twins?”
“Na san suna gidan Mama, amma ni na shirya su zuwa islamiya dazu”
Bai ce komai ba, illa lumshe idon shi cikin jin dadin abincin, idan dai abinci je matanshi biyu duk sun iya.
Fatima ainihin abinci babu wani tarkace kuma ya yi dadi, yayin da Blessing ta iya game-game, tun baya jin dadin kamshin wasu abubuwan yanzu ya fara sabawa. Amma sosai yana jin dadin abincin Fatima yadda komai yake fita da ainihin kamshin sa.
Bai kara cewa komai ba, sai dai lokaci zuwa lokaci yana yi wa Beauty wasa, wacce ke kwance a kasa kan katifarta.
Sai da ya kammala sannan ya cire jallabiyar da ke jikinsa ya kwanta sosai kan doguwar kujerar.
Shirun na shi ya damu Fatima shi ya sa ta ce “Kana lafiya kuwa?”
Ya dago kai yana kallon ta kafin ya ce “Idan babu, kina da matsala da hakan ne?”
Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Shi ma sai ya yi shiru.
Jin shirun ya yi yawa ta ce “Ya su Ihsan din?”
“Suna lafiya.” ya amsa ta daidai da dire maganarta.
“Madalla” ita ma ta amsa hade da mikewa ta shige bedroom.
Ya bi bayanta da kallo, wata irin budewa take yi, sosai take son komawa Aunty Ayyo.
Doguwar mace sosai, irin wacce kallo daya za ka yi mata ka fahimci hakan, don ma ƙibar da Aunty Ayyon ta yi ta boye tsawon nata.
Da alama ma Fatima haka za ta zama. Sai yau ne ma kara ganin kamanninsu da Aunty Ayyon sosai, don har tafiyarsu iri daya ce.
Cikin bacci ya rika jin korafin Beauty, shi ya sa ya mike hade da daukarta ya nufi bedroom din.
A lokacin Fatima wanka take yi, shi ya sa ya ci gaba da jijjiga Beauty din har Fatima ta fito daga wanka sannan ya mika mata.
Kwananshi uku, amma babu wata doguwar magana a tsakaninsu, ita ma kuma tun da ta tambaye shi ko akwai matsala, ya ki amsa ta ba ta kara bi ta kansa ba, idan dai ya bukace ta, ta kan ba shi hadin kai fiye da yadda ya saba gani, dalilin da ya sanya ku san ko wane lokaci yake nuna yana bukatar tan, kuma ba ta taba nuna mishi gazawarta ba, har abun mamaki yake ba shi.
Bayan tafiyarshi da, kwana biyar aka bukace ta wurin attachment din ta, kai tsaye gidansu ta sauka ba gidan Aunty Lami ba.
Ranar gyaran dakinta kawai ta yi, wanshekare kuma ta wuce gidan radion, inda tun daga ranar aka fara koya mata abubuwa, sai dai sun fada mata dole ta samu yar raino, da ta waiwayi Aunty Lami da batun, sai Aunty Lamin ta shaida mata waccan yarinyar ta yi aure sai dai a nemo mata wata.
Kwananta hudu da tafiya Mustapha ya zo, takaici ne ya hana shi bin ta Katsinar, ganin kamar ta raina mishi hankali har waya suna yi da ita, amma ba ta fada mishi ta wuce Katsinar ba, wannan abun yana bata mishi rai sosai, sai tai ta abu gaban kanta, ta ya zai ta bin ta kamar wani jela, shi ya sa kawai ya juya Abuja abun sa.
Fatima kam ta mayar da hankali ne kan aikin ta, ranar da Mustapha ta kira ta ta amsa, idan bai, kira ba kuma ta kan tura mishi da sakon gaisuwa, ba ta jiran reply, don ta san ba yi zai yi ba.
Yayin da a can Mustapha yake cike da haushin ta, jira yake ta tambayi canjin da ta gani daga gare shi, amma tsawon sati biyar ba ta taba tambaya ba.
Wani abu kam sai Fatima, bai taba ganin mace irin ta ba, Blessing na da masifar kishi da bin kwakkwafi, wanda har hakan yake bata mishi rai, don ita komai sai ta tambaya.
Successfully Fatima ke yin attachment din ta, inda ko wane lokaci take kara gogewa, musamman da muryarta ta fara fita a gidan radion cikin wasu shirye-shiryen.
Sai ta samu karbuwa sosai, duk masu sauraron gidan Radion kowa Fatima M. Sandamu. Kila hakan baya rasa nasaba da zazzakar muryarta mai laushi wajen gabatar da shiri, inda ma fi akasarin mutane ke son ganinta a zahiri, wasu ma sun dauka budurwa ce.
*******
Tun da ta fara attachment din ba ta je gida ba, to ba ta da matsalar komai kuma tana jin dadin aikin shi ya sa ma take ganin kamar sun yi saurin gamawa.
Don ma gidan radion sun dauke ta aiki na wucin gadi.
Bayan kwana biyu da gamawarta ne ta shirya don zuwa Sandamu, hutun dai ba yawa, amma ko ba komai za ta dan ga ƴan’uwa da kuma su Hassan tun da Hana da Ziyad suna Abuja.
Lokacin da ta isa karfe daya na rana, gidanta ta fara sauka, sosai gidan ya yi kura, shi ya sa tana isa ta hau gyarawa.
Ba ta samu kanta ba sai wajen karfe bakwai na dare, lokacin kuwa ta gaji likis kamar an yi mata duka, tuwon da Mama ta aiko mata ta ci, sannan ta yi wa Beauty wanka ita ma ta yi, sallahr isha’i gami da shafa’i da wutri ta gabatar sannan ta bi lafiyar gadonta.
Wanshekare da safe yan ayyukan gidan ta karasa, sannan ta kwanta ta dan runtsa, kafin yamma ta je gaishe da Mama da sauran ƴan’uwa.
Sama-sama take baccin kasancewar Beauty ba ta yi ba.
A cikin baccin ta rika shakar kamshin sa, shi ya sa ta bude ido a hankali wanda suka yi mata nauyi ta zuba su a kansa, a lokacin Beauty ya duko yana yi ma wasa.
Rabon da ta gan shi ya kai 2 months, tun ta fara IT din har ta gama basu hadu ba, sai dai a waya. Yadda bai taba requesting na son ganinta ba, haka ita ma ba ta taba nuna tana son ganinshi ba.
Duk da zuciyarta cike take da son ganinshi da kuma kishin kasancewarshi da wata macen ba ita ba.
A kasalance ta mike zaune daga kwanciyar da ta yi a 3sitter din tana fadin “You’re welcome”
“Thank you you Madame” ya amsata wasai abun shi babu wata alama ta fushi a tare da shi, lokaci daya kuma ya zauna kan kujerar bayan ya janye kafafunta.
“Me kike ba yarinyar nan ne? Ta yi girma sosai and she deserved the name *Beauty*she is very Beautiful. Har ta fi Ihsan girma fa.”
Fatima ta bi Beauty da ke hannunsa da kallo, gaskiya ya fada, Beauty kyakkyawa ce, fara tas, madaidaiciyar fuska mai dauke da dogon hanci hade da dogon gashi gira mai yalwa. Kanta cike yake da suma bakikkirin, amma irin mai cunkushewar nan kuma mai karfi, kila wannan ne ya hana ta cika goman da ake cewa dan’adam tara yake bai cika goma ba.
Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba.
“I really missed her” ya fada hade da manna mata kiss a goshi.
“Ita kadai?” Fatima ta tambaya idanuwanta zube a kansa.
“And you” shi ma ya ba ta amsa hade da kallon ta.
Ya dora “Shi ya sa na yo sammakon ganinku, na yi rantsuwa ne a kan ba zan je Katsina ba, amma I really missed you. Sai dai ke na fahimci ba haka ba ne, ko za a shekara ba ki da damuwa. Sai Aunty Hauwa ce ta fada min kin dawo fa.”
Siririn murmushi ta yi kawai, komai ba ta ce ba.
” I’m feeling hungry “
Ta kalli agogon da ke falon 10:09am.
“Ba fa mu jima da yin Breakfast ba”
“To ai ni ban yi ba na taho, I’m eager to see you”
Duk suka dan yi shiru kafin ya ce “Fatima anya kina sona kuwa?”
Dariya ta yi mai sauti kafin ta ce “Kai Ya Mustapha, wane irin So kuma ni Fatima yara biyar fa, kana maganar so kamar jiya muka hadu”
“Ba za ki gane ba, the way you act kina ba ni tsoro, rashina baya tayar miki da hankali ko kadan. Kalle ki, kin wani fresh abun ki alamun ba ki da damuwa”
Ta kalli jikin nata tana dan murmushi, Aunty Lami ma da Zainab duk cewa suka yi wannan karon ta yi kyau kamar ba goyo take yi ba.
To a kan me za ta wani daga hankalinta a kan Mustapha, ai kawai gara ta fuskanci gabanta, matsaloli ba karewa suke yi ba, ba za ta karawa kanta da Mustapha ba, ya fi mata ta tattara shi gefe ta ajiye.
Shi din ma ba ga shi nan fresh din ba, rashinta bai sanya shi yamutsewa ba, sai ita ce za ta tashi hankalinta.
Ya ajiye Beauty hade da mikewa tsaye “Ta shi ki ba ni abinci, yunwa nake ji”
Ya kai karshen magana tasa hade da nufar hanyar bedroom.
Kitchen ta shiga b tare da ta bi shi bedroom din ba.
Gas ta kunna ta sanya ruwan dafa indomie.
Cikin 30mns ta fito rike da plate din indomien sai kamshin albasa ke ta shi.
A lokacin kuwa kwance yake kan 3sitter Beauty na kan ruwan cikinsa yana mata wasa.
“Bismillah” ta fada hade da dauke Beauty daga jikinsa.
Wannan ya ba shi damar sakkowa kasa tare da ta tankwashe kafafunsa ya fara cin indomien, hade da kubar empty tea mai kamshin citta.
“Har yanzu kina nan da ita abincin ki”
Murmushi ta saki kafin ta ce “Allah Ya sa ba santi ba”
Dariya ya yi kadan, ba tare da ya ce komai ba.
Amma kam ka ci abinci ya yi dadi ba tare da an yi mishi gamje-gamje ba sai Fatima.
Yanzu da yake da mata biyu ne ya kara Sanin ko wace mace da irin halinta, kuma dole ka san yadda za ka zauna da ita.
Kuma sannan sai ka zauna da mutum ne kake sanin halinshi.
Bleassing bin kwakkwafi, sannan tana da kishi fiye da Fatima duk yadda ta so dannewa ba ta iyawa.
Wannan halin nata baya son shi, sai dai babu yadda ya iya, haka nan yake hakuri. Don ku san duk bayan kwana biyu sai sun yi fada. Saboda yawan tuhumarta gare shi.
Fatima haushi daya take ba shi, yin abu kai tsaye, shi ya sa ma a wannan karon ya shafawa kansa lafiya, ya bar ta da halinta, tun da ba gyarawa za ta yi ba.
“Za ki je walima ko?”
“Ta me?” ta tambaya hankalinta a kansa.
“Ta gidanki?”
“Gidana?” ta Kuma tambaya cike da mamaki.
Tea cup din ya ajiye kafin ya ce “Na so ni ma in rinka yi miki yadda kike min, sai dai kawai ki ga ina abubuwana amma na kasa yin hakan. Walimar tarewa sabon gidana ake yi hade da ta saukar Blessing”
Matar J✍🏻
Alhamdulilah
Alhmdllh